Author : Jidda Aliyu Category : Drama
zamanta, tana mushirikin murmushi ta ce ina
fatar kana sauke hakkinta yadda ya kamata?"
Kallon mamaki yake mata sai kuma ya murmusa tsaff....ya gane idan ta dosa sai ya
ce sosai ma kuwa momma duk abinda takeso ina mata.
"Gaban momma ya cigaba da dukan tara-tara babban tashin hankalinta bai wuce
asiri da Jarumi ya bata na kashewa Aliyu mazak'uta, sai gashi Aliyu yana fad'a mata
yana shagalinshi to.....ina zance asiri da suka yi mishi ana nufi ya karye.
"Gani yadda ta k'ura mishi idanu ba ko kaftawa yasa ya ce lafiya momma naga
kin tsareni da ido, kuma kinyi shiru?"
"Ta shiga kame-kame daga bisani ta yi nasarar cewa anyya kuwa Gadanga kana
had'a shinfid'a da yarinyar nan?"
Sam banga jikinta ya nuna hakan ba.
Tafad'a tana tsare shi da idanu, sosai wannan tambayarta ta tabashi haushi da
takaici ya 6ata fuska ya ce ki tambayeta momma za ta fad'a miki ko yau kafin mu
baro Yola muna tare a d'aki d'aya.
"Please....momma ki daina irin wannan bincike bashida amfani, ni fa ba k'aramin
yaro bane duk wani hakke aure nasani.
Kuma ina k'ok'arin sauke shi.
"Ni zan fita sai na dawo."
Ya k'arasa magana had'e da mik'ewa.
A dawo lafiya!
Cewar momma cikin yana yi na tsoro.
"Kaitsaye d'akinsu Zee-ze ya wuce ya tararda su suna fira yayin da Teema na
kwance a jikin barrister, sai wasa take da dogon bak'in gashinta.
"Sosai hakan ya yi mishi dad'i saboda yana k'aunar siblings d'inshi ba kad'an
ba miskilancinshi ke hanashi nuna musu hakan.
"Tsaye ya yi a bakin k'ofa yana kallonsu da girar ido d'age, Teema na arba da
shi ta sha jinin jikinta saboda Allah ya zuba mata tsoronshi.
"Zan fita"
Yafad'a k'asan mak'oshi.
Atsanake tad'ago tana fad'i adawo lafiya Allah ya bada sa'a!
Amin nagode!
Har juya ya sake waigowa ya ce Zainab ba abinci agidan naku ne da ba ki kawo mata
ba?"
Ko tsabar rashin iya tar6o guest ne?"
"Cike da tsoro Zee-zee ta ce Yaya kasan momma bata bari adafa abinci da yawa.
Mtsss.....ya ja tsaki had'e da barin d'akin yana cewa ki tabbata kin gayawa chef
Emmanuel ya girka mata abinda za ta ci.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
Not edited!
*23*
Yana k'arasa fita zee-zee ta kalleta tana dariya ta ce gaskiya matar Yaya Yayanmu
yana ji da ke, Allah yasa kema haka ki ke ji da shi.
'Yar siriryar dariya tayi ta ce sosai ma kuwa.
Momma wacce tun fitar Aliyu take la6e tana sauraren firar tasu, ta zaro manyan
idanuta tana huci, bankad'o k'ofar tayi ba ko sallama ta bi su da kallo.
Gani yadda suma suke kallonta yasa ta wayace ta ce Emmanuel girkin Alhaji zai doura
yanzu, Zee-zee ta bi ki ku je flat dinku ta tayaki ki girkawa mijinki abinda zai
ci.
"Da sauri Zee-zee ta d'ago tana kallon momma cike da zallan mamaki, ta ce "momma
yaushe na iya girki da har zan tayata?"
ki bar Emma ya dafa mata koda noodles ne.
makirin murmushi momma tayi kafin ta ce "miye amfaninta idan bata girkawa mijinta
abinci ba?"
Idan ke ba ki iya ba ai ita ta iya
daga yau ki fara girkawa mijinki abinci kinji my daughter?"
Ajiyar zuciya barrister A tayi tana mai cigaba da kallon momma tana karanta yana
yinta.
"Har zee-zee za ta sake yin magana barrister A ta katseta da sauri ta hanyar
cewa, to momma!
"Momma tayi murmushin mugunta saboda ganinta barrister A ta taso gidan huta
uwa-uba yana yin aikinta yaushe take da lokaci shiga kitchen har ta iya wani abu
wai shi girki.
Atunaninta tun daga wurin girki za su fara samun matsala da Aliyu saboda ta san
halinshi da tsirfa, ba ko ne irin abinci yake ci ba.
Saboda haka shiyasa tayi amfani da wannan damar tafara aiwatar da nufinta akansu.
"Shikenan my daughter tashi maza ku tafi ki had'awa yarona delicious, yana ci
kunnenshi na motsi.
Ta k'arasa magana tana washe hak'ora na kissa da kissisina.
Hannun Zee-zee barrister A ta rik'o zo mu je Zee ki tayani kema daga yau ki fara
learning.
"Ni ma zan je matar Yayanmu!
Cewar Teema tana sosa gashin kanta.
Kafin barrister A tayi magana har momma ta rigata cewa kema bi su ki koya.
"Har suka fice daga d'akin momma tana murmushinta na zallan mugunta.
Da suke iso compound idanuwan barrister A suka hango apartment d'in Maryam, ta
k'urawa wurin idanu tana mamaki yadda aka bar barandar wurin tayi k'ura, musanmman
da tayi la'akari ko ina na gidan tsaf-tsaf yake idan ka cire wurin.
Ajiyar zuciya ta yi ta kauda ganinta suka k'arasa flat d'inta.
A falon k'asa suka zauna zee-zee ta had'a kayan kallo, suna cikin kallo aka yi
kiran sallar la'asar, har barrister A tayi sallah ta dawo bata ga alamar Zee-zee da
Teema zasu tashi suyi sallah ba.
Sai tunanin dukansu suna period ne, don haka ta share su suka cigaba da kallonsu.
"K'arfe 5:00 ta buga Zee-zee ta kalli barrister A ta ce matar Yaya kin ce sai
kin yi sallah, za mu doura girki gashi har 5:00 o'clock ya yi.
"Barrister A tayi murmushi tana fad'i ko za mu fara girki nan zee-zee saidai
gobe, saboda na duba a store ba foodstuffs, kinga zuwa gobe Yayanki zai siyo.
"Shikenan matar Yaya bari na je sai na fad'awa momma tunda ita store d'inta
akwai sai, tasa akawo muku.
"Ba sai kin fad'a mata ba maybe fitarnan da ya yi zai dawo da su.
Daga haka su ka cigaba da firarsu har meenat ta dawo daga school, ta shigo da
murnarta na gani matar yayan nata.
"Lokaci sallar magarib ya yi still barrister A ce kawai tayi sallah, sosai abin
ya daure mata kai matuk'a ana nufi su duka uku suna menstruation period.
Sai kuma tabar tambayar k'asan zuciyarta.
Saida momma ta kira wayar meenat sannan suka koma flat dinsu, amma ba don ransu
yaso ba sun so tabarsu sai Aliyu ya dawo.
"Bayan tafiyarsu barrister A ta haura sama tayi wanka, ta shirya cikin
California candy strip ba k'aramin kyau rigar tayi mata ba.
Zanin ta doura akan rigar sakamakon tsagar da rigar take da a side by side, tayi
sallar isha'i tana gama sallah ta cire zanin ta like ta mayar a closet ta fice zuwa
downstairs falo.
"Misalin k'arfe 9:00 na dare Aliyu ya murd'a k'ofa ya shigo cikin sallama, ta
mik'e tsaye tana amsa mashi tare da yi mishi sannu da zuwa, sannan ta isa wajen shi
ta kar6i ledojin da ya shigo da su.
"Ya amsa gaisuwarta yana kallonta kallo ne irin na kwalliyarki ta ban sha'awa,
d'an zaman da ya yi da ita akwai abubuwa da dama da ta mallaka da ke matuk'ar
d'aukar hankalinshi, abu na farko ta iya kwaliyya ko yaya ta sanya kaya sai sun
kar6i jikinta, sun fito da kyakyawar surarta.
"Hakan na dauke mishi hankali ba kad'an ba.
Gashi ta iya tafiya ta jan hankali duk lokaci da take tafiya yana lura da yadda
take rausaya, ga66o6in jikinta na motsawa especially hips da boobs d'inta.
Idan kuma ya tsareta da lulu eye's dinshi, k'irjinta da fuskarta suna daukar
hankalinshi, idan kuma ya kusanceta k'amshinta yana tafiyarta ruhi da gangar
jikinshi, saidai yak'i bari ta gano hakan sau da yawa yana satar kallonta ne batare
da saninta ba.
Tana zuba sanyayye murmushinta mai tsada ta wuce kitchen da ledojin da ta kar6a
daga hannunshi, ta duba abinda ke ciki kayan tea ne had'e da bread sai shawarma ,
ice cream da kuma gassassun kaji sai k'amshi ke tashi.
Sai leda ta k'arshe mai dauke da tambari chicken republic restuarent, plates da
spoons had'e glass cup ta dauko ta wanke, ta juye abinci ta kuma doura kajin sama
plate ta nufi falon ta tararda ya haura sama, tasan wanka zai yi ta koma kitchen ta
dauko drinks da ruwa.
'Bata jima da zama ba ya fito sanye da wandon pajama as usual ba riga, ya zauna
a tsakiyar rugs carpet, ya mik'e kafafuwanshi hannunshi ya kai ya dauke remote
control ya canza channel.
"Ta kalleshi tana yaba fad'i da girman k'irjinshi a zuciyarta cikin wani shegen
voice mai dad'i ta ce "Yalla6ai ga abinci yanzu za ka ci ko sai zuwa anjima?"
"Ya Kalleta atsanake ya mayarda ganinshi akan Tv ya ce "Tunda na fita banci komai
ba sai coffee kawai, ko ke bakya ji yunwa ne?"
Murmushi tayi ta ce "inaji mana saidai ba sosai ba kaman kai.
Naso nayi girki kafin ka dawo koda na duba store ba foodstuffs"
Murmushi ya yi tare da girgiza kanshi yana cewa "barrister kenan ya za'ayi ki samu
foodstuffs anan saidai a apartment d'in momma.
Idan nayi wanka na fita tun safe sai dare nake dawowa, kuma ba kowane lokaci nakeci
abincin gidanan ba, saboda ina da k'yak'yami k'azantar chef Emma nake ji.
"Dariya tayi tana jinjina zance nashi tare da kallonshi ta ce "Gaskiya Yalla6ai
kai hukuma ne.
uhmmm......koh?"
Girar idonta ta d'age alamar eh!
Ya yi murmushi kawai had'e da fara cin abincinshi, yana cikin ci ya d'ago ya dubeta
ya ce yadai naga ke bakyaci abinci sai faman kallona ki ke yi, ko kallon fuskar
tawa ya k'ossar da ke?"
Sai da tayi dariya mai ban sha'awa kafin ta ce Yalla6ai kenan ina abun kallo a
fuskarka wanda har zai iya k'ossar da ni?"
Auu......kina nufi ba abun kallo afuskana?"
"Uhm.....ni dai ban ganshi ba.
Ashe ba iya snoring da kicking d'in d'uwawun mutane ba har da ciwo makata yana
damunki.
Yak'arasa magana yana kallon cikin idanunta yana murmushi.
"Ta kauda fuskarta da sauri da barin kallonshi, tana ya motsa fuska had'e da turo
baki.
Gaskiya Yalla6ai you kill me at all.....ni ce nake snoring?"
Ai ni ki ka kashe barrister can you imagine in my own room you kick me in the
middle of the night.
"Yadda ya k'arasa magana yana wani gesture ya yi masifar bata dariya, sosai da
ke dariya har tana dafe cikinta.
Ya k'ura mata idanuwanshi yana kallon yadda take dariya ba k'aramin burgeshi tayi
ba, musanmman yadda pink lips d'inta suke motsawa tsintar kanshi ya yi da kai
hannunshi akan upper lips d'inta ya rik'e shi yadda ba za ta ji zafi sosai ba, ya
ce lalle.....yarinya nan kin reni wato ma dariya ki ke mun?"
Ai kuwa sai na cire miki lips in yaso naga da wanda za ki sake yi min dariya.
Soft hands d'inta ta doura akan nashi ta shiga kici-kici ture hannun nashi cikin
sigar shagwa6a ta ce auuch....Yalla6ai da zafi fa.
Da zafi ko?"
Yafad'a yana kallon tsakiyar idanunta.
Turo baki tayi had'e da furta ni ka sakeni ko na cije maka hannu.
"Dungure mata kai ya yi yana fad'ar kura kawai.
Ita ma tayi dariya tana cewa na dai ji.
Ta mik'e tsaye ta koma gefe ta zauna yaja plate d'in nama gabanshi, ya ci sosai ya
kora da ruwan juice yana gamawa ya tura plate yana cewa gashinan ki ci raguwana ko
za ki sami tabarakina kidaina snoring, yana gama magana ya mik'e ya haura upstairs.
Ta bishi da kallo cike da nishad'i ashe Aliyu yana da sauki kai sai in ka zauna da
shi za ka fahimci haka.
"Ita dai komai nashi burgeta yake yi ta tabbatarwa da kanta shi d'in cikkake
namiji ne mai kwarjini.
Tsarin zubinshi yayi mata kullum kwanan duniya soyayyarshi na dad'a shiga
zuciyarta, alhali shi kuma ba burbushin sonta a tashi zuciyar, ta d'an girgiza
kanta cikin rashin jin dad'i sannan taja naman gabanta taci har ta k'oshi ta sanya
ragowa cikin fridge, ta dawo taci gaba da kallon channel d'in girke-girke.
Ta dauki dogon lokaci sosai ganin dare yayi sai ta mik'e ta had'a mashi coffee ta
hau sama ta tura k'ofar ahankali tunaninta yana cikin falon, sai taga ba kowa.
"Kaitsaye ta shiga master room d'inshi ta hango shi kwance akan tangameme
gadonshi, yana bacci sam bata yi mamaki ba tasan yana cikin gajiya.
Ta doura coffee akan d'an k'aramin center table, idanunta suka hango wasu documents
zube a k'asa ta shiga tattara mishi, tana waigowa ta ganshi zaune ta kalleshi tana
fad'in "Allah yasa ba motsi na bane ya tasheka ba?"
"Ya girgiza kanshi ya ce "Ah'ah dama baccin nawa bai yi nisa sosai ba.
Ta yi murmushi kafin ta ce akwai abinda ka ke buk'ata bayan coffee nima nafara jin
bacci.
"Ki je ki kwanta sai da safe.
Allah ya tashe mu lafiya.
Amin yafad'a can k'asan mak'oshi.
***"""****"""****
Washe gari da wuri ta tashi duk tasan basuda foodstuffs ta shiga gyaran gida, tana
cikin mopping d'in downstairs falo Aliyu ya shigo ta runsuna har k'asa ta gaidashi
ya amsa da murmushi akan fuskarshi.
"Ki shiga daga ciki tare da nake da maza zasu shigo da kayan abinci store.
Toh.....
Tafada had'e da daukar mopping bucket ta fice daga falo, dama already tagama
mopping d'in tana dai d'an k'ara goge wuri ne.
"Tana zaune a falonta ya tura k'ofa ya shigo, batare da ya bari sun had'a ido
ba ya ce ki tashi ga foodstuffs an shigo da su ki had'a mana breakfast.
Saidai karki yi amfani da gas yanzu nan aka jona cylinder d'in, ki yi amfani da
stove akwai kerosene aciki.
"Bai jira jin ta bakinta ba ya yi tafiyarshi, ta bishi da kallo cike da
sonshi.
Murmushi tayi a k'asan zuciyarta ta ce Aliyu hukuma zama da kai sai mai dogon
hak'uri, dubeshi don Allah kamar ba shi bane daren jiya muke nishad'i tare ba.
Koda misalin k'arfe 10:00am tayi har ta kammala girki ta yi arranging table,
agurguje tashiga wanka tafito bataso ya yi latti saboda lokaci da tana kitchen yana
downstairs falo taji yana waya yana da meeting around 11 o'clock.
"Simple makeup tayi tasaka material d'inki doguwar riga, ta yane kanta da veil
ta bi lungu da sak'o na jikinta da perfumes jikinta da d'akin suka dauki k'amshi ta
kalli mirror ta d'an saki murmushi, ita dai atsarinta tana masifar son turare
shiyasa bata rabuwa da shi hakan yasa take cikin dadd'add'e k'amshi mai tsawa a
rai.
Flip flops slippers tasaka a k'afafunta ta sauko k'asa, tana tsaye a dining area
taji footsteps d'inshi ta maida ganinta akanshi yasha farare suit hannunshi rik'e
da briefcase, tana kallonshi har ya k'araso cikin falon ya ajiye briefcase d'in
akan center table sannan ya nufo wurinta taja mishi kujera ya zauna tayi serving
dinshi.
Suna kammala breakfast ya dubeta ya ce mu je ki gaida Daddy jiya da dare ya dawo
daga Lagos.
"Yana gaba tana binshi a baya suna zuwa compound idanuwanta suka sauka a
apartment d'in Maryam, kamar yadda tayi jiya hakan ne yafaru tayi tsaye tana kallon
wurin.
Sosai taji tsigar jikinta ya tashi, ta tsince kanta da son sani miyasa duk cika da
girman gidan iya apartment d'in ne kawai keda k'ura da k'azanta.
"Mu je mana!
Sautin muryarshi ya dawo da ita duniyar tunani.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:02 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*24*
A dining area suka iske ahalin gidan suna breakfast.
Daddy yana ganinsu fuskarshi ta cika da farin ciki, wanda ya kasa 6oyewa sai zabga
murmushi yake yana fad'i barka ku da zuwa yaran albarka.
"Barrister A ta durk'usa har k'asa ta gaida daddy da momma yayin da su Zee-zee
suka gaidata ita da Aliyu.
Ku zauna ku yi breakfast tashi Zaituna ki yi musu serving.
Cewar Daddy yana washe baki yana kallon momma.
Sosai ran momma ya 6aci da jin furuncinshi duk da haka sai tashiga murmushi yak'e
wanda yafi kuka ciwo.
Kafin tayi magana Aliyu ya rigata ta hanyar cewa Daddy a k'oshi muke.
Daddy ya ce shikenan mu je sitting room dina zan yi magana da ku.
Har momma ta mik'e tsaye ya ce A'ha'h!.....Zaituna koma ki zauna da yarana kadi
nakeso magana mu je sultan.
momma tana kallo suka haura steps suka barta tsaye da baki galala, me Daddy yake
nufi da yaranshi kawai yake so magana?"
Tabbas.....akwai abinda yake nufi tasanshi farin sani bai cika fad'ar magana marar
manufa ba.
Jikinta ya yi sanyi tashiga wasi-wasi shin ko yafara hal6o 6oyayye sirrita ne?"
Idan haka ta kasance kashinta ya boshe awurin Jarumi ba ko shakka sai ya yi
gunduwa-gunduwa da naman jikinta.
Wani shegen fitsari taji yana k'ok'arin kuce mata, da sauri-sauri gudu-gudu take
haura steps.
"Duk magana da girls d'inta suke babu wacce taji, tana shiga bedroom kaitsaye ta
zarce bathroom, tsabar rud'ewa ko bathroom slippers bata saka ba.
"Ta ware k'afafunta a tsakiyar tiles ta tattare doguwar rigar leshi da ke
jikinta, tasaki fitsari daga tsaye ji ka ke sharrrrrr.......saida ta gama fitsarin
ta ankara da inda tasake shi, ruwa ta debo ta tsaftace jikinta da wuri sannan
tafito ta zauna gefen gado ta rafka tagumi, sai kuma ta mik'e zubur....ta dauki
wayarta tayi dialling contacts d'in Jarumi, rufi asirinta ta kira shi tun kafin
zarginta ya tabbata.
Yana dauka ko gaisawa bata bari suka yi ba muryarta na rawa ta shiga fad'ar
Ja.....ru.....mi.....akwai matsaloli domin ba guda d'aya bace suna da yawa ta farko
dai sultan ya sadu da matarshi, na biyu kuma kaman Alhaji yafara gano plans d'inmu
don Allah duk abinda ka ke yi ka ajiye ka zo Abuja mu had'u.
"Kittt.....taji an datse layin duk da haka ta cigaba da fad'ar
hello....hello...Jarumi kana ji na?"
Sororo tayi rik'e da waya a hannu tasake afkawa sabon tunani me kuma wannan d'an
iskan Jarumi yake nufi da ita....?"
"Ta zube akan gado kamar kayan wanki yayin da wani mashahuri tsoro ya k'ara
shigarta.
****"""****""""****
A sitting room d'in Daddy kuma suna zama daddy ya kallesu ya ce dama dangane da
aikin matarka ne, akwai wani team na independence lawyers shugabansu childhood
friend dina ne na yi magana da