Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gidan Rina Complete Hausa Novel by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  Drama

Chapter   9 / 26

24K to 27K   out of 76.6K words

ya takurawa mutane?"
Nifa Allah banaso damuwa mtsss....yak'arasa magana da jan tsaki.
"Saida ya gama jan ajinshi kamar mace sannan ya mik'e ya nufi k'ofar yayin da
barrister A ta rakashi da idanu, Kai wannan guy akwai yanga kalli yadda yake tafiya
tafad'a a k'asan zuciyarta.
"Yana bud'e k'ofa yaci karo da Isah direba tsaye dauke da basket da warmer a
hannu, barka da asuba maigida"
Cewar Isah direba yana murmushi.

Harara ya zuba mishi maimakon amsa gaisuwar tashi, cikin shan k'amshi ya ce Isah
banaso tsohon iskanci, gidan bak'onka ne da za ka tsaya kana min knocking?"
"Allah ya huce zuciyar maigida gani nayi bai kamata na shigo gaba gad'i, a
gidan ma'aurata ba izzini amma tuba nake yi ayi min afuwa.
"Shiru ya yi yana kallon Isah kafin ya ta6e baki ya ce dallah malam wuce ciki
banaso iyayi tsiya.
Ya wuce gaba Isah yana biye da shi ina kwana amarya?"
Cewar Isah yana washe hak'ora.
Cikin fara'a ta amsa da lafiya qalau ta mik'e ta kar6i warmer d'in hannunshi, ta
nufi dining area yayin da Isah ya bita rik'e da basket.
Ta ajiye warmer akan dinning table ta kar6i basket d'in had'e da furta sannu da
k'ok'ari an gode.
Yauwa amarya!
Isah ya fad'a had'e da juyawa ya koma parlour, cikin girmamawa ya ce maigida ko
kana da buk'atar wani abu na tsaya?"
"Girgiza Kai ya yi na barka lafiya Isah ya fad'a had'e da nufar k'ofar fita.
Saida ta dauko plate da mugs had'e da spoons a kitchen, sannan ta shiga bud'e
warmers d'in ta farko wainar shinkafa ce tayi laushi har ta gaji ta bud'e ta biyu
miyar taushe ce taji tantakwashi, k'amshi ya buge hancinta, sai guda d'aya mai
dauke da chips da fry plantain sai sauce d'in Koda da hanta ya ji karas da cabbage,
sai flakes mai dauke da kunu gyad'a yaji Madara fari kal....da shi ga Kuma farfesu
kayan ciki da na cow tail ta gyad'a kai ciki da yabawa, dole ta koma parlour domin
ta Kira d'an iko nata ya zo ya yi breakfast.
"Yalla6ai nayi arranging table ka zo kayi breakfast.

"Saida ya yi mata kallo na nashi na d'age girar ido kafin ya gyad'a kai, tsaye
tayi tana jira ya tashi Saida ya gama jan ajinshi sannan ya mik'e tabi bayanshi, da
sauri ta jawo mishi kujera ya kalleta ya yatsine fuska da sauri ta kauda nata
fuska, ya zauna ta dauki plate batare da ta kalle shi ba ta ce akwai waina da chips
wane za'a zuba maka?"
"Bana cin abinci mai nauyi.
Ya fad'a batare da kalleta ba.
Na zuba ma chips kenan?"
Ya gyad'a kai.
Ta zuba ta ajiye a gabanshi.
Ki je store ki dauko kayan tea ki had'o da nessacoffe.
"Yana gama magana ya koma jikin kujera ya lafe, ya Kuma yi folding hannayenshi
a kirji.
Mamaki ne ya lullu6eta gani yadda ya yi mata magana cikin izza da gadara, bata ce
komai ba ta tafi store ta dauko abinda ya buk'ata tea za'a had'a maka?"
"Coffee!
Ya fad'a a takaice.
Ta shiga had'awa za ta zuba sugar ya ce bana shan sugar, honey za ki zuba.

"Shiru tayi na seconds kafin ta ce ina zuma yake?"

"Ki je store ki duba.

"Dole ta koma store da kyar ta gano idan Zuma yake ta dauko, ta zuba tea spoon uku
ta juya ta ajiye mishi.

Na waye?"
Ya furta can k'asan mak'oshi.

Me kenan?"
Tafad'a tana kallonshi.
Coffee!
Ta hadiye yawu kafin ta ce naka ne.
Humm.... barrister bana Shan zak'i sosai Zuma da ki ka zuba ya yi over.
Yanzu kam sosai taji ranta ya6aci ya fara kaita bango da reni wayonshi, da kyar
tayi control temper ta ta ce Yalla6ai miyasa tun farko da nake had'awa ba ka
fad'amin adadin Zuma da zan zuba ba?
Ya d'ago idanuwanshi Yana kallonta gira d'age yayin da ta kauda fuska.
Ya ce had'a coffee yana miki wuya ne?"
Girgiza Kai tayi.
To sake had'a min wani banaso musu.
Batare da ta ce komai ta dauki wani mug ta sake had'awa, ta kalle shi ta ce spoon
nawa zan zuba na honey?"
Yatsanshi guda ya d'aga ta6e baki tayi ta d'an juya coffee ya rage zafi ta ajiye
mishi, sannan tayi serving kanta waina ta zuba ta ci ya rigata tashi duk da ta lura
bai wani ci abinci kirki ba.
Tana kammalawa ta kwashe plates d'in suka yi using ta nufi kitchen ta wanke, sannan
tadawo parlour Koda ta shigo Yana waya Yana gama waya ya mik'e ya dubeta ya ce ni
zan fita.
Muryarta asanyaye ta ce adawo lafiya.
Har ya juya ta ce Yalla6ai karka manta ajima around 9:00 o'clock za mu tafi dinner
da abokan aikina suka shirya mana.
"Ya juyo ya k'ura mata idanu kamar mai nazari, ta sunkuyar da Kai k'asa.
Wai ke har yanzu bidi'o'i naki ba su gadi k'arewa bane?"
Yalla6ai ba wani bidi'a abinci ne kawai za'a ci a wuri, don Allah ka taimaka min mu
je idan ba mu muje ba zasu ga kamar na musu wulak'anci.
Ta k'arasa magana kamar za tayi kuka.

Batare da ya ce da ita zai je ko ba zai je ba yai tafiyarshi, ranta ya sosu ba
kad'an ba saidai batada yadda zata yi ta zuba tagume ta afka tunanin irin zaman da
za suyi domin tun tafiya bata yi nisa ba tafara gajiya da halaye Aliyu.




Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO

*Haske writers association*

*GIDAN RINA*

_this page is for you Rahinerth alk'aluma shidda suna jin dad'in comments
d'inki keep its up dear!_

*18*

Zuwan barrister Z gidan ya rage mata tunanin Aliyu, nan take ta bata labarin yadda
tayi da shi.
Karki damu bebs ko wancan karon haka ya yi mana kamar ba zai je ba, sai gashi duk
events d'in da akayi ya yi attending.
"Ki saki ranki inshallah ko wannan zai je, Aliyu bahagon mutum ne ba kasafai ake
gane idan ya dosa ba.
Yakamata ki jajirce zama da irinshi sai an shirya.
"Talla6e kumatu tayi tana kallon barrister Z kafin ta ce ni zan gayamiki bebs
yau da safe wurin breakfast kawai saida ya haddasa min headache, labari abinda
yafaru ta shiga gayawa Zarah.
Dariya sosai barrister Z taci tabbas bebs Aliyu ne dai-dai ke kina tak'ama
miskilanci sai gashi kin had'u da Wanda yafi ki.
Bari kawai bebs na had'u da gamo na.
Gaskiya kam bebs kin had'u da gamonki sai hak'uri.
Dariya suka yi daga bisani suka mik'e suna zagaya gidan, yayin da Barrister Z sai
yaba kyau da tsarin gidan take.

*****""'***""******
Tun misali k'arfe 7:00pm wacce za ta yi wa barrister A makeup d'in zuwa dinner ta
zo, kuma har zuwa lokaci Aliyu bai dawo gida ba.
Saida ta sallaci sallar isha'i aka fara tsantsara mata makeover, black gown tasaka
aka nada mata bride turban White colour, tayi kyau na ban mamaki saidai duk
zuciyarta a chakud'e take sakamakon rashin sani manufar angon nata.
Sai k'arfafa mata gwiwa Barrister Z take duk da haka hankalinta bai kwanta ba.

Lokaci sai ta tafiya yake dole tafito, barrister Z na biye da ita har suka iso
parking lot, da sauri Isah direba ya bud'e mata mota kirar jeep Volkswagen farar
tass....da ita tana danna kanta ta gashi zaune ya yi relaxing sai faman operating
wayarshi yake, k'amshi perfume d'inshi ya cika motar.
Batasan lokaci da tasaki ajiyar zuciya ba.
"Batare da ya kalleta ba ya ce barrister ga ki da son bidi'a amma bakida kama
jiki, almost 20 minutes ina zaman jiranki har nafara tunani ko kin fasa zuwa dinner
ne, na kama gabana.
Saida ta zauna kusa da shi ta kuma k'are masa kallo, sannan ta ce lamarinka sai kai
Yalla6ai tunani bai bani za ka je dinner ba.
Sai gashi har zaman jiranki nayi.

Ya karasa magana yana ta6e baki tare da cewa wai Isah me kake jira ne da ba za ka
ja mota mu tafi ba?"
Umarninka nake jira maigida.
"To na ba ka umarni sai ka ja motar mu tafi, kana k'ara 6ata mana lokaci.
A tunaninta idan ya gama magana da Isah zai kulata sai taga sa6ani hakan.

Don haka ita ma taja bakinta ta tsuke Bata k'ara cewa uffan ba har sanda suka iso
hall d'in, suna fitowa ya rik'o hannunta suka k'arasa ciki hall, dinner ta
k'ayatarda Aliyu matuk'a a cewar shi duk events d'in suka yi ba wanda ya burge shi
irin dinner d'in, saboda ba hayaniya sai slow music ke tashi anci ansha anyi
couples dance sai kusan 1:00am aka tashi kowa ya kama gabanshi.

"Tun a mota tafara bacci har suka iso gida bata saniba, tasheta Aliyu ya yi ta
hanyar cewa barrister ki tashi mun iso gida.
ko motsawa bata yi ba ji ya yi zai iya tafiya yabarta anan, har ya bud'e mota ya
fita ko me ya tuna sai dawo gefen da take, ya shiga bubbuga hannunta da k'arfi bugu
d'aya zuwa na biyu ta bud'e idanunta masu cike da bacci.
"Fahimta abinda ke faruwa tayi shiyasa bata furta uffan ba tafito tana rangaji
tana had'a hanya ta nufi cikin gida, dai-dai k'ofar shiga main parlour ta kusa
fad'uwa da sauri ya tarota ya rik'o shoulder ta, ya d'an rungume rabin jikinta
yayin da ya sak'ala d'ayan hannunshi akan waist d'inta.
"Wani irin kunya taji ya lullu6eta sakamakon yadda ya rungume waist d'inta nan
take ta wartsake daga baccinta, a haka suka cigaba da tafiya har zuwa bedroom
d'inta.
A gefen gado ya zaunar da ita ya kalleta ta k'asan ido ya ga yadda take lumshe
ido alamar bacci bai gama sakinta ba, ya ce kiyi k'ok'ari ki rage kayan jikinki za
ki fi jin dad'i kwanciya.
Daga haka ya juya har ya murde handle ya d'an juyo cikin wani irin murya ya furta
"Good night!
Murmushi tayi kafin ahankali ta ce "Good night!
Haka kawai ta tsince kanta cikin nishad'i marar misaltuwa, umarninshi tabi ta
hanyar sauya kaya zuwa sleeping dress.
****""***"""'*****
Washe gari!

Kasancewar gajiya tayi musu yawa hakan ya basu damar yin bacci, Kuma da yake daga
gidan Daddy ake kawo musu abinci.
"A kwana na shidda da bikinsu tana zaune a falonta tana tunani fara girki a yau,
saidai batasan miye favorite d'inshi ba.

Gani za ta wahalada kanta a banza yasa ta mik'e ta nufi falonshi da ke upstairs, ta
tura k'ofar ta shiga da sallama zaune ta sameshi yana aiki a system.
Jin motsi bud'e k'ofa da kuma k'amshi fitinane turareta ya bugi hancinshi, yasa
d'ago da kansa ya kalleta sai kuma kauda kai ya cigaba da aikinshi.
Cikin tattausan lafazi ta ce barka da hutawa Yalla6ai!

Saida ya6ata almost 20 seconds kafin ya amsa da yauwa ya akayi ne?"

Yalla6ai dama zuwa nayi na sanarda kai yau inaso nafara girki da kaina, saidai
bansan abinda ka fi so ba.
"Uhm!
Ke nan kin iya girki ne?"
Bata yi mamaki tambayarshi ba saboda tasan fiye da hakan ma, zai iya aikatawa.
"Ba laifi ina k'ok'artawa.
Uhm!
Ba ki iya ba kenan?"
Sai an bani dama anan za'a gane iyawa na.
Ki yi hak'uri da girki nan har mu je Abuja, tsananin dad'ewarmu a garinan ba zai
wuce 7 days ba.
Shikenan tunda haka ka za6a na barka lafiya, takarasa magana had'e da ficewa.
Bayanta ya bi da kallo kafin dawo da ganinshi akan system.
Haka zamansu ya cigaba da kasancewa kowa yana sha'anin gabanshi, tun abin yana
damunta har ta zo tafara sabawa dama tasan baya sonta, bata tunani zai so ta koda
zuwa gaba ne.
Shiyasa tayi hak'uri da yadda ta tsince kanta aciki, ko ba komai ta fitarda
iyayyeta kunya, ta kuma yi musu biyayya dama kuma ance bin na gaba bin Allah.

***'"***'"***'''***
Da misali k'arfe 5:00pm na yammacin ranar tana zaune a falonta, Indian series take
kallo, text ya shigo wayarta a zatonta ko alert ne.

Saboda tana expected d'in wasu kud'ad'e da azama ta dauki wayarta, ta shiga inbox
*ki shirya za mu je ki yiwa su momma bankwana tomorrow morning za su wuce Abj ki
shirya yanzu nan karki 6atamin lokaci*
Murmushi tayi had'e da girgiza kanta ganin yanzu nan ya wuce ta, amma tsabar ya
tsaneta ba zai iya yi mata magana ba shine yake turo mata text.
"Ta tashi jiki asanyaye tashiga bedroom d'inta ta canza kaya zuwa wata French
gown, maroon colour tayi rolling da white scarf, tasaka takalmi heel tafito rik'e
da 'yar k'aramar purse d'inta a hannu sai zuba k'amshi take.



Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:59 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*



*19*
A main parlour ta tararda shi tsaye yana jiranta, yana sanye da fari material na
maza wanda ya yi masifar k'ara fitowa da kyakyawar halittarshi, tana fitowa yafice
zuwa parking lot.
Tabi bayanshi tuni Isah direba ya jawo mota, ya fito ya bud'e musu k'ofa suka
shiga yaja motar suka fice daga gidan.

K'amshin perfume d'inshi ya garwaye da nata ga kuma sanyi Ac motar, ya had'e ya
bada wani daddad'an k'amshi mai tafiyar da ruhi da gangar jiki.

"Tafiyar kurame ce ake yi daga shi har ita ba wanda ya furta uffan, afakace ya
sace kallonta ya dauke fuska.
Gani ba girmanshi bane satar kallonta yasa ya fito da wayarshi ya kira wani
business partner d'inshi.
"Hakan yasa ta mayarda hankalinta ga kallon gefen titi.

Koda suka iso gidan ya wuce gaba ta bi shi abaya har zuwa sitting room d'in gidan,
anan suka iske momma zaune da alamar tasan da zuwan nasu.
Barrister A ta durk'usa har k'asa gwiwa biyu-biyu ta gaidata.
"momma wacce ke hakince akan two sitter tana shan k'amshi wanda atsawon
rayuwarta ba'a ta6a gaidata haka ba.
"Kauda fuska tayi tana wani yatsina, ta bud'e baki da kyar ta amsa da kina
lafiya?"
"Lafiya qalau!
Cewar barrister A da yake ita ba k'aramar yarinya bace, ta hango tsan-tsan
kiyayyarta a kwayar idon momma.

Shi kanshi Aliyu bai ji dad'i yadda momma tayi mata ba, shine ya yi k'arfin hali
cewa tashi ki zauna akan kujera.
"Girgiza kai tayi ta gyara zamanta akan rugs carpet ta sadda kai k'asa, girls
d'in momma na shigowa falon suka yi arba da ita suka sa ihu, har rige-rige zuwa
wurinta suke.
"Hatta Teema da batada lafiya dariya take tana tafa hannayeta, tana jujjaya
kanta alamar tana farin ciki ganinta.

"Sai lokaci ta d'an saki jikinta, tana murmushin yak'e, hannunta Teema ta
k'ank'ame sai faman lek'e fuskarta take tana dariya.
"Sosai haushi ya turnuk'e momma gani yadda girls d'inta suke tarairayarta, tsawa
ta daka musu kai miye haka?"
Dallah ku ja Teema ku koma d'aki.
Kuka Teema tasa tana bubbaga k'afa a k'asa tana cewa momma ke muguwa ce, ki barni
na ganta ina sonta tana da kyau.
Ran momma ya k'ara 6aci afusace ta mik'e ta finciko Teema daga jikin barrister A,
taja ta kamar kayan wanki ta kaita d'aki ra rufe tadawo ta kalle zee-zee da meena
da ke tsaye wuk'i-wuk'i ta daka masu tsawa, nace ku 6ace min da gani shasshashu
yaran kawai kun zo za ku takurata.

"Da gudu suka nufi bedroom d'insu, duk abinda take ko ci kanki Aliyu bai ce da
ita ba, za ka ma dauka baya cikin sitting room d'in.
Hankalinshi kwance ya ce momma ga wifey ta zo yi muku bankwana, saboda na gayamata
gobe da safe za ku koma Abj.
"Yak'arasa magana cikin halin ko in kula d'inan.
Duk cikin zanceshi kalmar wifey ce tafi k'onawa momma rai, jin take kamar ya soka
mata mashi a k'ahon zuciya.
"zuciyarta kamar za ta fad'o k'asa tana murmushin dole ta ce, sannu daughter da
fatan kina kulamin da yarona?"
Kinsan ba son aure yake yi ba dole ne akayi masa, idan bakya bashi kulawa komai zai
iya faruwa, dole ki zage dantse ki bashi kulawa ta musanmman ko Allah zai sa kisami
fili koda d'an k'ank'ani ne a farfajiyar zuciyarshi.
"Duk sanyi da ke falon bai hanawa barrister A shar6ewa da gumi ba, atarihin
rayuwarta ba'a ta6a ci mata fuska a wulak'antata irin wannan ba, zuciyarta har
tuk'uk'i take yi mata.
"Gani shirme da momma take yasa Aliyu ya yi sauri mik'ewa ya isa wurin barrister A
ya rik'o shoulder ta ya mik'arda ita tsaye, yana kallon cikin idanuwanta.
"Gani yadda suka canza kala tausayinta ya kamashi yasan momma ta wulak'antata ba
kad'an ba.
"Wifey mu je upstairs parlour ki gaisa da Daddy!
Har suka takala steps yana rik'e da ita momma tabi su da mugun kallo tana kintsa
mugun nufi akan barrister A.
Sosai Daddy ya tar6eta yasaki jiki sai janta da fira yake, yana tambayarta akan
abinda ya shafi aikinta, hakan yasa tasaki jikinta ita ma tana bashi amsa, nan take
taji k'aunar dattijo ta cika ciki da wajen zuciyarta.
Fuskar Daddy dauke da murmushi ya k'ara duban barrister A ya ce "Da fatan ba dai
wata matsala atsakaninku?"

"Cike da kunya ta girgiza kanta ta ce ba komai Daddy Alhamdulillah muna zaune
lafiya.
"Masha Allah haka nakeso ji, ayi ta hak'uri da kuma biyayya don a cigaba da samun
zaman lafiya.
Insha Allah Daddy mun gode Allah yak'ara girma da nisan kwana.

Daddy yasaki murmushin jin dad'i zuciyarshi cike da farin ciki ganin d'anshi ya
mallaki iyali kamar kowa yanzu kam, hankalinshi ya kwanta sai kuma addu'a samun
zuri'a dayyaba"
"A shagwa6e Aliyu ya turo baki ya ce uhm.....Daddy tun dazu da ita kadai ka ke
fira ni ka wareni, kamar ba kasani ba.
Dariya Daddy ya yi kafin ya ce kadai ba ka rabuwa da rigima gadanga, ba ka gani ita
ce bakuwa ko ba kasan bako rahama ne ba dole a girmamashi?"
"Sake turo baki ya yi ba wani nan Daddy nagano so ka ke ta kwace min fada
awurinka.
Ba daddy kadai ba hatta barrister A saida ta dara.
Sosai sagarta Aliyu ya burgeta k'ato da shi yana shagwa6a, ta tuna yadda ita ma
take yiwa Abbanta, duk girman mutum a gaban iyayyenshi k'aramin yaro yake komawa.
"Amina kina ji na da

9 / 26