Author : Asmeetah writer Category : Drama
a gabansa, lokaci guda kuma ta zazzaro ido waje tana kallon cikin madubi tace "na shiga uku na! mai nace wa Yaya Junaid a lokacin da muke kwance? tabbas na faɗi wata magana ba'a cikin hayyaci na ba..."
a hankali take motsa ƙaramin lips ɗinta tana faɗin "fuck me, fuck me, fuck me..." a can ƙasan harshenta take faɗin haka,
fashe wa tayi da kuka irin na sakalan nan a shagwaɓe take cewa "shikenam yanzu Yaya Junaid zai rinƙa mun kallon marar kunya wacce bata da ajiii..."
lokaci guda kuma ta turɓune fuska tana turo baki, tana sheƙar numfashi da ƙarfi irin rantan nan ya ɓaci sosai tace "wato ni Yaya Junaid zaiyi wa wulaƙanci ko? saboda yaga ina damuwa dashi shine zaice wani zai gaya wa mommy ayi maganar Aure na Doctor Hasheem ko? kuma ƙarya yake shima nasan yana sona..."
"waye yake miki ƙarya...?"
Gabanta ne yayi wani irin yanke wa, zuciyarta yana wani irin bugawa kamar wanda ake buga ganga, ta wani zaro ido waje, lokaci guda kuma ta fashe da kuka tana waiwayo wa tareda faɗin "wallahi tallahi ba haka nace ba Yaya Junaiddddd..." ganin ba kowa a bayan natan ne yasa ta tsayar da kukan tareda jan sunan nashin,
tana waige-waige amma bata ga kowa ba, ta lelleƙa ko ina but no anybody ga kuma ƙofar ɗakin a rufe yanda yake, kuma duk wanda ya shugo zata ji ɗan ƙarar buɗewar ƙofar amma sai taga ba wanda ya shugo kuma kamar taji maganar Junaid, dafa goshinta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya tace "masha Allah ashe dai gizo yake mun, Allah ya isa bugun zuciyar da ka sakani..." ta turo baki ta koma yanda take a zaune a gaban mirror ta ɗauko cream tana shafawa duk ƙamshi ya gauraye ɗakin,
bayan ta shafa ta ɗan goga powder a fuskarta ta shafa lips cream a leɓɓenta mai sheƙi da maiƙo, ta kuma haɗa mayukan gashi kala-kala ta shafa a sumar kanta mai laushin gaske da tsayi, daga nan ta tashi ta nufi wardrop ɗinta buɗe wa tayi ta zaro jeans blue colour da rigar saƙa mai fuji-fuji da hannun rigar bubaa, gejin rigar iya zuwa kunkumi ne, sai dai kafin rigar tasaka best ta ciki saboda ana iya kallon jikinta indai iya rigar saman ne, ta saka jeans ɗin nan ya kama jikinta sosai, kunkumin ya fito sosai ƙafar wandon pencir ne ya ɗameta domin daƙer ta iya saka wandon nan, ta ɗauko bell mai duwatsu ajiki na ƙwalliya ta ɗaura a kunkumin ta duk da wandon ya kama kunkuminta amma bell ɗin tasa ne saboda ƙwalliya,
ta ɗauko rivon ta tuttuƙe gashin kanta tayi donut dashi, ta saka dogin ɗan kunne masu colour blue d same jeans and t-shirt, ta ɗaura agogo a hannunta sannan ta ɗauki turare duk ta feffeshe jikinta da shi har zuwa kayinta,
ta yafa ɗan ƙaramin gyale blue wanda ya tsaya mata a iya wuyanta, ta zura dogin ƙafafuwanta a cikin blue thorns mai botula ta sama, fuskar nan yayi fatt tsabar fari kamar jini zai fito, ba ƙaramin kyau Ayush tayi ba, ga sumar gashinta baƙi ƙirin sun ƙwanto ta gaban goshinta, girar ta kuwa kamar zasu haɗe dana juna, ga dara-daran manya-manyan idanuwanta nan fari ƙall, da zara-zaran gashin idonta sun mimmiƙe har wani ɗan lanƙwasa sukayi suna kallon sama 🫣🫣
ga kuma ɗan ƙaramin red lips ɗinta wanda suka sha oil sai sheƙi yake, shiyasa ita Ayush bata ƙwalliya daga pawder ne sai lips cream shima tana shafawa ne saboda bata son barin bakinta a bushe, iya kwalliyarta kenam! ba kwalli ba jagira sannan ba jan baki domin bakinta ma jawur yake halitta daga ubangiji an hutashe da masu kayan kwalliyar shago....
bayan ta kammala shirinta ta fara taku a hankali cikin nutsuwa kamar bazata taka ƙasi ba, da haka ta fice a room ɗin tana taka matakalar benin da zai sadata da falo,
jin maganar mutane ne a ƙasan falo yasa ta ɗan dakata tana faɗin "kamar baƙi akayi a gidan..."
ɗaga kafaɗunta tayi alamar bata damu ba just ta cigaba da takun ta tana sauƙowa downstairs..
Manya-manyan baƙi akayi a gidan wato abokan Ogah Junaid ne sojoji daga headquaters kowannen su yana sanye da kakin soja, matasa sun kai 10 sun zo taya Junaid murnan samun sauƙi na har abada, shima yana cikinsu sunata hira yana sanye da short jeans iya gwiwarsa mai kakin soja sai farar t-shirt mai zanen bindiga a gaban rigar, ya gyara sumar kansan nan ya kwanta luff dashi gashi gashin baƙi ƙirin dashi ya sauƙa masa har zuwa wuyansa, shima ya ƙara fari sosai kamar mai yin bleaching, ba ƙaramin kyau yayi ba shima...
ga gorinan lemuka baja-baja a wajen ga parantai masu ɗauke da naman chicken an soya su sun soyu har wani maiƙo-maiƙo yake fitarwa,
ta gefe guda kuma Mommy ce take zaune itama tasha danƙareriyar less mai ɗinkin bubaa! ba ƙaramin kyau itama tayi ba, daman can mommy ƴar wanka ce,
Ayush tana ganinta tasau murmushi saita tuno da farkon haɗuwarsu a asibiti wancan lokacin ma tasha wankan less..
ƙarasa sauƙa tayi daga benin ta shugo falon da sallama a bakinta duk ba wanda ya lura da ita sai datayi sallama tukun suka juyo gaba ɗayansu, kasa amsa sallamar sukayi sun zuba mata ido, wani a cikinsu kam har da miƙewa tsaye ganin Ayush,
tayi wankan ne na jan hankalin maza, sunga yarinya mai ƙirar coca cola...
Junaid shima kansa bai ɗage idonsa daga kan Ayush ba saida Mommy tazo ta tattaɓa shi tana nuna masa abokansa da duk idonsu yake kan Ayush, waran nan yayi tsitt kamar ba mutane,
wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar Junaid ya wani ɗaure fuska ya miƙe ya nufi gurin da Ayush take a tsaye ya kama kunkuminta sannan ya mannata a jikinsa yayi gyaran murya, sai a lokacin nan kowa ya dawo hayyacinsa suna faɗin "Ogah Junaid aina ka samo wannan zuƙeƙiyar yarinya ƴar india?.." wani ne daga ciki yayi maganar wanda ake ƙiransa da Commander yusuf,
wani ne kuma du yace "Ogah daga warkewarka har ka sambaɗo kyakykyawar yarinya ƴar oromia..." kamar wanda yasan ƙasar su ne daman Oromia dake ƙarƙashin ƙasar india...
Junaid ne ya ɗaga musu hannu yana faɗin "ku dakata mun haka, haba ku ba dama kuga mace sai kun nuna maitarku a fili? to wannan itace matar da zan Aura ehen kar wata rana ku ganta a hanya kuce zaku tarar mun da mata, dan ma bana barinta taje ko ina saboda maza irin ku....."
ya kuma maido idonsa kanta yana faɗin "kinsan da baƙi maza a falon shine zaki zo mun a wannan shigar? shin bakya tayani kishin kanki ne?.."
sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana maganar zuci "Hmm! anaso ana kaiwa kasuwa.."
ji tayi ya matso da kansa saitin kunnenta a hankali ya furta "kinyi kyau my wife...."...
*WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA NE GARE KU MY FANS AND MY LOVERS INA YINKU OVER..*
*SAURAN PAGE UKU BOOK ONE FREE YA ƘARE, KU HANZARTA KUYI PAYMENT 200 A FARA BOOK 2 DAKU..*
*ASMEETAH🦚NOVEL✍️✍️*
*typing📲*
🐅 *MATAR* *DAMUSAA*🐅
(the wife of a tiger)
*written* *and* *story* *by*
*Asma'u Muhammad Auwal*
( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)
*WhatsApp me 09065443871*
*BOOK ONE*⬇️
*95 to 96*
*FREE BOOK ZAI ƘARE NE A ƘARSHEN BOOK ONE*
*BOOK TWO PAID NE,*
*YANA TAFE DA SABON SALO, DA KUMA CAKWALKWALIN CAKWAKIYA, KADA KU BARI A BAKU LABARI DOMIN GANI DA IDO 👀 YAFI JII👉👂*
*MATAR DAMUSAA BOOK 2 PAY ONLY 200👌👇👇👇*
*DIP! DIP!! DIP!!!*
*FARASHI YA QARU DAGA 150 YA KOMA 200,*
*WADANDA SUKA BIYA 150 SU SUKA CI BONONZA*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*9065443871, OPAY BANK.*
*OR*
*ASMA'U MUHAMMAD AUWAL,*
*2267236949, ZENITH BANK*
*SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER*
👇👇👇
*09065443871*
*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________
💫💫 *{{N W A}}* 💫💫
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم
🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀🌀
Wani ɗan ƙaramin katafaren ɗaki ne wanda ya tsaru sosai, ga ƙatuwar katifa a shimfiɗe a gefe guda, da kuma toilet a cikin ɗakin,
Doctor Hasheem ne ya shugo cikin ɗakin yana ɗauke da Maimoon! a hankali ya kwantar da ita a saman katifar, tana lumshe da ido kamar mai yin bacci sai dai ba baccin take ba, wani irin raɗaɗi mai zafin gaske take ji a ƙasin ta, bayan ya kwantar da ita miƙewa yayi zai fice daga cikin ɗakin yaji tana magana a hankali "Ammy nah zanje, akaini gurin Ammy na, nafison na mutu a gaban Ammy naa, Abul nah! kazo ka ceceni a gurin wannan Azzalumin marar imani da tausayi...."
girgiza kai kawai yayi bayan ya saurari abun da take cewa, ficewarsa yayi ya rufe ɗakin tareda danna key ya kulleta a ciki,
ita kuwa tana kwance ba abunda take inba kuka ba, ta rasa mai yake mata daɗi a jikinta, tayi danasanin zuwan ta gidan nan gashi abunda ya faru da ita, yanzu bata san ranar barinta cikin wannan akurkin ba tinda har saita warke tukun...
shigarsa cikin falo ya tarar da Layla ta fito cikin shirinta ta yafa gyale,
yace "ke kuma ina zakije yanzun?.."
tace "Yaya zanje gidansu Maimoon ne inaso naga meyake going wrong.."
sauƙe ajiyar zuciya yayi sannan ya kuma cewa "kinga munsha aiki sosai domin gyaran ɗakin nan ba ƙaramin ciwon jiki zai sanya mu ba, ki zauna kisha maganin ciwon jiki saiki huta kema a ranki koh?..."
girgiza kai tayi tace "Yaya a yanzu babu lokacin zaman hutawa, zanje na cigaba da rarrashin Ammy akan ɓatar Maimoon, har Allah yasa ta warke saita koma gida.."
ɗaga kafaɗa yayi sannan yace "ok shikenam saikin dawo, nima inaso zan shirya na tafi hospital saboda jiya ban samu zuwa ba.."
a haka sukayi sallama Layla tayi ficewar ta, shi kuma ya nufi ɗakinsa, ga can kuma Maimoon a ɓoye a ɗakin da ba wanda yasan dashi a gidan..
☆☆☆☆☆☆
Abokanan Ogah Junaid ne suke zazzaune sunata shan hira, suna tsatstsara hidimar da za'ayi gobe na murnar samun sauƙin Junaid tareda murnar komawarsa gurin aiki, domin har an kawo masa takardar cigaba da zuwa gurin aiki..
shikenam yanzu Junaid ba zaman gida,
sun gama tsara abubuwanda za'ayi a goben da yawan kuɗaɗen da za'a kashe..
Bayan sun kammala sallama sukayi wa mommy tana zaune itama a gurin duk tattaunawar da sukayi tana jinsu har itama ta bada gudumowarta na mahaifiya wato kuɗi 5millions, kuɗin rabin hidimar da za'ayi kenam domin manya-manyan sojoji da baƙi ne zasu halarci gurin taron murnar samun warakar Junaid,
jinyar da akayi shekara da shekaru ana neman maganinsa amma anrasa, ƙasashen waje ba yanda ba'aje ba amma an kasa warkar da Junaid, sai lokaci guda ya samu sauƙi dole kowa yayi farin ciki,
wannan hidimar da za'ayi Abokanan Junaid ne suka shirya yinsa wato ƴan uwansa sojoji da shugabannin su,
bayan nan itama Mommy zatayi nata hidimar ita kuma bana shagali bane, har ta kai kuɗi 100𝗺 a babban masallaci za'ayi sauƙar alqur'ani mai girma da kuma sadaka da za'a bayar domin kawar da wasu 𝗳𝗶𝘁𝗶𝗻𝗮 kuma tana neman tsari daga ubangiji Allah ya tsare mata yaro daga faɗawa ramin mugunta na ɗan adam, sannan daga gobe zata fara azumi na neman tsarin ubangiji,
kuma a goben su Junaid zasuyi nasu hidimar sharholiya, domin har an gaggayyaci manya-manyan mutane da ƴan uwa da abokan arziƙi...
Junaid ne ya shugo fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna daf da Ayush yana faɗin "ƴan mata kinyi kyau fah..."
Ayush turo baki tayi ta tashi ta koma kusa da mommy tace "Mommy wai ya maganar mu ne?.."
Juyowa Mommy tayi tana kallonta cikin rashin fahimta tace "wani irin magana ne Ayush?.."
kallon Junaid tayi tana harararsa shi kuwa kwantar da kansa yayi jikin sofa yana danna wayarsa mai ƙirar iphone 15 pro max ko kallon yanda suke baiyi ba domin shi baya son raini da kuma shiga zancen da bai shafe shi ba..
kawar da kanta tayi daga kallonsa cikin shagwaɓa tace "ni ni Mommy ya maganar Auren mu ne?.."
Mommy zaro ido waje tayi cike da farin ciki tace "wow kuma fa zancen nan yana raina, ina zuci zuci nace wa Junaid hidimar da za'ayi gobe kawai a haɗa da baikon ku..."
shima Junaid murmushi yayi idonsa na kan