Author : Asmeetah writer Category : Drama
cewa ba kawai ta fisgi hannun yaro suka tafi....
Doctor Hasheem ne ya shugo ɗakin Junaid ganin Junaid a wannan halin ya firgita shi,
daman kafin yazo an bashi labari! shine yanzun yazo ya tabbatar, gashi kuwa har yanzun bai daina kukan ba
Shi kuma Junaid ƙara volume kukan luɗan yake idan ya kalli Doctor Hasheem sai kuma ya kalli fidar da yaron nan ya jefar, Doctor Hasheem ne kawai ya fahimci kukan yunwa yake yi kuma bazai iya sauƙa daga kan gadon ba,
Hannu Doctor ya kai kan fidar dake yashe a ƙasi ya ɗauka gashi kuwa cike yake da madara, zuwa gabansa Doctor yayi sannan ya miƙa masa fidar..
Dariya Junaid ya farayi yana mimmiƙo hannayensa, yana ƙara irinta yara masu wasa ga kuma yawun da ke zuba a bakin sa irin mai yauƙin nan na yara, kafa baki yayi akan fidar yana zuƙan madarar cikin, ya rirriƙe da hannu biyu yana lumshe ido,
Doctor Hasheem ne ya taimaka masa ya kwantar da shi yana shan madarar fidar a kwance har bacci ya ɗauke shi...
Tsabar takaici da tausayi haka Doctor Hasheem ya fice daga ɗakin yana hawaye....
*MASHA ALLAH*
( *kuga fah jaririn aljani aka turowa Junaid😭😭🤣🤣🤣* )
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ -------> 75 & 76 <-------
____________________________
mommy tana zaune a bakin gadon da Ayush take kwance tana kallon ceiling, da alamun tana tunanin wani abu ne ga hawaye kwance a saman fuskar ta..
Doctor Hasheem ne ya shugo da sallama a bakinsa,
cikin yanayin damuwa Mommy ta ɗago tare da amsa masa sallama,
ya nemi ɗaya daga cikin kujerun wajen ya zauna yana faɗin "Ayush bacci take yi ne"
Mommy ta juya ta kalleta taga ta ɗora hannunta saman fuskarta, tace "eh tayi bacci, jiya bata samu yin bacci ba.." ita kuwa tana jinsu kawai ta sharesu, Doctor yace "Allah sarki ya jikin nasun! jiya ban fito aiki ba, sai yau nake jin labarin abunda ya faru da su..."
Mommy tana sharar hawaye tace "jikinsu da sauƙi, ba kamar jiya ba sai dai Junaid abun ƙaruwa masa yayi"
Doctor shima baiji daɗin ganin Junaid a wannan halin ba yace "hakane Momy, nima yanzu na dubo shi abun ba daɗin gani, amma gaskiya wannan ciwon Junaid bana asibity bane, ya kamata mu nemi wani babban malami wanda zai tsaya masa, insha Allahu za'a dace tinda shafin aljanu ne..."
Mommy tana kallon Doctor itama ta gamsu da bayanansa malami ya kamata a nemo, tace "hakane Doctor kaima kace wani abu, zamu koma gida yau, akwai wani babban malamin mahaifin Junaid shi zan nemo yazo ya duba mun shi.."
Ayush tana kwance jin abunda suke tattaunawa akai yasa ta zaro ido waje,
kamar wanda aka zabureta ta tashi zane tana faɗin "Mommy! Yayana Junaid bai mutu ba daman? dan Allah inason ganin Yaya Junaid, ku taimaka mun dan Allah.."
ta fashe da kuka tana magiya akan akai ta gun Junaid,
Mommy ce ta riƙe hannunta tana faɗin "Ayushert kiyi hakuri ganin Junaid a halin yanzu zai iya jefa ki cikin damuwa"
Ayush ce ta katse Mommy da cewa "Dan Allah ku taimaka mun, hankali na bazai kwanta ba indai banga Yaya Junaid ba...."
Doctor Hasheem yana zaune ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa yana faɗin " Allahumma ajurni bi musifatu ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, Allah ubangiji yasa ba wata ƙulalliyar alaƙa ce a tsakanin Ayush da Junaid domin inhar hakan ta faru shikenam walwala zata ƙaurace mun, nashiga uku Ayush kar kimun haka please.." duk waɗannan maganganun a ransa ya yi su yana fuskantar Ayush wacce ta rikice wai ita sai an kaita gurin Yaya Junaid..
Ganin hawaye sharɓe-sharɓe akan fuskar Ayush yasa shi cewa "kinga Ayush tashi na kaiki gurin Junaid kinji, banson ganin kukan ki, kar kiyi mun asarar hawayenki" Mommy juyowa tayi tana kallonsa domin tasan mai yake nufi,
Ayush da sauri ta sauƙa daga saman gadon, ita ta farayin gaba sai Doctor ya biyo bayanta yana faɗin "tafiya a hankali mana, kar ki sanya ni cikin matsala"
suna tafiya a tare har suka isa ƙofar room ɗin, hannu Doctor yasa ya ture, cikin rashin sa'a suka same shi yanata sharar baccinsa, da gudu Ayush ta nufi gurinsa tana kiran sunan sa "Yaya Junaid! Yaya Junaid!! na gode Allah da yasa baka mutu ba, domin na tabbata dana rasaka a rayuwata gwara ni na mutu....."
gaban Doctor Hasheem ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, kafin kace me har gumi ya wanke masa fuska...
ita kuwa Ayush tana zaune a bakin gado ta rirriƙe hannunsa ɗayan hannun kuma tana shafa sajen fuskarsa mai shegen kyau da sheƙi,
Doctor Hasheem gani yayi bazai iya juran ganin wannan takwaicin ba, shawara ɗaya ya yanke cewa gwara shima ya sanar mata yana mutuwan sonta, domin yasan indai bai tara da wuri ba tabbas yana gaf da rasa Ayush duk da yasan Junaid ba Aure zaiyi ba...
gaban Ayush yaje ya tsaya sannan ya furta sunanta a hankali "Ayushhh.."
ɗagowa tayi da rinanan eyes ɗinta tana kallonsa bata ce komai ba tana sauraron mai zaice mata ne,
ganin ya ƙura mata ido kuma bashida abun cewa yasa ta kawar da fuskar ta gefe tana kallon kyakykyawan fuskar Junaid still hannunta na kan saman fuskarsa,
Hannu Doctor yasa ya riƙo hannun Ayush wanda yake kan fuskar Junaid sannan ya zamar da ɗayan hannun da take riƙe da hannunsa, ya miƙar da ita tsaye, yana mata wani irin kallo, ido cikin ido suke kallon juna ita dai Ayush abun mamaki ya bata a cikin ranta tace "wannan bawan Allah kuwa lafiyansa ƙalau? a gaban Yaya Junaid zai mun haka duk da yana bacci.."
haɗiyar yawu Ayush tayi sannan tace "Doctor ina jinka, kana riƙe da hannaye na sannan ka tasar dani daga zaune, shin wani irin kallo kake mun ne haka..."
Doctor Hasheem yana kallon cikin idanuwan ta yace "becouse i love you, I love you Ayushert, ke rayuwata ce sannan kuma mafarki na, ki cika mun burina na Auren ki dan Allah my Ayushert..."
Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace "bai kamata ace munyi maganar soyayya a nan ba, saboda majinyaci ne a gaban mu..
"No Ayushert idan kika amince da soyayyata ni kin gama mun komai, inaso Junaid ya zame mun shaida duk da nasan baya cikin hayyacinsa, please my Ayush..."
yana murza mata lallausar hannayenta yana ƙara matsowa daff da ita,
a tunaninsa zata dakatar da shi sai kuma yaga akasin haka, farin ciki ne ya fara wanzuwa a zuciyarsa, hakan ya bashi daman rugumarta jikinsa yana faɗin "sorry my Ayush, keɗin farin ciki nane"
Itama kwantar da kanta tayi akan kafaɗarsa tana zubda hawaye ta kasa cewa komai,
ita dai hankalin ta yana kan Junaid, Doctor ne ya ɗago ta suna fuskantar juna, bakinsa yake shirin kaiwa nata saitin bakin, ganin lokaci guda Junaid ya buɗe idonsa, da sauri Ayush ta kawar da fuskarta ta nufi gurinsa tana faɗin Yaya Junaid ka tashi ne Alhamdulillah, ta zauna daf dashi tana shafar suman kansa...
shi kuwa Junaid yayi shuru baya iya cewa komai, sai binta da ido yake yi, ita kuwa hawayen farin ciki take zubar wa tana wasa da sajen fuskarsa da hannunta,
Doctor Hasheem kuwa zuba mata ido yayi, shi dai takaicinsa Ayush tafi nuna damuwa akan Junaid sosai ma..
ganin ransa yana shirin ɓaci yasa yayi saurin fice wa daga cikin room ɗin...
( ta wani ɓangare Ayush ta magance matsala Junaid a rashin sani, domin tinda Ayush ta taɓa shi, shikenam jaririn Aljani ya bar jikin Junaid sai dai an toshe masa bakin magana, bazai iya aikata komai ba...))
suna cikin wannan halin Ayush taga bai kulata ba, ta ɗago da kanta tana kallonsa tace "Yaya Junaid kayi shuru kayi mun magana mana ko zanji sanyi a raina, insha Allahu zaka samu sauƙi.."
tana kaiwa ƙarshen maganar ta saiga Mommy ta shugo da sauri tana faɗin "Ayush na karɓi takardar sallama, Junaid maganin gida yake buƙata bana hospital ba.."
cikin rashin fahimta Ayush take kallon Mommy tace "meya samu Yaya Junaid ɗin har sai an nemi maganin gida..?"
Mommy ce tayo kan Junaid tana faɗin "kukan luɗa yake yi amma yanzu kuma naga baya cewa komai,"
ta dudduba shi naga jijiyoyin kwakwalwarsa basa motsi, kallonsa tayi cike da mamaki tace "Junaid meyake damunka ne haka?"
shi kuwa still idanuwansa suna kan Ayush ko ƙibta idon baya yi,
wasu likitoci ne suka shugo da keken guragu na asibity yanda zasu ɗora Junaid akai,
Ayush ganin yanda aka ɗauki Junaid aka ɗora shi akan keken yasa ta faɗin "wai meyake faruwa ne da Yayana Junaid, Mommy inadai ba gurguncewa yayi ba, dan Allah Mommy ki sanar mun mana..!
Mommy ce ta zauna ta sanar da Ayush abunda ya faru har zuwa wannan lokacin...
Ayush ba abunda take sai kuka, idon nan ya yi jawur tsabar kuka har kayinta ya soma ciwo....
Da haka aka fitar da Junaid har harabar asibitin suna tura shi, sannan suka saka shi a cikin mota, Ayush ce ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta shugo,
Junaid ta kwantar a saman cinyarta, Mommy kuma ta zauna a gaban motar,
Doctor Hasheem ne ya shugo cikin motar yana draving ɗinsu yana kallon Ayush ta cikin madubin motar....
isar su gidan sukayi horn da ƙarfi,
Mommy tana faɗin "bansani ba ko Baba mai gadi ya dawo.." kafin ta rufe baki sukaji an buɗe gate, direct miƙar hanyar da zai sada su da harabar gidan suka nufa,
bayan Baba mai gadi ya rufe gate yana gudu ya biyo motarsu Doctor, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gare su yana faɗin "Hajiya ashe Junaidu ne ba lafiya..?"
tsayawa Mommy tayi tana kallonsa tace "Baba ina kaje? ka barmun gate a buɗe, sannan meya samu yarana?.."
Baba mai gadi murya na rawa yake cewa "wallahi Hajiya bansan meya faru dasu ba, nidai abunda na sani shine ina zaune akan dadduma na sai najiyo ƙaran ihu daga cikin gidan, wallahi tsoro ne yasa na gudu, nayi tunanin Damusan sa ne ya motsa shiyasa..."
Ajiyar zuciya Mommy tasau tana kallon Baba mai gadi tace "Baba kaifa namiji ne, bayan Junaid kai kaɗai ne namiji kuma baza kaso wani abun cutarwa ya cutar dasu ba, dan Allah Baba a kiyaye dokar aiki..."
Baba jiki na ɓari ya amsa da "toh shikenam hakan bazai sake faruwa ba"
tace "Allah yasa"
ta shige cikin falo tana kara waya a kunnenta, tareda faɗin "Assalamu Alaikum Malam ya gajiya, dan Allah ina nemanka ne a gidana akwai babban matsala.."
sun gama waya ta katse kiran,
Upstairs ta haura yanda Doctor Hasheem ya kai Junaid wato ɗakinsa tare da Ayush, itama zuwa tayi ta samesu har an kwantar da Junaid akan gadonsa, daga nan Doctor ya yi wa Momy sallama yayi tafiyarsa domin bazai iya juran ganin Ayush tana manne da Junaid, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba....
After 1 hour
Sai ga Malam har yayi parking motarsa a harabar gidan, sannan ya nufi cikin falo kai tsaye,
jin tsayar da motor yasa Mommy sauƙowa downstairs tana ƙiran malam tare da cewa "Dan Allah Mallam kazo ka duba mun jikin Junaid abu yayi tsanani ko tashi baya iya yi balle magana.."
Mallam da sauri ya haura upstair yana faɗin "subhanallah meya faru haka?"
Mommy fashewa tayi da kuka itama tabi bayan Malam, ɗakin Junaid suka shiga gaba ɗayansu, da sallama a bakin malam ya shiga tareda jera wasu add'o'i, yana shiga kuwa idonsa ya sauƙa akan Ayush a razane malam ya tsaya cak yana faɗin "Ayshert..."
itama Ayush tashi tayi tsaye ta zaro ido waje tace