Author : Jidda Aliyu Category : Drama
kai ka
hau gado.
"Murmushi ya yi batare da ya furta uffan ba ya mik'e ya hau gadon ya kwanta,
yayin da tayi tsaye tana kallonshi.
"Zo ki kwanta barrister banaso kallon nan naki mai kama da na tuhuma.
"Tayi murmushi batare da ta musa ba ta isa kusa da shi ta kwanta, yaja duvet ya
rufa musu ya shak'i k'amshin turarenta ya lumsashe idanuwanshi bayan ya sauke
zazzafar ajiyar zuciya.[7/27, 12:04 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA
ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*25*
Suna gama waya agurguje ta shiga wanka.
"kafin tashiga bathroom saidai ta nemo disposed cup, tayi fitsari aciki duk da har
zuwa lokaci atsorace take.
Musanmman lokaci da tazo fitsari a cup d'in tana kammala wanka tafito daure da
towel ta d'ebo layoyin inda ta ajiye su ta shiga bathroom ta zubesu a k'asan
tiles , jikinta na rawa saboda tsananin tsoro ta dauko cup d'in fitsari gabanta na
fad'uwa ta juye fitsarin akan layoyin, abinda bai fi 20 seconds ba hayyak'i ya
turnuk'e gaba d'aya bathroom sai kace gobarar wutar nepa.
A rikice barrister A ta balla da gudu ta nufi k'ofar fita.
"Har ta rik'e handle sai kuma taja birki tayi tsaye a k'asan zuciyarta, ta ce
bari dai na tsaya naga abinda zai turewa buzu nad'i.
Masu iya magana nacewa matsoraci bashi gwani.
Yayin da hayyak'i ya dinga bin window bathroom d'in yana fita da yake gilashi
window a bud'e yake sai net ne kawai arufe, tanan ciki net ya dinga fita har wurin
ya washe kaman hayyak'i bai wanzu ba.
Gani haka yasa barrister A tadawo cikin bathroom din ga mamakinta sai taga babu
layoyin, sun zama hayyak'i.
"Naunauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin faruwar wannan al'amari, sai yau
tak'ara yarda da furuncin malam bahaushe da yake cewa tsafi gaskiyar mai shi.
Ba shakka irin wannan sihiri sai mai k'arfin imani sai kuma wanda Allah ya tsare.
"Ruwa zafi ta d'ebo ta wanke wurin duk da haka saida ta kunna tap na ruwan sanyi
tak'ara wanke wurin sannan tafice.
"kayanta tasaka tayi sallah had'e da neman tsarin Allah daga shed'anun aljanu
da mutane.
Tana zaune downstairs falo su Zee-zee suka dawo daga school ko apartment d'insu
basu shiga ba suka yo nata, sosai tasake musu fuska anan suka ci abinci sai santi
da yaba mata suke yi.
"Cikin siga ta kwarewa da aikinta take tambayarsu dangane da ciwon Teema, basu
kawo komai aransu ba suka shiga bata labarin duk abinda suka sani akan ciwon nata,
har magani da momma take bata mai wari saida suka gayamata.
"Tattara bayanan nasu tayi ta adana a kwakwalwarta.
"Kamar yadda tafaru jiya hakan ne yasake faruwa, lokaci sallar la'asar ya yi tai
sallah su kuma suna zaune suna kallo.
"A wannan karon tasha alwashin tambayarsu, kasancewar lamarin gidan yanzu ya
dawo abin tsoro agareta.
"Yan matan momma dukanku kuna menstruation ne?"
Cikin rashin damu da tambayarta ta Meena ta girgiza kanta, had'e da cewa a'a....me
ki ka gani matar yaya?"
Gani nayi lokaci sallah har yana k'ok'arin wucewa, amma ba ku tashi ku ka yi ba.
"Kusani ba k'aramin bala'in bane musulmi ya dinga wasa da lokutan sallah,
especially sallar la'asar.
"Bambancin musulmi da kafiri shine sallah, miyasa za ku dinga wasa da ita?"
Jikinsu ya yi masifar sanyi kunya ta lullu6esu, da suka tuna ba koda yaushe suke
cika sallah ba.
Idan suka yi sallar asuba ba lalle bane su yi azhar da la'asar ba, sai sun zo
kwanciya suke yi sallar isha'i, ranarda suke ji k'arfi sai su ranka gaba d'aya amma
zance na gaskiya sallah bata damesu ba.
"Saboda momma ya kamata tayi musu fad'a sai akayi dace ita ma ba koda yaushe
take yi ba, sai tayi mata dad'i.
Daddy kuma ba mazauni gida bane balle yasan wainar da suke toyawa, kuma uwa-uba
suna da k'arancin ilmin addini.
Gani yana yin da suka shiga yasa barrister A tayi amfani da wannan damar, ta shiga
yi musu nasiha da tsoratar da su da irin azabobin da Allah[S.W.T] ya tanadarwa masu
yi wasa da sallah.
Sun tsorata ba kad'an ba sun kuma yi nadama, cike da jin dad'i barrister A ta ce ku
tashi ku je kuyi, ku dage ku rok'i gafarar ubangiji domin shi mai yafiya ne.
"Godiya suka yi mata sannan suka nufi bathroom, domin yin alwala ta bi su da
kallon tausayi saboda tayi imani rashin dace da uwa tagari ne ya janyo musu hakan.
"around 9:30pm Aliyu ya shigo gidan tun safe da ya fita sai yanzu ya dawo,
lokaci da ya shigo main parlour tana d'akinta da ke upstairs bai nemeta ba ya wuce
nashi bedroom ya yi wanka, ya shirya ciki three quarter da rigar armless farare as
usual yana k'amshin suave perfume karo na farko da ya ji yana son ganinta, shiyasa
ya nufi d'akin nata ya turo k'ofa ya shiga da sauri ta waiga waya manne a kunnenta
ga alama tana waya koda ya shigo, tsaye ya yi ya jingina jikinshi a jikin k'ofa
yana mata kallon nan nashi na k'asan ido.
"I'll will call you later tafad'a had'e da hanging up, sannan ta dawo da
ganinta akanshi "sannu da zuwa Yalla6ai...bansan kadawo ba ya office?"
Ta ya za'a yi ki sani bayan kina d'aki a k'unshe kamar amaryar k'auye.
Tunda yafara magana bai dauke ganinshi akanta ba.
K'ayattace murmushi ta yi kafin ta ce waya sani ko ni amarya k'auye ce.
Ni dai mu tafi na ba ka abinci maybe ba ka ci komai ba tun breakfast.
Ya tabe baki yana cigaba da kallonta ba ko kyaftawa, mamaki ne ya kamata ko me yake
kallo a jikinta ta bi jikinta da kallo boomshort ne a jikinta sai top mai k'aramin
hannu iya cibiyarta bai k'arasa rufe bombom d'inta ba sai gashinta da ya sha gyara
tasake shi ya sauka a shoulders d'inta, iya ganinta bata ga wani abu a jikinta da
yake kallo ba saidai in reni hankalinshi ne ya motsa.
"6ata fuska tayi ta dubeshi still yana mata mayattace kallonan nashi gira
d'age sai taga kaman yana yinshi ya sauya a zaman da tayi da shi bata ta6a ya yi
mata irin wannan kallon ba.
"Yalla6ai.....lafiya"
Da sauri ya kauda fuska had'e da furta nothing"
"Cike da mamaki ta ce "nothing....then why are you looking at me like stranger?"
juyawa ya yi batare da ya bata amsa ba, jikinta ya yi sanyi kodai akwai laifi da
tayi mishi batare da tasani ba.
"ko don ya ganta da bomshort ne?"
Ta6e baki tayi da tayi niyyar doura kimono akan kayan nata, amma yanzu tafasa ko ba
komai za taji dad'i indan ya cigaba da kallonta.
"Saida tak'ara fashe jikinta da turare sannan ta sauko k'asa yana zaune a dining
area talla6e da kumatunshi, I'm sorry Yalla6ai na barka kana jira tana magana ne
had'e da daukar plate tayi mishi serving ta tura gabanshi.
"Ajiyar zuciya ya yi yana cin abinci lokaci zuwa lokaci yana mata fitinanne
kallonshi, mai jefata cikin wani yana yi abinda yake k'ara daure mata kai idan yana
da magana me zai hana ya furta ba ya fitine ta da kallo ba.
Gani kallon nashi ba mai k'arewa bane yasa ta mik'e za ta bar mishi wuri, ya had'e
rai ya ce ke....koma ki zauna ai ban sallame ki ba.
Ya k'arasa magana yana cije lips dinshi.
Komawa tayi ta zauna ya ce ya akayi ne naga ba ki ci abinci ba, ko kin k'oshi ne?"
D'aga eyebrows d'inta ta yi ta ce bana jin yunwa.
Ya ta6e baki ya cigaba da cin abincinshi, yana kammalawa ta tattare plates ta
shigarda su kitchen ta wanke, koda tadawo main parlour ya koma bedroom dinshi da ke
sama, bata yi k'asa da gwiwa ba ta bishi yana zaune a gefen gado yana waya.
Ya dauki dogon lokaci yana magana a wayar, kafin ya yi hanging up ya dawo da
ganinshi akanta.
Ya mik'e ya shiga bathroom ya wanke bakinshi ita kuma ta nemi gefen gadon ta zauna
tana jiran fitowarshi, ta ji ko za'a had'a mishi coffee.
Ya fito ya isa kan gadon ya kwanta.
Ta bishi da kallo daga bisani ta ce Yalla6ai za ka sha coffee?"
Ya mik'e zaune.....ya cire rigar jikinshi da sauri ta kauda kanta, ya dubeta da
lulu eyes dinshi yana lumshe su...."in a very romantic voice ya ce zo ki yi min
massage gaba d'aya jikina ciwo yake min.
Yana k'arasa magana ya kwanta a ringingine ya kuma lumsashe idanuwanshi.
"Ta tsorata matuk'a da jin kalamanshi, saboda bata yi tsanmani jinsu daga
bakinshi ba.
"Aminaaa!
Kamar daga sama taji ya kira sunanta wanda iya saninta sau d'aya ya ta6a kirata da
sunan nata saidai ya kirata da barrister.
Ta mik'e ta isa kusa da shi ta zauna tasaka soft hands dinta akan jikinshi tana
mamatsa masa ga66o6inshi ahankali.
"Wani irin sanyi dad'i ya yi mishi ziyarar bazata, ahankali yake sauke numfashi
tsawon lokaci ta dauka tana mishi massage jikinshi, yadda ta ji numfashinsa yana
sauka yasa tagano ya yi bacci ta janye hannayenta ta ja duvet ta rufe mishi rabin
jikinshi, ta kashe bulb sannan ta nufi nata d'aki zuciyarta cike da annuri tafara
janyo hankalin mijinta.
Washe gari da wuri ta tashi ta shirya masa lafiyayyen breakfast ta kuma ca6a
kwaliya cikin mini skirt da 'yar figillaliyar top bata saka bra ba, boobs dinta
kamar zasu yaga rigar su fito.
Lokaci da ta kalli mirror saida kunya ta kamata, tana tunani ta yadda zata
fita gabanshi da wad'annan kaya, da tuna irin kallo da yake mata jiya kallo ne mai
cike da ma'anoni da yawa.
"Ta shirya janyo hankalinshi zuwa gareta ko ta kowane hali, yanzu ta fahimci wannan
shiri nata ya fara aiki baza tayi wasa da damarta ba.
"With full confidence ta bud'e d'aki ta sauko downstairs, kaitsaye ta wuce dining
ta zauna tana jiran fitowarshi.
"Bata wuce 5 minutes da zama ba sai gashi ya fito sanye da suit, k'afarshi sanye
da wing tip cover shoe sai zuba k'amshi yake yi hannunshi na dama rik'e da
briefcase.
"Kaitsaye ya wuce dining ta ja mishi kujera ya zauna "Good morning sir!
Tafad'a batare da ta kalleshi ba "morning how was your night?"
Tana murmushi ta ce "Alhamdulillah!
Abincin da tayi mishi serving ta ajiye agabanshi, ya d'ago suka had'a ido ya yi
mata sanyayye murmushi can k'asan mak'oshi ya ce kinyi kyau ya k'arasa magana yana
tsareta da idanuwanshi.
"Thanks!
Tafad'a kaman mai koyon magana flasks d'in ruwan zafi ta dauka tana tsiyaya ruwa a
mug zata had'a mishi tea, yadda yake kallonta ta ji duk ta tsalgu "by
mistake......flasks d'in ya zame ruwan zafi suka zuba mata ahannu da sauri ta dire
flask tana yar6e hannu ta hau sakin ihu "auuchhh.....hannuna....ahhh....auuchh" Da
sauri ya ture kujera ya tashi tsaye kawo naga hannu garin ya ya ki ka k'ona
hannunki?"
Ta mik'a mishi hannun nata kaman zatai kuka.
Iskan bakinshi ya shiga haura mata kaman shima zai saki kuka sai faman cewa
sorry....sorry....ruwan sanyi ya dauko ya zube mata a k'onuwar har wurin ya yi ja
ko za mu je hospital a dubaki ya d'ago kanshi yana kallonta girgiza kai tayi ba
wani k'onuwa mai yawa bane zuwa anjima k'adan zai daina, duk da haka saida ya dauko
wani cream da ake sawa k'onuwa a first aid box ya shafa mata.
"Yana cin abinci yana mata sannu yayin da ita kuma sai murmushi take yi, da ya
kammala cin abinci ya kalleta ya ce tunda bakida lafiya ki nemi wurin ki kwanta
kada kiyi aiki komai, zan biya ta flat din momma ta turo d'aya daga cikin housemaid
d'inta suyi miki 'yan aikace-aikace kafin akawo miki naki.
"ko kitchen ban yarda ki shiga ba, zan aiko Isah direba ya kawo miki lunch.
"Yalla6ai ba sai ka aiko shi ba zan iya ba fa wani ciwo bane sosai.
Na fahimci kina so wasa da lafiyarki.
Ba haka bane Yalla6ai Allah zan iya.
Shut up......I hate people to argue with me....sai kiyi abinda ki ke so in fact
jikinki ne ba nawa ba don ma kin samu na nuna damuwana akanki.
Mtssss.....yak'arasa magana da tsaki ya dauke briefcase ya fice afusace.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:04 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*26*
Da sauri ta bishi tana kiran sunanshi "Yalla6ai....Yalla6ai!
Don Allah kayi hak'uri ka tsaye ka saurareni.
Ba nufi na nayi argument da kai ba.
Yalla6ai......I said I'm sorry"!
Tafad'a cikin d'aga murya saboda har ya kai compound ita kuma tana tsaye a bakin
k'ofar fita main parlour, yana yin kayan da ke jikinta ya hanata ta bishi tana
kallon direbanshi ya bude masa mota ya shiga, har suka fice daga gidan tana kallo.
"Gyad'a kai tayi sannan tadawo cikin parlour ta zauna, tana backward d'in abinda
ya faru wani shegen murmushi tayi mai nuna tsantsan farin cikinta.
***"""****"""*****
Momma tsaye a cikin bedroom d'inta sai faman sintire take yi abin duniya yana so ya
yi mata yawa, ta kira wayar Jarumi yafi a kirga a kashe tun jiya da tayi waya da
shi har wayewar garin yau, bata ji wani feedback daga gareshi ba.
"Tunanin mafita take yi taji wani heavy knock kamar za'a cire mata kyaure, da
hanzari ta nufi k'ofar tayi unlocked Daddy tagani fuskarshi ba bu annuri sai kace
wanda aka aikowa da sak'on mutuwa.
"Sai aika mata da mugun kallo yake yi, ta hadiye yawun fargaba muryarta yana
rawa ta ce alh....a...ji...lafi....ya ka ke min irin wannan knocking?"
"K'ara 6ata fuska ya yi a ganinshi tana mishi tambayar reni ne cikin wani irin
fushi ya ce miyasa duk yawan housemaid d'in gidanan da ba ki tura wasu daga cikinsu
flat d'in sultan su dinga yi ma matarshi aiki ba, har sai ya kira ya rok'a?"
Ni narasa meke damunki Zaituna kwakwalwarki yadawo kaman na dusa, sam ba kya aiki
da shi.
"Hanta cikin momma ta motsa ta dask'are kaman statue bakinta a bud'e dogon
tsaki da Daddy ya ja mtsss......ya dawo da ita natsuwarta ya juya ya fice ta bishi
da kallon mamaki.
"Na shiga uku....meke shirin faruwa da ni?"
Kada zance boka ya tabbata Aliyu zai auro yarinyar da zata rusamin al'amurana,
tsawon zamana da Alhaji bai ta6a yi min shouting irin haka ba.
Ba tsinane irin Jarumi duk shine silar jefani cikin wannan halin.
Cikin rashin sanin mafita kaman za ta fashe da kuka tanemi gefen gado ta zauna.
****""****"""*****
Aliyu yana isa office ya kira wayar momma ya ji layinta busy, sai ya yi decided ya
kira Daddy tunda yana gida yafad'a mishi buk'atarshi, wannan shine dalilin da yasa
Daddy ya shiga bedhroom d'in momma yana mata fad'a.
"Yana gama waya da Daddy.
uncle Suraj ya shigo office d'inshi cike da farin ciki ya mik'e ya yi hugging
uncle yana fad'i....what a pleasant surprised uncle?
Murmushi uncle ya yi kafin ya ciro Aliyu daga jikinshi, suka yi shaking hands suka
nufi kujeri da suka k'awata office d'in suka zauna.
Aliyu yana blushing ya dafa cinyar uncle suraj ya ce uncle ashe abinda ka ke
fad'a gaskiya ne.
Duk da uncle bai fahimci inda zance nashi ya dosa ba, sai ya yi dariya ya ce ni fa
ban fahimci zance da ka ke yi ba Aliyu?"
"Uhm......uncle da ka ke cewa aure rahama ne sai yanzu nagane zancenka gaskiya ne,
ba aure kadai ba uncle har mata rahama ne.
"Ya karasa magana yana dariya.
Shima uncle dariya ya yi ya daki shoulder Aliyu yana cewa ka ji min shak'iyin yaro,
wato sai yanzu da mu kayi maka aure ka d'add'ani zuma 'ya mace ka fahimci haka.
"Aliyu ya yi dariya har sautin dariyar nashi ya fita, ya ce "Allah uncle ba
abinda nayi in fact bana jin son Amina a zuciyata, amma kuma ina ji a jikina I
can't do without her....uncle Amina ta iya girki abincinta so delicious komai nata
dabam ne da sauran mata.
Bana jin za'a dauki longtime za ta yi winning zuciyana.
"Komai nata perfectly the way I like, kasan me uncle?"
Uncle suraj ya yi nodding head saboda ya zama speechless, yadda Aliyu yasaki baki
yana zance mace abinda tsawon rayuwarshi baita6a gani ya yi ba.
"Idan Amina tana bacci snoring take yi.
Ya k'arasa magana kaman wani wawa, ga shegiyar blushing da yake yi mai ban haushi.
"Sosai uncle yasa dariya har da dafe ciki yayin da Aliyu yake cigaba da taya
shi.
Bayan sun gama dariyar nasu uncle suraj ya kalleshi da murmushi akan fuskarshi, "ya
ce Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a tagari ka kula sosai saboda kasan Zaituna
ba so auren naku take yi ba.
''Amin......uncle amma ni sai nake gani da farko don na nuna banaso auren,
shiyasa momma bataso yanzu Kuma tunda inaso ita ma nasan zata so.
Uhm.....haka ne kuma kasan iyayye mata su fi supported d'in 'ya'ya akan abinda suke
so.
Murmushi Aliyu ya yi kafin ya ce ai shiyasa uncle nima nake ji da mommana.
"Mik'ewa uncle ya yi yana cewa bari na lek'a office ka turo kamal ya kawo min
documents d'in da muka yi magana a waya.
Uncle yana k'arasa magana ya fice.
Aliyu ya shiga tunani yadda ya shak'u da uncle suraj, duk da ya kasance k'anin
mahaifinshi.
Shak'uwar tasu ta samu asali tun Aliyu yana yaro, shiyasa Aliyu ya dauke shi
tamkar friend d'inshi duk wani secrets dinshi baya 6oyewa uncle kaman yadda shima
uncle yake sharing nashi secret da Aliyu, idan ka ga sometimes yadda suke fira za
ka dauka age mate ne.
Uncle suraj ya jima bai yi aure ba wanda gaba d'aya family anrasa dalilinshi na
k'in yi aure.
duka yin aurenshi a yanzu ba zai wuce 10 years ba yaronshi d'aya.
***----***---***
Tun lokaci da Aliyu ya fita take kwance a falo hannunta sai zugi yake mata,
musanmman yanzu da yafara jan ruwa ya yi bororo tana cikin wannan halin kiran
barrister z ya shigo wayarta, jikinta yana rawa tayi