Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MATAR Damisa BOOK ONE Complete Hausa Novel by Asmeetah Writer

Author :  Asmeetah writer Category :  Drama

Chapter   24 / 44

69K to 72K   out of 131.4K words

ka tashi kuma?"
Murmushi ya yi sannan yace "bakomai inaso zanje nima nayi wanka yanzu dawowa ta, kinsan idan na dawo inhar banzo duba lafiyar ki ba hankalina baya kwanciya.."

Murmusawa tayi tace "proud of you my Bros, nagode da irin kulawar da kake nuna mun.."

Ficewa ya yi daga cikin ɗakin
ita kuwa Laila murmushi tayi tasan saboda Maimoon yabar ɗakin....

zama tayi a bakin gado tayi tagumi wasu siraran hawaye ne suke gangaro mata daga gani kasan tana cikin damuwa.
dai den lokacin da Maimoon ta fito daga toilet ɗaure da towel a ƙirjin ta, ganin Laila a cikin wani hali yasa tazo itama ta zauna kusa da ita ta zauna jikinta duk a mace tace "Laila what's wrong with you? kina kuka akan meye?..."

Laila ta juyo tana kallon Maimoon tace "ke ma ai kuka kika yi, ganan eyes ɗinki sun canza launin jaa, nasan ke kukan ki akan Doctor Hasheem ne wato Yayana."
Jinjina kai Maimoon tayi sannan tace "haka ne a duk lokacin dana ci karo da Yaya Hasheem gabana faɗuwa yake tsabar tsananin sonsa da nake yi, muna son junan mu amma narasa meyasa Yaya Hasheem lokaci guda ya canza mun,
ga halin da muke ciki ni da ke, abun kunya ne ace ni ina lesbian da ƙanwar mijin da nake sa ran zan Aura, tirr da wannan rayuwar kuma hakan ma a iya junan mu muke wannan ƙazantar, ni na lura Laila a duk sanda muka yi wannan abun akwai rashin jituwar da yake shiga tsakanin mu, dole sai munyi faɗa, shin meya jawo hakan?.."

Ajiyar zuciya Laila ta ja sannan tace "nima ban saniba Aunty Maimoon, a koda yaushe ina kuka akan wannan al'amarin, sai dai mu cigaba da addu'a domin muna cikin babban masifa ina tsoron kar wata rana a kama mu.."

gaba ɗayan su kuka suke yi,
"Aunty Maimoon Oga Junaid ciwon sonsa zai hallaka ni wallahi, amma
shi baya sona.."

Maimoon ta juyo tana kallon Laila tace "Laila ke ma kin ɗora ranki akan Junaid wanda shi ba mace bane a gabansa, mutumin da bashi da lafiya, ba cikakken mutum bane, shin ina zaki kai shi?.."

Laila hura iskar bakin ta tayi tana faɗin "insha Allah Oga Junaid shine mijina kuma uban ƴa ƴana,.."

Murmushi Maimoon tayi sannan tace "Allah ya temaka ya bada sa'a.." ta tashi tana ƙoƙarin zura rigar da Laila ta fitar mata..

ita kuma Laila kallon Maimoon take tana maganar zuci "ina tausaya miki Maimoon domin nasan duk lokacin da kika ji Yaya Hasheem ya samu new budurwa haƙiƙa zuciyar ki bugawa zata yi, Yaya Hasheem yanzu ba kece a gabansa ba, amma shima ya yi rashin adalci sai da kuka shaƙu soyayyarku tayi ƙarko tukun zai bar ki ya koma gurin wata wai Ayush..."
tsuka taja ta tashi ta saka hijabi tare da shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah...

jin yanda Laila tayi tsuka yasa Maimoon yin murmushi ta girgiza kai a tunanin ta tsukar da Laila tayi da ita take.....

*****

Zaune yake a bakin gado ya yi tagumi yana magana ciki-ciki "kiyi hakuri Maimoon nasan nayi miki babban laifi, kece mace ta farko dana so a rayuwata kuma nake da burin Aura amma tinda naci karo da Ayush komai na jefar shi gefe, nasan kina matuƙar ƙauna ta fiye da yanda nake tunani, amma yanzu na canza Ayush nake gani a gabana ita ce ta maye gurbinki Maimoon duk da kema har yanzu kina raina.."
haka ya cigaba da maganganun sa shi kaɗai.

*WACECE MAIMOON*

wata yarinya ce ƴar shekara 21 mai ilimin gaske na boko dana arabic, sau uku Maimoon tana sauƙe Alqur'ani mai girma, hadisai ne da Ahlari a kwakwalwar ta,
Itace ta ɗaya a gasar karatun qur'an a cikin ɗalibai na ƙasashe..

asalin iyayen Maimoon larabawan makkah ne, suka baro makka zuwa nan nigeria garin Abuja,
Maimoon fara ce tas itama ga gashi tana da dirin jiki domin tafi Ayush dirin jiki gaskiya
sai dai bayan nan bata fi Ayush da komai ba,

Ayush da Maimoon farare ne sai dai launin fata ta banbanta,
ita Ayush fara ce tasss, Maimoon kuma farin ta launin jaa ne.
gashin Ayush mai murɗi-murɗi ne ga laushi gaban goshinta kuwa gashi ne a kwance har yaso ya haɗe da girar ta, yanada tsayi sosai zuwa tudun bayanta,
ita kuma Maimoon gashin ta tsantsi ne dashi a ware gashin yake itama ya rufe gadon bayan ta,
Ayush ta fi Maimoon Eyes da ƙaramin baki,
Maimoon kuma tafi Ayush tsayin hanci duk da itama Ayush tana da tsayin hanci,
Amma kuma Ayush tafi Maimoon tsayi nesa ba kusa ba domin ita fa Ayush da kaɗan Junaid ya ɗarata tsayi..

kowa da kalar suffar ƙasar daya ɗauko,
zuriyar mahaifin Ayush ƴan fulanin indiyawa ne dake ƙasar Oromia daganan kakanta ya samu mulkin ƙasar California....

Ita kuma Maimoon balarabiya ce ciki da waje,
duk ɗin su ba laifi ta ɓangaren kyau...

Mahaifin Maimoon babban abokin mahaifin Doctor Hasheem ne marigayi alhaji Bukar,
tin suna ƙananan yara suka fara soyayya da Dr Hasheem da kuma Maimoon, har Allah yasa suka mallaki hankalin kansu yanzu kuma Docter Hasheem yake so ya juyar da soyayyarsa kan Ayush haɗuwar sama...

*DALILIN YIN LESBIAN TSAKANIN MAIMOON DA LAILA...*

Akwai wata rana Maimoon da Laila suna tafe kan hanyar su ta zuwa hospital zasu je gurin Doctor Hasheem to daman Maimoon ita take draving motar ta suna tafe suna hira, kwatsam sai suka bugi wata tsohuwar mata da baƙaƙen kaya a jikin ta,
da gudu suka fito daga cikin motar suna faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, ta mutu ko?"
ita ko Laila fashe wa tayi da kuka dake lokacin yarinya ce bazata wuce 15years ba, ita kuma Maimoon ta kai 18years suna ƙoƙarin ɗaga tsohuwar nan suka ji ta tintsire da dariya ta ɗago tana musu wani irin kallo, lokaci guda kuwa ta rungumo su jikinta kowanne sai data zura harshenta a cikin bakin su, cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta ɓace ɓatt, tin daga lokacin ta juyar musu da kwakwalwa wanda idan basu kusanci juna ba basa jin daɗi duniyar zafi take musu,
to tin daga wannan lokacin suke wannan harkar ba tare da son ransu ba, sai bayan sun kammala suke dana sanin aikatawa kuma suke faɗa a junan su, tsawon shekara uku yanzu kenam....

idan har ba tsafi bane ai Maimoon tafi ƙarfin zuciyar ta saboda kullum a cikin karatun kur'ani take, a yanzu ta kammala N.C.E, Laila kuma ta kammala S.S.E, shaƙuwar dake tsakanin su ne yasa Laila take ƙiran Maimoon da Besty ita kuma Maimoon ta ƙirata da ƙawas amma ai Maimoon ta girmi Laila sosai....


*MASHA ALLAH*

Rashin comments ɗinku ne yasa zamu tsaya anam.

ku gyara dan Allah🙏🙏



*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

typing📲

🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)

*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)


*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫


بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ------->71 & 72 <-------

✈️✈️✈️ ƘASAR CALIFORNIA...

Sarki Raamud ne zaune akan kujerarsa ta mulki ya ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya yanata huci,
ga Mahaifiyar Ayush kuwa durƙushe a gabansa ya sata tayi kneeldown, tana kuka ga gumin dake yanko mata daga sumar kanta, tana faɗin "Shugaba kayi hakuri ka bar hukunta ni haka, nifa temako nayi...." kafin ta ƙarisa maganar ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa "your very stupid, ni zaki munafurta? kin sace mun zoben Dish kin kaiwa Ɓingel kuna ganin shine hanyar da zaku bi ku magance matsalar ku, kin toshe mun kafar da zanga Ɓingel da kuma Junaidu! toh amma ina so ku sani cewa kafin ku aiwatar da aikin ku na rigada na tura Aljanin ƙudus yaje ya murɗe mun wuyan Junaidd...." Hahahaha ya kwashe da wani irin mahaukaciyar dariya..

tsabar tsoro da firgita sai da Bara'at ta faɗi zaune daga kneeldown ta dafe ƙirjin ta tana faɗin "shugaba ka kashe Junaid? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!" ta fashe da kuka "meyasa ka ɗauki wannan tsatstsauran hukunci? shikenam nima kuwa zaka rasani yanzu domin rayuwata batada wani amfani tinda har na gaza ceton Junaid."

Da gudu ta tashi ta miƙi hanyar fita daga cikin falon masarautar kai tsaye ɗakinta ta nufa tana shiga ta danna key, zuwa tayi ta ɗauko poisen zata sha,
wani irin bugu akayi wa ɗaki ya buɗu, cafko hannun ta yayi sannan ya yi wurgi da ƙwalbar gubar ya zabga mata mari ya hankaɗata saman gado yana faɗin " ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, idan kika kashe kanki kin mutu kafura..."
katse shi tayi da cewa "wanda yayi kisan kai kuma fa?? ya kamata kaji tsoron Allah Abul Mayush, ka sani fa wata rana zaka mutu, bawai kai kaɗai za'a bari a doron duniya ba,
Ka kashe Junaid ita kuma fa Ayush shin zata rayu ne? bakayi tunanin haka ba, ka yanke hukunci saboda ita to ka sani ko da ran Junaid ko ba ran Junaid Ayush zata mutu ne,
an zo wajen da bazata iya rayuwa ba tare da Junaid ba....."
ta tinshire da dariya tana tafa hannayen ta biyu ta kuma cewa "shin baka san Junaid da Ayush jininsu ɗaya ba ne?
to ka ɓarar yanda ka kashe Junaid haka Ɓingel ɗinka ma mutuwa zata yi, bazata rayu ba......"

Ja da baya Sarki Raamud ya soma yi tabbas maganganun Bara'at sun juyar masa da kwakwalwarsa, zuciyarsa ne ta fara harbawa da ƙarfin gaske,
lokaci guda kuwa ya yi regret akan abunda ya aikata, "haƙiƙa Ayush itace mahaɗin Junaid, kuma jininsu ɗaya yanaso ya warware wannan al'amarin amma ya kasa..." haka ya tsaya cak yana maganar zuci, jikinsa ya sake baya jin daɗin jikinsa sosai, ga wani irin zazzaɓi da ya rufe shi..
lokaci guda kuwa ya zabura da sauri ya fice daga cikin room ɗin Bara'at wacce itama tsayawa tayi tana kallonsa cike da tsana da kuma mamaki ga hawayen da suke gangaro mata, kamar tasan abunda yake ransa ta furta cewa "yanzu haka nasan zai tafi ƙasar nigeria ne domin yaje ya dubo su Ayush...."
itama da gudu ta nufi waje, ta samu Sarkin har ya hau kan wani dokinsa mai ƙarfin gaske da kuma gudu, domin zai iya zuwa nigeria da wannan dokin ba tareda ya hau jirgi ba, domin yasan ta ko ina nemansa ake..
har ya fara tafi ta ƙwalla masa ƙira da ƙarfi tana faɗin " *kasa a ranka cewa kana barin cikin masarautar nan shikenam ka barshi har abada, kuma ba kai ba mulki! ƙa'idojin dokar kenam, na tunatar dakai...*

Sarki da jin hakan ya tsayar da dokinsa, gabansa na yankewa, idanuwansa
kuwa har sunyi jawur, fuskarsa ya nuna alamar damuwa ajiyar zuciya yaja sannan ya kanne idanuwansa sosai, yana so yayi kuka amma ba hali domin zubda hawayensa shima wani makaryin asiri ne a jikinsa...

Ba yanda ya iya haka ya juyo da dokinsa saboda mulkinsa shine babban abun tasirinsa kuma shine tushen sa na iyaye da kakanu...
Haka ya sauƙo yana tangaɗi hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfin bala'i, tabbas shima yasan idan babu Ayush shikenam tashi tazo ƙarshe,
saida yazo daf da Bara'at ya tsaya yana kallonta cike da tausayawa kansa, bazai iya control hawayensa ba haka ya durƙusa da gwiwowinsa sannan ya fashe da wani irin matsanancin kuka kansa a sunkuye....

zaro ido Bara'at tayi tace "Innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, nashiga uku *SHUGABA* tinda uwata ta haifeni ban taɓa ganin damuwa a fuskar ka ba balle hawaye uwa uba har da rera kuka, abun babba ne, shikenam ka korar da ALJANUNKA sunga hawaye a idonka...."

Aljanun da suke cikin masarautar sa kuwa haka suka rinƙa ɓacewa,
duk wani abun tsafi sai ɓacewa suke,
duk abubuwan tsoro dake cikin dajin maƙarƙashe duk sun ɓace daman shi ya ƙirƙire su da yarjejeniyar bazasu ga hawaye a idonsa ba har

24 / 44