Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gidan Rina Complete Hausa Novel by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  Drama

Chapter   26 / 26

75K to 76.6K   out of 76.6K words

Daddy kamar zan yi hauka gaba d'aya
hankalin su ya tashi cikin nasara aka cirewa Barrister A bullets d'in jikinta,
saidai numfashinta da bai dai-daita ba dole aka wuce da ita ICU aka sanya mata
oxygen ita ma momma an cire mata harsashen saidai tana under police custody.
*Few hours later*
Momma ta farfad'o sai faman rusar kuka take yi, ga tsananin azabar injury da ke
jikinta ga shi sai faman rok'o take yi a kira mata Daddy tanaso ta rok'i gafarsa,
hakan yasa nurse d'in ke on duty tayi mata allurar bacci.
Lokaci da Aliyu ya ji cewa ba momma ce ta haife shi ba maryama ce saura
kiriss....ya yi 'yar k'aramar hauka shi kan shi Daddy ya girgiza da jin wannan
sabon al'amari, yayin da Maryama ta rungume Aliyu tsam....a jikinta tana gunji kuka
duk wanda ya gansu a lokaci dole ya tausaya musu, saboda abin ya zama musu goma da
goma uncle Suraj ya rasu ga barrister A unconscious, Shiyasa Aliyu ya dawo kaman
wani zarare.
Da kyar Abba ya rarrashe Aliyu ya amince suka tafi gida saboda yanda ya gigice
ya shiga damuwa yasa Abba ya dawo tausayin shi musanmman ya hango ta cikin
idanuwanshi yanda yake tsintsan so Barrister A.
Sai a washe gari Daddy ya samu kar6a gawar Uncle Suraj, aka wuce da ita Yola
cikin 'yan uwa da abokan arziki da yake ba kowa Daddy ya gayama musanbabbin mutuwar
tasa ba.
Ana gama jana'izzar sa Aliyu ya juya Abj Daddy kuma sai dai aka yi sadakar
bakwai.
"Cikin hukunci ubangiji barrister A ta farfad'o, yayin da jikin momma ya
rikiceDaddy yana rik'e da hannunta tana kuka had'e da rok'on gafara Aliyu kan kasa
jure kallonta ya yi yafice daga d'akin suna cikin wannan halin d'a momma ta baro a
Nijar yana jariri a baiyana da photon ta tun tana budurwa duk da yanzu girma ya
kamata hakan bai hana su Sheda ta ba.
Tashin hankalinsu ya k'aru a lokaci da Ibrahim ya gabatar da kanshi a matsayin
d'a da ta haifa, tabbas ga kamanu shi d'aya da Momma babu ko tambaya kasan ita ce
ta haife shi duk da tana cikin mayuwaci hali bai hanata rungume Ibrahim tana kuka
tana rok'onsa gafara.
Cikin dare Momma ta ce ga garin ku nan, rai bakon duniya su Zee-zee sun ci kuka
kamar ba gobe dole suka dangana.
Yayin da Daddy yake dorawa kan shi laifi abin da yafaru akan momma da Uncle
Suraj, a cewar shi da bai zalinci Uncle Suraj ba duk haka bata faru ba.
***---***----*****
*FIVE MONTHS LATER*

Barrister A sanye da night gown light pink tafito daga bedroom dinta zuwa na Aliyu,
koda ta shigo yana wanka.
ta bud'e closet ta ta fito masa da kayan shi tana shi shiryawa a luggage d'in da za
su yi tafiya zuwa los angeles a cikin k'asar California, in ka ganta kaman bata yi
ciwo ba ta warke sumul ta6o kawai ya rage shima tana amfani da magani 6acewar ta6o
sannu-sannu zai 6ace.
Aliyu ya fito daga wanka d'aure da brown towel iya waist d'inshi, Barrister A
ta d'ago tare da wanke shi da k'ayattace murmushi shima ya mayar mata da marni yana
zuwa kusa da ita ya fizge Coat d'in sa da ta dauko da nufi sakawa a trolley, ya
zauna daff....da ita tare da rungumo ta yana rad'a mata "Wifey I miss you so much I
really need you in my bed right now kar ki ce ah'a Baby kin sani nayi hak'uri
almost five months please.....
Kafin ya k'arasa ta had'e bakinta da nashi ta shiga ba shi wani irin zazzafan
French kiss, sosai Aliyu ya rikice ya dimauce tuni ya yi undressing d'inta ranar ta
gurzu kaman first night d'insu.
Ta 6agare Daddy ya had'e kan iyalinshi yayin da Maryama ta had'e kan yaran ta
yanda take kulawa da su Zee-zee za ka dauka ita ce ta haife su, musanmman Teema da
ta dawo 'yar gaban shi kowa sonta yake yi, tuni ta daina k'arya iskokai dama
depression ne ya yi mata yawa, yanzu kuma batada sauran damuwa.
"Daddy ya kira lawyer shi da na Uncle Suraj aka raba dukiyarsa kashi biyu ya
mallakawa iyalin uncle, rayuwa ta dawo musu sabuwa saboda hatta da Ibrahim d'a
Momma Daddy ya dawo da rik'onshi hannunshi, ya bashi aiki a kamfaninsa.
*LAX LOS ANGELES INTERNATIONAL AIRPORT*

Ahankali suke takowa daga steps d'in jirgi Aliyu yana gaba sanye da white long suit
jacket k'afarshi na cikin Chelsea boots.
Yayin da barrister A take sanye da brown frock jacket tare da stirrup
trouser, k'afarta na cikin velvet ankle boots ta yane kanta da siririn scarf
kallo d'aya za ka yi musu ka gano cikkaku masoya ne musu masifar k'aunar juna, da
yake jirgin na su da dare ya yi landing ga wani masifaffen sanyin garin ya yi musu
marhaban.
"kowane su yana janye da luggage suka fito wajen airport texi suka hau zuwa,
hotel d'in da ya yi musu booking tun kafin su iso suna zuwa batare da 6ata lokaci
ba aka nuna musu room dinsu irin suite dinan ne ya kama sai masifar tsada.
Washe gari da yamma lis....suka fita yawon bud'a ido a wani had'adden wurin
hutawa, mai suna frank national park & beach.
Bayan sun zauna waiter ya kawo musu menu suka za6i drink d'in da za'a kawo
musu, saboda ba su ji yunwa.
Wayar Aliyu ya yi ringing gani Daddy ne kira yasan za su tattauna ne akan abin da
ya shafi business, maganar su zai dauki longtime yasa Aliyu ya mik'e neme wurin da
ba zai dame mutane ba.
Tun lokaci da ya shigo wurin tayi bala'in daukar hankalinsa, sai faman kallonta
yake yi sanye yake da blue jeans tare black hoodie kanshi dauke da pcap Dr Joel
Kenneth kenan matashin likita da tauraro sa ke haskawa a yanzu Joel d'an kwalisa ne
mai ji da kud'i da kyau.
Iyayyen shi 'yan asalin Nigeria ne zama ne ya kawo su California tun yana yaro
suke a k'asar shi kadai iyayyen nashi suka haifa.
Mahaifinshi ya mutu kusan shekaru goma kenan hakan yasa mahaifiyarsa ta koma
Nigeria a yanzu tana zaune ne a d'aya daga cikin gidaje da mahaifinshi ya bari a
Abj, shi ma yana daff....da komawa Nigeria.
Tun ya shigo yake kallon barrister A k'asa hak'uri ya yi ya mik'e ya nufi
wajenta cikin husky voice dinshi ya ce "hey......beautiful!
Barrister A ta d'ago kad'an ta kalle shi saura kirisss....ta kwalla ihu
sakamakon yanda ta tsorata tare da bud'e idanuwanta, ba don long necklace mai dauke
da cross da ke sanye da wuyan shi da tace Aliyun ta ne.
Tabbas ba ko tambaya tasan wannan twin brother Aliyu ne, saboda tsananin
kamanun su kuma kafin momma ta mutu ta sanar da cewa abokin haihuwar Aliyu bai mutu
ba ranshi ta jefar da shi.
Cikin tsadadd'en turancin shi ya ce zan iya zama.
Cakk.....barrister A ta mik'e tsaye ta shiga rarraba idanuwa ko za ta hango
Aliyu, can.....ta hango shi tafe tun kafin ya k'araso ya ga wani k'ato tare da
matar sa hakan yasa ya k'ara sauri da yake iya bayan shi yake iya hangowa.
Yana k'arasawa dai-dai Joel yana jiyowa karaf.....suka had'a idanuwa sauri
kad'an kowane su ya saki fitsari a wando, Joel ya fi Aliyu shiga firgici saboda bai
san yana da d'an uwa ba saboda iyayyen shi shi kadai suka haifa sa6ani Aliyu wanda
bai dauki dogon lokaci ba ya dawo cikin natsuwar shi, bai san lokaci da ya rungume
Joel ba.
Duk da Joel bai san alak'arsu ba sai kawai ya tsince kanshi da k'amk'ame Aliyu
d'in.
Bayan sun saki juna Aliyu yake mishi bayani ba wai haka kawai suka yi kama ba,
su Twins ne Joel ya 6ata tun yana jinjiri hatta da 6th finger irin na Aliyu Joel
yana da shi.
Shi kanshi Joel ya yarda da abin da Aliyu ya fad'a duk da ana kama a duniya
amma kamanun shi da Aliyu, dole ta kasance ta jini ce.
Babu 6ata lokaci suka nufi gidan Joel d'in inda ya kira mahaifiyarsa mrs Kenneth
domin ya ji daga bakin ta, da yake a vidoe call ya kira ta ya nuna mata Aliyu ya
kuma sanar da ita abin da ya sanar da shi.
Nan take ta fashe da kuka cikin kuka ta sanar da shi gaskiya mr Kenneth adopted
dinshi ya yi a gidan marayu kasancewar bashi haihuwa, amma ya sani har gobe tana
kallonshi a matsayin d'an su tana kuma taya shi murna gane biological parents
dinshi da ya yi.
Tsabar farin ciki da kuma suna so su yi surprising family su yasa washe gari
suka dawo Nigeria tare da Joel.
Lokaci da Umma maryama tayi arba da d'anta da ta fidda ran gani saida ta suma
aka yayyafa mata ruwa ta farfad'o, Daddy ranar kamar zai yi hauka.
*AFTER THREE MONTHS*

A cikin watani uku abubuwan farin ciki sun samu a M Ardo family, inda Joel ya kar6i
musulunci ya tashi daga Joel zuwa Abdulrazaq sai cikin da Barrister A take dauke da
shi na tsawon watani uku.
Burin Daddy ya cika iyalinshi sun kammala kuma suna cikin farin ciki.
Bayan wata biyar barrister A ta haihu ta sami baby boy, ranar suna ya ci sunan
Uncle Suraj saboda tunawa da Uncle yasa.
"suna kiran shi da Aiman rayuwar Barrister A da Aliyu gwanin ban sha'awa kullum
k'ara k'aunar Juna suke yi.



*TAMMAT BIHAMDILLAH*

_ANA NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN GIDAN RINA KUSKURE DA KE CIKI ALLAH YA GAFARTA MIN,
IDA NAYI DAI-DAI ALLAH YASA YA AMFANI AL'UMMAH MUSULMI_

Sai mun had'u a cigaban novel d'ina mai suna *ZAZZAFAN KISHI*
Jeeddah Aliyu




Jeeddah Aliyu

26 / 26