Author : Jidda Aliyu Category : Drama
ce ta karad'e mata kunne shigo likita ki ganta.
"Da sauri ta nufi d'akin da taga baaba laraba ta shiga, tana jefa k'afarta cikin
d'akin gabanta ya yi mashahurin fad'uwa har batasan lokaci da ta dafe k'irjinta da
dukan hannayenta ba a k'asan zuciyarta kuma ta furta....hasbunallahu waa'imaal
wakil.....!
Sosai tadawo natsuwarta tasami damar k'arewa Maryama da ke daure da sark'a
k'afafunta da hannaye, abin gwanin ban tausayi.
"kanta na sunkuye tana rera kuka marar sauti, sai ka saurara sosai za ka iya jin
sautin kukan nata ba sai ka tambaya ba kasan na bakin ciki ne.
"Wani irin tausayinta ne ya yi ma barrister A dirar mikiya a gadon zuciya, cike
da rashin tsoro ta durk'usa gabanta sai lokaci Maryama ta d'ago da fuskarta wacce
ta rine ta koma bak'a, gurbin idanuwanta ya dusashe ya yi bak'i wulik.....yayin da
lips d'inta suka bushe kaman 6a66ariyar fadama.
"Ta k'urawa barrister A idanu ba ko kyaftawa kaman tanaso ta tuna idan ta ta6a
ganin wannan kyakyawar fuska saidai kash.....kwakwalwarta bazata bata had'in kai
ba.
"Sai kawai tasoma k'ok'arin d'ago da hannunta mai daure da sark'a ta ta6a
barrister, zaman 'yan bori barrister A tayi dabasss.....ta d'ago da ganinta ta
kalli baaba laraba da ke tsaye tana kallonsu ta bud'e bakinta da kyar ta ce "baaba
tana duka ne....?"
"Baaba laraba ta girgiza kanta tana kya6e baki, ta ce ba ko d'aya tsabar mugunta
ne da zallunci irin na Hajiya Zaituna yasa tasaka akai mata irin wannan d'auri na
k'ask'anci, amma don Allah yarinya karki fad'a mata abinda nace.
"zazzafar ajiyar zuciya barrister A ta sauke kafin ta ce karki damu baaba ba zan
gayamata ba, asalima ni ba likita bace.
"Zare idanu baaba tayi cikin kad'uwa tace wacece ke 'yar nan....?
Mekika zo yi anan...?
Sunana Amina nice amaryar Aliyu baaba ki kwantarda hankalinki wallahi ban zo
wurinan don in cutarda ku ba.
"Baaba ina da tarin tambayoyi da nakeso ki bani amsoshi su, amma bansaniba ko zan
sami had'in kanki.
"Baza ki samu ba muguwa wato tanan Zaituna ta bullo, shine zata yi min ije ki zo
ki bugi cikina ko zan fallasa sirrinta to ba abinda zan fad'a rayuwata da ta
Maryama tafi min komai, zo ki fita tak'arasa magana had'e da finciko hannun
barrister A ta nufi k'ofar fita da ita yayin da barrister sai magiya take mata don
Allah.....baaba ki tsaya ki saurareni duk abinda kike zato akaina ba haka bane ni
ba muguwa bace, inaso na taimake Maryama she really need my help.....don Allah ki
d'an dakata koda d'aya daga cikin tambayoyina ne ki amsa min.
"Wulgata waje baaba tayi scarf d'inta da ya fad'i k'asa garin janta da Baaba ke
yi ta dauko ta jefa mata a fuska ta datse k'ofar da key wanda tun lokaci da ta
budewa barrister A tashigo yana rik'e da hannunta.
***---****----*******
Tana dawowa flat d'inta takasa zaune ta kasa tsaye, sai takai gwaro takai mari
tanaso tasan cikkake labarin maryama, wacece ita...?
ya akayi ta haukace...?
Kuma menene matsayin Baaba laraba awurin maryama...?
There's is lots of questions da take da buk'atar amsoshinsu, amma wa zata tambaya.
yini ranar gaba d'aya cikin tunani tayi shi gani taji sauki hannunta ga kuma tarin
tunani dole tana buk'atar, abinda zai d'ebe mata k'ewa sai kawai ta nufi kitchen ta
doura dinner kasancewar Aliyu bai cika cin abinci mai nauyi ba yasa ta dafa pasta,
tayi miyar hanta da k'oda da had'in conslow sai meat balls & patato da ya nuna ta
juye a warmers ta jera a dining table, gani akwai sauran lokaci kafin magarib tayi
sai kawai ta shiga had'e lemon carrots tasaka a fridge domin ya yi sanyi, agurguje
ta nufi upstairs bedroom tayi wanka had'e da alwala koda ta fito anfara kiran
sallah, ta tsane jikinta da k'aramin towel sannan ta daura zani tasaka hijabinta na
sallah tayi sallah.
"Tana gama sallar magarib ta shiga azkar kafin lokaci sallar isha'i ya yi.
Bayan tayi sallah isha'i ta mik'e ta linke pryamat da hijab ta adanasu ma'ajiyarsu,
taja stool ta zauna gaban mirror ta mulke fatar jikinta da lotion mai k'amshin
gaske, ta gogawa fuskarta powder kad'an ta k'awata lips d'inta da pink lispstick ta
gyara gashin kanta tayi mishi style mai kyau ta bude closet d'inta tayi tsaye tana
k'arewa kayan da ke ciki kallo can dai ta zaro romper red colour pants kawai ta
sanya bata saka brazier ba rigar ta sauka iya rabin cinyoyinta, ta bi lungu da
sak'o na jikinta da pure royal & asarar alhub perfumes ta dauki k'amshi mai jan
hankali da tsinke zuciyar d'an-namiji tasaka gladiator shoe irin mai igiya nan da
ake daurewa ta daure igiya ya tsaya dai-dai gwiwar k'afarta, bata rufe gashin kanta
ba saboda style d'in da tayi mishi.
"Ta sauko downstairs falo ta zauna a one sitter ta kira barrister z ta bata
labarin maryama, alokaci da barrister z taji labarin ta kad'u ba kad'an ba cike da
zallan mamaki ta ce bebs wacece wannan mahaukaciyar....?
Menene alak'arta da gidan....?
I don't know bebs.....nima I was shocked da naga matarnan daure da sark'ar har zuwa
yanzu abin ya kasa fita daga idona.
"Gaskiya al'amarin akwai rikitarwa ki daure bebs ki nemo cikkake labarin maryama,
tabbas akwai wani 6oyayye sirri a haukan nata.
ba ko shakka thats your wicked mother in law is behind of everything.....
"k'arfaffiyar ajiyar zuciya barrister A tayi kafin ta ce "kaman kin shiga
tunanina bebs nima zargin da nake yi akanta kenan, saidai banida kwakwarar hujja.
"Gaskiya ne yanzu abinda ya kamata ki yi ki cigaba da zuwa flat d'in a asirce
har sai baaba ta fayyace miki komai, domin daga bakinta ne za ki samu hujja wacce
babu k'arya aciki.
"Haka ne bebs nagode da shawarwarinki sai da safe suka yi sallama.
Bata jima da gama waya da barrister z Aliyu ya dawo ya shigo da sallama dauke da
bakinshi.
"Ta mik'e da sauri tana wanke shi da tsadadd'en murmushinta, tsaye ya yi yana
kallonta saboda kwalliyarta ba k'aramin gigita shi tayi ba, shu'umin kallonan nashi
na k'asan ido yake aika mata yayin da yake tsotsar lower lips d'inshi tsigar
jikinta ya tashi yarrrrr.....tasaki 6oyayyiyar ajiyar zuciya.
Yanufo ta walking majestically yana wani shegen smile na gefen baki, cikin sauri
ta sadda kanta k'asa gabanta na fad'uwa ya iso daff....da ita tana jin heart beats
d'inshi, yasaka soft hands dinshi ya d'ago face d'inta, yana kallon cikin
idanuwanta yana mata shegen kallo still yana lasar lower lips dinshi......Ba zata
iya jure cigaba da kallon nashi ba, shiyasa ta runtse idanuwanta gamm.....ya matsa
fuskarshi daff....da nata kaman daga sama taji saukar tattausan lips dinshi akan
nata ya saki mata wani hot peg....wanda ya haddasa mata mutuwar jiki zuciyarta ta
cigaba da bugawa very past kaman zata zaga k'irjinta tafito, da kyar ta tattaro
raguwar k'arfin da ya rage mata ta matsa daga jikinshi kad'an da sauri ya rik'o
waist d'inta da hannayenshi biyu, ya motsata sosai yana sauke mata numfashinsa akan
fuska, yana goga karan hancinshi akan nata.
"Wani irin shock suke ji yana jansu saboda dukansu wannan shine first time da
suka ta6a tsintar kansu acikin irin wannan yanayin, daff....da kunnenta ya kai
bakinshi cikin sexy voice ya kira sunanta Aminaaaa......!
Yadda yaja sunan nata iskar bakinshi tashiga kunnenta yasa, saida ta hadiye yawu
kafin ta amsa da uhmm....!
Inaso lips d'inki kin bani izzini na tsotsa...?"
Ba k'aramin gigita brain d'inta kalamanshi suka yi ba, da kyar ta iya girgiza
kanta.
"Ya shagwa6e murya cikin sexy tone ya ce please....Amina koda k'adan ne ba zan yi
da yawa ba.
K'arin bugawar zuciyarta ya tsananta ta d'an dafe k'irjinshi da hannayenta, hakan
ne yak'ara d'imauta shi ya matse waist d'inta sosai, kin amince Amina...?
Akaro na uku yasake tambayarta tayi nooding head saboda babu bakin magana gaba
d'aya tayi loosing control wani shauk'i take ji yana yawo a jininta bata dawo
natsuwarta ba yasake connecting soft lips d'insu ya shiga bata hot French kiss
yayin da hannayenshi suke squeezing bayanta, batasan lokaci da tayi rubbing
hannayenta a bayanshi ba.
"Hakan ya k'ara mishi k'arfin gwiwar cigaba da kissing d'inta tare da romancing
all over her body especially boobs d'inta da ya ji su very softly saura
kirisss....numfashin barrister A yafita daga gangar jikinta k'afafunta suka dauki
rawa, kaman zata fad'i k'asa da sauri ya taro ta ya yi hugging d'inta tightly kafin
ya cire bakinshi daga nata.
Alokaci d'aya suka saki zazzafar ajiyar zuciya, yana shisshinar neck d'inta closing
his two eyes sun dauki six good minutes ahaka sai saukar ajiyar zuciyarsu kake ji,
daga bisani ya saketa ya rad'a mata wifey.....muje ki had'amin ruwan wanka na d'ebo
gajiya throughout a conference hall na yini muna meeting ga 'yar uban yunwa da nake
ji.
"Kanta na kallon k'asa tayi murmushi acikin zuciyarta kuma ta ce "d'an duniya
kawai saida ka shanye min baki sannan ka tuna da kana jin yunwa, ka ji da shi wai
ciwon ajali a d'an yatsa...lol
Ya d'ago fuskata yana mata sanyayye murmushi ya yi holding nose d'inta yana
kallonta kafin yasaki nose d'in nata ya yi kiss forehead d'inta ya haura steps,
yana fad'in ke nake jira barrister karki shanya ni.
"barrister A ta dauki few minutes tana jinyar dafin da Aliyu yasake mata,
kafin tadawo natsuwarta wani irin nishad'i mai cike da zallan farin ciki ya yi mata
ziyarar bazata tadaka tsalle had'e da furta....yessss!
Da sauri ta rufe bakinta kada ya jiyo ihunta class d'inta ya zube.
Hummm......ka ji su barrister bayan tagama shan mazankwaila.....lol.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:17 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*29*
Koda ta isa d'akinshi har ya cire kayan jikinshi yana sanye da bathrobe, kallo
d'aya tayi mishi ta dauke kanta.
Ta wuce bathroom yayin da ya bi bayanta da kallo ta cika masa bathtub da ruwa masu
d'umi-dumi ta zuba turaren wanka aciki, tana fitowa ta ganshi tsaye bakin k'ofar
bathroom.
Na had'a ruwan.
Tafad'a batare da ta kalleshi ba, ya yi murmushi ya ce nagode my wifey.
"Ta d'an murmusa tanufi kayan da ya cire ta linke su ta mayar a closet saboda
basu yi dirty ba.
Boxer da vest dinshi ta saka su a laundry basket.
Kafin ya fito har tafice zuwa dining area tana cikin yi mishi serving ya iso taja
mishi kujera ya zauna, sosai yaci abincin nata sai santi yake hade da yaba mata.
Bayan sun kammala ya wuce bedroom dinshi ita ma ta wuce nata, ta sauya kayan
jikinta zuwa na bacci, sannan tanufi d'akinshi
Sosai ta kalleshi kafin ta ce "Yalla6ai koda akwai wani abinda da kake buk'ata nayi
ma kafin na kwanta...?
Hannunshi ya nuna akan gado had'e da furta bissimillah....je ki kwanta inda ina
buk'atar wani abu zan tashe ki.
Sosai ta dubeshi tana d'an siriri murmushi kaman za tayi magana sai kuma tafasa,
ta nufi gadon ta kwanta tana kallonshi ya kashe bulbs ya kunna diff one ya dauko
laptop d'inshi yana tura wasu bayanai tsawon lokaci ya dauka kafin ya rufe laptop
d'in, atunaninshi ya dauka tayi bacci shiyasa ya mik'e ya nufo gadon ahankali, tana
jin lokaci da ya hau gadon ya kwanta kusa da ita ya kalleta duk da d'akin baya da
wadattace haske hakan, bai hana shi ganin kyakyawar fuska da surar jikinta ba, ya
kai hannunshi ya shafa gefen neck d'inta ahankali kaman mai shafar jikin jinjiri
tana jinshi amma tak'i tayi wani kwakkwaran motsi da zai gano ba bacci take yi ba.
Ya d'an matsa ya yi hugging nata tightly yana shak'ar k'amshin perfumes d'inta ya
rasa gane wane irin perfume take shafawa, yana matuk'ar son k'amshinta tunda yake
bai ta6a jin irin wannan k'amshin ba, sai a wajenta wato ita komai nata na
musanmman ne ya lumshe idanuwanshi tare da sauke sanyayyar ajiyar zuciya sai dai
kuma baya tunani zai nemi kusantar ta nan kusa zai daure har su fara son junansu
sai ya barje shagalinshi atsanake.
Da wannan tunanin bacci ya dauke shi yayin da mamakinshi ya lullu6e barrister A yau
gata kwance the same bed da Aliyu yana kuma rungume da ita yana bacci, tabbas duk
abinda hak'uri bai ba ka ba rashinsa ba zai ba ka ba.
Gashi yau a sanadin hak'urinta tafara winning zuciyar shu'umin Aliyu tayi
murmushi tare da ajiyar zuciya tak'ara shigewa jikinshi daga bisani bacci ya
dauketa.
***----****---****
Washe gari bayan sun kammala breakfast zai wuce office tayi mishi rakiya zuwa
parking lot , suna tafiya side by side hannunta rik'e da briefcase d'inshi ya kar6i
jakka nashi ya matsota sosai ya sauke mata peg a forehead, har ya gangaro zuwa lips
d'inta anan kam ya jima kafin ya saketa ya shiga mota yana fad'i bye wifey please
take care of yourself.
Tana kallo har motarshi tafice daga gidan, sannan ta juya zuwa flat d'in Maryam a
barandar wurin ta tsaya kafin ta yafito d'aya daga cikin housemaids da saurinshi ya
zo, cikin daure fuska ta ce "inaso nan da one hour wurinan ya zama very neat indan
ka sake naga dirty a bakin flat d'inan you will be fired understood....?
"Yes ma'am!"
oyaa....go your time is started now.
Da gudu ya juya bai wuce three minutes da barin wajen ba sai gashi tare da wasu
maids gudu biyu suka zama su uku, ta koma gefe tayi folding hannayenta a k'irji
tana kallonsu kafin ka ce kwa6o har sun fara shara jin motsin mutane had'e da shara
yasa Baaba laraba bude k'ofa ta lek'o gani abinda ke faru yasa ta dauki dogon
salati, ta k'arasa fito da gangar jikinta waje tayi arba da barrister A tana tsaye
sai faman commanding 'yan aikin take yi da mugun sauri har tana had'awa da tuntu6e
Baaba laraba ta nufeta, tana fad'in 'yarnan ki dubi girman Allah ki rufawa mana
asiri ki kuma rufawa kanki, banaso abinda zai ta6a numfashinmu ke kuma ya ta6a
lafiyarki muddin ba ki daina shiga sabgarmu ba har abinda bana tunani zai iya
faruwa.
"Har ta dasa aya azanceta barrister tana kallonta, daga bisani ta gyara
tsayuwarta ta fuskance Baaba da kyau ta ce "ki kwantarda hankalinki Baaba ki
tattaro natsuwarki ga baki d'aya ki saurareni, ban shigo rayuwarku don na cutarda
ku ba asalima ni taimakonku nakeso yi Baaba na rok'e ki ki barni nayi aikin lada.
Baiwar Allah nan tana buk'atar taimako ki barni na taimaka mata.
"Duk abinda zan fad'a 'yarnan baza ki gane ba saboda haka ina gargadinki da ki
daina zuwa nan.
Kafin Barrister A tayi magana suka ji muryar momma tana fad'ar da kyau isasshiya
wato ke kissa da munafuci ne suka kawo ki gidanan ba zaman aure ba.
To kisani idan kinason kanki da lafiya, karki kuskura ki yi tako sak'a da ni domin
baza ki ci riba ba.
Tun daga lokaci da tafara magana jikin Baaba laraba ya dauki rawa wani fitinane
tsoro ya lullu6eta, yayin da barrister A take kallonta tana wani shegen murmushig
ta nisa had'e da cewa "Allah ya huce zuciyarki momma wace ni da zan yi takon sak'a
da ke, kawai dai amatsayina na surukar gidanan nima ina da 'yanci da zan yi abinda
nakeso in fact ni banga abin tada jijiyoyin wuya anan ba.
"Ke.....!saurara marar kunya fitsarariya karki sake ki gayamin maganar banza.
Haba! Mo.....!
Ya isa nace banaso nasake jin koda kalmar hak'uri ce daga bakinki.
Shiru barrister A tayi tana kallon ikon Allah wanda yafi gaban mamaki.
Momma ta juya wurin Housemaids da ke tsaye cirko-cirko cikin tsoron irin hukunci da
za ta dauka akansu, ta daka musu razananiyar tsawa maza ku 6ace min dagani kuma
jira makomarku a gidanan, tunda har zan aza doka ku karyata.
"Hak'uri suka shiga bata d'aya daga cikin Housemaids d'in mai suna Sa'eed ya
nemi ya kare kansu ta hanyar cewa ba laifinmu bane, ma'am saka mu tayi ta ce idan
ba muyi ba zata kore mu aiki don Allah ki taimaka mana.
"Dallah...rufe min bakinka an gayamuku har ita d'in tana da matsayin da zata
kore ma'aikaci agidanan.
Jikinsu na rawa suka tattara mop da bucket had'e da tsintsiya, suka bar wurin.
Momma tadawo da ganinta akan Baaba laraba sai taga wayam....batasan lokaci da take
zazzagawa housemaids fad'a ita kuma Baaba ta sulale ta datse k'ofarsu, da key ta
barshi a jikin k'ofar saboda tasan momma tana da spares key na flat d'in yanzu kuma
duk tsabar masifarta ba zata iya shigowa ba, balle ta d'aga musu hankali.
"Da taga Baaba ta gudu tadawo kan barrister A tana fad'i to bak'ar munafuka ki
bud'e kunnenki da kyau ki saurare ni, daga yau sai yau karna sake gani k'afarki
anan wuri ki tsaya iya apartment dinki bakida hurumin zuwa wajenan.
"Ya motsa fuska barrister A tayi ta ce "momma yanzu laifi ne don na taimaki wanda
ke neman taimako?"
"kinga Amina ni ba tsara ki bace da za ki yi min titse, ina gargad'inki da
babban murya da kada ki sake rud'in kurciya ya rud'e ki, yi min katsalanda a
al'amurana.
"Banyi nufi nayi miki katsalanda ba momma gani nayi anbar baiwar Allah nan a
cikin k'azanta, don kawai Allah jarabce ta da cuta shine za'a barta a wulak'ance
wannan bai dace ba.
Duk yawan ma'aikatan gidanan ace anbar flat d'inta da k'azanta ki yi tunani momma
duniya zata zage ki.
"Matsowa kusa da ita momma tayi ta shiga k'are mata kallo kafin tayi kwafa ta ce
"lalle Amina ba kisan wa kika ta6o ba shiyasa kike da courage d'in musanya yawu da
ni.
Allah ya ba ki hak'uri momma idan akan aikin Allah ne bana fargaba ta6a koma
waye ballantana, nasan alkhairi na ta6o.
"Shikenan za ki san ni kika yi ma rashin kunya bari wanda ya ajiye ki ya dawo,
sai nanu miki ruwa ba sa'ar kwado bane tunda ke bakida tarbiyya bakisan yadda ake
daraja uwar miji ba.
Daga haka ta juya tanufi k'ofar maryama ta dinga heavy knock kaman zata k'arya
k'ofar sai surfawa Baaba laraba zagi ta uwa ta uba take yi, yayin da Baaba tana ji
tayi biriss...da ita.
Barrister A tana tsaye kaman andasa ta sai kallon momma take yi, da momma tagaji da
knocking k'ofar ta juya ta nufi flat d'inta tana mai cigaba da bambamin fad'a.
Barrister A tayi ajiyar zuciya had'e da fad'in "cab....lalle ma momma tunda yanzu
na fahimci abin naki ba rawa ba tumami mu zuba ni da ke, sai na fitarda baiwar
Allah nan daga k'agin da kika jefata.
Ba don ke kika haifi Aliyu ba da yau nayi miki rashin