Author : Asmeetah writer Category : Drama
wayar.
yamutsa fuska tayi ta turo ɗan ƙaramin bakinta tace "nifah Mom ba Yaya Junaid ba.."
da sauri mommy ta juyo tana kallonta tace "eh to waye inba Junaid ba?.."
cikin yanayin shagwaɓa tace "Doctor Hasheem nake sooo.."
ta ƙarasa maganar tana kallon Junaid ta gefen ido tana son ganin yanayin reach ɗinsa,
sai taga ko kallonta baiyi ba yanata pressing phone ɗinsa,
zuciyarta ne yake ta hargutsuwa tsabar takaici.
Mommy tace "ah toh shikenam ai indai kina sonsa ai ba mai miki dole koh? domin Hasheem da Junaid duk ɗaya suke a wajena, bari ma na ƙirashi yazo ayi maganar inyaso gobe sai ayi baikonku..." ta ƙarasa maganar tareda ɗaukar wayarta zata yi ƙira.
da sauri Ayush tace "amm mommy da gaggawa haka! ni ki bari ba yanzu ba"
Mommy tace "why? ki bari yazo ayi mishi maganar ko.." lokaci guda Ayush ta rikirkice tace "ah nidai ki bari mommy, zan sanar masa da bakina amma ba yanzu ba.." tana yi tana kallon Junaid wanda har yanzu bai tanka musu ba kuma babu wani alamar damuwa a tattare da fuskarsa, ita kuwa tayi hakane saboda taga irin son da yake yi mata,
tsaki taja acan cikin harshenta tana maganar zuci "daman ashe duk soyayyar da ya nuna mun a gaban abokansa ƙarya ne, daman yana son kashe mun kasuwa na ne, kuma Doctor Hasheem ɗin zan aura ehen.."
tana cikin wannan tunanin taji wayar Junaid yana bada sound na ƙira, da murmushi a saman fuskarsa ya kara wayar a kunne yana faɗin "Hy my Angel, how s day?.."
wani irin faɗuwar gaba Ayush taji jin Junaid ya ƙira wata da my Angel, nan danan ta shiga wani irin yanayi na kishi, wani irin haɗiyar yawu tayi jikinta yayi sanyi, tana kallonsa ido duk ya cicciko da ƙwalla..
bayan ya kammala wayan ya kalli Mom yana cewa "tomorrow we have a biggest visitors..."
Mommy da murmushi a fuskarta tace "su waye zasu zo?.."
yace "Angel ce zata zo gobe kuma a gidan nan zata sauƙa yakamata yau a canza kayan furnitures na falon nan saboda baƙin da zamuyi..." ya ƙarasa maganar yana ƙarewa falon kallo,
Mommy tace "waiii kace sarkin tsiwa ce zata zo macen soja kenam, daga ƙasar California zata yo nan ne ko kuwa?.."
Ajiye wayarsa yayi a gefen kujera yace "𝗲𝗵 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗰𝗮𝗻 𝘇𝗮𝘁𝗮 𝘇𝗼 𝗻𝗮𝗻, kinsan abunda zai kawota ma saboda hidimar nan da za'ayi ne.."
Mommy tace "har ta ji labari kenam.."
murmushi ya yi sannan yace "haba mom kema dai kinsan duk wani motsina Angel ta sani, tana bibiyata sosai kuma wannan hidimar da za'ayi ana ɗorawa a social media ta gani shine yanzun ta ƙira take cewa har ta biya kuɗin jirgi gobe da sassafe zasu taso,
ina ji da Angel a raina sosai domin ita take bincika mun yanda za'ayi a samo sarkin matsafa, kuma tana iya ƙoƙarinta sosai yanzu ma ta sanar mun cewa akwai magana babba da zarar ta zo kuma nasan bazai wuce akan mutumin ba..."
Dariya Mommy tayi tana tafa hannu tace "ai daman nasan Angel jarumarka ce shiyasa zakayi faɗa da kowa amma banda Angel, to kodai da Angel za'ayi Auren ne naga idan kuna tare bakwa ƙaunar rabuwa..."
murmushi Junaid ya yi yana kallon saman ceilling yace "Hmmm! aini mata uku nake son Aura a lokaci ɗaya..."
zaro ido waje Mommy tayi tace "kaiii dawa dawa?.."
saida ya gyara zamansa kafin ya fuskanci mommy yace "ta farko itace jaruma ta wato Angel, ta biyu kuma itace Rumana ita ƴar french ce baturiya, sai ta uku kuma Adity ita a ƙasar china take, kuma duk sojoji ne suna masifar sona, inba sa'a ba kuma duk zasu zo hidimar nan..."
Mommy dai kallonsa kawai take can ta jinjina kai tace "ahh lallai ka samu lafiya, yanzu fisabilillah Junaid duk arna zaka kwaso mun a matsayin sirikai?.."
kafin yayi magana wayarsa ta fara ring sound ɗaukar wayar yayi yace "kinga ƴar halak Rumana ce.." ya saka wayar a speaker ba tareda ya Kara a kunne ba yace "hello girl.."
ta ɗayan ɓangare kuma tana magana ta yaren french "Beb jiya na ƙira wayarka you didn't pick my call, Beb i really miss you too, naji labarin gobe kana hidima shine ko a gayyace ni, to yanzu ma zan sanar maka ne zan hau jirgi zanzo nigeria, hotel zaka kama mun ne ko a gidanku zan sauƙa? kasan banson hayaniya kuma mommy ta cika sa eyes..."
murmushi yayi sannan shima ya mayar mata da reply cewa "don't worry zaki zauna ne a gidan mu, kinsan bana son hotel ɗin nan.." shima ta yaren french ya yi maganar...
daga ƙarshe ya katse ƙiran.
duk tattaunawar nan da sukayi mommy ko kaɗan bata ji yaren ba,
sai murmushin da take ta zubawa..
ita kuma Ayush ta zauna kamar wacce ruwa ta cinye ta,
duk wayar nan da sukayi kaf daga A har Z Ayush taji, domin itama ta iya yaren french sosai, ta koya daga waran mahaifiyarta,
Mommy ce ta kalle shi tace "to ita kuma wannan mai ta ce?.."
yace "tace yau zata sauƙa a gidan nan,
kuma wannan kishi a waran ta ya ɓaci kinsan bature baya son haɗakar.."
Mommy tace "toh fah karfa kasa suzo suyita faɗa acikin gidan nan?."
yace "haba baza suyiba ai suna jin shakkata..."
yana danna wayarsa ya kuma cewa "bari na ƙira Adity tin kafin ta ƙirani saboda nasan ita ta cika raki.."
cikin sa'a wayar ta shiga bugu ɗaya ta ɗauka murya a kasalance tace "ka manta dani daman ina jiran ƙiranka naga an ɗora ka a media cewa gobe zakayi party ko?.." tayi maganar ne da yaren china,
amsa mata yayi da cewa "to sarkin complain, ya aiki, a wannan satin mutane nawa kika harbe da bindiga?..."
dariya tayi sosai saboda tasan indai tana cikin fushi to Junaid yasa yanda zaiyi ya faranta mata,
domin ita indai ta ɓangaren mugunta ne ta ƙwarai sosai batada aiki sai mugunta haka kawai zata ƙaƙulu faɗa don ta zalinci mutum, Adity ta iya faɗa sosai faɗanta kuma irin na chainoni,
ita ta sanar masa zata zo gobe kuma a gidansu zata sauƙa,
da haka suka kammala wayar ya katse yana dariya....
idon Ayush ne ya kaɗa ya yi jawur tsabar takaici da baƙin ciki da kuma ciwon kishi dake damunta, kuka ne yake shirin kuɓuce mata ta tashi da sauri ta nufi kitchen, tana zuwa kuwa ta tsaya a gaban gas tana rera kukan ta,
ita har ta fidda rai akan Auran Junaid yanda taga yana waya da ƴan matansa waɗanda suka fita class bama a nigeria suke bama, kuma yanada tabbacin Aurensu zaiyi tinda gashi da bakinsa yake faɗa, kuma tasan Junaid baya taɓa faɗan abunda bazai faru ba...
tana cikin rera kuka taji an zagayo hannaye ta gaban kunkuminta ya manne jikinta da nashi yana shaƙar ƙamshin wuyanta, yazo saitin kunnenta ya hura mata iskar bakinsa sannan yace "kina kuka akan meye?.."
shuru tayi bata bashi amsa ba,
ta tsayar da kukan tana ajiyar zuciya!
hannunsa ya cusa cikin rigarta ta ƙasi yana shafar ɗan ƙaramin tumbin ta yace "ko kinaso a ƙira miki Doctor Hasheem ne?..."
juyowa tayi da sauri ta hankaɗa shi baya a fusace tace "to tinda ni ba taka bace ai taɓa jikina ya haramta a gareka, baka sona toh meyasa kake son jikina? idan zaka so ni ka soni saboda Allah bawai dan tada sha'awa ba, ina Arnakun ƴan matan nakan suke ka bari idan sun zo saika cigaba da tada sha'awarka akansu daman can halinsu ne, ni kuma zan Auri Doctor Hasheem ɗin domin ya fika ƙaunata...."
Junaid fah ran maza ya ɓaci kawai rufe idonsa yayi sosai ya cizai gefen leɓɓensa na ƙasi, tinda yake a rayuwarsa mace bata taɓa tsayawa a gabansa tana faɗa masa maganganu ba sai yau, kuma hakan ma macen daya rainawa shekarunta, wacce a baya take matuƙar jin tsoronsa,
inda ace babu girman soyayyar Ayush a cikin zuciyarsa da tinin yayi ball da ita, da ba abunda zai hana yayi mata dukan tsiya a gurin nan,
Ayush tana huci tazo zata wuce ta gefensa ta fita taji ya riƙo dantsenta da ƙarfin gaske ya finciko ta sannan ya mannota saman faffaɗar ƙirjinsa suna kallon juna, numfashinsu ma haka yake ta gaurayuwa, cikin ɓacin rai yake kallonta leɓɓensa na rawa muryarsa cool yace "inda ace ɗaya ce daga cikin sojojin ƴanmata na take gaya mun wannan maganganun wallahi tallahi dana murɗe mata wuya...." ya ƙarasa maganar yana zaro mata disasshun idanuwansa waɗanda suka kaɗa sukayi jaa tsabar baƙin cikin da ya ƙunsa a yanzu..
ya kuma cewa "inda ace sha'awa ce take sa na taɓa jikinki wallahi tallahi da baki isheni kallo ba, saboda ni ƴan matan nigeria ma gaba ɗayansu a tafin hannuna suke, kinyi mun ƙanƙantar da zan taɓa jikinki saboda sha'awa,
Angel! Rumana!! Aditi!!! duk zasu zo zakuma ki gansu duk babu wacce shekarunta yayi ƙasa da shekara 30 a duniya, cikakkun ƴanmata, wayayyu, dirjajjun ƴanmata wanda class ɗinsu ya wuce yanda kike tsammani to su suke bibiyata kuma duk acikinsu babu wacce na fara cemata ina sonta, kafin su shawo kaina ki tambayesu irin wahalar da gwagwarmayar da suka sha kafin na amince musu da soyayyata,
kamar yanda kike kishi akansu to su basuda lokacinda zasuyi kishi akanki domin idan sukazo bazasu banbance ki da namiji ba, saboda su a wajensu ke ƴar jaririya ce,
idan kika ƙara tsayawa a gabana kina faɗamun maganganu makamancin haka saina......"
yasa hannu ya jawo ɗan ƙaramin lip ɗinta na ƙasi yana kallon cikin eyes ɗinta,
itama tin daya fara maganganunsa ta ƙura masa ido ko ƙibtawa batayi ba, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta...
lokaci guda kuma yasau murmushi yace "Doctor Hasheem ko? to kije ki Aure shi mana,
wai ma shin menene sha'awa? na daɗe ina taɓa jikin ƴanmatan ƙasar waje cikakku amma ko kaɗan ban taɓa jin wani abu a jikina ba.."
saketa yayi yana dariya tareda faɗin "wai sha'awa ce tasa nake taɓa jikinki, gaskiya kin ban dariya yarinya, ok tinda haka kika ɗauka ki jeki ni kuwa insha Allahu bazan ƙara kusantar ki ba, nigerian hausa fulani girls baƙauyawa...."
yana kaiwa ƙarshen maganarsa yayi ficewarsa daga cikin kitchen rai a ɓace domin ransa ya sosu sosai kawai jurewa ya yi...
ita kuwa Ayush tsabar baƙin ciki durƙusawa tayi a ƙasi ta fashe da wani irin raunannen kukaa...
*typing📲*
🐅 *MATAR DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written and story*
*by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*BOOK ONE*⬇️
*97 to 98*
*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
*OR*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*
*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
Misalin ƙarfe 1 na dare wayar Junaid ne yake bada sautin ƙira, sau biyu ana ƙira yana katsewa ana uku ne sautin ƙiran ya bugi dodon kunnensa wanda tinin bacci ya yi gaba dashi, a hankali yake wutsil-wutsil da idonsa yakai hannunsa kan drower yana lalumen phone ɗinsa, cikin sa'a ya hannunsa ya sauƙa a kan wayar ya ɗaga ƙiran ba tareda ya duba sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar ba,
cikin muryar jin bacci ya ce "Hello.." yana lumshe da ido..
"Hy my king kanata shan baccin ka ni kuma ka barni a airport sai faman ƙiran ka nake.."
tayi maganar ne da yaren french.
a hankali ya buɗe eyes ɗinsa ya duba screen ɗin wayar domin ya tabbatar da wa yake wayar, gani ya yi sunan daya saved ya bayyano wato "Girl" Rumana kenam sunan da yake ƙiranta da shi.
murmushi yayi sannan ya mayar da wayar saitin kunnensa cool voice yace "sorry my girl, yanzun kina airport ne?.."
amsa masa tayi! ba tareda ya ƙara cewa komai ba ya katse ƙiran sannan ya miƙe yana hamma domin ba ƙaramin bacci yake ji ba, idanuwansa duk sun ƙanƙance, kai tsaye toilet ya nufa yayi brush sannan ya watsa ruwa a jikinsa shaf-shaf saboda shi a rayuwarsa inba dole ba baya son fita ba tareda yayi wanka ba komin dare..
can bayan wasu mintina ya fito yana ɗaure da towel a kunkuminsa, ya tsane ruwan jikinsa sannan ya shafa mayukansa masu bala'in ƙamshi, ya nufi werdrobe ɗinsa ya zaro ƙananun ƙaya three-quater da rigarsa marar hannu sai da ya ƙara feshe jikinsa da turare kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya zura phone ɗinsa cikin aljihun wandon