Author : Asmeetah writer Category : Drama
Mommy itama rarrashinta ta shiga yi tana faɗin "kiyi hakuri ai gani nam ko, kin tabbata ba Junaid bane ya sanya ki kuka ba?"
Ɗaga kai kawai Ayush tayi ba tare da tace komai ba,
Shi kuwa Junaid tsayawa yayi yana kallonsu yayi wani tur6une fuska cikin 6acin rai yace "wai mommy meyasa kike son ɗora mun laifi ne, komai akayi sai kice ni komai ni, haka a hospital kika hau kaina da masifa wai ni nayi wa Doctor Hasheem dukan mutuwa alhalin ni bansan komai ba haba haba...."
Yana kaiwa karshe ya haura upstairs....
Mommy kuwa kallo kawai ta bishi da shi daga karshe kuwa ta jinjina kanta tace "Allah ya shirya mun kai Junaid..."
Ayush itama jin Abunda Junaid ya gaya yasa zuciyarta bugawa
"Wai daman Yaya Junaid ya yiwa Dr Hasheem duka?? Innalillahi zan so naga Dr Hasheem"
Maganar zuci take har kwalla yaso ya ku6uce mata,
Sai ji tayi Mommy ta dafa kafad'arsa tana tace "My Doughter tunanin mai kike yi?"
Murmushin yaƙe kawai tayi, tace "babu komai"
"Ok karki damu kinji komai zai dawo normal, bari na shiga kitchen nasan yarana suna jin yunwa ko?"
Tayi tambayar tana kallon Ayush
Wacce kanta ke ƙasi tana wasa da yatsun hannunta,
Ajiye mayafin ta tayi sannan ta nufi kitchen, itama Ayush bin bayanta tayi tana faɗin nima zan taya ki girkin,
Juyowa Mommy tayi da murmushi a fuskar ta tace "to shikenam zo mu fara nasan baki iya girkin ba"
Rufe fuskarta tayi tana dariya, tana so ta koyi girki sosai....
******
Junaid kuwa bayan shigarsa room
Kai tsaye ɗakin sirrin sa ya nufa,
Zama yayi akan sofa da ƙaramin glass table a gabansa sai faman daddanna laptop yake,
Duk bincikensa baya wuce akan *SARKI* *RAAMUD* wanda mutane suka fi saninsa da sarki zalimun wanda ba kowa ne yake iya ganinsa ba sai a wanda ya bama ikon ya kalle shi,
Wadanda suka sanshi sun sanshi wanda basu san shi ba sune suketa wahalar da kansu kamar dai Junaid...
Ga dai drowing dinsa a jikin poster amma an rasa a yanda za'a ganshi,
Haka ya rinƙa faman bincike amma ya kasa gano a yanda yake,
Har bacci ya yi awun gaba dashi akan sofa..
Around 4pm Ayush ta shugo ɗakin Junaid da sallama a bakinta, jin shuru ba'a amsa mata ba yasa tayi tunanin yana toilet,
Tsayawa tayi tana ƙarewa ɗakin kallo!
Taci kwalliya ba ƙaramin kyau tayi ba
Tasha doguwar riga na atampa mai launin black and red ga tayi ɗaurin ɗan kwali mai tuta a gaba, tasau gashin nan ya baje har saman qugunta, ga wani irin makeup da bata taɓa yin irinsa ba sai kamshin turare take ta fitarwa......
Karo na biyu kenam tana zuwa ɗakin Junaid akan yazo suci abinci amma bata samun sa
Har ta gyara masa room ta sauya bedsheet, ta feffeshe ɗakin da air-fresh mai shegen kamshi...
Sannan ta fice a ɗakin a tunanin ta yana toilet!
Sai wannan zuwa karo na biyu still bata same shi ba,
Hakan yasa tayi knoking door ɗin toilet shuru ko motsin ruwa bata jiyo ba
Ta tura kofar ta leƙa cikin toilet babu kowa
"To kodai ya fice a gidan ne babu wanda ya sani"
Fuskar ta ne ya nuna damuwa kamar zatayi kuka,
Saitin wadrobe ɗinsa ta tsaya
Zata jingina bayanta a jikin bango, ƙofar ɗakin sirrin ne ya buɗe bata ankara ba sai ji tayi ta tafi luuuuuu yaraff ta faɗi ƙasi tayi matukar tsorita tasau ihuuu,
Bata ta6a tsammanin akwai ɗaki a gurin nan ba..
Jin ƙarar ihun ne yasa Junaid ya razana daga baccin ya tashi yana "waye ne"
A gigice Ayush ta tashi tana waigawa bayanta, ba karamin tsorita tayi ba
Jikinta yana 6ari "wayyo Allah na nashiga uku ina ne nam.."
ƙarasa shugowa cikin ɗakin tayi tana kalle-²
Har Junaid yazo gabanta bata ganshi ba,
Kafin ta ankara dashi ya janyo hannunta sunyi wajen asalin room ɗinsa
Ya rufe wannan ɗakin yasa mata key!
Yayo kanta yana faɗin "meya shigar dake cikin ɗakin can? Na baki damar ki shugo nan ɗakin amma banda can....." ya nuna secret room da yatsar sa idonsa kuwa akanta.
"To t t too ni bansan akwai ɗakin a cikin ɗaki ba, ban ban saniba wallahi, wayyo Allah na zuciyata zata fashe! Tsoro nake ji.."
Gaba ɗaya ta kiɗime ta ruɗe.
Shi kuwa sai binta yake da kallo
Shima yasan a cikin tsoro take
Ganin yanda take ta magana a har harɗe yasa ya jawota ya haɗe bakinsa da nata
Ji kake tsitt kamar wanda aka ɗauke wuta..
A tunanin sa yin hakan zaisa hankalinta ya dawo jikin ta!
Hot kiss yake bata kamar zai cinye bakin ta
Ita kuwa tinin ta fita hayyacin ta
Kwakwalwarta bazasu iya ɗaukar irin wannan bada saƙon ba
Ta ƙankame shi sosai, jikinta ne yahau ɓari sai kakkarwa take tayi
Nan take numfashin ta ya ɗage cakk
Ta tafi duniyar suma!
Shi kuma bai san ta suma ba haka ya riƙeta yanata faman tsotse mata baki,
Shi jin bakinta yake kamar zuma,
Zaƙin masifa ne da yawunta shiyasa idan ya kama baya yi da wasa.....
Ita ta ɗanɗana masa shiyasa 😅😅
( to fah idan yawun kamar zuma yake 🤔 shi kuma cann ƙasan ya za'a ji shi kuma 🙈🙈🙈😜😜😜🤣🤣🤣))...
Jin bata motsi yasa ya ɗan dakata, tayi baya zata faɗi da sauri ya riƙota ya karata a saman faffaɗar kirjinsa! kwantar da ita yayi akan gado yana furta sunanta cool "Yushert! Yushert!! wakeup please,
kinga banason irin wannan wasan ki tashi mana..."
Dubata yayi yaga bata numfashi!
Hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba,
jijjigata yake sosai amma ba alamar motsi, bakinta ya buɗe ya ɗora nasa yana hura mata iskar bakinsa tare da daddanne mata kirji, ganin har wannan lokacin bata farfaɗo ba yayi toilet da gudu ya ɗebo ruwa yana kwara mata
a gigice ta tashi tana jan numfashi sama-2
wani irin dogon ajiyar numfashi yaja ganin ta farfaɗo,
"Sorry Yushert, sorry you not feelling well?"
Ita kuwa wani irin kallo take wurga masa da shanyayyun eyes ɗinta,
kafin ya ƙara furta wani abu ta jawo kwalar rigar sa ya rufu akanta ta zagaya hannayenta ta bayansa ta ƙanƙameshi,
"ina sonka Yayana! ina matuƙar ƙaunarka!! kada ka ce oh'ohhh Yayanah,
jikinka laushi, surarka gwanin burgewa ina so ka kasance dani Yayaa naah......"
toshe mata baki yayi da hannunsa
"Shiuuuuuu🤫🤫🤫 ya isa haka, kiyi shuru"
"Oh'ooh! kace kana sona toh"
tana kallon cikin idanunsa kamar mai jin bacci.
"kinga banson yarinta fa tashi mu sauƙa falo yunwa nake ji ..."
yanaso ya tashi daga samanta amma taƙi barinsa ta rungume shi sosai,
"Uhm uhmm ni saika furta mun idan ba haka ba mutuwa zanyi..."
murmusawa yayi sannan ya manna mata kiss akan goshi
yace "I love you my Yushert...."
dai den lokacin da Mommy ta shugo da kulolin food a hannun ta,
ganinsu a haka yasa tasau baki tana kallon su cike da mamaki tace "mezan gani haka JUNAID?????"
TOHH MY FANS KUYI HAKURI DA QARANCIN TYPING YANAYIN NE SAI A SLOW,
SANNAN NAYI TAFIYA NE SAKAMAKON RASHIN WAYA, AMMA YANZU NA DAWO......
*COMMENTS* *AND* *SHARE* *PLEASE* 👏👏👏
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of tinger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️✍️)
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
https://www.facebook.com/103637491942644/
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
*BOOK ONE*
🅿️ -------> 61 & 62 <-------
___________________________
A razane Junaid ya tashi daga kan Ayush yana faɗin "subhanallah Mom meya kawo ki ɗakina?"
zuba masa ido tayi tana ƙara jinjina kai "aah ƙwarai dole kace mena zo yi ɗakin ka, kana shan sharholiyar ka! marar kunya har kana da bakin magana ka danne ƴer mutane sai faman nishi take..."
shafa suman kansa ya soma yi kai a sunkuye.
ita kuma Ayush tin shugowar Mommy ta danna kanta a cikin pillow tsabar kunya ta kasa ɗagowa, Mommy ce ta kalli yanda take tace "Ayusher kin nuna mun cewa Aure kike so, acikin mutum biyu ki zaɓi ɗaya Junaid ko Doctor Hasheem? zuwa gobe ki fitar da gwani,
kai kuma Junaid idan ta fitar da kai zuwa wani satin za'ayi muku baiko, kar ina zaune naga an ajiye mun jariri..."
Mommy tana kaiwa ƙarshe tayi ficewar ta ga flask na kayan abinci wanda ta ajiye su akan table.
Ayush tana zaune jin abunda mommy ta gaya yasa tayi firgit bata san lokacin da ta tashi zaune ba, tana ta zazzaro ido waje zuciyar ta kuwa kamar wanda ake buga ganga a ciki! "tashin hankali" abunda ta furta kenam a cikin zuciyar ta.
shi kuwa Oga Junaid tinda mommy ta fara maganar Aure yaji kamar an zare masa rai, a hankali yake motsa lips ɗinsa "Aure kuma! ni Junaid? a'a bada ni ba, i can't marry any girls, bana tunanin zanyi Aure a rayuwata bani da ra'ayin yin Aure.." haka yake ta maganar zuci kansa a ƙasa.
itama Ayush da abunda take faɗi a ranta "taya zan zaɓi ɗaya a cikin Yaya Junaid da Dr Hasheem alhalin ba wanda ya taɓa cewa zai Aure ni, hankali na yafi kwanci da Yaya Junaid sai dai matsala ɗaya shine mahaifina bazai taɓa yadda da al'amarin nan ba, ni kuma bazan taɓa Auran kowa ba inba Yayana Junaid ba domin shine makami na.."
******
*FADAR SARKI RAAMUD*
zaune yake a kan kujerar mulkinsa na alhurma gwanin sha'awa, da wasu ɗirma-ɗirman mutane a ta gefensa suna tsatstsaye da baƙaƙen kaya a jikinsu wanda kana ganinsu kasan ba mutane bane, su kai biyar ga kuma damusa a gefen kujerar sarki!
makeken madubi yasa a gaban sa yana ta kallon abunda ke faruwa ata ɓangaren su Ayush, murmushi yasau mai ƙayatarwa ya lumshe kyawawan idanuwan sa yace "Ɓingel Mayushert na gaya miki Auren ki da Junaid ba mai yuwa bane, duk abunda nace bazai yu ba toh bazan taɓa barin hakan ya yuba domin shi ɗa ga ɗan uwa nane kuma maƙiyi na"
yana kallon cikin mirrow yana kuma furta kalamansa ba tare da su Ayush sun san yana yi ba.
"Hummm! zanga ta yanda za'ayi baikon nan, ni na yadda ki zaɓi kowa a matsayin mijin ki amma banda Junaid, idan kuwa ba haka ba zanyi maganin shi..."
******
wata kyakykyawar mata ne black beauty ga hanci kamar zai shige baki tsabar tsayi, idanuwan ta manya-manya farare tass ga zara-zaran gashin ido! girar ta kuwa har sun haɗe biyu, da ƙaton mayafi a kanta ta rufe duk ilahirin jikin ta,
a hankali take motsa ɗan ƙaramin bakinta ta ɗaga hannu sama idonuwanta suna kallon sama tana roƙon Allah (S.W.T)
"Yaa Allah ka dube ni da idon rahma kaji ƙaina ka tausaya mun ka dubi maraici na yaa Allah ka gafarta mun, ka yafe mun! a baya ni christal ce amma a yanzu ni tubabbiya ce na riƙe addinin musulunci hannu bibbiyu Allah ka kankare mun zunubai na,
ya Allah bansan a wani hali ƴata take ciki ba, Allah ka taimake ta ka bata nasara akan JUNAID! ka bata ikon aiwatar da aikin ta akan Junaid waran samar masa da lafiya, Allah ka kuɓutar da Junaid daga halin da yake ciki duk da nasan ni na jefa shi cikin mawuyancin halin nan yaaa Allah......" lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai
"Yaa Allah ka haɗa zuciyoyin mutum biyu JUNAID DA AYUSHERT kasa su zamo ma'aurata......
"Ba