Author : Jidda Aliyu Category : Drama
wannan rigimame mijin naki ko?"
Sadda kanta k'asa tayi cikin sanyi murya ta ce rabuda shi kawai Daddy ai ya riga
yaci lokacinshi, a wurinka yanzu lokacina ne.
"Shigowar momma ya katsi musu nishadinsu, ko zaunawa bata yi ba ta ce kai Sultan
tashi ku tafi gida babu kyau mace tayi sallar magarib ba k'ofar d'akinta ba.
Mun gode da ziyara ku gaida gida.
"Daddy ya daure fuska ya ce korarsu ki ke yi?"
Wai kin ma basu ruwan sha?"
Kafin ta bashi amsa Aliyu ya mik'e da sauri ya ce Daddy bari mu wuce Allah ya tsare
hanya ya kai ku lafiya sai mun zo.
"ita ma mik'ewa tayi tai musu sallama tafice Daddy ya dauko bundle na 'yan one
thousand ya mik'awa Aliyu gashi ka ba wa matarka, mun gode Allah ya ba ku zaman
lafiya, Allah yak'are ku da sharrin mahassada.
"Amin Daddy cewar Aliyu ya juyo wurin momma ya ce mun tafi.
Ku gaida gida.
Tafada kamar za tayi bindiga.
"Koda ya fito tuni har ta shiga mota shi ma ya shiga Isah ya ja motar suka
tafi.
Akan hanyarsu ya doura mata kudin da daddy ya bata akan cinyarta, ya ce inji daddy
ya ce abaki.
Nagode Allah yasaka mishi da alkhairi
Amin!
Yafad'a yana kallonta kauda fuskarta tayi tana murmushi k'asa-k'asa.
Suna isowa gida ta wuce sashen tayi wanka had'e da alwala saida ta sallace sallar
isha sannan ta tashi, ta shirya cikin Indonesia straight silk gown ta yane kanta da
scarf, ta sauko downstairs parlour bata jima da zama ba ya shigo sanye da farar
jallabiya mai gajeren hannu.
"Sannu da zuwa!
Tafad'a cikin cool voice.
Yauwa Yafad'a batare da ya kalleta ba ya cigaba da cewa idan kina jin yunwa akwai
abinci akan dining.
"Daga haka ya haura upstairs yabarta da kallon bayanshi, girgiza kai tayi taji
koda yunwa za ta kasheta ba za ta ci abinci ba gara ta kwana da yunwa.
"Kitchen ta wuce ta had'a coffee ta shige bedroom d'inta tana gama shan coffee,
tayi brush tabi lafiyar gado saidai da kyar tasami bacci sakamakon yadda tunanin
momma ya rufeta ga kuma na uban gayya, ita kam ta shiga uku wannan wane irin aure
ne tayi?"
****"""****"""***
Washe gari sai misalin k'arfe 11:14am tafito downstairs parlour, waya take yi da
wani client d'inta ya shigo sanye da white sport wears k'afarshi sanye da sneakers
farare, dawowarshi kenan daga jogging.
"Ina kwana Yalla6ai?"
Ya tsaya cak....yana kallonta girar ido d'age daga bisani ya ce ya akayi jiya ba
kiyi dinner ba?"
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA NA KUD'I NE IDAN
KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*20*
Murmushi tayi kafin ta ce bana jin yunwa shiyasa ban ci ba, amma before in kwanta
nasha coffee.
"Ta6e baki ya yi had'e da mak'e kafad'a irin I don't care d'inan ya k'arasa haura
steps.
Ta bi shi da kallo tana tausayin kanta yadda ta tsunduma soyayyar mutume da bai ma
san tana yi ba.
Ta rafka d'an uban tagumi, k'amshin turarenshi yadawo da ita natsuwarta ta bishi da
kallo har isa dining area bata dauke idanunta daga akashi ba, sosai dressing dinshi
ya burgeta white long sleeve had'e da white trouser yasaka. "Sumar kanshi
tasha gyara ya yi masifar yi mata kyau.
"Saida ya zauna sannan ya waigo wurinta ya yafito da hannunshi, jikinta asanyaye
ta mik'e ta nufo wurinshi.
"Ya kalleta da girar ido d'age ya ce dai barrister ko yanzu dinma bakyaji
yunwa?"
Murmusa had'e da zarar plate tayi serving dinshi, sannan ta zauna ta yi wa kanta
serving.
"Suna cin abinci tana satar kallonshi afakace, yi ya yi kamar bai ganta ba.
"Yana gani za ta dame shi da kallo yasa ya ce Barrister ki ci abinci kada ya yi
sanyi, ko abinci ne bai miki dad'i ba?"
Sosai taji kunya ta rufeta, ta shiga cusa chips d'in tana taunawa kamar mai cin
mad'aci, kafin ta ankara ya mik'e yabar mata dining d'in.
Ajiye fork tayi ta talla6e kumatunta tayi zurfi atunani, taji sauti muryarshi
yana cewa ni zan fita.
Da kyar iya furta adawo lafiya!
Yajuya abinsa ta bishi da kallo.
***"""***""****
Misali k'arfe 8:00 na dare bayan sun kammala dinner, ta tattara plates da suka yi
using ta kai kitchen ta wanke.
"Koda tadawo downstairs parlor ya fice, shiru tayi tana nazarin wayar da ta yi
da barrister Z d'azu da safe.
_Inda take cewa Bebs ki cire kunya da miskilanci ki nemi kusanci da mijinki, shi
namiji ne ko a yanzu yana da damar auro mace har uku, sa6ani ke kinga kenan kece a
wahala ki yi wa kanki fad'a bebs tun kafin lokaci ya k'ure miki, karki mata ke mace
ce Allah ya yi miki ni'imomi da yawa da za ki janye hankalin d'a namiji da su karki
yi wasa da damarki, kafin ku wuce Abuja ki yi k'ok'ari ki nemi kusanci da shi_
Ajiyar zuciya tayi had'e da dafe k'irjinta, daga bisani ta nufi bedroom d'inta ta
sauya kayan jikinta zuwa Indonesia gown mai santsi gaske talafe a jikinta, ita
kanta da ta kalle kanta da mirror saida ta firgita sakamakon yadda gown d'in ta
baiyana surorin jikinta.
"Arabian perfumes tayi amfani da su saboda sun fi k'arfi da jan hankali,
tasaki gashinta ya sauko har gadon bayanta ta yanne kanta da d'an siriri mayafi.
"Tasaka wasu slippers masu taushin gaske a k'afarta
Kai tsaye ta wuce kitchen ta had'a mishi coffee sannan ta nufi falonshi da ke
upstairs, tun kafin takarasa take jin sautin muryarshi, tasan waya ne yake yi.
"Da sallama tashigo ya juyo ya kalleta ita ma kallonshi, tayi kafin ta kauda
kanta ya yafito ta da hannunshi ya yi, alamar da ta k'araso.
Ta ajiye mug din coffee akan center table da ke gabanshi, ta nemi sofa ta zauna
bai wani jima yana waya ba ya ajiye.
"Ya dauki coffee yana sha ahankali yayin da ta sadda kanta k'asa tana wasa da
gefen gyaleta, shiru ya biyo baya karar TV kawai ka ke ji sai kuma zuciyar
barrister A da ke bugawa very fast.
Ya canza channel zuwa idan ake haska movie na horror, satar kallonshi tayi anan
ta ga hankalinshi na kan movie d'in hakan yasa ita ma ta maida hankalinta ga Tv.
"Tuni hanta cikinta yafara kad'awa gani yadda zombies ke wasa da jinin bil-
adama, ta runtse idanunta gam....
Ita kam sam bataso irin movies dinan tsorata ta suke yi.
"Kallonta ya yi ya ta6e baki ya cigaba da kallonshi, can yasake kai dubanshi
wurinta still idanunta a rufe ruff....ya yatsine fuska kafin ya ce barrister tashi
ki koma bedroom dinki kada ki yi bacci anan.
Sai lokaci ta bud'e idanunta ta girgiza kanta muryarta, asanyaye ta ce ba bacci
nake ji ba.
"Bai ce da ita uffan ba ya cigaba da kallonshi sai around 11:20pm aka gama film
d'in yana k'ok'arin tashi ta kalle shi ta ce sai da safe Yalla6ai.
Batare da ya kalleta ba ya ce "sai da safe.
kafin ta k'ara wata magana sai ya mik'e yabar mata falon ya nufi bedroom, ta bishi
da kallo tana sanyaye murmushi.
Ita da ta zo mashi fira ya tafi ya barta da gadin falonshi, ta d'an jima zaune tana
zance zuci daga bisani ta mik'e ta koma nata sasshe, da kyar bacci ya yi nasarar
dauke ta.
"Tabbas akwai jan aiki agabanta ba kad'an ba.
"Shi ma ta6angareshi yana kwance zuciyarshi cike, da tunani abinda yafi tsaya
masa arai duk yadda barrister A tayi kwaliyya sai ta burgeshi, zai dauki dogon
lokaci kafin ya manta da kwaliyyar ta ta.
Uwa-uba mayyen turarenta da ke addabarshi muddin ya shak'i k'amshinta sai ya tsince
kanshi a wani yanayi wanda shi kanshi ya rasa gane na menene.
"Washe gari da safe suna zaune a dining table tana serving d'inshi, ya d'ago ya
dubeta afakace ba shiri ya dauke kanshi zuciyarshi na bugawa da k'arfin gaske,
sakamakon yadda tayi mishi kyau kamar wata aljana.
"Ya sadda kanshi k'asa yana cin abinci ba don yana jin dad'inshi ba, adaddafe
yaci abinci yana kammalawa yabar dining area ta bishi da kallo har ya haura steps
idanunta na kanshi.
"""****"""****""""
A kwana atashi asarar mai rai gashi yau kusan sati biyu kenan da auren Aliyu da
barrister Amina.
"Da Yammacin ranar talata barrister A tana tsaye a kitchen tana gyaran fruits za
ta had'a fruits salad, taji shigowarshi saida ta kammala had'awa ta zuba mishi
nashi a bowl tasaka ice cubes sannan ta nufi falonshi.
Zaune ta sameshi yana operating waya jin motsinta da kuma k'amshin fittinane
turarenta, da ya bigi k'ofufin hancinshi ya haddasa masa d'agowa da kanshi, ya
kalleta ya kauda fuska ya cigaba da dannar wayarshi, ga alama chat ne yake yi.
Ta ajiye bowel d'in hannunta akan center table.
Sannan ta isa ga kujerar da ke facing dinshi ta zauna tana mishi sannu da dawowa.
Ya amsa batare da ya d'ago da kanshi ba ya kalleta.
Ta kalleshi sosai kafin ta ce "Yalla6ai ga fruits salad na kawo maka bansani ba ko
kana da sha'awarshi.
Asanyayye yai murmushi ya d'ago suka had'a ido cikin tsadaddiyar muryarshi ya furta
nagode!
Daga haka suka yi shiru shi yana dannar wayarshi ita kuma tana aikin kallonshi, can
dai ya d'ago tai sauri kauda kanta.
Ya yi murmushi saboda ya ganota sarai....kallonshi take yi ya dauki fruits salad
d'in yana sha yana kad'a kai alamar ya yi mishi dad'i.
"Yana gama sha ya mik'e ya shige shi bedroom ya barta zaune.
Da tagaji da zama ita kadai ta koma nata falo.
**"""***"""****
Misali k'arfe 10:00 na dare fitowarta daga wanka kenan, tana daure da towel wanda
ko cinyoyinta bai gama rufewa ba. Barrister Z ta kira ta ta duba email d'inta akwai
sak'o da ta turo.
"Laptop d'inta ta dauko da ke aje akan bedside drawer, ta nemi gefen gado ta
zauna ta shiga duba email d'in ta shagala sosai har rabin towel d'in ya zame daga
k'irjinta rabin boobs d'inta a fili.
"Jin an murd'a k'ofar d'akinta yasa ta tsorata da sauri ta juya Aliyu tagani
tsaye ya yi folding hannayenshi a k'irji, mayyun idanuwanshi ya zuba mata masu kama
da na mai jin bacci, kamar mai koyo magana ya ce coffee za'a bani.
"Ta gyad'a kai alama amsawa sai dai kuma tana matuk'ar jin kunyar yadda za ta,
tashi da wannan d'an towel a gabanshi.
A tunaninta ficewa zai yi sai ta tashi sai taga sa6anin hakan.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:01 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Not edited!
*21*
Ya gyara tsayuwarshi ya kuma rik'e handle d'in k'ofar, ya cigaba da kallonta ta
gefen ido.
Ta waiga gefenta ba wani abin da za ta rufe jikinta da shi.
Can Allah ya taimaketa ta hango hijabinta na sallah akan praymat, ta d'an sosa
tsakiyar kanta, cikin tsananin jin kunya yadda za ta tashi gashi ya tsareta da
brown eye's dinshi.
Gani bata da niyar tashi yasa ya ce I'm waiting barrister!
Ta d'an kalle shi cikin jin kunya ta ce "Yalla6ai ka tsaya a bakin k'ofa ban san
yadda zan yi in fita ba, ina jiran ka janye sai in tashi"
"Dama idanuwanshi na kanta ya dan murmusa sannan ya juya ya fice, daga d'akin.
Gani haka yasa ta mik'e cikin sauri ta isa wajen praymat, ta dauki hijabinta ta
sanya ya sauka mata har k'asa, sannan ta fice.
"Ta had'a coffee a mug ta nufi falonshi a tunaninta yana nan falo, sai taga
sa6anin hakan.
"Dole ta wuce bedroom d'inshi zaune ta sameshi akan resting chair, asanyaye
cikin girmamawa ta runsuna ta mik'a masa coffee.
"Garin amsa by mistake ya had'a da hannunta, wani irin shock ya ja su, sai kace
electric shock jikinta ya dauki rawa cikin zafin nama ya rik'e mug d'in da coffee
ya zube mishi a jiki.
kallon k'asan ido ya yi mata ta kauda fuskarta, had'e da furta "I'm sorry!.
Ki zauna mana ki yi tsaye!
Yafad'a yana kallon gefen face d'inta.
Girgiza kai tayi had'e da cewa bacci nakeji idan akwai wani abu da ka ke buk'ata,
ka fad'a nayi maka kafin na kwanta.
"Ya kai mug d'in coffee abakinshi ya d'an kur6a ya kalleta a tsanake, ya ce ki
je ki gyaran min bed tunda komai sai na rok'e ki.
Sosai ta dube shi kamar ba za ta yi magana ba, sai kuma ta daure ta ce "Ba ka bani
fuskar yin hakan bane, da ba sai ka rok'a ba.
D'auke kanshi ya yi daga barin kallonta ya cigaba da shan coffeenshi, kamar ba zai
ce komai ba ganin yadda take tsaye yasan tana jiran jin ta bakinshi ne.
Duk mace tagari tasan responsibility da yake kanta.
Uhm....Yalla6ai karka jefe ni da magana mana sanin kanka ne, komai da mazauninshi.
"Haka hasasshenki ya baki za ki iya tafiya idan gyara d'akin nawa zai ba ki
matsala, dama girl's like you ba abinda ku ka iya sai kwaliyya, always cikin makeup
kamar masu zuwa za6e miss world.
"Ya salaam! Sam bata yi tsanmani jin irin wad'annan maganganu daga bakinshi ba,
shiyasa taji wani irin tai shiru tana kallonshi da mamaki shinfid'e akan fuskarta.
Gani yadda take kallonshi yasa cikin low voice "ya ce please you can leave
barrister!
"Ta cire kai ta kalle shi coffenshi kawai yake sha, kamar ma ba da ita yake magana
ba.
Sosai hakan ya 6ata mata rai sai kawai ta juya tabar d'akin, batare da tasake cewa
komai ba, saidai kuma ta shiga tunanin me yake nufi da _girl's like her ba su iya
komai ba sai makeup which means yana kallonta amatsayin wacce bata iya komai ba
shiyasa ya hanata fara girki_
Ta isa bedroom d'inta zuciyarta cike da damuwa na rashin sani manufar idan
maganarshi ta dosa.
"Tabbas Aliyu ya cika cikakke d'an reni hankali wato yana jira sai ta kawo mishi
kanta, to kuwa tabbas za ta shayar da shi mamaki.
Har ta kwanta sai kuma ta ga rashin dacewar abinda tayi ko ba komai, yana matsayin
mijinta yana kuma sama da ita dole ta yi mishi biyayya.
Zubur.....ta mik'e tsaye ta bud'e closet ta dauki wrapper ta daura akan sleeping
dress d'inta.
Ta murd'a handle gabanta na fad'uwa yana nan zaune idan ta bar shi, sai dai yanzu
yana operating wayarshi.
kallo d'aya ya yi mata ya kauda fuska, ba ta ce da shi uffan ba ta cire bedsheet
d'in ke shinfid'e duk dai bai yi wani dirty ba, ta shinfid'a new one ta kunna water
burner ta zuba perfume mai k'amshi strewberry, tuni d'akin ya dauki k'amshi.
Ta shiga tattare files d'in da ke zube a k'asa ta adana su ciki bedside drawer.
Ta waiga ta kalle shi "ta ce Yalla6ai na kammalla gyara gadon ko akwai wani abu da
ka ke buk'ata?"
Harara ta yi ya da brown eye's d'inshi yana yatsine fuska, "ya ce ba fushi ki ka yi
ba waye shawarce ki ki ka dawo?"
"murmushi ta yi kafin ta ce, ba fushi nayi ba zani naje na dauro.
Uhm....za ki iya tafiya nagode!
Sai da safe!
Tafada had'e da ficewa.
***""****""""*****
Washe gari suna kammalla breakfast Aliyu ya koma d'aki ya yi wanka, sai gashi ya
fito cikin white three quarter as usual had'e da armless shirt, lokaci tana zaune a
falonta ya shigo ya nemi kujera ya zauna, cikin husky voice "ya ce ki shirya
kayanki gobe za mu wuce abuja nagaji da garinan.
"Kamar za ta yi kuka take kallonshi har ga Allah bata saka rai da wuri za su
wuce abuja ba.
kinji koh?"
Ya katse mata zance zucci.
Naji!
Tafad'a asanyaye.
Sai ki shirya zuwa anjima mu je ki yi wa su Ummi bankwana.
"Nan take tasaki murmushi saboda tayi kewar gida ba kad'an ba.
Ya mik'e yabar falon ta bishi da kallo tana murmushi a k'asan zuciyarta kuma ta ce
"A dai juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, insha Allah za ka shigo hannuna sai
na sauke ma miskilanci da girman kai.
"Mik'ewa tayi ta nufi kitchen kasancewar akwai kayan abinci da duk wani abu da za'a
buk'ata wurin girki, yasa ta yi decided ta nuna mishi bata cikin girl's d'in da
yake tsanmani.
"Aliyu na fita direct garden ya wuce saboda yana buk'atar fresh air, newspaper na
leadership ne a hannunshi yana dubawa.
"Cikin k'ank'ani lokaci gidan ya dauki k'amshi girkinta, ta had'a fry rice da
pepper chicken, with comslow sai juice na coconuts & pineapple.
Tun daga garden ya keji jiyo k'amshi girkita, da yake kafin tafara girkin ta bud'e
windows.
"Koda k'arfe 1:30pm ta yi ta shirya table ta koma d'akinta ta yi wanka ta shirya
tsaf cikin California authentic gown mai open neck tasaka bohemian sterling
earring, sallah ta yi sannan ta yane kanta da scarf wanda ya yi match da gown
d'inta.
Ta sanya ballerina flats shoe, sosai tayi kyau na ban mamaki sai k'amshi take yi.
Ta fito ta zauna bata jima da zama ba sai gashi yana saukawa daga upstairs, bai
zauna a falo ba direct ya wuce dinning area ya kagara ya ci abinci nata ya ji
menene yake k'amshi a cikinsa.
Tasowa tayi ta dauki plate tayi mishi serving, ta mik'a hannu ta janyo warmer da
pepper chicken yake ciki, yadda ta ware hannunta yasa rigarta ta sauka a fuskarshi,
ya shak'i k'amshin jikinta wani shauk'i na ban mamaki ya ziyarce shi.
Ya d'ago da kyar ya Kalle irin shigar da ke jikinta, ya yi sauri dauke kanshi, ya
juya yana kallon TV da ke manna a bangon dinning.
Ta ajiye plate agabanshi ya dauki spoon yana ci a yangace, yana mamaki sam bai
dauka ta iya girki har haka ba.
Kamar ya tambayeta ya akayi ta kware da girki har haka, mai dad'i saboda ya ji
dadin abincinta ba kad'an ba.
Fasa tambayarta ya yi saboda baya so reni, atunaninshi tambayarta zai iya kawo reni
a tsakaninsu.
Sosai ya ci abinci musanmman juice duk lokaci da ya kur6a shi sai ya lumshe ido,
afakace take satar kallonshi duk abinda yake yi.
Taji ya yi bala'in burgeta.
Yana gama cin abinci ya mik'e ya koma falo, ta tashi tabi bayanshi.
har k'arfe 4:30pm tayi bata ta ji ya ce ta taso su tafi ba, gashi kusan sau biyu
tana komawa bedroom tana gyara makeup d'inta.
Gani tayi