Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gidan Rina Complete Hausa Novel by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  Drama

Chapter   7 / 26

18K to 21K   out of 76.6K words

ko ya yi shiru.
***----****----****
*™YOLA*

Tafiya Abba ya shiryawa ummi da Barrister Amina zuwa Dubai, siyayyar kayan aurenta
milliyoyin kudi ya basu ita kanta Ummi sai da ta zare kud'ad'e masu dibin yawa a
account d'inta da za tayi tafiyar da su Barrister A ita ce 'yarsu ta fari kuma 'ya
mace daga kanta za suyi shekaru kafin su aurarda Rahma don haka duk wani tanadinsu
akanta suke yi.
Ana sauran kwana biyu tafiyar Barrister ta zauna tayi nazarin irin makud'an kud'in
da take da a account d'inta tarawa kawai take batare da tana amfani da su ba, don
haka yanzu amfaninsu yazo, zarar abinta tayi za tayi tafiyar da su.
"Kwanansu tara a Dubai suka juyo Nigeria duk tsawon lokaci nan Aliyu bai nemi ta
ba, kamar yadda ita ma bata nemi shi ba duk da koda yaushe cikin tunaninshi take,
amma ba za ta iya karya bulleta ba ta nemi shi.
****''''****'''''***
*ABUJA*

Aliyu zaune a sitting room d'in Daddy suna tattauna nasarar da ya yi a business
trip d'in da yadawo, Daddy ya gyara zamanshi ya dubi Aliyu da kyau kafin yace wane
irin shiri ka ke yi dangane da aurenka?"
Yatsine fuska ya yi ya ce babu.
meaning?"
cewar Daddy a fusace.
Daddy babu duka fa jiya-jiyanan nadawo ko hutawa banyi ba, yanzu haka gajiya bata
gama sakeni ba.
"Sosai ran Daddy ya 6acin sai kallon Aliyu yake kamar ya rufe shi da duka.
Ya ce wannan zance banza ne yau duka saura kwanaki tara a daurama aure, amma ba ka
shirya komai ba.
Kai kenan duk lokaci da akayi maka magana akan aurenan sai kasan yadda za ka kare
kanka, ka sani sultan ina nema maka alkhairi ne ba sharri ba domin duk uba nagari
yana fatan d'anshi ko 'yarshi suyi dace da abokanan rayuwa masu nagarta da mutunci.
Abinda nake so ka gane Sultan shi ne wannan auren umarnina ne, ba wai ina
shawartaka ba don haka ka kasance a shirye ka kuma yi abinda kowane ango yake yi
yayin aurenshi, saboda ba abinda za'a fasa sai in dai mutuwa ce ta dauke ni kafin
lokaci, shi ne ka ke da damar fatali da umarnina, shiyasa da na fahimci
mahaifiyarka tana min zagon k'asa a zance aurenka na tsigeta a tafiyar domin banaso
abinda za kawo min tangard'a saboda haka ka kiyayye.

Sosai jikin Aliyu ya yi sanyi ya kalli inda Daddy yake zaune, ya ce Daddy kayi
hak'uri wallahi abubuwa ne sukayi min yawa har narasa ina zan sa kaina.
"Takaici ne yak'ara kama Daddy batare da yace da shi komai ba, ya mik'e ya shiga
bedroom bai dauki dogon lokaci ba yadawo hannunshi dauke da led'a fara ya jefawa
Aliyu gashinan abinda ka kasa yi ne nayi invitation ne na dauri aure in ka ga dama
ka ba wa friends da business partners d'inka, tashi ka bani wuri.
Salun-alun Aliyu ya mik'e ya fice zuciyarshi ba dad'i.




Jeeddah Aliyu[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
NA KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*13*

B'acin rai ya bayyana k'arara akan fuskarshi hakan yasa idanuwanshi ma'abota kyau
da kwarjini, suka canza launi daga farare zuwa ja.
picking lot yanufa da gudu direbanshi isah ya taso ya jawo mota ya bude masa k'ofa
ya shiga.
Sai da suka dauki hanya kafin yace gidan Jamal za ka kaini kira shi a waya ka ji ko
yana gida.
Okay....boss"
Cewar Isah direba yana ciro wayarshi daga gaban aljihu farar shirt da ke jikinshi,
ya yi dialling numbern Jamal.

Boss ya ce yana River plate park ka sami shi acan.
Omg! Uban me Jamal yake tsinta a park sai ya lura mutane na cikin damuwa yake tsira
yawo marar amfani "mtssss....ya ja tsaki cike da takaici ya umarce Isah ya kai shi
can.

Suna isowa Isa ya bude masa k'ofa yafito ya kai hannu ya kar6i ledar da ke
hannunshi, sai lokaci Aliyu ya tuna da ledar.
"Please.....Isah sake kiranshi ka ji yana dai-dai ina.
kafin ya kai da kirar nashi suka hango shi, yana k'arasowa ya mik'awa Aliyu hannu
suka gaisa jerawa suka yi yayin da Isah ke bin bayansu.

Cikin wasu bukkoki da ke dauke da kujeri kamar na kaba had'e da table a tsakiyarsu,
suka nufa Jamal ne yafara jan d'aya daga cikin kujeri ya zauna, da sauri Isah
yajawa Aliyu kujerar ya zauna cike da damuwa ya dafe goshinshi waiter ne ya kawo
musu menu ko da akwai abinda suke buk'ata Jamal ne ya yi musu order.
"A natse yake kallon abokin nashi kafin ya ce ya akayi ne king naga kamar da
damuwa akan fuskarka?"
Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfin gaske ya ce ba kama bane Jamal, damuwa ce takeso
yi min yawa.
Subhnalillah......meke faruwa ne?"
Hannun ya mik'awa Isah batare da ya yi magana ba, ledar da ke hannunnshi ya mik'o
mishi shi kuma ya mikawa Jamal.
"Invited card ne na dauri aure koda na dawo daga Zurich har Daddy ya bugu su.
Ya k'arasa magana kamar zai yi kuka.
"Fito da cards din Jamal ya yi yana kallo yana murmushi saboda tsananin kyau da
tsadarsu, ya ce lalle Aliyu kai d'an hutu ne sam baka san wahala ba, gaba d'aya
rayuwarka cikin gatanci ka ke yi ta hatta aure ma baka san wahalar nemanshi ba, yi
maka akayi.
"ka tsinci zankad'edd'iyar mace kyakyawa ajin farko a gidanka wallahi ka ji
dad'inka.

"Yalwattace murmushi ya yi sannan ya jan tsaki mtsss.....ya ce ina gatanci ga aure
da ba soyayya a cikinshi, wasu lukuta inda na zauna ina nazari har misalta yadda
zamana da Barrister zai kasance, saboda ita kanta ba son nawa take yi ba dole ne
akayi mata kamar yadda akayi min.

Yanzu dai mu aje zance kana so ko baka so, tana so ko bataso muyi wanda ke gabanmu.
Ya raba card's d'in biyu ya mik'awa Aliyu kashe d'aya ka ba wa business partners
dinka, wannan zan ba wa friends d'inmu, sai abu na gaba ka shirya muje Yola domin
muji nata bangare me take shiryawa ka san dole ba za'a rasa events d'in da za suyi
ba irin su dinner, cocktail party.
"Dallah ya isa ana zaune qalau za ka daukowa mutane bidi'a, ba da ni za'a yi
wannan iskanci ba.
yakarasa magana yana hura hanci.
Dariya Jamal ya yi ya ce ka ji da shi wai ciwon ajali a d'an yatsa aure ne dai ba
fashi sai ayi.

"Sai kuyi tayi amma dai ba wanda isa ya sani zuwa party da ban yi niyya ba.
Ba wannan ba yanzu yaushe za mu tafi Yola?"
Mu bari koda zuwa ranar labara ne, duk da ranar ina da aiyyuka da yawa a gabana.
"Koma menene agogo sarki aiki jingine shi za kayi, har sai muje mun dawo, ka
godewa Allah abokina da yabaka zuk'ekk'iyar mace irin Barrister Amina wallahi kayi
dace da mata.
Yarinya natstsiya mai kunya uwa-uba wayewa da gogewa na tsantsa ilimin zamani, kuma
ga dukan alamu har na addini tana da shi.
"Aliyu ya yi murmushi sannan ya ta6e baki ya ce nima ai tayi dacen miji
santalele, business tycoon irina wanda mata suke haukar so amma sai gashi ita
tasamu a arha.....
"Jamal yaja tsaki....mtsss had'e da cewa kai dai anyi tsoho d'an iska wallahi,
wato kana sane da haukar da mata suke yi akanka, basarwa kawai ka ke yi.
"Ba gashi hakan ya yi wa barrister rana ba zata kwashi gara6asa.
Duka Jamal yakai mashi yana cewa ka shiga uku king ka dai anyi 6aud'add'e mutum, a
lokaci d'aya sukayi dariya har suna tafawa.

"Ka shirya kawai gobe muje sai mu dawo a ranar, ka ga ba za mu koma ba sai an
sakata a lalle alokaci ta dau k'amshi sai ka shinshshina kayanka a tsanake.

"Sosai maganar ta Jamal ta bashi dariya don haka ya shiga kyakyatawa abinshi,
wanda hakan ya janyo hankali Isah direba ya kura mishi idanu, a zuciyarshi ya ce
lalle yau za'a yi ruwan sama boss yana dariya.
"Shikenan ka shirya mu bi jirgi safe kamar yadda mu kayi a wancan lokacin.
****----*****---****
*YOLA*
*10:44am*

Barrister Amina tana zaune akan dining table ta sanya abinci agaba, tana kallo ta
kasa ci gaba d'aya tunanin Aliyu ya cakud'e mata zuciya, wani lokaci sai tayi
yunkuri kirar numbernshi sai zuciyarta ta haneta saboda aganinta kiranshi zai zama
ta zubarda ajinta ne.
"muryar Barrister Z taji tana gaisawa da Ummi, hakan yasa ta saki nannauyar
ajiyar zuciya ta yi wulgi da folk d'in hannunta sannan ta mik'e tsaye dai-dai
Barrister Z na isowa, amaryaaaa....
Cewar Barrister Z tana mai rungume Barr A murmushi Barr A tayi had'e da dan gajere
tsaki, ke zo muje room d'ina akwai abubuwa da yawa da za mu tattauna.

Gefen gadon d'akin sauka zauna barr Z ta ce ya dai bebs naganki wani irin ko dai
har kin fara shiga cikin fargaba aure ne?"
"Da yake muddin zakayi aure sai kayi ta faman da zullumi barin gidanku, amma
karki damu bebs na d'an lokaci ne za ki saba mu ma can takalminmu ya tsinke sai
gashi yanzu mun manta da gida sai dai mu kai ziyara.
"Barr A ta dalla mata harara tana mai jan dogon tsaki mtssss......
Barni da wannan zance bebs ni ai na jima da shiga wannan fargabar tun kafin zuwan
lokaci gaba d'aya komai ya cakud'e min, babban tashin hankalina bai wuce irin zaman
aure da zanyi ba.
"Tak'arasa magana kamar za tayi kuka.

"Dafa ta Barri Z tayi cikin tausassa harshe ta ce miye dalilinki na fad'i haka
bebs?"

"Dalilina bai wuce har zuwa yanzu da ya rage sauran 'yan kwanaki k'alilan azarga
min igiyoyin aurenshi akaina, amma babu wata kyakyawar fahimtar juna atsakaninmu
bana tunanin Aliyu Ardo yana jin burbushin sona azuciyarshi, ni kuma gashi
soyayyarshi ta mini mummunan kamu shiyasa natsuwa da kwanciyar hankalina suka
kaura.
Damuwa tayi min katutu har cin abinci naso gagarata, ni narasa yadda zanyi da
rayuwarta.

"Ba wata kulawa da nake samu daga gareshi, bai damu da ni ko kad'an ba ya yi
halin ko oho da al'amurina babban takaicina Ummi sai faman shirye-shirye take ba
abinda ya dameta, na tabbata da Abba yana da masaniyar da rashin fahimtar da ke
tsakaninmu da tuni zai yi fatali da zance aurenan, to abinda ni kaina bana fatan
faruwarshi duba da yadda na tsunduma
kogin soyayarshi.


_Just to manage_


Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:54 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*14*

murmusawa Barrister Z tayi tare da girgiza kanta sannan kuma ta, gyara zamanta ta
fuskanci Barrister A ta ce don ya nuna halin ko oho akanki, baya nufi bashida
ra'ayinki,
Benbs kiyi la'akari da yanayin aikinshi ba na zama wuri d'aya bane.
ke da kanki kin sani don ya gayamiki, kuma duk da rashin kulawarshi ba'a fasa
gudanarda komai ba.
Don haka "don Allah ki kwatarda hankalinki kada ki haifarwa da kanki da wata
matsala.
"Amma bebs ai yana da number wayana miyasa bai kirani ba?"

Kema ai kina da numbernshi miyasa ba kira shi ba?"

Saida ta galla mata harara kafin tace haka kawai zan kira shi salon ya daukeni
marar aji.
Oh! Haka ne ashe ba shi kadai bane mai laifi, kema kina da naki saboda haka ki
jingine wannan k'orafin naki bai samu kar6uwa ba.
Muyi magana da ke gabanmu.
Dole barrister A ta share zance duk da yana nuk'urk'usar zuciyata ta dauki invited
cards suka fice wurin rabawa 'yan uwa da abokan arziki.
A washe gari mai gyara jiki ta musanmman da Ummi ta kira daga Sudan ta iso, tun
daga ranar ta shiga gyara Barrister A.
***---***---***---****
*ABUJA*
*10:37am*

Aliyu yafito cikin shirin shi na farar shadda daga flat d'inshi yanufo na
iyayyenshi, a sitting room ya tararda Daddy da momma zaune.
Tun kafin ya k'arasa yake jin tashin muryoyinsu, tsinta kanshi ya yi da jin 6acin
rai saboda yasan duk saboda zance aurenshi ne yake saka su hayaniya.
Jikinshi asanyayye
ya nemi kujera can gefe ya zauna ya talla6e ha66arshi yana kallonsu, batare da ya
tanka musu ba.
Daddy ne ya yi k'arfin halin cewa Sultan ina zuwa da sanyi safiyanan?"
uhmm....saida ya yi ajiyar zuciya kafin ya ce Yola...
Daddy ya fad'adda murmushinshi ya ce da kyau my fav boy, shigowar nan taka
maganarka ce muke yi ni da mahaifiyarka, bisa wani tunani da nayi na yanke hukunci
a gidanka da ke Yola za ka fara zama kai da matarka, na wani d'an lokaci kafin ta
tare anan Abuja duk wani abu da gidan yake buk'ata an zuba maka.
Idan akwai abinda bai maka ba in ka je sai kayi min magana kaji ko?"
Dafe goshi Aliyu ya yi ya shiga nazarin maganar Daddy tsawon some minutes kafin
yad'ago wearing a killer smile on his face "ya ce thank you Daddy Allah yak'ara
lafiya da nisan kwana ni zan wuce.
Yak'arasa magana had'e da mik'ewa Allah shi yi maka albarka Gadangan Daddy Allah ya
tsare min kai, yakare ka daga sharri mutum da na aljan, yadda ka ke min biyayya
kaima Allah yabaka masu yi maka.
Cak...Aliyu ya tsaya saboda sosai addu'ar Daddy ta ratsa k'ashi da 6argon
jikinshi, saida ya juyo sannan ya amsa da Amin summa Amin Daddy.
Momma ta tur6une fuska ta ce zo nan Sultan nima a matsyina na wacce ta haifeka ina
da magana.
Har Aliyu ya juyo Daddy ya ce je ka abinka Gadanga za ta 6ata maka lokaci ne a
banza, shiru Aliyu ya yi shi bai tafi ba kuma shi bai dawo ya zauna ba.
Sosai ran momma ya 6aci tasaki tsaki ta kuma shan alwashin sai ta raba Barrister A
da numfashinta, gashi tun kafin ta shigo ta fara raba mata kan iyali.
Ta cije le66enta na k'asa ta yi kyaci ta mik'e fuuuu...tafice daga sitting room.
Daddy ya dubeshi yana murmushi cikin sigar kwantarda hankali ya ce yi tafiyarka
Allah ya kiyayye hanya barni da ita zan rarrashe ta.
Cike da gansuwa Aliyu ya gyad'a kai ya fice.
***--****----*****
Daga Airport Aliyu ya wuce gidanshi shi kanshi gidan ya burge shi sosai, bai kuma
ci karo da wani abinda bai mishi ba saida suka huta shi da Jamal kafin su nufo
gidansu Barrister A lokaci da sak'o ya riske Barrister A Aliyu ya iso ana mata
gyara jiki tsakanin jiya da yau fatar jikinta tak'ara glowing, sai fitarda k'amshi
mai jan hankali take.

Scrub d'in da ke jikinta ta nufi bathroom a gurguje ta wanke tafito daure da towel,
ta dube k'awarta Fadila wacce cousin d'inta ce 'yar wurin Aunty Khadija ce.
Tq ce Fadila please ki je wurinsu kafin na shirya, saida Fadila ta tsokaneta kafin
ta fice tanufi falon bak'i.

Cikin abinda bai wuce 10-12 minutes ba Barrister A ta shirya ciki atamfar exclusive
d'inki riga da skirt ya zauna dass....a jikinta d'an siriri veil kalar atamfarta ta
yane kanta da shi, ita kanta lokaci da tayi arba da dressing mirror saida tasaki
k'ayatattace murmushi, sakamakon kyau da tayi ta fice daga d'akin cikin yanayin
tafiyarta mai matukar daukar hankali.
"Tun kafin ta k'arasa shiga falon iska ya kai musu fitinanne k'amshinta, ta tura
k'ofa bakinta dauke da sallama ta shigo.
Jamal da Fadila suka amsa mata sa6ani gogan naku da lips dinshi ne kawai suka
motsa, saida ta zauna kafin ta gaida su a lokaci d'aya dukansu suka kalle ta, sosai
kyawota ya rud'asu da sauri Aliyu ya dauke fuska.
Jamal ya yi murmushi yana mai cigaba da kallonta ya ce amarya da fatan za'a yi mana
afuwa, kasancewar kin ganmu kwatsan ba sanarwa, muyi ta neman layinki baya shiga
kinsan dai yadda lamari network yake.
Sadda kanta k'asa tayi tana wasa da yatsun hannunta, tasan duk abinda Jamal ya
fad'a ba gaskiya bane yana dai neman ya kare abokinshi ne.
"Da kyar ta d'ago tayi murumushi, batare da tace komai ba Jamal ya dubi Fadila
ya ce malama Fadila zubamin lemo muje daga waje, naji shirye-shiryenku kafin ango
da amaryar nan su gama zantawa dariya Fadila tayi tana mai cewa lalle kam gara mu
basu wurin naga sai fik'i-fik'i da idanuwa suke yi.
"Murmushi Aliyu ya yi cikin husky voice d'inshi ya d'ago yana lumshe lulu eyes
dinshi, ya ce Fadila daina biyewa Jamal kinsan nace ke ce ta hannun dama na.

Dariya Fadila da Jamal suka yi yayin da Fadila ta tsiyayawa Jamal juice a handle
cup, sannan ta kalli Aliyu ta ce na daina ranka ya dade Jamal ne yakeso ya had'amu,
ba kuma zai yi nasara ba.
"Karka dai manta da alk'awalinmu.

Tafad'a had'e da nufar k'ofar fita Jamal ya biyo bayanta yana cewa ai bai isa ya
manta da wannan alk'awalin ba.
Bayan fitar Jamal da fadila suka yi shiru na some minutes shine ya fara d'agowa
cike da isa da tak'ama ya kalle ta ya ce Barrister ya gida ya kuma shirye-shirye
biki?"
Ita ma ta d'ago da murmushi akan fuskarta wacce sai glowing take, ta ce
Alhmdulilah!
Yalla6ai ina neman alfarma wurinka da, ka kirani da ainihim sunana Amina ko ka ce
Minal.
"D'an gajere murmushi ya yi kafin ya ce nima sunana Aliyu ko ki ce Sultan ba
yalla6ai ba, don haka sai kindaina kirana da Yalla6ai zan daina kiranki da
barrister.
Turo d'an k'aramin bakinta tayi mai kama da gidan tsuntsu, tana gunguni k'asa-
k'asa.
"mekika ce ne?"
Ni ba da kai nake ba.
Tafad'a cikin sigar shagwa6a.
Ta6e baki ya yi ya dauke fuskarshi da barin kallonta.
Shiru suka sake yi na tsawon lokaci daga bisani Aliyu ya ce taimaka kiyi min text
din account numbernki.
Tayi rau da idanu ta ce me za kayi da shi?"
Cikin daure fuska ya ce ina ruwanki da abinda zan yi ke dai ki turomin kawai,
batare da ta furta uffan ba tayi mishi sending.
yana jin shigowar text a wayarshi ya duba ya ga ita ce, sannan ya d'ago ya sake
cewa dame-dame za ku yi na shagalin biki?"

Ta d'an kad'an idanunta ta ce za muyi Fulani night sai mother night sai kuma dinner
da abokan aikina suka had'a mana.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:55 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO


*GIDAN RINA*

*15*

Ya d'an yi rolling lulu

7 / 26