Author : Jidda Aliyu Category : Drama
"Amin!
Ummi.
Daga haka su ka cigaba da fira duk dai akan zance auren nata ne.
***----***----*****
Alhaji Muhammad Ardo ya na isowa garin Yola direct Ardo Family house ya wuce, anan
ya had'u da 'yan uwanshi suka dunguma zuwa gidan Barkido nemawa d'ansu Aliyu auren
Barrister Amina wanda nan take Barkido ya tsayar da lokaci nan da watani biyu masu
zuwa.
"Sosai Alhaji Muhammad Ardo ya ji dad'i yadda Barkido ya karrama Su da kuma
lokaci da ya sanya na bikin.
Duk zance da ake alokaci Alhaji Abdallah kallonsu kawai yake, saboda ya sha
al'awashi muddin Barrister A ta ce bataso Aliyu yasan hanyoyin da dama da zai da bi
ya hana auren.
*8:37pm*
Alhaji Abdallah yana zaune a parlounshi, ya aika Ummi ta kira shi mishi Barrister
A.
Da sallama ta shigo dauke da bakinta.
"Alhaji Abdallah ya amsa mata yana murmushi.
Barka da hutawa Abba.
"Yauwa Minal.
Ta nemi bisa carpet kusa da k'afafunshi ta zauna
Cikin sanyi murya Alhaji Abdallah ya fara magana, Minal na kira ki ne domin na ba
ki damar da za mu tattauna akan zance aurenki.
Ya d'an numfasa daga bisani ya cigaba da cewa har ga Allah Minal naso ki fito da
wanda ki ke so za6in ranki, duk nasan zan sha matuk'ar wahala kafin Barkido ya
amince.
"Amma hakan ya gagara daga gareki duk lokaci da na zo miki da zance, sai ki ce
ba ki samu wanda ki ke so ba.
Ba komai yasa nake miki gudun aure zumunta sai irin zaman da mu ka yi da
mahaifiyarki, mun sha bak'ar wahala da hak'uri ni da mahaifiyarki ba kad'an kafin
mu fara k'aunar junanmu.
"Banaso ki fuskanci irin wannan rayuwar agidan aurenki.
shiyasa koda yaushe addu'a nake Allah ya kawo miki miji wanda ba daga zuri'ar
Barkido ba.
Sai gashi Allah ya kar6i addu'a ta, Barkido da kanshi yai miki za6i ba daga
zuri'arshi ba.
"Tun daga lokaci da ya gayamin mijin da ya za6a miki farin ciki ya lullu6e
ni, saboda nasan wanene Aliyu ba shi wata matsala ko kad'an yana da halaye masu
kyau wanda kowane uba nagari yakewa 'yarshi fatan samunshi amatsayin mijin aure.
"Yayin da Alhaji Abdallah ya cigaba da cewa, duk da Barkido ya gama zartarda
hukunci har ya kuma sanya lokaci bikinki nan da watani biyu masu zuwa kamar dai
yadda ya fad'a tun kafin zuwansu.
"Saboda haka banaso ki tashi hankalinki, nayi magana da mahaifin yaron, ya ce
next week zai zo ku gane ki kwatarda hankalinki idan bai miki ba, nasan ta hanyar
da zan biyowa Barkido ya hak'ura batare da rayuka sun 6aci ba
"Murmushi ta yi cike da jin kunya ta, sadda kai k'asa tana wasa da babban yatsar
k'afarta.
Jin Shiru ta ya yi yawa yasa Abba ya d'ago ya kalleta,
shima ya yi murmushi ba ki ce komai ba Minal?"
Idan kuma ba ki da abin cewa za ki iya tafiya.
cikin sanyi murya ta ce Abba ya yi min duk ban ganshi ba, dama ni auren zumunci ne
banaso.
"Good girl.....Allah shi yi miki albarka
Amin...Abba.
Tafad'a had'e da mik'ewa tsaye sai da safe Abba zan je na kwanta bacci nake ji.
Allah ya kai mu
cewar Abba.
"Kitchen tafara shiga ta had'a coffee ta wuce da shi zuwa d'akinta.
Gefen gado ta zauna ta yi crossing legs d'inta, ahankali take sipping coffee
d'inta.
Yayin da wani gefen na zuciyarta ke nuna ma ta, tayi kuskure na saurin amincewa da
mutume da ko sunanshi sai yanzu ta ji.
Tana gama shanye coffee ta wuce bathroom ta wanke bakinta, ta dauko laptop d'inta
ta duba wani civil case da za ta yi presenting gobe.
Doguwar hamma ta yi had'e da shafa fuskarta hakan yasa ta rufe laptop d'in ta yi
addu'a kwanciya bacci, ta kashe wuta ta kwanta, ta rufe rabin jikinta da blanket.
****----****----***
*WASHE GARI*
*Abuja 11:08am*
Aliyu yafito daga apartment d'inshi jikinshi sanye da white suit, kamar yadda ya
saba shigarshi ta farare kaya, wannan yana d'aya daga cikin d'abi'unshi gaba d'aya
tufafinshi farara ne.
Baya ta6a saka wani colour kaya idan ba white ba Hannunshi rik'e da brief case
cikin yana yin tafiyarshi ta k'asaita ya fito compound, da gudu direbanshi isah ya
zo ya kar6i brief case d'in.
shi kuma ya nufi apartment d'in momma zaune ya tararda ita har k'asa ya durku'sa ya
gaidata, wannan yana d'aya daga cikin kyawawan d'abi'un Aliyu yana girmama
iyayyenshi sosai.
"Momma ta amsa tana fara'a saida ta dube bakin k'ofa ta ga ba kowa, ta gyara
zamanta Sultan tun jiya mahaifinka ya dawo daga Yola.
"Uhm! Nasani momma naga lokaci da ya dawo ina tsaye a balcony.
Momma ta d'an yatsina fuska sannan ta ce, ya ce an tsayarda lokaci bikinka watani
biyu masu zuwa.
tak'arasa magana cikin murmushin yak'e.
"Ta6e baki ya yi had'e da mik'ewa tsaye momma ni zan wuce office.
Afakace ta galla masa harara, ina magana ka mik'e tsaye kuma ba ka ce da ni komai
ba.
"Me Zan ce momma?
Auu.....ba ka da abin cewa?"
D'an bazawari murmushi ya yi momma sauri nake in nadawo za mu yi magana anatse,
saidai gaskiya idan har Daddy ya nace akan lalle sai nayi aure to ya barni na nemo
wacce nakeso da kaina.
in fact ban shirya yin aure a wannan shekara ba, balle nan da wata biyu ban so
Daddy ya yi sauri yanke lokaci biki ba
ahali ni da nake aure ban amince ba.
Rausayar da kai momma ta yi ta ce yanzu kan aikin ga ma ya rika ya gama, ni kaina
ban zace zai yanke iri wannan hukunci ba.
Amma ba komai ni ma nasan ta hanyar da zan bulluwa al'amarin.
"Kamar ya momma?"
Ya fad'a da alamar mamaki shinfid'e akan fuskarshi.
wayacewa ta yi ta hanya cewa je ki kawai kada na 6ata maka lokaci kamar yadda ka ce
in ka dawo za mu k'arasa
magana.
"Batare da yasake magana ba ya juya ya nufi sitting room d'in Daddy.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:42 PM] Jiddah Aliyu: *GIDAN RINA*
Na Jeeddah Aliyu
Free page
*Haske writers association*
*5*
Yana had'a ido da Daddy yafara murmushi yana sosa k'eya alamar rashin gaskiya,
dariya Daddy ya yi ya ce lale marhaban da bak'on Scotland barka da zuwa Gadanga
k'usar yak'i.
"Dariya ce ta subucewa Aliyu ya rufe bakinshi da tafin hannu, Kallonshi Daddy
yake yana girgiza kai "Good morning Daddy Aliyu yafada yana shafar gemunshi,
Morning Sultan idonka kenan sometimes da sultan Daddy yake kiranshi kasancewar
sunan mahaifinshi da yake da, murmushi ya yi yace Daddy am sorry.
"Ba komai sultan...Daddy ya fad'a but zo ka zauna mu yi magana ta fahimta.
zaunawa ya yi kusa Daddy kafin Daddy ya yi magana saida ya rik'o hannunshi d'aya,
Sultan dangane da zance aurenka ni da iyayyen yarinyar mu yi fixing din Date nan da
watani biyu masu zuwa, saboda muna so ku same isasshe lokaci da za ku fahimce
junanku.
"This time around idan ka sake ka ruguza aurenan Sultan I won't forgive you....don
haka make sure ka shirya this weekend ka je Yola ku gana da yarinyar.
Ka ji ko?"
Daddy ya tambayeshi, yana kallon yadda ya 6ata fuska tamkar zai yi kuka ga wani
uban gume da yake ta faman shawagi akan face d'inshi, da kyar ya hadiye wasu yawu
sakamako bakinshi da ya bushe ya ce Daddy please.....idan har ya zama dole sai nayi
aure ina neman alfarma ka ba ni dama na nemo wacce nakeso, Saboda ba lalle bane
kanemo min kalar mace da nakeso ba...
Shut up....my friend!
Daddy ya daka mishi tsawa wallahi sultan ka shiga taitayinka da ni, muddin ka ga
ba'a yi aurenan ba k'addara hakan amatsayin bana numfashi tashi maza ka 6ace min da
gani, shassha banza da wofi.
K'asa da murya Aliyu ya yi ya ce Daddy am so sorry karka yi fushi da ni
please.....duk abinda ka ke so zan yi saboda ba zan iya jure fushinka ba.
"Dauke fuska Daddy ya yi da barin kallonshi, hakan yakara rud'a Aliyu ya durkusa
agabanshi, Daddy nace na amince muddin zan sanyaka farin ciki koda mayya ce zan
aureta.
Sai lokaci Daddy ya saki fuskarshi ya ce that's my boy.....saidai ba mayya ba ce
jikar Barkido ce sunanta Barrister Amina 'yar manyan mutane ce shiyasa banaso asame
matsala, daga bangare na.
''Zaro idanu Aliyu ya yi hade da Squeezing face.....Daddy kana nufi yarinya
lawyer ce?"
Kwarai kuwa independent lawyer ce[lauya mai zaman kanta]
Whatever! Daddy ni ko lawyer government ce I don't care kawai dai kasan I hate
liar's kuma mostly lawyers mak'aryata ne, hararrashi Daddy ya yi had'e da furta
banaso shirme Gadanga don kawai tana lawyer shi zai sa ta zama mak'aryyarci?"
"Turo baki ya yi a sangarce ya ce ni dai Daddy I don't love her.
mak'e kafad'a Daddy ya yi irin I don't care dinan, kafin ya ce kai dai karka yi
gaggawa ka jira har ka ganta ido da ido.
Mik'ewa Aliyu ya yi Sai na dawo Daddy ina da meeting around 12 o'clock.
asauka lafiya....Daddy ya fada da murmurshi akan fuskarshi.
Ficewa ya yi yana fitowa isah direba ya jawo mota ya bud'e mishi back sit ya kame a
owners corner, isah ya ja motar cikin kwarewa da tuk'i ya fice daga gidan.
****--*****-----****
Sai around 2:20pm Aliyu ya fito daga conference hall, kaitsaye office d'inshi ya
wuce ya ajiye laptop dinshi da wasu files akan desk ya wuce ya bathroom ya dauro
alwala, yana fitowa P.A shi Kamal na shigowa rik'e da white coat d'in Aliyu yanufi
wata hanger da ke ajiye a cikin office d'in ya sarkafe rigar.
"Aliyu yana fitowa daga bathroom da
sauri kamal ya shinfid'a mishi praymat
Batare da Aliyu ya kalle shi ba ya ce Kamal ka yi min order food a chicken republic
restaurant, yunwa nake ji cikina sai k'ugin yake.
"An gama Boss!
Har kamal ya juya ya sake cewa ba ka ji ba kamal.
Chak...kamal ya tsaya.
"please help me call Jamal tell him I wants to seen him urgently.
Yes boss!
Cewar kamal yana mai ficewa daga office din.
Aliyu yana gama sallah ya koma kan resting chair ya kwanta, ba abinda yake tunawa
sai babban k'alubali da yake tunk'aro shi, duk duniya ba abinda ya tsana irin aure
duk yadda ka ke da shi idan ka yi invited nashi daurin aure ba ya zuwa, ko a family
su ake aure sai ya k'irk'iro tafiya don kada ya je sosai abin yake ciwa Daddy tuwo
a kwarya.
"Mtsss....ya ja d'an siriri tsaki ya dafe goshinshi duk lokaci da ya tuna Daddy
ya ce dole sai ya je Yola wurin yarinyanan, sai ya ji fad'uwar gaba wanda ya rasa
na menene babban tashin hankalinshi bai san yadda zai ga yarinyar ba, ko yaya take
bashi da mafita dole ya aureta don ya farantawa mahaifinshi rai.
"Turo k'ofar da aka yi ya katse mishi tunani da sallama kamal yak'araso, kusa da
Aliyu ya ajiye ledar hannunshi.
"Boss na kira maigida Jamal ya ce zai zo nan ba da jimawa ba.
Okay.....ba damuwa za ka iya tafiya.
Ficewa kamal ya yi yayin da Aliyu ya dauki takeaway guda yafara ci kasancewar yana
jin yunwa yasa yaci fiyye da rabin abincin.
"Abinci yake ci amma zuciyarshi cike da zance zuci, turo k'ofar da aka yi ya
katse mishi zance zuci da ya ke yi, sallamar Jamal ta bugi dodon kunnenshi, ya dubi
k'ofar yana mai amsawa Jamal ya shigo ya zauna kusa da Aliyu yana mai mik'a masa
hannnu suka yi musabaha.
"Ya garin JB kwana biyu ka 6oye?"
Aliyu ya fad'a yana kallon fuskar Jamal.
Alhmdllh....kwana biyu nan am too busy tun lokaci da Abba ya yi rashin lafiya
abubuwa su ka min yawa.
"Sauke numfashi Aliyu ya yi kafin ya ce gaskiya iyayyenmu suna bukatar hutu
musanmman yanzu da k'arfi kullum k'ara ragewa yake, gara kai JB kana da siblings
maza su na taimaka maka a business d'inku sa6ani ni da bani da kowa
"Ta6e baki Jamal ya yi kafin ya ce kadai ayi sha'ani kawai amma lamarin 'yan
uwan nawa sai addu'a daga mai shaye-shaye sai manemi mata, shiyasa kullum jini Abba
k'ara hawa yake.
Girgiza kai Aliyu ya yi ya ce Allah ya kyauta ya shige mana gaba.
Amin summa Amin!
cewar Jamal yana mai daukar robar ruwan Faro ya bude, ya kafa baki ya sha daga
bisani ya ajiye.
Ya dube Aliyu ya ce king ya zance da mu ka yi a waya yanan ko ka watse shi?"
Yak'arasa magana yana dariya.
Uhm! Bari kawai JB wannan karo zance ba zai watsu ba.
Yanzu haka neman da nake maka zance nakeso, mu tattauna akai.
"Daddy ya ce na shirya ranar Saturday naje naga yarinyar, sai ka shirya mu tafi
tare.
"Allah yakaimu cewar Jamal.
Cigaba da tattauna zance suka yi.
****----*****-----*****
Yammacin ranar Juma'a Barrister Amina tana zaune a office d'inta black suit ne
sanye ajikinta, ga farin gilashi d'inta da ta manna a fuskarta ya yi matuk'ar
fitowa da kwarjininta.
Ta tattara hankalinta akan system, aka yi knocking k'ofa, yes.... come in.
Tafad'a tana mai cigaba da aikinta aka turo k'ofa tare da sallama ta amsa batare da
ta d'ago kanta ba, ta ce bebs sai yanzu ki ka fito?"
Uhm....bari kedai bebs case din yau ya bani kashi ba kadan ba kinsan shegen iyamuri
nan Barrister Obi shi ne defendant lawyer, yanzu dai an d'age zama sai on 16 za'a
cigaba da saurare k'arar.
"Hmm!
Barrister Amina ta yi ajiyar zuciya had'e da cewa karki damu bebs insha Allah za ki
yi nasara, Allah yana tare da ma su gaskiya.
"Haka ne bebs thanks for the courage me.
You're welcome!
Suka yi shiru na few seconds daga bisani Barrister Amina ta kawo karshen shiru nasu
ta hanyar cewa, bebs kamar yadda ki ka bani shawara na yi istahara akan mutume nan
na yi, ba zan 6oye miki ba bebs akwananki nan kullum sai nayi mummunan mafalki
wanda na rasa gane me hakan yake nufi.
*DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE
WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:44 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Na Jeeddah Aliyu
Free page
*6*
Ajiyar zuciya Barrister Zarah ta yi ta gyara zamanta, ta fuskanci Barrister Amina
ta ce ki kwatarda hankalinki bebs insha Allah ba abinda zai faru sai alkhairi, ke
dai ki cigaba da addu'a zan kuma je waje Malam(tana nufi kakanta da ya haifi
mamanta) ya taimaka miki da addu'a.
"Numfashi Barrister Amina ta sauke kafin ta ce gashi gobe ne ranar zuwanshi,
zuciyata cike take da fargaba had'uwa da shi.
"Murmushi Zarah ta yi ta ce kidaina fargaba bebs, insha Allahu alkhairi ne zai
biyo baya.
Allah yasa.
Cewar Amina.
***----***----****
*8:34pm*
Aliyu na zaune a falonshi yana duba wasu documents na wani project da yake yi, Zee-
zee ta yi sallama ta shigo ya amsa tare da d'agowa ya dubeta sanye take da 'yar
fingilalliyar riga wacce ta wuce gwiwarta, kanta ba d'an kwali ta gyara gashi ta
sai kyalli yake.
"Ya Ali momma ta ce ka zo tana so ganinka.
Mtsss.....ya ja tsaki cikin hargowa ya ce wai Zainab meke damunki ne?"
wannan wacce irin banzar shiga ce?"
Dube yadda ki ka fito tun daga apartment d'inku har zuwa nan, baya kinsan gidanan
cike yake da maza wanda ba muharamanki ba.
"Ya motsa fuska Zee-zee ta yi tana wani turo baki, yi hak'uri Yaya Momma ce ta
azalzale ni akan lalle sai nazo na kira ka, insha Allahu ba zan sake fitowa a haka
ba.
Shikenan je ki ki ce mata ina zuwa.
Ficewa ta yi yayin da ya shiga tattara takardu da ya zube akan carpet, sannan ya
fice a falo ya tararda momma ta hard'e akan sofa.
''Barka da hutawa momma!
Yafad'a had'e da zaunawa akan kujera da ke facing d'inta.
Shin da gaske ka amince da za6in mahaifinka, kuma gobe za ka tafi Yola ka gana da
ita?"
Gyara zama ya yi kafin ya ce Eh....haka ne har nayi magana da Jamal zai rakani,
morning flight za mu bi saboda mu dawo da wuri.
Har ya dasa aya azancenshi tana mishi kallon k'asan ido, wanda ke nuna mamakinta a
6oye.
"Sultan!
Ta kira sunanshi tana mai sauke kwayar, idanunta akan fuskarshi
Na'am momma!
"Ba na gayamaka kada ka amince da aurenan ba, da yake ka fi so farin ciki
mahaifinka akaina shine ka amince ko?"
Girgiza kai ya shiga yi Allah momma ba haka bane daga ke har shi inaso farin
cikinku, na amince da aure ne ba don raina yana so ba sai don na farantawa Daddy
rai.
Amma wallahi momma babu son aure ko k'ank'ani a zuciyata, bana kuma tunani ko da
anyi aure zan sauya ra'ayina.
"Sai anan gaba za ka gane kuskure da ka yi na amicewa da aurenan.
Momma....please karki k'aramin damuwa akan wacce nake ciki sanin kanki ne banso
aurenan ko sunanshi naji an fad'a sai gaba na yafad'i to miyasa za ki d'aga
hankalinki?"
Aure dole ne banaso ayi ma Sultan, shiyasa ka ga na shiga damuwa amma tun da ba ka
ciki damuwa Shikenan Allah yasanya alkhairi.
Amin!
Yafad'a had'e da mik'ewa momma ni zan koma ciki akwai aikin da nakeso na k'arasa.
Bai jira jin ta bakinta ya juya ya fice ta bi wani irin kallo mai wuyar fassarawa,
daga bisani ta yi kwafa.
***---***-****---****
*YOLA*
*10:07am*
Da sanyi safiyar assabar Barr Amina na kwance akan gadonta, ta k'uddudune cikin
wani lallausan blanket barci take yi cikin natsuwa da kwanciyar hankali musanmman,
kasancewar yau bata zuwa court shiyasa ta baje abinta tana sauke gajiya.
"Ummi ta turo k'ofar d'akin, ganin Amina kwance yasa ta d'an girgiza kai tare da
duba wall clock wanda ya nuna k'arfe 10:07am.
Matsawa tayi gaban gadon ta yaye blanket d'in jikinta ta shiga girgiza ta had'e da
kiran sunanta Minal......Minal! Ki tashi hakanan mana ko kin manta yau za ki bak'o
ne?"
Omg....!
Tafad'a cikin magagin barci.
Bubbuga k'arfata Ummi tayi ta bud'e idanu da kyar ta kalli Ummi, sannan ta tashi
zaune tana murtsike idanuwanta masu cike da zallan barci, a sanyaye ta ce Ummi ki
barni nayi barcina ki fad'awa Asabe ta shirya masa meals.
Tak'arasa magana had'e da yin doguwar hamma, alamar barci bai isheta ba.
"Harararta Ummi tayi kafin ta ce banaso shirme Minal ki tashi maza Asabe za ta
tayaki da wasu ayyuka, ba wai ki sakar mata aikin duka ba.
"Yatsina