Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gidan Rina Complete Hausa Novel by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  Drama

Chapter   8 / 26

21K to 24K   out of 76.6K words

eyes d'inshi ya ce kai duk ku kadai, lalle barrister kina
so bidi'a.
Ta d'ago ta zuba mishi idanu tsananin kyau da kwarjininshi suka cika mata idanu.
Ta kasa dauke idanuwanta daga kanshi, gani yadda tai mishi kurrr.....da idanu yasa
ya dafe goshi "Omg barrister daina yi min kallon tuhuma ai gaskiya na fad'a ya
k'arasa magana yana d'age girarshi.
Sosai hakan ya k'ara mishi kyau.
lumshe idanu tayi eyelashes d'inta suka kwanta kamar ta k'ara da na katti, daga
bisani ta bud'e idanun nata ta ce idan ba kada ra'ayi events d'in zan yi magana sai
a fasa Yalla6ai.
Ta k'arasa magana tana kallon shi.
"Ya d'an shafo gashin kansa yana ta6e baki ya ce uhm....a'a kuyi kayanku dama ku
mata ba'a rabaku da bidi'a.
Tayi murmushi kawai ta rausayarda kanta gefe, kafin tadawo da ganinta akanshi ta ce
hope za kayi k'ok'ari kayi attending events din ko?"
Yalwatattacen murmushi mai narkarda zuciya yasaki, yana kallon kwayar idonta wani
yarrr.....taji yayin da sanyi ya ziyarce sassan jikinta batasan sanda ta lumsashe
idanunta ba.
Cikin sanyi murya ya furta ya na iya dole na zo, kada nasake wani laifi saboda na
fahimci kallon mai laifi ki ke min.
A hankali tayi 'yar siriryar dariya mai ban sha'awa.
"Ya d'an gyara zamanshi yana kallon cikin idanuwanta ya ce kin ji sabon canji da
aka samu yanzu anan za ki fara zama kafin ki tare a Abuja.
Yalwatattace murmushi tayi kafin ta ce ni wallahi hakan ba k'aramin dad'i ya yi min
ba.
Ta k'arasa magana tana sunne fuska.
Uhm....ya fa'da had'e da kallon tsakiyar idanunta ya ce dole ya yi miki dad'i
saboda ba ki gaji da cinyewa Abba tuwo ba.
Sosai maganar tashi tabata dariya ai kuwa ta dara har kana ji sautin fitar
dariyar ta, ta.
Yadda take dariya ba k'aramin burgeshi ta yi ba har baisan lokaci da ya shagala da
kallonta ba, jikinta ya bata ana kallonta hakan yasa ta mayarda ganinta akanshi.
"Gani ta fahimci yana kallonta yasa ya waiyace ya mik'e da sauri yana kallon
wrist watch da ke daure a tsintsiyar hannunshi, yana mai cewa za mu wuce saboda yau
zamu koma Abuja sai ranar da za ku fara programs d'inku zan iso.
"Mik'ewa tayi fuskarta cike da murmushi ta ce Allah ya kaimu, ya Kuma kai ku
lafiya ka gaidamin da su mommy.
"Sai da ya nufi k'ofar fita sannan ya ce Amin!
Bayanshi tabi parking lot ta hango Jamal da Fadila, suna fira abinsu yadda yake
tafiyarshi ta k'assaita yasa har ta ci mishi suna tafiya side by side sosai suka
dace da juna.
Suna shiri tafiya motar Barrister Z ta danno kai, cikin sanyi murya mai
d'and'ano gaske, Barrister A ta ce yalla6ai d'an tsaya ku gaisa da best friend
d'ina Barrister Zarah.
Cak.....ya tsaya har Zarah ta k'araso wacce tun kafin ta iso take zuba
murmushi, ta ce sannunku!
Jamal ne ya amsa mata da yauwa Barrister ya hak'uri da Jama'a.
"Alhamdulillah!
Ashe na taki sa'a yau dai gani ga angon namu mai tsada ai na dauka sai na rubuta
requested letter zan samu ganinka.
"Sosa keyarshi ya yi yana murmushi kafin ya ce laifin k'awarki ne da bata
dauke ni ta kaini gidanki na kwashi gaisuwa ba.
Lokaci d'aya dukkaninsu suka yi dariya sannan suka gaisa fira suka d'an ta6a,
daga bisani suka yi sallama.
Bayan sun wuce s d'akin barrister A suka yi direct, nan suka bud'e sabuwar fira
duk dai akan Aliyu ne, Barrister Z da Fadila sai shawara suke bata, yadda za ta
sami matsugunni a zuciyarshi sosai tayi na'am da shawarar tasu.
***---****---****---***
*ABUJA*

Momma wacce abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tarasa inda zata tsoma ranta taji
sauki ta kira Jarumi ko da wata mafita daga gareshi, sai ma lullu6eta da fad'anshi
na raini wayo da ya yi har yana had'awa da yi mata barazana mai firgitarwa, shiyasa
tak'ara tsundumawa damuwa fiye da ta farko ga kuma Daddy ya ce su had'a kayansu ita
da yara gobe zasu wuce Yola.
"Dole bata da za6i ta shiga had'a abubuwan da za tayi amfani da su, ita kanta
tasan ba abu mai yuwa bane ayi shagulgulan bikinan ba uwar ango, dole ta rarrashi
zuciyarta ta danne abinda takeji tashiga jama'a ayi da ita muddin bataso jama'ar
duniya su saka alamar tambaya akanta.

Washe gari jirgin safe suka biyo zuwa Yola.
"Girls d'inta sai murna da annashawa suke, bros d'insu zai yi aure zai kawo musu
sister in law, afakace momma take danna musu harara.
"Daga Airports gidansu suka wuce wanda uncle suraj ne ya yi picking d'insu.
Ta 6angare gidansu Barrister A shirye-shirye suke ba kama hannun yaro tuni 'yan uwa
da abokan arziki na nesa da na kusa sun fara cika gida, gani yadda gidan yafara
haltsunewa yasa barrister A da k'awayenta komawa gidan Barrister Z a can suke nasu
shirye-shirye.
***---****---****
_RANA BATA K'ARYA_

musu iya magana suka ce saidai uwar d'iya taji kunya, daren yau da misali k'arfe
9:00pm za'a yi Fulani night tun wayewar gari ake yi wa barrister A gyaran jiki daga
ciki har da k'umshi na zane lalle baki da ja, abinka da farar fata lalle ya yi
dass....a fatar hannunta da k'afafunta duk wannan shirye-shirye da suke hankalin
barrister A atashe yake, sakamakon rashin jin d'uriyar ango tun daga ranar da ya zo
ko a waya bai kirata ba.
Sai ma ita ce ta kirashi sakamakon alert na mak'udan kudad'e da ta gani daga
gareshi, kiran nata ma k'in d'agawa ya yi sai d'an guntun text da ya turo mata I'm
busy I'll call you later, bai kuma kirata ba hakan ba k'aramin kada mata anta
jikinta ya yi ba, har yamma lis bata ji daga Aliyu ba zai zo ko ba zai zo ba, sosai
tasha jinin jikinta.

Kasa hak'uri tayi taja Barrister Z agefen ta kora mata bayanin damuwarta, shiru
Barrister Z tayi kafin ta ce ko za mu kirashi ne da sauri Barrister A ta girgiza
kai, ba za mu kirashi ba saboda zai dauka kamar na damu da shi ne.
Ya zo ko kar zo duk uwarsu d'aya ubansu d'aya awurina duk irin zaman da ya tanada
mana shi za muyi, koda sonshi zai yi ajalina ba zan ta6a zubarda ajina na bishi ba.
Karki ce haka Minal komai na duniya a hankali ake binshi sai ka ga ka ci ribar
abin.
Cewar barrister Z.

"Ba za ki gane ba Zarah duk aure da aka gina shi ba soyyayya dama hakan zai faru.
murmushi barrister Z tayi ta kuma rik'o hannun barrister A, karki matsantawa kanki
da yawa bebs Allah ya na tare da mu, insha Allah komai zai tafi yadda mu ka tsara.
Nodding head kawai barrister A ta yi.

Misali k'arfe 8:30pm amarya ta sha makeover cikin kayan Fulani na sak'i royal blue
in colour, ba k'aramin kyau kayan suka yi mata ba musanmman yadda wuyanta ya sha
sark'a tsakiya na duwatsu masu launi dabam-dabam sosai ta fito bafullatana.
Yayin da k'awayeta su ma sun had'e cikin kayan Fulani saidai nasu farare ne.
Tuni motoci suka fara daukar mutane zuwa hall d'in da za'a yi events d'in.
Har zuwa lokaci barrister A bata ji daga Aliyu ba, sai k'ok'arin danne abin take a
ranta saboda bata so mutane su farga su gano halin da take ciki.


_Fans ba yawa Just to manage_


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*

*16*

Daga ita sai fadila ne a cikin mota har suka iso hotel d'in zuciyarta a cakud'e,
direba nayi parking k'awayeta suka lullu6e motar.
lokaci da take k'ok'arin fitowa daga mota barrister Z ta kutso ta matsa daf da ita
ta rad'a mata, Aliyu yafi almost 10 minutes a mota yana jiran zuwanki.
"Ajiyar zuciya ta sauke wani irin dad'i ya ziyarceta, tana gama fitowa Aliyu ya
fito daga nashi mota sanye cikin tsadaddiyar shadda fara tass....kanshi sanye da
hula zanna bukar, lokaci da suka had'a idanu ba k'aramin kyau ya yi mata ba.
Yayin da shi ma yake yaba tsan-tsa kyau da ta yi.
"D'an siriri murmushi ya saki mata, ta mayar mishi da martani har da k'arin
lumshe idanu.
Saboda murmushi nashi ba k'aramin awon gaba da ruhinta ya yi ba.
Ga mamakinta ya na k'arasowa kusa da ita ya rik'on palm d'inta cikin nashi, sai
kuma ta kawarda mamakin nata sakamako tunawa da ta yi Aliyu wayayye ne ya kuma
wadatu da ilmin zamani, don ya rik'o tafin hannunta baya nufi komai a wurinshi.

"Suna shiga hall Siblings sisters d'inshi suka mik'e suka nufo su, sosai
Barrister A ta burge su musanmman Meena da ta k'asa 6oyewa saida ta furta ta hanyar
cewa wow....tubarakallah masha Allah you're so beautiful sister in law.
Kalamanta ya sa barrister A ta gano sister din Aliyu ce ta yi mata murmushi had'e
da furta thanks!
You're highly welcome.
Cewar Meena.
Wurin da aka tanada domin su suka zauna aka soma gabartada da programs d'in, anyi
rawa an kuma zuba naira ba kad'an ba sai around 12:30am aka tashi kamar yadda suka
shiga hall rik'e da hannu juna haka suka fito har mota ya rakata, duk wanda ya ga
yadda yake bata kulawa zai dauka akwai soyayya mai k'arfin gaske atsakaninsu.
Da kanshi ya bud'e mata k'ofar mota tana murmushi ta zauna ta dube shi cike da
kulawa ta ce "Good night!
Saida ya haskata da tsadadde murmushinsa sannan ya amsa da "Good night nd have a
nice dream.
Yatsunta ta guda biyu ta d'aga mishi had'e da furta bye da haka direba ja mota suka
tafi, ya kalli Jamal da ke tsaye a gefe yana kallonshi ya ce mu tafi ko?"
Suna tafiya Jamal ya ce gaskiya abokina ka yi dace da mata kyakyawar gaske ba ko
shakka za ku haifa mana kyawawan yara.
Aliyu ya yi dariya marar sauti ya ce ni fa har yanzu ban ji son barrister a
zuciyata ba, ga kuwa zai yi matuk'ar wahala ku sami yara.
"Jamal ya ja tsaki mtsss.....kafin ya ce wai kai wane irin tintirin d'an iska ne
me zuciyar dutse?"
Ba zaka gane ba Jamal shi so ba mutum yake dasa shi a zuciya ba, Allah ne yake
jarabta d'an Adam da shi.
Murmushi Jamal ya yi ya ce zancenka haka yake, amma akwai sakawa rai idan har ka
sakawa ranka soyayyar barrister ba za'a dauki dogon lokaci za ka afka a sonta, ko
don kyau halinta.
"Girgiza kai kawai Aliyu ya yi sakamakon yadda ya fahimci duk abin da zai fad'a
ba lalle bane abokin nashi ya fahimce shi ba shiyasa ya ja bakinshi ya tsuke.
***---****---****
*WASHE GARI*

Akayi mother night wanda har iyayyensu sun je, sai lokaci momma ta ga barrister A
duk da girls d'inta sun ba ta labarin kyawonta har da nuna mata pics d'inta, tsabar
takaici ya hanata kallon pics d'in.
Sosai momma ta firgita lokaci da ta yi arba da barrister A cikin wedding gown
golden in colour, kanta dauke da bridal turban Royal blue colour, yayin da Aliyu ke
sanye da farar shadda as usual sai dai ta yau babbar riga ce kamar yadda ya rik'o
hannunta a events d'in jiya haka ma yau suka shigo, ba k'aramin kad'awa hanta cikin
momma ta yi ba.
Ba abin da take sai zufa K'awarta Dijama ce, tadawo da ita natsuwarta ta hanyar
cewa lafiya Zaituna duk sanyi Ac da ke wurinan naga ke sai had'a gumi ki ke?"
Wasu yawu masu masifar d'aci ta hadiye tashiga kame-kame uhm....uhm.....lafiya
qalau kawai sanyi wuri ne bai wadace ni ba.
Ta6e baki Dijama ta yi had'e da yatsine fuska kafin ta furta kedai ba kya rabuwa da
zance wofi, ko munafuki ba zai ce wurinan da zafi ba.
"Batare da momma ta kula ta ba gaba d'aya hankalinta ya raja'a da kallon Aliyu
da barrister A, da ke ta faman zabga murmushi suna gaisawa da jama'a bata ankara ba
har suka iso gunta, zazzak'ar muryar barrister A mai shegen dad'i ta dawo da ita
hankalinta da kyar momma ta iya controlled kanta, ta amsa gaisuwar da Barrister A
take mata.
"Tsabar kwarewa da bariki yasa momma ta mik'e ta had'e su duka ta rungume, sai
faman zuba musu albarka take sosai Barrister A ta ji dad'i a tunaninta uwar mijinta
na sonta, har suka nufi high table suka zauna momma ta na cikin tashin hankali
saboda har ga Allah ba ta dauki za ta ga barrister A haka ba. kyawo da wayewar
yarinya suna neman zuzuta tunaninta.
Lokaci da mc ya umarce ango da amarya su fito filin domin su taka rawa, gudun
abin fad'a yasa momma ta fito tana yi musu lik'i ita ma Ummi ba'a barta a baya ba.
"Kud'in da Abban barrister A ya zuba fad'arsu ma k'auyanci, ne gudan aure shalele
shi dole naira ta koka.
Kasancewar events d'in yau ya kera na jiya yasa sai around 1:30am aka tashi, yau ma
sai da Aliyu ya raka barrister A a wajen mota sannan suka yi sallama.
A washe gari misalin k'arfe 2:30pm ana gama sallar juma'a aka daura auren Aliyu
da barrister A akan sadaki naira dubu 100, daurin aure da ya tara duban jama'a.
Misalin k'arfe 5:00pm Ummi ta shirya walima ta musanmman a gidanta, wanda mata
manya suka halarci wurin anyi wa'azi mai shiga jiki akan zamantakewar aure daga
bisani aka ci abinci serve yourself duk abin da ranka yake so za ka ci idan za ka
wuce abaka jakka mai dauke da pic d'in ango da amarya, acikin jakka har da atamfa
ak'allan kud'inta za su kai 6k.
*9:45pm*
k'anwar Abba ta fito da barrister A lullu6e cikin farar lafayya ko fuskarta ba'a
gani, ga wani k'amshi na musanmman da take yi direct setting room d'in Abba aka
wuce da ita sosai Abba ya yi mata nasiha, daga bisani ita ma Ummi tayi mata.
"Abin mamaki Ummi nagama mata nasiha Abba ya rik'o hannunta ya kalli k'anwarshi
mai suna Maimuna ya ce mu je Maimuna ki rakani na kai, 'yata d'akinta.
Jin furucinshi yasa mamaki ya rufesu sanin halinshi da suka yi yasa ba su
tambaya ba, dole Maimuna ta mik'e tana rik'e da barrister A wacce ke ta faman
shasshak'ar kuka, Abba da kanshi ya yi driving da suka iso gidan, har cikin bedroom
d'inta ya kaita sannan ya yi mata sallama ya fito, sai daga baya k'awayeta suka iso
wanda sosai abin da Abba ya yi yai matuk'ar burgesu.



Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*17*

Misali k'arfe 10:30 na dare ango Aliyu ya iso tare da tawagar abokanshi, bayan anyi
wasa da dariya kowa ya kama gabanshi, Aliyu yana dawowa daga raka su ya rufe k'ofar
main parlour ko kallon d'akinta bai yi ba, ya nufi master bedroom d'inshi da ke
upstairs.
"Gyagyad'i tafara daga zaune hakan yasa ta tashi da kyar saboda tsananin gajiya
ga Kuma bacci da ya cika idanuwanta.

Ta cire kayan jikinta ta maye gur6insu da wata pitch colour nightgown wacce ta
tsaya iya gwiwarta, ta tufke gashinta wurin d'aya tabi lafiyar gado bata matsantawa
kanta da dogon tunani ba, shiyasa barci ya yi sauri dauketa.
"Washe gari sai misali k'arfe 11:00 na safe ta falka inda Allah ya taimaketa
tayi sallar asuba, agurguje ta gyara bedsheet ta kunna burner ta zuba turaren wuta
d'akin ya dauki sanyayye k'amshi sannan tanufi bathroom tayi wanka.
Simple makeup tayi fuskarta sai glowing take yi.
Tasaka wani tsadadde lace jikinshi marrow colour anyi mishi Zane flowers baby
pink da sky blue style d'in doguwar riga sosai kayan suka k'awata kyakyawar surar
jikinta, tasaka half cover baby pink in colour bata daura d'an kwali ba sai tayi
using d'an siriri veil ta yane dogon bak'in gashinta.
Jikinta na fitarda k'amshi na musanman, ta dauki wayoyinta had'e da burner ta
nufi parlounta nan ma ta k'amsashi, daga bisani ta sauko downstairs parlour komai
na parlour White colour ne.
Tayi tsaye tana kallon tsari parlour ta gyad'a kanta a zuciyata tana yaba yadda
Aliyu yake matuk'ar so White colour.
Burner ta jona ta sake zuba turare ta shiga arranging throw pillows d'in da ke kan
kujeri.
"Daga bisani ta nufi kitchen tasaki murmushi hatta da kitchen cabinet fari ne
tass....ta lek'a store cike yake taf da foodstuffs iri dabam-dabam.
Ta dawo parlour ta zauna akan one sitter ta dauki phone d'inta ta bud'e data, ta
shiga handle d'inta na Instagram tana karanta comments d'in well-wishers, hanci da
dodon kunnenta suka ji footsteps da k'amshi desingner perfumes d'inshi gabanta ya
shiga dukan tara-tara.
"Kasa d'agowa tayi har ya k'araso cikin parlour ya sha ado da dakakkiyar
shadda fara sai walk'iya da daukar ido take.
K'afarshi sanye da fari sandal kanshi ba hula amma ya gyara sumar kanshi ta
kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa.
Hannayenshi zube ciki aljihun wandonshi ya nemi sofa da ke facing d'inta ya zauna
ya yi crossing legs d'inshi, sai wani shan k'amshi yake.
"Sai lokaci ta d'ago ta d'an zame daga kan kujera, cikin muryarta mai d'and'ano
gaske ta ce ina kwana?"

"Saida ya k'are mata kallo ta k'asan ido a zuciyarshi yana yaba tsananin kyau da
tayi, cikin k'asaita ya amsa da lafiya qalau kintashi lafiya?"
"Lafiya qalau Alhamdulillah!
Ta amsa mishi, komawa tayi ta zauna daga haka ba Wanda yasake cewa da d'an uwanshi
ci kanka.
Ita tana operating phone d'inta shi Kuma yana girgiza k'afarshi a hankali, knocking
d'in k'ofa akayi ya yi kamar bai ji ba, cigaba da knocking akayi da d'an k'arfi
still ko motsawa bai yi ba balle tasa ran zai tashi, kallonshi tayi a tsanake, taga
tabbas ba shida niyar tashi gani yadda ya kwanta akan kujera hadda su lumsashe
idanuwa.

"Ta6e baki tayi kafin tace Yalla6ai ana knocking.

Shiru bai amsa ba sake mai-maitawa tayi cikin d'aga murya Yalla6ai ana knocking.
"Bud'e idanuwanshi ya yi ya zuba su akan fuskarta ya d'age girar ido, kasa jure
kallon eye's ball d'inshi tayi ta kauda fuska, ya yatsine fuska yace wai waye da
wannan sanyi safiya zai nemi

8 / 26