Author : Asmeetah writer Category : Drama
'konewa qauri ne ya gauraye gidan.
Jin motsin mutum a bayanta ne yasa ta waiwaya da sauri cike da tsoro da fargaba take bin Junaid da kallo Wanda shima 'kaurin da ya jiyo ne yasa shi fitowa
Hannu yakai ya kashe gas d'in duk da yaji zafin wutar haka ya jure bai nuna ba
Ya sau'ke tukunyar da yayi ba'ki 'kirin hannunsa har yayi jawur tsabar 'Kunar wutar, ga kuma indomie fa shima yayi ba'ki 'kirin gwanin ban kwad'ayi ๐๐
Juyowa yayi yana kallon ta da sauri ta sunkuyar da Kai 'kasi.
Juyawa yayi yakai hannu kan wata flass mai ruwan tea a ciki ya tsiyayi ruwan a jug ya had'a tea mai kaurin gaske ga yasha madara sai dai suger kad'an yasa saboda baya son suger sosai ya d'auki bread mai yanka-yanka rufaida bread dai,
Yayi had'insa a sau'ka'ke ya mi'kawa Ayush cup na tea da kuma bread shima ya d'auki nashi ya fice daga kitchen upstairs ya haura sai bedroom d'insa
Itama fitowa tayi ta zauna a kujerar falo da murmushi a fuskarta "wow godiya nake daman yunwa nima nake jii" Ayush ce tayi maganar tana d'an Kora tea tare da bread kunnenta har rawa yake tsabar had'in da yasha..
Shima ata 6angarensa yana cikin karyawa yayi dialing call number Mom d'insa amma sai dai switch up yayi tunanin idan ya kammala break zai samota a hospital domin bazai iya wuni baiga Mom d'insa ba abun alfaharin sa, yana cikin wannan tunanin yaji sau'kar message a wayarsa Wanda daman yana hannunsa bud'e sa'kon yayi (( *captain* *junaid* *sorry* *for* *your* *loss* *doctor* *fateemah* *she's* *die,* *idan* *ka* *tuna* *da* *mahaifiyarka* *tana* *hospital* *kazo* *ka* *dauki* *gawarta* ))
Da sauri Junaid ya mi'ke tsaye yayi wurgi da wayarsa yana fad'in "whatttt my Mom, impossible" kafin kace mai gumi ya wanke masa ilahirin jikinsa da gudun gaske ya sau'ka falo ya wuce sai da Ayush ta tsorita kofin shayin ya zuba mata a cinya 'Kara tayi jin zafin ruwan shayin a jikinta ..
Shi kuwa Junaid har ya fizgi motarsa ya nufi hanyar get da gudun gaske!
Shi da kansa ya sau'ka a motar ya bud'e get d'in bai tsaya sauraron mai gadi ba
Fincikar motar yayi sai tafiya hospital ga gida a wangame bai tsaya rufe get d'in ba.........
Ga kuma mai gadi a cikin d'akinsa rai a hannun Allah, ya tsorita da ganin junaid a cikin Daren nan ga kuma jefo masa manya-manyan gardawa akai har su biyu, Allah sarki dattijon Allah.........
*ASMEETAH* *CE* โ๏ธโ๏ธโ๏ธ
*FREE* *BOOK*
๐
*MATAR* *DAMUSA* ๐
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โ๏ธโ๏ธ
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦalaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
๐ซ๐ซ *{{N W A}}* ๐ซ๐ซ
ุจูุณูููููููููููููููููููููููู
ู ุงููููู ุงูุฑููุญูู
ููู ุงูุฑููุญูููู
*BOOK* *ONE*
*PAGE* โก๏ธ29 & 30
________________Yana shiga cikin harabar asibitin ko tsayar da motar baiyi ba ya bud'e yayi cikin compound da gudun gaske duk ya fita hayyacinsa, sauran kad'an ya buge wata nurse yana duba d'akunan da aka kwantar Mom dinsa sukayi kici6us da Dr Hasheem
Kwalar rigar Dr ya ri'ke da hannu bibbiyu yana fad'in "where is my Mom, what happened to her?" yana magana ya na huci ya zazzaro ido waje...
"Look Junaid sau nawa kakeso na Kira akan batun mahaifiyarka?......... Dr. bai 'karisa maganar ba Junaid ya katse shi da cewa "am not felling well, I wanna see my Mom right now" murya a disashe yake magana kamar zaiyi kuka.
Dr. yace " it's okay, muje kaga mahaifiyarka" Dr. yayi gaba shima Junaid d'in ya bishi a baya kamar zaiyi tuntu6e suka shiga emergency room na alfarma har da plasman aciki ga wani 'karamin glass table a ta gefen gadon da Mom take kwance, anyi covered d'in baki da hanci da Oxygen ga ledar drink da aka d'aura mata, ido a rufe.....
Da gudu Junaid ya 'karisa gurinta yana fad'in "Mom don't leave a way please, meya faru da ke har haka bansani ba" kuka ne yaci ransa ya kifar da kansa a bakin gadon hannunsa ri'ke da nata.
Ji yayi an dafa kafad'arsa ya d'ago da rinanan idanuwansa yana kallon Dr. Hasheem wanda ya dafa shi!
"Am Sorry Junaid naso ace na sameka a waya na fahimtar da kai halin da mahaifiyarka take, amma sai dai na kira wayar since 3:00am anyi picking sai dana sanar maka rashin lafiyarta amma you didn't answer me daga 'karshe ka katse wayar, idan nayi call sai ayi rejected daga karshe akayi switch d'in wayar abun ya d'aure mun Kai matuka, har gidan naje amma ankasa bud'e get har na gaji nayi tafiyata!
Gata nan munyi iya 'ko'karin mu kuma Allah ya bamu nasarar ceton ranta, yanzu haka bacci take munyi mata allurar baccin tana bu'katar hutawa"
Duk maganganun da Dr. yake Junaid na sauraronsa ya jinjina kai yana maganar zuci "tabbas nayi mamakin ganin wayata a kashe domin ni bana kashe wayata haka take kwana a kunne ko don saboda gurin aikinsu Head quarters na sojoji, zasu iya turo masa aikin da zaiyi daga gida yana duba files a cikin computer! hakan ma a cikin wardrobe ya samu wayar, tabbas yaga missed call d'in Dr. Hasheem sai dai kafin yabi bayan kiran message ya shugo"...... yana cikin wannan tunanin yaji muryan Dr ya katse shi da cewa "Security ne suka kawo ta ciwon heart d'inta ne ya tashi".
"Meye silar faruwar hakan?"
Junaid ne yayi maganar yana kallon fuskar Mom.
Dr yace "I don't know, but a hasashen mu akwai wani abu wanda ya firgitar da ita, kuma lokacin da aka kawota ba abunda take furtawa illa sunanka, Junaid! Junaid!! Kawai take ambato..
Amma yanzu da sauki sosai"
"Ina Bodyguards"
Junaid ne yayi maganar adai den lokacin da ya mi'ke tsaye yana fuskantar DR....
'Daga kafad'ar sa Dr yayi yana fad'in "eh toh tin lokacin da suka kawo Hajia ban sake ganinsu ba
Duk da naga akwai firgici a fuskarar su tareda tsoro"
"Su su d'in Bodyguards?" Junaid ne yayi tambayar harshensa na hard'ewa cike da mamaki "toh wani irin abu ne ya faru haka ba tare da na saniba?" Ya sake maganar yana kallon Dr.
Shima Doctor d'in kallon Junaid yake shima abun ya d'aure masa Kai
Asaninsa da Bodyguards d'in nan basa tsoron komai basa fargaba duk wani abun cutarwa tin karar sa kawai suke....
Junaid ne ya goya hannayensa ta gaba ya hura iskar bakinsa yana fad'in "dole sun san abunda ya faru, dole shima mai gadin yasan abunda ya faru domin fitowata ban ganshi a bakin get ba"
Dr ne yace "tabbas kuwa zuwan danayi da asuba babu shi a bakin get saboda da yana nan nasan zai bud'e mun"
Suna cikin tattaunawar su Junaid yayi firgitt yasau hannayensa ya furta "that girl"
Yabi hanya zai fuce
Doctor yace "ina zuwa kuma Junaid?"
"I'm coming back" abunda Junaid ya fad'a kenam
Yayi waje..........
********
Ayush ce zaune a kan sofa ta dafe goshin ta da hannayenta biyu Kai a sunkuye tana tunanin Mommin Junaid dake kwance a gadon asibiti
Abun duniya duk yabi ya isheta!
"Allah Allah ka bawa Hajia ta lafiya, nasan na tabka babban kuskure da ban sanarwa Junaid kiran da akayi masa akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ba, wayyo Allah nah, ban san da mai zai d'aukeni ba, gashi ba wani sha'kuwa mukayi ba"
Zama ya gagareta ta tashi tsaye tana ta zarya a cikin falon,
"Naga ya fita a firgice Allah yasa ba mutuwa tayi ba!"
Hawaye duk ya wanke mata fuska, ga gumin da yake kwararowa daga cikin suman gashinta ko kwali babu a kanta
Gashin nan ya kwanta a kan gadon bayan ta, zirin gashin yana gogan tudun duwaiwayan ta ๐
Tana cikin wannan iftila'in kamar daga sama taji muryar mutum yana fad'in "ki kwantar da hankalinki insha Allahu babu abunda zai sameta, zata samu sau'ki"
Murya na kakkarwa yake maganar..
Saida Ayush ta tsorita ta waiwaiya da sauri ta kalli bakin 'kofa mai gadi ne tsaye jiki na rawar sanyi alamar yana cikin jinya!
'Karasowa yayi gaban ta yana fad'in "Dan Allah ki taimaka mun da abunda Zan ci tin jiya bansa komai a bakina ba"
Ayush cike da tausayi take kallon Dattijon mai gadi tace "toh Bari na duba maka"
Ta kalli wajen da ta ajiye bread ko rabin ci bata yi ba tin lokacin da Junaid ya fita ta tsayar da yin breakfast...
Dauka tayi ta mi'ka masa tare da kakkauran tea!
"Zauna anan kaci" ta fad'i haka a lokacin da itama ta zauna.
Zama yayi shima ya soma tura biredin nan a bakin sa
Ta zuba masa ido har saida ya kammala, yasha ruwa yana fad'in "alhamdulillah"
Gyaran murya tayi sannan tace "Dan Allah Baba kafin ka tafi inaso zanyi magana da Kai"
Shima gyara zamansa yayi yace "inajinki yarinya, fadin duk abunda kike son fad'a insha Allahu Zan sanar miki komai"
Ayush ta d'ago cike da damuwa a fuskarta tace "inason sanin tarihin gidan nan"
Baba ya kalleta yace "ke kuwa meyasa kike son sanin tarihin gidan nan?"
Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace "jiya da daddare naga abun mamaki akan yaron gidan nan kuma naga idanuwan sa sukan canza kala su koma na irin namun daji shin sun had'a dangantaka da namun daji ne??"
Jinjina Kai Baba yayi yace "tabbas zakiji komai daga bakina, nayi shekara aruruwa ina aiki a tare da mutanen gidan nan tin kafin a haifi Junaid wato yaron gidan nan, Junaid ya samu jinyarsa ne ata sanadiyar wata karuwa wacce Alhajin gidan nan ya taimaka, munafukar mata, arniyar banza arniyar wofi da zan sameta ni da kaina zan fille mata wuya da takobi na 'yar banza ita tayi sanadiyar mutuwar mai gidan nan sannan tayi sanadiyar kamuwar ciwon zuciyar hajia ga Junaid tayi sanadiyar fad'awarsa cikin masifa da bala'i, duk da basu tabbatar da cewa ita bace AMMA ni Malam shehu Aljanuna sun sanar mun cewa itace munafuka,
Wai ita sunanta AGAZA (Aghata) ko wacece oho sunan yaren su ne haka Alhaji ya sauya mata suna da BURA'ATU (Bara'at) taje tayi cikin shege ta kawo mana Algunguma ta ce Alhaji ne yayi mata, wannan mutuwarta bazaiyi kyau ba......."
Ya tsayar da maganar yana huci.
Ita kuwa Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka jin tsohon akan mahaifiyarta yake magana....
Tabbas jikin ta ya bata cewa anan gidan Umanta ta zauna!
Sai kuma a yanzu ta 'Kara tabbatarwa,
"Wannan shine Junaid d'in da Uma taketa ambato, kuma shine ya kasheta har lahira, shikenam ya d'auki fansar mahaifinsa, babu abunda zance yanzu,
Amma duk lokacin da suka ganeni cewa ni diyar Bara'atu ce tabbas kashina ya bushe....."
Duk wad'annan maganganun a cikin raanta takeyinsu...
Shi kuwa Baba ganin kukan da takeyi ya'ki tsayawa
Yace "Allah sarki dole kiyi kuka da tausayi mana
Bari na tashi najeni kar masu gidan su dawo...
Yana fita kuwa yaji Ana horn da motor
Da sauri yaje ya bud'e,
Ganin Junaid ya shugo da gudun gaske yace "Allah yasa dai lafiya, oh Allah ya baka lafiya yaron kirki"
Zuciyar Junaid kuwa cike yake da takaici da kuma tsananin tsanar Ayush domin a tunaninsa itace silar rashin lafiyar mahaifiyarsa tinda har ta iya kashe masa waya ta wurga cikin wardrobe
Kuma ta gagara sanar masa, alhalin Doctor ya sanar mata ana nema nah,
"tana son kashe mun Uwa, yau saita bar gidan nan, abunda ya faru a baya bazai 'Kara faruwa ba, mahaifiyata bazata mutu ata sanadiyar wata ba,
Anyi akan mahaifina,,,,
I can't trust anybody again, daman ban yadda da ita ba......"
Haka ya dinga sambatu shi kad'ai, ya sauka daga cikin motar ko rufe murfin motar baiyi ba
Yayi cikin compound da sauri.............
*ASMEETAH* *CE* โ๏ธโ๏ธโ
๐
*MATAR* *DAMUSA* ๐
(the wife of tiger)
*MALLAKIN*
*ASMEETAH* โ๏ธโ๏ธ
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alฦalaminmu ฦดancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
๐ซ๐ซ *{{N W A}}* ๐ซ๐ซ
ุจูุณูููููููููููููููููููููููู
ู ุงููููู ุงูุฑููุญูู
ููู ุงูุฑููุญูููู
*BOOK* *ONE*
*PAGE*โก๏ธ31 & 32
Shigarsa cikin falo ya tarar da Ayush zaune tana ta faman rera kuka!
Da sauri ya 'karasa gurinta ya ri'ko hannunta yayi filli da ita 'kasan carpet, a razane take shirin tashi ya cabko sumar gashinta ya ri'ke sosai ya d'agota 'Kara tasau take fad'in Dan Allah kayi hakuri Yayana bazan 'kara ba, nayi kuskure a gafarce niiii ta fashe da matsanancin kuka tana ri'ke da hannunsa wanda ya ri'ke gashin.
................."Mahaifiyata kike so ki kashe? metayi miki haka har kikeso ki d'au hukunci, matar data taimake ki??" Bud'an baki tayi zatayi magana ya darara mata tsawa "Shut up" har saida dodon kunnenta ya girgiza ta toshe kunnenta da hannayenta biyu tsabar karfin tsawar....
Yayi wulli da ita gefe yana fad'in "kina son cewa wani abune? Daman kinada bakin magana? Shameful girl"
Ja da baya take dasauri tana fad'in "wallahi bani bace, ni ni niiii bansan komai baa, kai kainee......." Bata 'karisa maganar ba ya cabko wuyanta ya d'agata sama da hannu d'aya "ni ne mai??" Har idanunsa sun fara canza colour zuwa tiger eyes, jijiyoyin jikinsa sun fara bayyana...
Ayush ganin haka yasa jikinta ya soma kakkarwa da bakinta hakoranta suka fara dukan juna da 'karfi, ga kuma 'kafar ta dake lilo ga yayi mata kyakykyawar sha'ka ga kuma yana shirin zama tiger tsabar firgici saida ta sau fitsari a jikinta..
Ganin numfashinta ya soma d'agewa