Author : Jidda Aliyu Category : Drama
"Wani mushirikin murmushi momma tayi tana k'arewa Maryam kallo, sannan ta juyo
ta nufi k'ofar fita yayin da Ruky ta mara mata baya flat d'inta suka nufa.
"A main parlor suka tarar da Tima zaune tana wasa da yatsun hannunta, kamar mai
lissafi momma ta dube ta ta ce Tima me ki ke yi anan?
Ba na hanaki zama a falonan ke kadai ba, ina zee-zee da Minat da suka barki ke
kadai?"
Har momma ta gama zuba mata tambayoyi bata kalleta ba, sai wasanta take da
yatsunta.
"Tima.....magana nake da ke fa.
Wani irin d'agowa tayi idanuwanta sun yi jajir sai kace abinda aka zubawa Barkono,
ta mik'e zubur ta nufi wajen momma da sauri momma ta ja da baya cikin wata
rikitattaciyar murya ta ce "za ta zo tabbas tana gam da zuwa ita ce za ta tone
rijiya mai dauke da macizai da kunamu ta fito da jar jakka mai dauke da kundin
sirri.
Tana gama magana ta juya ta nufi d'akinta tai barking k'ofar da k'arfi gaske.
momma da Ruky suka bi ta da kallo, girgiza kai momma tayi cikin rashin daukar
Maganar Tima da muhimmanci ta nufi sofa ta zauna wacce ke kallonta ta nunawa Ruky
ta zauna.
Hajiya ina tausayi Tima wallahi, har nake gani kamar zunubin da ki ka aikata ne
yake bibiyarta.
Murtuk'e fuska momma ta yi kamar bata ta6a dariya ba, hakan yasa Ruky ta sha jini
jikinta.
"Duk haka sai da momma ta nuna mata k'ofar fita da d'an yatsanta, tashi maza Ruky
ki fice min daga gida aiki ki ke min kuma ina biyanki mak'udan kudi bana wasa ba,
daga yau sai yau ina gargadinki kar ki sake yi min kutse a cikin al'amurana duk
duniya bani da babban mak'iyi irin mai fad'amin gaskiya.
"Allah ya ba ki hak'uri Hajiya na tu.......
Ya isa dallah kin riga da kin batan rai ki fita kawai sai gobe in kin zo.
Mik'ewa Ruky tayi sahunta a likkafa ta fice cike da takaici irin wulak'ancin da
momma tayi mata.
****---****----****
*YOLA*
Misali k'arfe goma sha biyu na rana jirgin da Aliyu ya shigo ya yi landing,
direbansu na yola ya kira ya dauko shi daga Airport gidansu da ke nan Yola ya sauka
ya yi wanka ya shirya masjid ya fara wucewa ya yi sallar Juma'a daga masallaci, ya
wuce gidan uncle suraj anan ya ci abinci suka shiga tattauna zance business duk
lokaci da uncle Suraj ya dauko zance aurenshi sai ya shasshata zance.
Anan ya yi sallar la'asar, kafin ya yi sallama da uncle ya nufo gidansu Barrister
Amina.
"Barrister Amina ta kammalla shirinta tsaf cikin Arabian gown ash colour tayi
rolling da d'an siriri veil orange colour, ta fito sak'ale da handbag d'inta ita ma
kalar orange tayi masifar kyau da yake Ummi ta fita shiyasa ta lek'a d'akin mai
aikinsu Asabe ta ce koda Ummi ta rigani dawowa ki fad'a mata na fita saloon gyara
gashi, gudu-gudu ta fito saboda daga wurin saloon tana so ta biya gidan Barrister
Zarah Ladan tun kafin ta k'arasa parking lot tai using remote k'ofufin motarta suka
bude ta shiga tayi ma motar key tayi reverse, ta nufi gate sai gate d'in a bude
wata dalleliyar mota kirar Jeep Volkswagen, ta shigo dole tai reverse ta koma baya
ta bata wuri ta wuce a tunaninta ko d'aya daga cikin guest d'in Abba ne, wani abin
takaici ba kowa a gida dole ta tsaya tai entertained d'insu, ta kashe motar had'e
da jan tsaki mtssss!
Ta bude k'ofa ta fito yayin da bak'in suka yi parking, direba ne yafara fitowa ya
bud'ewa Aliyu k'ofa ya fito tai tsaye turuss....tabbas ta shaida fuskar Aliyu cikin
salon tafiyarta mai daukar hankali ta isa wurinshi, fuskarta dauke da sanyayye
murmushi sannu da zuwa!
Ta fad'a kamar mai koyon magana.
Cikin husky voice dinshi ya ce Yauwa mun same ku lafiya?"
Lafiya qalau ya su mommy?"
Lafiya qalau suke.
masha Allah!
juyawa tayi wajen gate man ta yafuto shi da hannu, cikin azama ya iso ta ce ka
shiga da bak'o falon bak'i ina zuwa tak'arasa magana had'e da nufar cikin gida.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:52 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*11*
Ta kwalawa Asabe kira ta tayata had'a mishi abinci da drinks, ta dubi Asabe ta ce
dauki ki kai masa Asabe ki ce mishi ina zuwa.
"Bayan Asabe ta kai mishi abinci ta dawo ta lek'a d'akinta ta ce ta kai mishi
saida iya juice ya sha ya ce ya k'oshi da abinci, shikenan Asabe ki mayarda abincin
kitchen.
Ta mik'e ta isa gaba dressing mirror ta gyara fuskarta, ta fesa Asrar alhub perfume
sannan ta fice cikin sanyayar muryarta tayi sallama ya amsa can k'asan mak'oshi,
sai da ta zauna a sofa da ke facing nashi sannan tasake gaidashi ya amsa a tsanake,
shiru ya biyo baya kowanesu da abinda yake sakawa a ranshi wayarshi tayi ringing
hakan yasa ta d'ago ta sace kallonshi ya yi receiving call d'in cikin tsadadd'en
turancinshi yake magana, da business partner dinshi tsawo 30 minutes ya dauka yana
waya kafin ya katse kiran ya d'an sace kallonta dai-dai ita ma ta d'ago ta kalleshi
karaf idanuwansu suka sark'e, wani irin kwarjini na musanmman kwayar idanunshi tayi
mata fiyye da farkon ganinta da shi, kamar daga sama taga yasake mata k'ayatattace
murmushi wani irin sanyi ya ratsa tun daga tsakiyar brain d'inta har zuwa tafin
k'afarta.
"Ita kanta batasan lokaci da ta mayar masa da martani murmushin na shi ba.
"Cikin salon maganarshi mai cike da yanga da aji ya ce Barrister da fatan
za'ayi min afuwa kasancewar kin gani daga sama ba sanarwa, wannan ya faru ne a
dalilin rashin sanin phone number dinki kiyi hak'uri da rashin ganina ayyuka ne
suka sha min kai, yanzu dai bani digit dinki gudu kar a koma 'yar gidan jiya.
Yakarasa magana yana shafar geminshi.
Ta sadda kanta K'asa fuskarta dauke da yalwattace murmushi, ta shiga karanto masa
numbers dinta duka guda biyu da ta ke using da su.
"Ya shigar da digit din a wayarshi ya yi saving da Barrister 1 da kuma barrister
2 ya kira numbers da wayoyinshi a lokaci d'aya phones d'inta guda biyu babban da
k'arama suka yi ringing ta kai dubanta ga wayoyi ni ne kiyi saving numbers d'in
yafada kamar mai koyo magana.
"murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, haka Kuma bata kalleshi ba.
Shiru ya biyo baya na tsawo wasu dak'ik'u, gani za su 6ata lokaci a banza shi kuma
ba abinda yafi ba muhimmanci irin lokacinshi saboda kowace dak'ik'a tana da matukar
amfani a wurinshi, a cewarshi idan lokaci yawuce shikenan ba zai ta6a dawowa ba
shiyasa yake matuk'ar mutunta lokaci.
"Don haka ya gyara zama duk da shi d'in ba gwani surutu bane, amma kuma ya zama
dole ya yi shi a gaban barrister sakamakon fahimtar da ya yi ita ma gwanace a fagge
miskilanci, sosai yake mamaki yadda zamansu zai kayya shi da ita.
Ya yi gyaran murya kamar mai shirin kiran salla, ya ce Barrister maganarki tsada ne
da ita ko ya ke ki ke presented case a court oho!"
Yadda ya k'arasa magana yana rik'e habbarshi yai masifar bata dariya, har batasan
lokaci da tasaki dariya mai k'aramin sauti ba har tana had'awa da rufe fuska da
tafin hannunta.
"Shi din ma murmushi ya yi ya cigaba da cewa kodai har yanzu fushi ake da rashin
zuwa na.
"Girgiza kanta tayi ta kalle shi da raguwar murmushi a fuskarta ta ce "A'a Allah ni
ba fushi nake ba duk abinda ka fad'a ina saurare kuma na fahimci bayaninka.
"To amma ai ba ki ce da ni komai ba duk da hak'uri da na bayar anyya kuwa
barrister kin hak'ura kodai na nemo paper da biro na rubuta miki I'm sorry ma'am
sau dubu?"
"Zaro golden eye's d'inta ta yi had'e da furta rufa min asiri yalla6ai, ni asuwa
da zan ba ka wannan danye aiki.
Ke barrister mana masu murd'e gaskiya ta koma k'arya ku murd'e k'arya ta koma
gaskiya.
"Turo baki tayi cikin shagwa6a da ita kanta batasan tayi ba, abinka da
sangartattaciya ta ce ni gaskiya ba haka nake ba ka je ka bincika sosai za'a
gayamaka bana d'aya daga cikin masu aikata wannan aiki saidai in kuma akasi aka
samu, wannan kam ba zan maka musu ba saboda d'an adam azaji ne.
"D'an ta6e baki ya yi ya d'age girar ido yana kallonta wanda hakan ba k'aramin
masifar k'ara masa kyau ya yi ba, ya ce gashinan yanzu ina ba ki hak'uri kin k'i
hak'ura.
"Ta d'ago ta dube shi da yalwatattacen murmushinta har sai da dimple d'inta duka
biyu suka lotsa, hakan yasa kyawun fuskarta ya k'aru cikin sanyinta had'e da
tattausan lafazi ta ce "Don Allah yalla6ai ka rufa min asiri kuma ai zance bani
hak'uri bai ma taso ba saboda ba wani laifi da aka yi min ba.
"Murmushi ya yi ya ce shikenan tunda kin ce haka.
Daga haka ya yi shiru dama can ya gaji da surutu saboda har kanshi fara ciwo, shi
kanshi yana mamaki yadda ya barke baki yana zuba a gabanta.
"Gani yadda ya yi shiru ta gano fuel dinshi ya k'are saboda haka ta gyara
zamanta, tana wasa da bangles d'in hannunta ta ce yau ina ka baro Jamal?"
"Saida ya dauki lokaci kafin ya ce "lafiya qalau yake munyi waya da shi kafin na
iso nan da yake daga Lagos nake kaitsaye daga can nayo nan, shiyasa ba ki gan mu
tare ba.
"Ayya!
Ta fad'a tana murmushi.
Sai kinyi hak'uri da ni Barrister saboda yana yin aikina ban cika zama ba sosai
yanzu haka on Monday zan tafi business trip a Zurich sai satin bikinmu zan dawo don
haka duk abinda ki ke buk'ata Jamal ko kamal P.A na za su kawo miki, amma zaki
rik'a jin wayata duk lokaci da na samu sarari.
"Ba dawuwa Allah ya taimaka!
"Amin ya fad'a yana mik'ewa tsaye zan wuce sai gobe in na shigo, ki gaida mommy in
sun dawo.
"Ita ma mik'ewa tayi had'e da cewa zasu ji an gode kwarai Allah ya tsare.
Ya gyad'a kai had'e da ficewa da sauri shiyasa bata sami damar raka sa ba ta koma
cikin gida, ko zama bata yi ba maigadi ya dinga shigowa da manya-manya shopping
bags yana ajiye had'e da wasu manyan kwalaye.
Ya kuma mik'a mata envelope mai dauke da kud'ad'e masu yawan gaske, ita kanta sai
da ta jinjina yawan kud'in.
"Ta zuge zip d'in handbag d'inta ta jefa envelope d'in ta kira Asabe ta shigarda
kayan store.
Ta dauke jakkarta ta sake fitowa ta ja motarta ta nufi wajen saloon.
****"""*****"""****
*WASHE GARI*
Barrister A da kanta ta shiga kitchen ta had'a mishi had'add'u dishes, sai misali
k'arfe 4:20pm ya iso lokaci da sak'on isowarshi ya riske ta tana zaune ta shirya
cikin red colour din straight rubber gown mai adon stones a jiki tai masifar fitowa
da shape d'inta, ta yane kanta da scarf multi colour jikinta na fitarda k'amshi
Dima da Asrar ahub perfumes.
"Ta dauki phones d'inta tafito kaitsaye ta nufi falon bak'i tayi sallama, ya
amsa ciki zazzak'ar muryarshi saida ta zauna sannan ta gaida shi, ya amsa fuskarshi
sake.
"Sai lokaci ta kalli kayan da ke jikinshi farin material ne na maza transperent,
saboda har ana iya hango white vest dinshi sosai kayan suka k'ara fitowa da
kyawunshi, ita kam tsawo rayuwarta bata ta6a gani farar fata da farin kaya yake
masa kyau irin Aliyu.
"Ba laifi yau ya ci abincin da aka kawo mishi saidai kad'an yaci, yau d'in ma ya
yi k'ok'ari ba kad'an ba wurin yi mata fira bai wuce 1 hour da zuwa ba ya ce zai
wuce ta rako shi had'e da yi mishi godiyar kayan jiya.
"Yana batun shiga mota direban Abba yadano kai dole ya jira fitowar Abba suka
gaisa, saidai babu wata walwala akan fuskar Abba ya tank'e fuska kamar maigadin
mak'abarta sai ma wajen 'yarshi ya juya yana washe mata hak'ora, ta shige jikinshi
tana cewa whats a pleasant surprise Abba!
"I'm sorry my princess I come without informing.
Yafad'a yana ciro ta daga jikinshi.
It's okay Abba...saidai gaskiya ba ka kyautawa Ummi ba duk dai ba wannnan ne first
time da ka fara yin haka ba.
Ta k'arasa magana kamar da fushi akan fuskarta.
Yayin da Aliyu ya zama d'an kallo sai sata kallonsu yake, saboda sun yi masifar
burge shi da alama akwai shak'uwa mai k'arfi atsakaninsu, kamar shi da nashi
mahaifi ba san time d'in da ya yi murmushi ba da ya tuna da yadda wani lokaci suke
daro shi da Daddynshi.
"Abba ya ce ki je sallame bak'onki ki dawo naji laifina naga fuskar my cute
princess ta nuna fushi.
Murmushi tayi wanda bai wuce le6enta ba ta ce uhum!
Abba ya nufi cikin gida ta juyo wajen Aliyu tana murmushi ta ce sai anjima yalla6ai
amma gobe kafin ka wuce za ka biyo muyi sallama ko?"
"Insha Allah Abba's girl!
'Yar dariya tayi had'e da cewa ka ganka ko...
Batare da yasake cewa komai ba ya bude mota ya shiga direbanshi yaja suka fice daga
gidan, sannan ta juya zuwa cikin gida.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:52 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- RUYUWATA
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*12*
Washe gari bai samu damar biyawa wajenta kafin ya wuce Abuja ba, ya dai kirata a
waya suka yi sallama duk wannan abin yana yi ne don kawai ya farantawa Daddynshi
rai ba wai don ya ji yana sonta ko kuma ra'ayin aure ba.
***----***---****
*ABUJA*
Da yake jirgin safe Aliyu ya shigo yana isowa direbanshi Isah ya yi picking d'inshi
daga Airport, lokaci da ya iso Ardo mansion ba nemi kowa ba ya wuce flat dinshi
dama wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unshi, za ka san tafiyarshi amma ba lalle
bane kasan dawowarshi.
"Freshen up ya yi gani lokaci sallar azhar ya yi yasa yasaka farar jallabiya mai
gajeren hannu, ya nufi masjid da ke gidan ya yi sallah yana dawowa ya cire
jallabiyar ya jefa akan sofa ya nufi master bedroom dinshi ya haye tangameme
gadonshi, ya k'ara gudu Air con ya lumshe shanyayun idanuwanshi masu cike da bacci
bai dauki dogon lokaci ba bacci ya yi awon gaba da shi.
sai misali k'arfe 5:17pm ya farka a gurguje ya yi wanka saboda jikinshi ya sake
bayan ya yi sallah la'asar ya canza jallabiya jikinshi zuwa fari three quieter da
white colour hoodie armless, wacce ta fito da muscles d'inshi farare slippers masu
taushin gaske yasaka, ya kwashi wayoyinshi ya nufi flat d'in momma.
A falo ya tararda ita da girls d'inta sai faman zazzagawa Tima fad'a take akan
tak'i shan maganinta.
Ya yi sallama can k'asan mak'oshi Minat ta amsa mishi sannan ta gaidashi, ya amsa
mata kamar yadda ya yi sallama.
"Zee-zee ma ta gaidashi ya yi banza da ita, Tima da ke shasshek'ar kuka ya
dakawa tsawa ke!
A firgice ta d'ago ta dubi shi rufewa mutane baki tun kafin na take miki wuya, me
akayi miki da za ki tsirawa mutane kuka duk kin cika min kunne?"
sadda kanta k'asa tayi tana sharar hawaye, ke Zainab me take yi ma kuka?"
Magani ne momma ta bata tak'i sha shine momma take mata fad'a.
"Yatsine fuska ya yi ya ce momma please....ki dinga hak'uri da yarinyar nan
mana, tunda ta ce bataso magani ba sai ki kyalleta ba in fact wannan magani mai
wari tsiya ko waye dole ya yi kuka shan shi, ni narasa ina ki ka samo shi.
"Kafira harara momma ta zanga masa kafin ta ce gidan ubanka na samo shi,
wallahi Sultan ka shiga taitayinka da ni.
Dama ina cike da kai zaman jiran zuwanka nake.
"Kallo da yakewa su Zee-zee yasa suka gano me yake nufi da sauri suka mik'e
Minat ta kamo hannun Tima suka nufi upstairs parlor.
"Ya tsare momma da idanuwanshi da suka nuna zallan 6acin rai, duk duniya ba
abinda ya tsana irin fad'a tun yana yaro da ka yi mishi fad'a gara ka rufe shi da
duka.
Gani yadda ya tsareta da idanu yasa tagano ya hasala, dama haka takeso saboda duk
lokaci da ya harzuk'a tafi sauri aiwatarda shirinta akanshi.
"Don haka ta cigaba da cewa wai har da kai sultan za'a had'a kai a munafuce ni,
wato shine za'a kai kayan lefen aurenka Yola ina matsayin mahaifiyarka ba d'an
banza da ya gayamin sai da naji a bakin shannu talla, hakan da ku ka yi kai da
mahaifinka kun kyauta?"
Tak'arasa magana tana share hawayen kissa.
Ta gefen ido take satar kallonshi.
Sosai jikinshi ya yi Sanyi gani yadda take kuka kuma duk a dalilinshi, ya sausauta
muryarshi cikin tattausan lafazi yafara magana ki yi hak'uri momma bansan cewa
Daddy bai gayamiki zance lefen ba, ni kaina ba sanarda ni ya yi ba sai ana gobe
za'a kai kayan Aunty Salma ta kirani a waya take sanarda ni.
Kada wannan abin ya dameki momma Daddy ya yi haka ne duba da banaso aure, ya kuma
san duk abinda banaso ba lalle bane ki so shi, ki kwatarda hankalinki momma aure ma
ba sonshi nake ba balle wacce aka kai ma kayan lefe.
"Gyara zama momma tayi ranta fari tasss.......ta ce ni na dauka ko had'uwarka da
yarinyar kafara sonta, musanmman da naji ance kyakyawa ce ajin farko.
"Uhm....yafada had'e da dafe goshi ya ce kema momma kina da wani zance sai kace
kin manta da waye Aliyu, ko kayan sawa nace banaso to ta tabbata banaso su kuma har
abada ba zan so su ba, balle mace wacce kiyayyata darsu azuciyata.
"Hamdallah momma tayi ta cika fuskarta taff da murmushi, ta ce ka bi hankali
sultan kada Daddynka ya yi sauri hal6o jirginka ka ko san ba za ku kwasheta da kyau
ba.
"Insha Allah bama zai gane ba saboda ko cikin kuskure banta6a fad'a mishi bana
sonta ba.
Madallah d'an albarka bari nasa Laure ta kawo ma abinci.
Da sauri ya ce no am okay"
Sama-sama suka cigaba da fira yawanci firar tasu duk tambayoyi ne momma take mishi,
akan barrister wani ya bata amsa wani kuma ya ta6e baki