Author : Asmeetah writer Category : Drama
"Baba Malam..." lokaci guda tasau murmushi a saman fuskarta,
Mommy ce ta katse su da cewa "ha'aa daman kunsan juna ne?"
Malam ne ya dubi Mommy sannan yace "ai wannan....." Ayush tayi saurin katse shi da cewa "am am daman maƙwabcin mu ne, shi yayi magani a mahaifiyata har Allah yayi mata rasuwa, bamuda kowa shi ya temake mu, daga baya muka tashi a unguwar da yake.."
Ayush ta ƙarisa maganar tana girgiza wa malam kayi.
shima biye mata yayi da cewa "eh hakane.." yana kuma mamakin yanda ta iya zura ƙarya har haka, a cikin ransa yana faɗin "duk yanda akayi yarinyar nan tana ɓoye musu wani abu a cikin gidan nan, toh ma ya akayi tazo gidan nan bayan mahaifiyar ta Bara'at ta zauna har suka kore ta...." ya ƙarasa maganar zuci yana kallon Ayush wacce tin tinin gumi ya wanke mata fuska, tsoro ne ya bayyana akan fuskarta yau ta haɗu da wanda yasan labarinsu da mahaifiyarta kuma yanada alaƙa da gidan nan,
a cikin ranta kuwa cewa tayi "wayyo Allah na, asiri na ya kusan tonuwa idan har suka san cewa ni ɗiyar Bara'at ce shikenam kasheni Yaya Junaid zaiyi..." itama ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye..
shima kansa malam ya fahimci Ayush tana cikin damuwa kuma zai temaka mata, yanada wannan niyar a ransa..
nufar gurin da Junaid yake kwance yayi, sannan ya zauna a bakin gado ya riƙe hannunsa sosai tareda rufe idonsa yana karanta wasu abubuwa,
cikin ƙanƙanin lokaci ya buɗe idonsa yana kallon fuskar Junaid, ga hawaye yanda yake gangaro masa daga cikin ƙayar idanunsa,
sannan ya juyo ya kalli Ayush ya karkaɗa kayi tareda yin murmushi, ya buɗe cikin jakar daya zo da ita ya ɗauko turare mai ruwa anyi rubutu ta larabci a jikin turaren,
yace "Hmmm! Aljanu aka turo masa, wanda zasu hanashi yin komai,"
Mommy tace "to malam daga farko kukan jariri yake yi yanzu kuma ya daina" malam yace "waɗannan ƙananun aljanu ne kuma suna matuƙar jin shakkar wata yarinya ce mai ƙarfin iko, wanda raɓarsa tayi ne yasa suka gudu, yanzu wani Aljani ne a jikinsa wanda bansan dalilin zamansa a jikinsa ba, amma yanzu zamuji abunda zai ce.
Wannan turaren ne malam ya watsa a saman fuskar Junaid,
nan take fuskarsa ta koma yellow ya kanne idonsa sosai!
Malam yana fuskantar Junaid yace "inason sanin meya kawo ka jikin bawan Allah nan..?"
Junaid ne ya buɗe baki kamar shine mai maganar, wata ƙatuwar murya ne yake magana kamar
"NI SUNANA ALJANI ƘUDDUS, AN TURO NI NE DOMIN NAZO NA KASHE JUNAID DAGA MASARAUTAR RAAMUD, TAUSAYINSA DA NAKE JI NE YASA BAN KASHE SHI BA, SHINE NA RAƁI JIKINSA, BAZAN TAƁA BARIN JIKIN JUNAID BA SAI AN CIRE ZOBEN DISH DAKE JIKIN CIBIYAR ƳAR SARKI RAAMUD..."
daga nan Aljanin yayi shuru,
kallon Ayush malam yayi sannan yayi murmushi,
yace wa Mommy "kindai ji abunda yace, amma insha Allahu zai samu lafiya...."
Mommy ce tayo kan Junaid tana kuka,
shi kuwa ganin haka yasa yayi wa Ayush magana yace "inaso zanyi magana dake Ayush, ki isoni a cikin motata ina harabar gidan.....
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ -------> 77 & 78 <-------
💫💫✨ Ayush tana zaune a cikin motor tare da mutumin da ake kira da Malam Lawan, tana zubda hawaye kai a sunkuye tace "malam wallahi banzo gidan nan don nayi musu leƙen asiri ba, ni da farko ban san su ba, dan Allah ka rufa mun asiri..."
Dariya Malam yayi da farin gemunsa yace "Ayshert kenam! inda ace zan tona miki asiri ai da tun farkon zuwanki gidan nan na tona, saboda har aka kaiki asibiti daga nan Hajia Fateema take riƙe da ke, nasan da alkhairi kika zo gidan nan, sannan zoben dake jikin cibiyarki sanan shine maganin ciwon Junaid,
ki temaka ki ceto Junaid ke kaɗai ce zaki iya magance masa matsalarsa Ayshert, insha Allahu baza ki mutu ba...
Ayush tana kuka tace "malam ina tausayawa Junaid a halin da yake ciki, shi ɗin rayuwata ce kuma farin ciki na, ko zan mutu zan cire zoben a jikin cibiyata..." ta fashe da kuka ta kuma cewa "duk laifin mahaifi nane da kuma mahaifiyata ina zasu kai alhakin Junaid da suka ɗauka..."
malam yace "mahaifiyarki bata da laifi domin itama ana amfani da itane ta hanyar tsafi, mahaifinki shine babban mai laifi domin a rayuwarsa ba abunda ban saniba, hatta mahaifiyarki bata san abunda na sani akan mahaifinki sarki Raamud ba, da ƙwacen mulkin da yayi wa mahaifin Junaid..."
Ayush tana kuka idanuwan ta sunyi jawur ga leɓen bakinta ya bushe domin rabon da ta ci abinci tin shekaran jiya, ruwa kuma banda ruwan da aka ɗaura mata bata sa ruwa a bakinta ba, duk ta rarrame ƙashin wuyanta sun fiffito, damuwa ne ƙarara a saman fuskarta bakinta na kakkarwa tace "ba komai Junaid zai samu lafiya, amma dan Allah Malam inaso kamun wani alfarma.."
malam yace "inajinki ƴata.."
tace "kamun alkawarin kar kowa yasan wannan batun, kar ka sanar musu cewa inada alaƙa da maƙiyansu wato iyaye na, koda na mutu kar ka sanar musu cewa ata sanadiyata Junaid ya samu lafiya dan Allah malam.."
Malam ya dube ta dakyau sannan yace "Ayshert ya za'ayi kiyi sadaukarwa sannan ace bazasu sani ba? wannan fa wasa da rai zakiyi.."
"Eh malam duk da hakan inaso ya zama sirri.." kuka ne yaci ranta da sauri ta buɗe murfin motar ta yi ficewar ta,
a falo ta tarar da Mommy tana zaune akan sofa tayi tagumi sai hawayen da ke kwance saman fuskar ta,
Ayush haura wa upstairs tayi domin bazata iya ganin mommy a cikin damuwa ba, direct ɗakinta ta wuce...
malam ne ya shugo falon ya tarar da mommy shima zama yayi yana faɗin "kin kusa ki kashe kanki indai bazaki daina shiga damuwa haka ba, karfa ki manta ciwon zuciya gareki, kuma bugu biyu yake yi yayi bugun farko sauran na biyu wannan kuma zaki rasa rayuwarki ne...."
mommy ta ɗago tana hawaye tace "to ya zanyi malam wannan al'amarin yana shirin fin ƙarfi na, bazan iya juran ganin yarona a cikin wannan matsalar ba, shi kaɗai Allah ya bani, wani irin ciwo ne haka an rasa maganinsa...." kuka ne yaci ranta sosai take kukan,
Ajiyar zuciya malam yayi sannan yace "Addu'a shine mafita kuma shine maganin ciwon Junaid idan kin dage da yinsa, shiga damuwan nan bashi zaisa Junaid ya warke ba, ki yawaita tashin dare kina salloli kina kaiwa Allah kukan ki, ai ba abunda ya gagari Allah..."
"Shikenam malam insha Allahu zan rage shiga damuwan, sannan zan cigaba da yin Addu'a, banaso na rasa ɗana kamar yanda na rasa mijina..."
kawar da kai malam yayi yana murmushi sannan ya girgiza kai yace "ina mai miki albishir da cewa Junaid zai samu sauƙi, ki zuba ido daga nan zuwa gobe,
Ki kasance cikin Aminci Hajia Fateemah, na barki lafiya.."
daga nan ya tashi yayi mata sallama sannan ya tafi..
Maganganun malam ba ƙaramin tasiri yayi wa mommy ba, domin lokaci guda taji wani sanyi a ranta, tashi tayi itama ta nufi ɗakinta...
Bayan Ayush ta shige ɗakinta tsaya wa tayi a gaban mirrow ta ɗaga rigar ta sama tana ƙoƙarin cire zoben,
zafi take ji bana wasa ba, ga kuma tana ji kamar wata jijiya zata tsinke a cikin cikinta,
abun bazai fita da daɗin rai ba jin zafin yayi yawa yasa tayi ƙara ta sake zoben jikinta yana wani kakkarwa, har cibiyar yayi jawur hatta idanuwan ta ma sun kaɗa sunyi jaa, wani irin zazzaɓi ne ya rufe ta,
duk da hakan bata daina fisgar zoben ba,
ganin bazata iya cire wa ba yasa ta daina jan zoben ga kuma raɗaɗin da take jii,
zama tayi a bakin gado tana kuka, ga ciwon kai daya dameta,
idonta ya faɗaa kamar majinyaciya daƙer ta tashi tana jan ƙafa ta fice a ɗakinta ta nufi ɗakin Junaid ga hajijiyan da yake ɗiban ta da haka ta shige ɗakiin,
shi kuwa Junaid yana kwance a saman gadonsa yana fuskartar ceiling ido a rufe, da alamun bacci yake yi.
zama Ayush tayi daf da shi ta ƙwantar da kanta saman ƙirjinsa tana kuka mai cin rai,
ta ɗago tana kallonsa hannunta a kan fuskarsa tana shafar sajensa,
Junaid ya rame sosai shima fuskar ya yi fiyau, ga yayi wani irin fari lips ɗinsa kamar wanda aka shafa cream sai sheƙi yake tayi..
ƙara fashe wa tayi da kuka tana faɗin "Yaya Junaid na kasa wallahi, bazan iya cirewa ba, inajin raɗaɗi sosai, ina matuƙar ƙaunarka Yayana...."
*WASHE GARI*
Ayush tana zaune a bakin gadon Junaid tana ɗiban milk a spoon tana bashi a baki,
shi kuwa yana zaune yana motsa bakinsa a hankali, ko motsa yatsansa baya iya yi,
zama ma saida mommy da Ayush suka zaunar dashi,
cikin kulawa Ayush take feeding ɗinsa,
idonsa kuwa akanta ko ƙibtawa baya yi.
suna cikin wannan halin
aka turo ƙofar ɗakin da sallama aka shugo, waiwaya wa Ayush tayi tare da amsa sallama tana binsu da kallo!
Doctor Hasheem ne ya shugo shi da ƙanwarsa Laila sunzo duba jikin Junaid.
Laila ganin Ayush tana feeding ɗin Junaid ta dafa ƙirjinta tana faɗin "na shiga uku,"
Doctor Hasheem ne ya dube ta yace "lafiya kuwa?"
tayo kan Ayush tana faɗin "wacece ke? daga ina kike? meye alaƙarki da Oga Junaid?.." ta ƙarasa maganar tana zazzaro ido waje.
Ayush murmushi kawai tayi ta cigaba da bawa Junaid madara a baki,
Laila ce ta zuciyo tace "ke magana fa nake miki kodai keɗin kurmiya ce.."
Ayush sake yin murmushin tayi ga dimple yanda yake ta lotsewa, ta ɗago da manya-manyan eyes ɗinta tana kallon Lailah, murya a sanyaye tace "me kike son sani...?"
Laila tana ɗaga murya sama tace "alaƙar dake tsakaninku nake son sani.."
Ayush lumshe ido tayi ta sake buɗesu kamar mai jin bacci tace "sanar miki bashi da wani amfani,"
Laila tace "oh hakane ko! to kawo madarar ni ya dace na bashi ba ke baa..."
Ba takuri Ayush ta miƙawa Laila madarar tana faɗin "gashi nan duk ba wani abun damuwa bane, akan namiji bai kamata kina tada jijiyoyin wuya ba, gaki ga oga Junaid ɗinki..." tashi Ayush tayi ta bata wuri ita kuma ta zauna a wajen da Ayush ta zauna tana hararar Ayush,
Ita kuma Ayush martanin murmushi take jifarta dashi, Ayush tana da kishi sosai amma sai dai kishinta bana hauka bane sannan bata bayyana kishinta, abunda Laila tayi mata ya sosa mata rai sai dai bata nuna ta damu ba...
( *masu suna Aishat kenam, duniyan kishi da kuma sani yakamata*)..
Ayush kallon Doctor Hasheem tayi taga itama kallonta yake yi, abunda ya sanar mata ne a asibiti ya faɗo mata a rai cewa yana sonta..
murmushi ya sau mata itama martani ta mayar masa.
Laila ce ta ɗebi madarar a spoon ta kai saitin bakin Junaid da sauri ya kawar da kansa gefe ganin ba Ayush ba ce, tayi akan ta bashi madaran nan amma Junaid yaƙi buɗe bakin,
ƙololuwar baƙin ciki ne ya ishi Laila kamar zata rausa ihu haka ta ajiye cup madarar a saman gado ta tashi, sai data taka ƙafar Ayush kafin ta wuce ta zauna akan kujerar ɗakin,
girgiza kai kawai Ayush tayi ta koma ta zauna ɗaukar cup tayi ta cigaba da bawa Junaid madarar yana buɗe bakin