Author : Asmeetah writer Category : Drama
abada...
gashi kuwa yanzu komai ya rushe masa ata sanadiyar Ayushert!
Haka masarautar nan ta dawo babu komai na tsafi a ciki, daga shi sai matarsa Bara'at sai kuma DAMUSAR JUNAID wanda shi kuma makaryin tsafinsa yana jikin zoben cibiyar Ayush,
Shima Sarki Raamud akwai sauran tsafi a jikinsa wanda shima makaryinsa yana a tattare da wannan zoben cibiyar Ayush,
suna tsaye a harabar masarautar sai ga wasu tsuntsaye suna shirin shugowa, da gudu Sarki ya miƙi hanyar babban gate wanda ya buɗe yaje ya rufe ya danna ƙwaɗo
haka tsuntsayen suka juya ba halin shugowa domin akwai hayaƙin da suna shugowa zasu ƙone...
ita kuwa Bara'at jikinta ne yayi sanyi domin za'a iya kawo musu hari a koda yaushe idan aka fiskanci babu masu kula da masarautar nan, tana cikin wannan tunanin taji ya riƙo hannunta suka shiga cikin falon masarautar, gaban Damusa yaje ya durƙusa yana shafarsa
murya na kakkarwa yake magana da Damusar "kai kaɗai ne ka rage mun a halin yanzu daga kai sai matata, itama Allah yasa kar ta gujeni, ga shi na rasa ɗiyata tilo, nasan Ɓingel mutuwa zata yi! banaso na rasa masarautar nan saboda amanar mahaifina ne.."
Hmmm! ajiyar zuciya yayi sannan yakai idonsa kan Bara'at wacce take tsaye kanta a sunkuye, ya taso yazo gabanta ya riƙe hannayenta yana faɗin "idan bakya son zama dani akwai sauran tsafi a jikina zan mayar dake nigeria a yanzu, sai dai amma gurin zama zai gagare ki..."
Bara'at tana kuka tace "ba yanda zanje ina tare da kai, gurin wacce zanje a nigeria nasan ta mutu, ina zanje to? sai dai mu mutu tare...." ta ƙarasa maganar tana kuka ta rungumi Sarki,
shima hawayen yake zubar wa yana mamakin ta yanda al'amarin nan ya afko masa lokaci guda,
Abubuwa sun taɓarɓare masa, lokaci ɗaya ya zamo kalar tausayi,
kamar ba shi bane *SARKI RAAMUD, SARKIN MATSAFAN DUNIYA*....
(( *Yaaa Salam!*
*ku duba abunda ya faru da Mahaifin Ayush lokaci ɗaya,*
*ba'a jayayya da ikon Allah, duk abunda Allah ya tsara ba makawa sai ya faru kafin ƙiftawar ido,*
*Allah shine mai komai a hannu kuma shine mai mulki shine mai yin abunda yaso, duk tsafin mutum, duk izzar mutum, duk ƙarfin ikon mutum, duk zalincin mutum a lokaci ɗaya Allah zai gama da shi,*
*ya Allah kasa mufi ƙarfin zuciyar mu 🙏🙏* ))
******
Doctor Hasheem ne ya fito falo yana zaune akan sofa idonsa akan plasman,
Muryar Laila ya jiyo tana faɗin "Bros kai kaɗai ne a falon?.."
Juyawa yayi zai mayar mata da amsa kwatsam eyes ball ɗinsa suka sauƙa akan Maimoon wacce tasha doguwar riga da gyalensa iri ɗaya tasha makeup ba ƙaramin kyau tayi ba,
ta ƙaraso gaban Dr Hasheem ta durƙusa gwiwowinta ƙasi sannan ta kamo hannayensa tana zubda ƙwalla tace "Yaya Hasheem! bansan laifin mai nayi maka ba, kasan ina matuƙar ƙaunarka, bazan iya juran rashin ganinka ba, bazan iya juran rashin jin muryarka ba, amma meyasa ka daina zuwa gidan mu? ka daina ƙirana a waya ko da saƙo ne,
why my Doctor! why!! why!!!...."
Laila ce tayo kan Maimoon tana faɗin "dan Allah Besty ki tashi ba girmanki bane, Aji down wallahi.."
Maimoon katse ta tayi da cewa "Laila ko cewa yayi na kwanta ya takani ya wuce da gudu zan kwanta indai zamu dawo da soyayyar mu,
Soyayyar yarinta har zuwa girman mu ai ba wasa bane, cikin zuciyata tafarfasa take"
Doctor Hasheem kuwa yana jin raɗaɗi a cikin zuciyarsa baya son jin kukan Maimoon tin tana ƙarama ma!
eyes ɗinsa na kan plasman yana kallo kunnuwansa suka fara jiyo masa kukan Ayush, da sauri ya kalli Maimoon sai yaga fuskar Maimoon ta koma ta Ayush tana kuka tana riƙe da hannayensa,
Da sauri Doctor shima ya durƙusa ƙasi ya riƙe hannayen ta yana faɗin "Ayush! Ayushert meya sameki kike kuka, bazan iya juran ganin hawayen ki ba..."
yana share mata hawayen kan fuskar ta.
zaro ido Maimoon tayi leɓɓen bakin ta na kakkarwa tace "wacece Ayush?.."
itama Laila ta girgiza ganin yanda Yaya Hasheem yake kiran Maimoon a matsayin Ayush, cikin firgici Laila ta dafa kafaɗar Doctor tace "Yaya baka gani ne? Maimoon ce fa a gabanka ba Ayush ba" ta ƙarasa magana itama tana zubda hawaye,
domin ta tsani taga Maimoon tana kuka wani irin takaici take ji....
Doctor Hasheem ƙamewa yayi a wajen ya zuba wa Maimoon ido sai a lokacin ya lura ashe Maimoon ce ba Ayush ba,
Ayush gizo take masa....
Da gudu Maimoon ta tashi ta nufi hanyar waje direct hanyar gate ta nufa.
Laila ma biyo bayanta tayi tana ƙiran ta "Aunty Maimoon! Aunty Maimoon!! ki tsaya mana dan Allah, Besty!!!" Ganin har ta buɗe gate ta fice yasa Laila ta koma ciki tana faɗin "haba Yaya mekayi ne haka, shin meyasa bazaka iya ɓoye soyayyar Ayush ba, gashi yanzu soyayyar da kuka yi shekara da shekaru kuna ginata lokaci guda ka rushe ta..."
buɗe baki yayi a hankali yace "please Auta don't disturb me, am not feeling better"
"toh ka tashi Yaya kaje ka mayarta gida dan Allah, kaji Bros" tana bubbugan kafaɗunsa "Yaya ka ƙona mata rai sosai, ka ƙuntata mata akan wata banza Ayush....."
kafin ta rufe baki Doctor Hasheem ya kwashe Laila da wani irin gigitaccen mari har sai da taga taurari,
ya miƙe tsaye yana faɗin "are you mad? kinsan abunda kike faɗa kuwa Laila, get out from my side..." ya ƙarisa maganar yana nuna mata yatsa,
da gudu Laila ta bar wajen tana kuka hannunta kuwa na riƙe da kuncin ta...
shi kuma ba abunda yake sai huci yana faɗin "sorry my Ayush, forgive me my Ayush ba wanda zai zage ki na kyale shi a gabana..."
******
Gab da mangrib Mommy ta shawo kwana da motar ta, ganin gate a buɗe abun ya bata mamaki ita dai kawai shigewa cikin gidan tayi a bakin gate ta tsayar da motar ta fito tana kiran "Baba mai gadi! Baba mai gadi!!" har cikin ɗakinsa ta leƙa amma bata ganshi ba, rufe gate tayi sannan ta shige motarta ta miƙe hanyar da zai sadata da harabar gidan, tayi parking motar ta hankalin ta a tashe bata ga Baba maigadi ba,
ganin motar Junaid yasa tajaa ajiyar zuciya, ganin motarsa yasa hankalinta ya kwanta,
falo ta shugo bakinta ɗauke da sallama, ga falo wayam babu kowa direct ɗakinta ta nufa taje tayi wanka ta sauya kayan jikinta zuwa doguwar riga Bubaa!
ta ƙara fitowa ta nufi kitchen gani tayi anyi girki an saka a flask, fried rice ne ga naman kaji a saman food flask,
Murmushi Mommy tayi tare da faɗin "Allah yayi muku Albarka yarana, gashi Mommyn ku ta dawo da yunwa.."
sai data cika plate kafin ta dawo falo ta zauna akan 1 seater tana cin abincin ta cikin nutsuwa, bayan ta kammala ta ɗauko milk a cikin frig mai sanyi ta kora da shi....
ta miƙi hanyar ɗakin su Junaid tana faɗin "bari na dubo yaran nan a ɗakunan su ko kuma suna manne da juna sai Allah.."
ta haura upstairs tana taka matakala a hankali..
Ɗakin Junaid ta fara shiga ta duba bata ganshi ba
Murmushi tasau tana girgiza kai tace "nasan kuna tare ai daman..."
Ɗakinsa har yayi ƙura ta gyara masa komai har da wankin toilet, daman tin kafin Ayush ma ita take gyara masa room ɗinsa,
ta feffeshe ɗakin da turare...
Daga nan ta fito ta miƙi ɗakin Ayush, tsayawa Mommy tayi a bakin ƙofa ta fara knocking,
kar ta kutsa musu ɗaki tazo taga abunda zaisa taji kunya domin su ba wani kunya suka sani ba especially JUNAID...
*MASHA ALLAH*
Na gaji da typing wollah bacci nake ji, sai da safe zaku ga new update kuma du...
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّه الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ -------> 73 & 74 <-------
🗣️🗣️ Knocking Mommy take tana ambatar sunayensu amma shuru ko motsi babu,
"Junaid ko baka ɗakin ne..?
Ayushh kizo ki buɗe mana ina muku magana..."
Jin shurun yayi yawa yasa Mommy ta tura ɗakin tana faɗin ko ba mutane ne aciki...." kafin ta rufe baki idonta ya sauƙa akan Junaid da Ayush suna manne da juna ko motsi babu, hakan ma a ƙasin ɗakin ba'a kan gado ba.
"kutt wani irin iskanci ne haka ai ko baccin mutuwa kuke yaci ace kun ji ƙiran da nake muku,
wai ma abun nakun yakai hakane daman? ku rasa a yanda zaku kwanta sai a ƙasa?..."
Jin ko motsi basu yi ba, gaban Mommy ne ya yi wani irin bugawa a wahalce ta haɗiyi yawu tana zazzaro ido waje, ta nufi gurin su tana bubbugan bayan Ayush dake itace a saman Junaid! ganin bata motsa ba tasa hannu ta ɗago Ayush gani tayi wuyanta a karye ta faɗa jikin Mommy, a tsorace Mommy tace "Innalillahi nashiga uku, meya faru da ku?.."
Kwantar da Ayush gefe tayi tana ƙoƙarin cacumar Junaid shima jin jikinsa tayi ya sake,
a firgice Mommy taja da baya zuciyar ta na tafarfasa kasa cewa komai tayi tsabar yanda numfashin ta yake hargutsuwa sama-sama take jan numfashi, daƙer ta iya tashi ta nufi hanyar fita hajijiya na ɗibar ta, da gudu take sauƙa downstair har ƙafarta ya sulale ta faɗi tana gangarawa daga saman benin tana zuwa ƙarshe goshin ta ya bugu da ƙasin tiles a wannan lokacin ne Mommy tayi ƙara tana dafe da kayinta domin ba ƙaramin buguwa tayi ba har gurin sai da ya fashe,
duk da hakan bata yi ƙasa a gwiwa ba ta nufi ɗakinta tana ɗingishi alamun taji ciwo a ƙafar,
wayarta ta ɗauko a saman gado tana laluman number hospital cikin sa'a taci karo da shi ta yi dialing call cikin ƙanƙanin lokaci ta kara a kunne murya a disashe take faɗin "Ambulance! Am bu lance!!..." daƙer take fitar da numfashi, daga nan tasau wayar ƙasi ta dafe ƙirjinta ta kafa gwiwowin ta a ƙasi ta fashe da wani irin matsanancin kuka ga jini duk ya wanke mata fuska, goshinta ba ƙaramin buguwa tayi ba, gashi tana buƙatar taimakon gaggawa domin ciwonta ne yake shirin tashi..
tana cikin wannan halin taji yo jiniyar Ambulance har sun iso....
Wasu ma'aikata ne masu fararen kaya suka fito da gudu suka shige gidan,
fararen likitoci ne daka gansu kasan ba ƴan nan ƙasar bane,
bayan sun shige falo raba hanya sukayi wasu suka haura upstairs wasu kuma suka nufi ɗakin Mommy kamar wanda aka sanar musu a yanda majinyatan suke,
haka suka firfito dasu duk aka shigar dasu cikin