Author : Asmeetah writer Category : Drama
"oh ke yarinya ce kin tabbata?"
kaɗa masa kai tayi alamar eeh!
"Ok tinda ke yarinya ce cire kayanki muje nayi miki wanka ai daman tinda muka dawo bakiyi ba.."
zaro ido tayi waje tace "Allah na girma Yaya Junaid, barni nayi wanka na"
"Allah Yushert baki girma ba ni da kaina zan miki wankan nan.." har ya soma zame mata kayan jikinta, yana kokuwar cire mata kaya ita tana ƙoƙarin hana shi, duk da hakan sai da ya cire mata rigar jikinta ya barta daga ita sai breziya da short troza iya gwiwar ta,
ganin zai mata tsirara yasa ta fashe masa da kuka tinin hawaye sun wanke mata fuska, bata so yaga tsaraicinta...
shi kuwa tsaya wa yayi cak ya tsayar da idonsa akan wani abu,
jin yayi shuru kuma idonsa akan abun yasa Ayush ta dakata da yin kukan itama takai idonta kan abunda Junaid yake kallo
wato wani irin zobe ne mai jikin zinare sai sheƙi yake yana manne a cibiyar Ayush,
bakin Junaid na motsi a hankali yace "meye wannan abun mai ɗaukar ido akan cibiyar ki???"
itama Ayush abun take kallo daga bisani kuma
tace "wannan nima haka na tashi na ganshi a jikina kuma baya ciruwa" ta ƙarasa maganar tana shafar abun dake manne da cibiyar tatan.
shima Junaid hannu ya kai yana shafa zoben jikinsa laushi gareshi sai sheƙin da yake yi, abun kuma kamar ɗan kunne ɗan ƙarami da shi, mariƙar abun kuma yana can cikin cibiyar Ayush ya riƙe ta ciki...
Abun ya bawa Junaid mamaki sannan yayi matuƙar burge shi,
kansa ya kai saitin cibiyar Ayush ya manna mata kiss akan *RING NAVEL* ɗin ta, sai sheƙin da yake yi!
ya ɗago kansa still eyes ɗinsa akan zoben cibiyar, Ayush duba kanta tayi ganin daga ita sai brezy da short pant ta jawo bedsheet ta rufe kanta da shi,
murmushi ya yi sannan yace "kije kiyi wankan ki sai ki fito kici abinci.."
gudu² sauri² ta shige cikin toilet tana tare ƙirjinta da hannayen ta,
shi kuwa binta yayi da kallo da smile asaman face ɗinsa, shi tinda yaci karo da zoben cibiyar Ayush daga nan hankalinsa ya kasa kwanciya shi bai taɓa lura da zoben ba sai yau,
zuciyarsa ne yake wani irin bugawa, ga wani sanyi da yake ratsa cikin jikinsa....
itama Àyush shigar ta cikin toilet tsayawa tayi a gaban mirror tana shafa zoben kan cibiyar ta tana maganar zuci!
"Yaya Junaid ka kwantar da hankalinka wannan zoben kan navel ɗina shine maganin warakar ka, zaka samu sauƙi insha Àllahu, da žaran na cire wannan zoben sai dai zan rasa rayuwata..." ƙwalla ne ya zubo mata akan fuskar ta....
tana gaban madubin toilet taji an ƙira sunanta ta cikin mirror da wata iriyar sassanyar murya, da sauri takai idonta jikin mirror haske ne ya bayyana a jikin mirror kafin daga baya sufar mutum ya biyo baya,
Ido Àyush ta zaro cike da murna tace "Umma kece! Nagode Allah da baki mutu ba, nayi kewar ki Ummanah..." ta ƙarasa maganar tana washe white teeth ɗin ta.
Kamar masu video call murmushi Uma tayi sannan tace "nima haka my Ayush nayi kewarki sosai"
"Uma toh yaushe zaki dawo gare ni, rayuwa ba ke babu daɗi."
"kinga Ayush kina magana a hankali kar Junaid ya jiyo ki nasan kuna tare, bamu da isheshshen lokaci nazo miki ne domin na taimaka miki waran magance matsalar Junaid, yanzu haka a ɓoye nake miki magana ta cikin madubin tsafin mahaifinki ba tareda saninsa ba, idan har kuma yasan ina magana da ke zai ɗau mummunan mataki a kaina nasan ke bazai miki komai ba saboda ke takobinsa ce, Ayush a gaggauce zan baki wasu sirrika ne wanda sai kinyi wannan kafin ki fara samawa Janaid lafiya!
Ga waɗan nan zobina guda biyu sunansu zoben dish na tsafi ne kije ki sanyawa Janaid a ƙaramin yatsansa na hagun, kema ki saka a ƙaramin yatsanki na hagun, idan kuka sanya su toh daga lokacin Mahaifinki zai daina ganinku a cikin madubin tsafin sa daga nan ke kuma saiki fara aikin ki, idan har mahaifinki yana kallonki bazai taɓa bari ki warkar da Janaid ba!!!
sai dai kuma wannan zoben da zaki cire a jikin cibiyar ki zai sa ki rasa rayuwarki idan ba'a yi sa'a ba, amma kuma Junaid zai samu lafiya ba wani abun cutarwar da zai sake shugo mishi rayuwa har abadan abadann, kuma duk wani tsafin mahaifinki zai karye, zai rasa ƙarfin ikonsa, Aljanun dake biye a bayansa zasu ɓace su barshi, ni ce kawai bazai rasa ba saboda ni matarsa ce, kema zaki iya mutuwa Ãyush da zaran zoben ya bar jikin ki.."
Ajiyar zuciya Ayush ta sauƙe tare da faɗin "Uma indai Junaid zai samu lafiya kuma tsafin mahaifina zai karye ni na yadda na mutu, zan mutu Uma! sai dai nasan Junaid zai je ya Auri wata ba ni ba, Uma inason Junaid sosai burina bai wuce na Aure shi ba, amma sai dai hakan bazai yuba nasan mutuwa zanyi.."
ta ƙarasa maganar tana kuka itama Uman kuka take zata rasa ɗiyarta
Murya a dashe Uma tace "wannan sadaukarwa ne Ayush ki kwantar da hankalinki zaki samu rahamar ubangiji insha Allahu, zan tayaki da Addu'a ina miki fatan alkhairi ƁINGEL ABBANTA..."
lokaci guda ta ɓace a jikin madubin,
kuka Ayush take sosai amma taƙi barin Janaid ya jiyo kukan...
tana cikin wannan halin idonta ya sauƙa akan zobina guda biyu dake saman mirror, murmushi Ayush tasau ta ɗauke su tana juya su,
tana riƙe dasu ta samu tayi wanka shab shab tayi brush sannan ta fito cikin room tana ɗaure da towel a ƙirjin ta,
ganin Junaid a kwance saman gado ido a rufe tace "wato kaji ɗaki mai sanyi shine har da baccin ka..."
cikin sanɗa tayo kan Janaid tana faɗin "yawwa ga dama ta zomun bari na samu na sanya masa zoben nan kafin ya ankara da shi"
yatsar hannunsa ta kamo a hankali ta sanya masa itama tayi gaggawar saka nata, tana sauƙe ajiyar zuciya "shikenam hankali ya kwanta mun rabu da masifar farko sauran na biyu shine zan rasa rayuwa ta," ta ƙara sa maganar tana zubda hawaye........
*MASHA ALLAH TO BE CONTINUE NEXT*
*INA MASOYAN AYUSH KUZO KU TAYA AYUSHERT DA ADDU'A NEXT PAGE KO TAYI RAI KO TA MUTU OHO, YAWAN COMMENTS ƊINKU SHI ZAI CETO RAYUWAR AYUSH, ƘARANCIN COMMENT ƊINKU KUMA SHI ZAI SHEƘE AYUSH HAR LAHIRA YACIIIN...*
*ASMEETAH NOVEL✍️✍️✍️*
typing📲
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ ------->69 & 70 <-------
____________________________
Ɗaga hannu tayi sama tana roƙon Allah "ya Allah ka temake ni, ka bani nasara akan ceton Junaid daga kogon hallaka..."
har ta gama Junaid bai motsa ba, ta tashi ta nufi gaban mirror, gabanta ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ta tsaya cak ta zazzaro manya-manyan idanuwan ta waje ganin anyi rubutu a jikin mirror da jini, "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un.." abunda ta furta kenam, jikin ta na kakkarwa ta soma karanta rubutun da akayi da jini a jikin madubi...
{{ "kun munafurce ni Ɓingel ke da mahaifiyar ki, kun toshe mun kafar da zan sanya ku a idanuwa na balle nasan abubuwan da suke faruwa daga ɓangarenku, hakan yasa na ɗauki mummunan mataki akan shi wanda kike so ki rasa rayuwar ki akansa, kafin ki mutu ya rigaki mutuwa Ɓingel, daki rasa rayuwarki gwara shi ya rasa tasa rayuwar, kiyi hakuri na kashe Junaid har lahira, babu ta yanda zan ganki shiyasa nayi miki wannan rubutun BISSALAM" }}
tsabar firgita da tsoro Ayush har faɗuwa tayi ƙasi ƙafafunta bazasu iya ɗaukar ta ba, jiki na rawa tayi kan Junaid wanda yake kwance kan gado ƙafafunsa rabi suna ƙasi, jijjigar sa ta farayi tana ƙiran sunansa cikin yanayin kuka "wayyo dan Allah Junaid ka tashi, na shiga ukuna na lalace Junaidd! Junaidd!! Junaid ka tashi mana...." ta fashe da matsanancin kuka tana bubbugar ƙirjinsa, ta tashi da gudu ta nufi toilet ta fito hannun ta ɗauke da ruwa ta soma kwara masa amma Junaid ko motsi babu ido a rufe, tsabar kiɗimewa daga ita sai towel a jikinta haka ta jawo Junaid kanta suka faɗo ƙasin gado tare tana rungume dashi, ihu take na fitar hankali tana ƙara ƙanƙame shi a jikinta,
idonta sunyi jawur hatta fuskar ta shima ya yi jawur abinka da farar mace,
kanta ne ya soma juyawa ta soma kwashewa da dariya daga dariya ta koma kuka haka ta rinƙa haɗawa dariya da kuka, still tana ƙanƙame da Junaid!
Inta kwashe da dariya lokaci guda kuma sai dariyar ta juye ihu ta soma ihu kamar ranta zai fitaa,
Da haka har ta fara shiɗewa, ta soma magana ciki -ciki "Yaya Junaid bazaka mutu ka barni ba, bazan rayu ba..." lokaci guda kuma ta yi wani irin ƙaara na gaske har sai da madubin ɗakin ya dagargaje tsabar ƙarfin ƙarar ihun data yi, shine last ihun ta itama wuyan ta ya karye ta kwantar da kanta saman ƙirjin Junaid, numfashi ya tsaya cakk,
ihun nan har sai da ya daki dodon kunnen maigadi tsabar ƙarfin ƙaarar,
shi maigadin da yake can bakin gate mai shegen nisa.
Jin wannan ihun mai razanarwa yasa mai gadi tsorita jikinsa ne ya hau ɓari yana faɗin "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, shikenam kwanan mu ya ƙare yau kam Junaidu ya koma Damusa ya kashe ƴar mutane, nasan yanzu kaina zai dawo bari na hau kan hanya na bar gidan nan tin kafin ya fito gare ni.
Da gudu Baba mai gadi ya buɗe gate ya fice a gidan...
(Shin mutuwa tayi ne ko suma Allahu A'alamu..).
******
Besty ce take kwance saman gadon Laila sai danna phone take tana watsa chiwgun a baki sai kara take tayi da su tana taunasu cikin salo, can saiga Laila ta fito daga toilet da ɗaurin
towel a ƙirjinta tana faɗin "my Besty yakamata kizo ki watsa ruwan musulunci a jikin ki koh, gashi time to pray sai ƙiraye-ƙirayen sallar la'asar ake.
Besty kuwa idon ta nakan wayar hannun ta tace " kiyi sallar ki mana idan na tashi zanyi ai." Laila ce ta taho gaban Besty tana faɗin "ke ki tashi nace kije kiyi wanka bazan zauna dake haka duk jikin ki ƙazanta" ta ƙarasa maganar tana fizge wayar hannun ta,
tashi tayi Besty tana ɗura ashar tace "kutumar bura uba, nice baza ki iya zama dani ba a haka? saboda nazo gidan ku ne yasa kike mun wulaƙanci son ranki, shikenam zan bar gidan ku yanzu ai nima muna da gidan, kuma ke bazaki nuna mun musulunci ba," ta ƙarasa maganar tare da tashi ta fizgi wayar ta, ta jawo kayan ta zata saka suka ji bugan ƙofar ɗaki, a tsorace Laila tace "waye ne"
jin muryar Yayanta yana faɗin "Auta ki buɗe ƙofar mana" gaban ta ne yayi wani irin bugawa ta kalli Bestin ta murya ciki-ciki take cewa "ina kinga har Yayana ya dawo daga hospital shiyasa nake ta binki ki samu kiyi wankan kar yazo ya ganki a haka, gashi yanzu, ai saiki samu ki shige cikin toilet ɗin.."
wani irin harara Besty ta wurga wa Laila ta ja tsuka sannan ta shige toilet, itama Laila binta da kallo tayi kafin tayi ƙwafa ta nufi yanda wardrobe ɗinta yake ta ciro wata doguwar riga na material da gyalen ta mai ɗigon black and white ta ɗora su akan gado wannan ta fitar su ne wanda Besty zata saka..
itama ta ciro riga da skit blue da hular sa tayi saurin sanyasu, taji Yayanta yana faɗin "ke shanyar da kika yi fa ya bushe, wai mekike yi haka ne?"
"Yaya kayana dai nake sakawa nayi wanka ne..."
shuru yayi bai ce komai ba, sai da ta gama shirya wa tsab tukun tazo ta buɗe ƙofar da murmushi akan fuskar ta tace "your welcome my dearest bros" ɗan hararar ta yayi ta gefen ido yana faɗin "ni kike wa jan aji ko?"
taɓe baki tayi sannan tace "sorry my Bros...."
bakin gado ya samu ya zauna bakin sa cike da tambayoyi sai kalle-kalle yake ta yi a ɗakin kamar baƙonsa...
"waɗannan kayan waye..."
ya yi tambayar yana kallon Laila..
cikin ƙinƙina tace "Yaya! Aunty Maimoon ce tazo tinda rana, har bacci ya ɗauke mu yanzu tana wanka ne..."
Gabansa ne ya yanke jin an ambaci Maimoon, jinjina kai ya yi sannan yace "okay.."
tashi yayi zai fita Laila tace "Yaya meyasa