Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR Damisa BOOK ONE Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  Drama

Chapter   35 / 44

102K to 105K   out of 131.4K words


Ki rin'ka control kanki Hajia Fatima da kuma furucin da zai fito daga bakin ki, ba kowani magana zaki rin'ka furtawa yaronki ba da zaran ranki ya 6aci,
Kin dai san halin Junaid, sharar dashi zakina yi, ki ringa hakuri da shi, Allah ya d'ora masa wani iriyar zuciya ne, bazai iya control kansa ba...."

Had'iye kukan da take tayi sannan ta girgiza kai ta fice daga cikin room d'in...

Ajiyar zuciya Malam yaja yana sau'ke numfashi ya maida kallonsa kan Junaid yakai hannu ya dafa kafad'arsa yana rarrashinsa,
Yace "Junaid meye ribarka dan kasa mahaifiyarka kuka? shin kasan halin da take cikine yanzun?
Uwa Uwace fa, ba ko wane irin magana zakana gaya mata ba, ka kula sosai akan mahaifiyarka Dan Allah...."

Ri'ko hannunsa yayi yana fad'in "kazo muje gida, insha Allahu Ayshert zata dawo, muje ka kuma bawa Mahaifiyarka hakuri, kada ka bari ta wuni da fushinka..."
yana ri'ke da hannunsa suka fita..

Gaba d'aya jikin Junaid ya yi weak, kamar ba laka a jikinsa haka yake tafiya,
Sai yanzu ya gane cewa ya yi kuskure sosai, bai kyauta wa Mom d'inshi ba, bai ta6a ganin 6acin ranta kamar na yau ba,
ya tsani ganin hawayen Mommy amma yau gashi ta tsaya a gabansa tana kuka tana gaya masa maganganu cikin 6acin rai,
Motsa lips d'insa yayi yana maimaita kalmar data gaya, a 'kasin harshensa ya furta

"idan baka je ka sanar haka ba to tabbas baka ci sunanka Junaid ba......"
Abunda yake ta maimaita wa kenam a cikin ransa,
"Tabbas Mommy ranta ba karamin 6aci yayi ba, tinda har zata iya furta mun wannan kalmar..".
siririn hawaye ne ya zubo masa
Daiden zai shiga cikin motarsa...
Domin kowa da motarsa yazo cikin asibitin daman,
Mommy ta dad'e da tafiya da motar da tazo dashi,
Shima malam shiga motarsa yayi ya tafi, sai kuma Junaid shima tafiya ya yi da motarsa,


******

Kwance take tana fuskantar ceiling ta fara bud'e idonta a hankali tana kallon haske² da haka har idon ya washe,
tana jujjuya eyes ball d'inta hagun da dama, ganin bata san a yanda take ba yasa ta zabura ta tashi zaune tana kalle²!
Idonta ta sau'kar akan NARASIMHA yana zaune a daddumarsa ido a rufe yana ta juya hannayensa, yana motsi da bakinsa kamar mai karanto addu'a amma ba addu'a yake ba wani tsafinsa daban yake aiwatar wa,
Ayush zaro manya² eyes d'inta tayi waje ganin mutum mai fuskar Biri jikinsa kuma duk gashi,
saida ta rufe idanuwanta sosai tukun ta rausa uban ihu tana 'kiran "Mommy wayyo Allah Dodo, kizo ki temake niiii, Yaya Junaidddd na mutu naaa DoDooo zai cinye ni, wallahi Dodon Biri ne...."

Narasimha bud'e ido yayi yana kallonta,
Ganin bazata iya yin shuru ba yasa ya watsa mata ruwan sihiri a fuska, kamar wanda aka datse mata harshe haka tayi miqitt tana kallonsa cike da tsoro,
Zaro mata ido yayi yana fad'in "ki kiyayi harshenki domin a gabana aka haifi ubanki dan uwarki 😳😳!!!
shegiyar Yarinya ni ne DODO? to Ubanki ma yaci Uwarsa....."

Ayush gaba d'aya jikin ta ne yahau kakkarwa ta manne a jikin gini, ga yanda gumi yake ta keto mata ta gama tsorita sosai ganin yanda Old Monkey yake magana yana zaginta...

Shi kuwa saida ya gama zage ta tass sannan ya kuma cewa "wato kin warke shine zaki tashi kina Kira na da Dodo dan Ubanki, ashe baki da mutunci? tashi na kai ki gurin iyayen nakin, na gama aikin da zanyi..."

tashi yayi ya kamo hannunta yaja ta suka fice daga cikin room d'in na magani,
Jikin Ayush ne yake kaf² kaf² kaf² tsabar tsananin tsoro, ta gwalo ido waje,
ita tinda take bata ta6a ganin mai irin halittan nan ba, gashi masifaffen Dattijon Biri,
har saida ya shiga falon masarautar yana ri'ke da hannun Ayush,

Bara'at ce ta tafo gurin da Ayush take tana fad'in "'yata Ayush.."

Sakin hannun ta Narasimha yayi yana fad'in jeki gurin "uwarki gata nan...."

Ayush ganin Mahaifiyarta yasa ta baje baki tayo kan Bara'at tana fad'in "Umaaa.." tana nufi kanta ta rungumeta, itama Uman rungumar Ayush tayi sosai tana kukan farin cikin ganin d'iyarta tsawon watannu..

shima mi'kewa Sarki Raamud ya yi daga zaune cike da tsananin farin ciki da soyayya yake kallon 6ingel d'insa,

Saida suka gama rungumar juna suna farin ciki Bara'at ta d'ago tana cewa "Ayush da rabon zamu sake ganawa da juna, nayi kewarki sosai, ban ta6a tunanin zanyi nisa dake har haka ba indai da raina da numfashi na...." tana zubda hawaye take maganganunta,

Itama Ayush rasa abun cewa tayi sai hawayen farin ciki da yake ta zubo mata tana ambatar "Uma! Uma!! nayi kewarki Nima.."

Cikin sassanyar murya Sarki Raamud yace "6ingel!!.."
juyo wa tayi tana kallon Abbanta lokaci guda ta d'aure fuska cike da tsana take kallon mahaifinta...

Shi kuwa baiji komai a ransa ba sai ma ware mata hannayen da yayi yana fad'in "zo mana 6ingel Abbanta.."

Kawar da Kai gefe tayi tana fad'in "Uma bana son ganinsa, shine ya kashe mun Junaid d'ina, wallahi bana son sa, bana son ganinsa...." tana kuka tana furta kalmomin da suke fito wa daga bakinta marasa dad'in jii,

Bara'at ce ta katse ta tana fad'in "me kike fad'a hakane Ayush? kin manta cewar shi d'in mahaifinki ne? ki dakatar da wad'annan kalmomin nakin..."

Tace "to Uma shifa ya kashe mun Junaid d'ina..." ta fashe da kuka..

Bara'at tace "kinga ki kwantar da hankalinki Junaid d'in ki yana nan cikin 'koshin lafiya bai mutu ba.."

Da sauri Ayush ta kalli Umanta tace "da gaske Junaid bai mutu ba?.."
tace "eh bai mutu ba..."
ta kuma cewa "Amma meyasa yake wahalar mun da Junaid yake koma wa kamar DAMUSA?.."

Ajiyar zuciya Bara'at tayi sannan tace "bashi yake wahalar miki da Junaid ba..."
tace "to waye ne.?.."

Bara'at tace "kalli cann.." ta nuna da yatsar ta.
abunda Ayush ta gani shine Damusa Sujjur dake kwance a gefen kujerar sarki,
a hankali Ayush take taka 'kafarta saida taje har gaban Damusa ta dur'kusa sannan ta had'e hannayenta biyu tace "nagode Allah da ya kawoni gurinka Damusa, dan Allah ka daina cutar mun da Junaid bawan Allah, bai cutar da kowa ba kaima ka daina cutar da shi duk da nasan wancan mutumin ne yake saka ka azabtar da shi...". ta 'karasa maganar idonta akan mahaifinta Sarki Raamud tana huci cike da jin haushinsa,

zuwa ya yi gabanta shima ya dur'kusa yana kallonta yace "6ingel ki daina jin haushina Dan Allah, Junaid ya warke har abada, kin manta zoben da kika cire a cibiyarki? wannan zoben shi ya ceci rayuwar Junaid,
yanzu inason komai yazo 'karshe, ki kawo 'karshen kiyayyar da kike nuna mun, kiyi hakuri 6ingel, ki yafe mun, na tuba, na kuma shiryu bazan 'kara aikata wani makamancin laifi ba,
Auranki da Junaid kuma halattacce ne a gurina, kuje kuyi Auren ku...."

Murmushi Ayush tayi wani irin farin cikine ya ziyarci cikin zuciyar ta,
fashe wa tayi da kuka ta rungumi mahaifinta.
Shima rungumarta yayi yana rarrashinta...

Sai a wannan lokacin Narasimha yayi magana yace " toh idan kun gama koke² ku zan mayar da yarinyar yanda ta fito, domin zaman ta anan bazai yuba jininta yana can...."

Ayush tafo wa gurin Umanta tayi a hankali ta furta cewa "Uma ni wannan wayene mai siffar Biri 🐒🐒?.."

Bata ankara ba taji yace "Wanda ya raini ubanki ne, ni zaki zo ki tambaya ba uwarki ba, sakaliyar yarinya"

d'an turo baki tayi kamar zata yi kuka tana mutsil-mutsil da baki kamar maiyin magana..

Bara'atu ce tayi magana tace "Narasimha muna so kafin Ayush ta tafi zamu nuna mata cikin masarautar nan tinda bata ta6a zuwansa ba sai wannan lokacin, a bamu dama d'aya.."

Kallon ta yayi a fusace yace "baku da wannan damar, a yanzu zata tafi, idan kuma kina son binta zan had'a da ke ne..."

Girgiza kai Bara'at tayi tana fad'in "a'a² Allah ya huci zuciyar ka, idan na bita Junaid harbeni zaiyi wallahi..."

Narasimha ko tsaya sauraronta baiyi ba ya had'e hannayensa biyu sai ga wannan haske mai 'karfin gaske ya bayyano,
Gaba d'ayan su rufe idanuwansu sukayi Banda Narasimha daya je gaba Ayush yasa hannu ya d'auke ta a saman kafad'arsa nan take suka 6ace 6att,
Bai sau'kar da ita a ko Ina ba sai a babban falon gidansu Junaid,
ya kwantar da
ita a kan kujera a yayin da ita kuma idonta a rufe bata san a halin da ake ciki ba....

Shi kuwa Narasimha 6acewa yayi da wannan hasken nasan ya koma masarauta.

A can kuwa Bara'at rungumar sarki Raamud tayi tana kuka mai sosa zuciya,
"wai tana ji tana gani a rabata da yarinyarta, kuma babu ranar sake had'uwa."

Shima Sarki Raamud baiji dad'in tafiyar 6ingel d'insa ba, sai dai ba yanda ya iya dole zata koma ta kasance da Junaid...

*SHARING AND SHARHI FISSABILILLAH🙏🙏🙏🙏🙏🙏*


*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

*typing📲*

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*


*BOOK ONE*⬇️
*91 to 92*


*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*

*BOOK TWO PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*

*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*

*DIP! DIP!! DIP!!!*

*FARASHI YA QARU DAGA 150 YA KOMA 200,*
*WADANDA SUKA BIYA 150 SU SUKA CI BONONZA*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*

*OR*

*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*

*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*



*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________



💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم



https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt



🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀


Knock! Knock!! Knock!!!
Knocking ake da ƙarfin gaske, da ƙer ya iya buɗe bakinsa murya a shaƙe yace "waye ne..."
"Yaya ni ce Laylah.."

a tsorace yake kallon bakin ƙofa yace "you are very stupid, meya kawo ki ɗakina da sassafe?.."

turo baki tayi tana gunaguni daga baya tace "yoo Yaya nazo tambayar ka Maimoon ce ko kasan yanda taje ta, yanzu Ammynta ta ƙira waya tana tambaya wai bata kwana a gida ba..."

gaban Doctor Hasheem ne yayi wani irin bugawa yana zazzaro ido waje lokaci guda kuwa ya rikirkice yana ƙiƙƙina yace "ba b b ba ban san inda taje ba, ki tafi ki ba ni guri..."

Laylah cike da mamaki ta kama baki tana maganar zuci tace "subhanallahi ya naji Bros kamar yana cikin matsala? yanzu haka nasan bazai wuce akan wancan daƙiƙiyar yarinyar ba.." taja dogon tsuka sannan ta nufi ɗakinta..

yana zaune yasa Maimoon a gaba ya yi tagumi, har zuwa yanzu ya kasa tsinana komai ga jini baje-baje akan gado, bata farfaɗo ba har yanzu,
lokaci guda ya zamo abun tausayi, shima kansa yayi regreted akan abun da ya aikata wa Maimoon, domin tinda yake bai taɓa aikata zina ba, yau sai gashi ƙaddara ta riga fata, yana fitar da furuci a bakinsa "wai yau ni ne Doctor Hasheem na yi fyaɗe a yarinya? ni ne mai ceton rayukan al'umma yau gashi an wayi gari zanyi sanadiyar rasa rayuwar yarinya..." bubbuga goshinsa yayi tare da fashe wa da kuka...

wata zuciyar ce ta sanar masa cewa "ka tashi ka ceci rayuwarta..."
a zabure ya tashi ya rungumota caɗatt ya ɗagata ya nufi toilet da ita,
ya kunna ruwan zafi a cikin seat bith ya tsundumata, sai da tayi 5 minute a cikin hot water kafin ya wanke ta, sannan ya ɗagota suka nufi bedroom, kwantar da ita yayi a ƙasan carpet ya cire bedsheet mai jini ya canza wani sannan ya kwantar da ita akai,

a hankali take buɗe eyes ɗinta, ruwan zafin ya ratsa jikin ta sosai, sai hawayen da yake ta faman zirya a saman fuskar ta, ta kasa motsawa ko da ɗan yatsanta ma,
ganin ta farfaɗo ne yasa ya haura saman gadon yana ƙiran sunanta "Maimoon! Maimoon ki kwantar da hankalinki zaki warke kinji, kiyi haƙuri na aikata miki babban kuskure ki yafe ni dan Allah, duk ke kika jawo hakan ta faru...."
ya ƙarasa maganar yana goge mata hawayen da suke zubo mata...

ita kuwa kallon sa kawai take ta kasa motsa lips ɗinta ma, bazata iya magana

35 / 44