Author : Jidda Aliyu Category : Drama
sark'ewar halshe momma ta ce Ti....Ti...ma me ki ke yi anan?"
Tashi maza ki koma bedroom d'inki.
"Wata mushirika dariya Tima ta yi mai amon gaske ta ce ba Tima ba ce, rijiya ce
mai dauke da kunamu da macizai sun lullu6e wata 'yar jakka mai dauke da kundin
sirri.
"kafin kyaftawa ido har Tima ta mik'e kamar walk'iya, ta kai k'ofar d'akinta.
Da mugun tsoro momma ta bi ta da kallo, da kyar ta hadiye yawu sakamakon yadda
mak'oshinta ya bushe.
"Har Tima ta kama handle d'in k'ofa ta juyo tasake
Kyalkyalewa da dariya ta ce je ki momma je ki maza kada jirgi ya tashi ya barki ba
lalle bane ya dawo daukarki.
"Kafin momma ta yi yunk'uri furta wani abu har Tima ta shige d'akinta.
Mtsss.....!
Momma ta ja tsaki ta girgiza kai tai ficewarta hankali kwance.
Abinda zai ba ka mamaki momma na isa Hotel d'in ta ciro bak'ar jallabiya daga
k'asan seat din motarta ta sanya had'e da yane kusan rabin fuskarta, da mayafin
rigar, ta ciro wani k'ato black shade ta lullu6e kwayar idonta duk sani da kayi
mata ba za ka gane ta ba nan take ba.
"Kaitsaye ta wuce receptionist ta yi magana da ba za ta wuce ta 60 seconds da
wanda yake kula da dakunan hotel din.
Sannan ta nufi upstairs ba ta yi wata doguwar tafiya ba ta iso wani dogon corridor,
rooms ne birjik.....suna facing juna ahankali take duba d'an k'aramin allo da ke
dauke da rooms numbers, har ta yi nasarar gani room 402 hankali kwance ta yi
knocking, wani mutum mai matsakanci tsawo fuskarshi lullu6e da face masks kwayar
idanuwanshi kawai ka ke iya hangowa ya bude mata k'ofa ta shiga d'akin.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:50 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*9*
Rigar jikinta ta fara cirewa ta jefa bisa gado, ta nemi gefen gadon ta zauna yayin
da Jarumi ke safawa da marwa daga farkon bangon gabas zuwa bangon yamma, ya nad'e
hannaye a bayanshi.
"Zai kyau ka nemi wuri ka zauna mu yi magana da ke gabanmu.
Cewar Momma tana nuna masa kusa da ita da d'an yatsanta.
Cikin kaukkausar muryarsa mai cike da ban tsoro ya ce ba zan zauna ba Zaituna har
sai kin fad'a min ta ya ki ka yi sakaci har asiri da ke jikin Muhammad ya karye,
har yake da gwari gwiwar nemowa Aliyu aure?"
"Karka yi min wannan tambayar banza Jarumi saboda banida amsarta, kawai ka nemo
mafita ba wai ka tsaya kana dawo da hannun agogo baya ba.
Kukan kura ya yi ya chafke mak'oshinta, ya shek'eta kamar zai rabata da ranta
tsananin azaba yasa momma kwantawa ya bi ta ya haye ruwan cikinta, sai da ya ga ta
kusa daina motsi sannan yasake ta ya sauka daga kanta.
Yayin da tari ya turnuk'e ta, da kyar ta iya tashi zaune robar ruwan Faro ya dauko
a fridge ya jefa mata.
Jikinta na rawa ta balle murfi ta kafa baki tasha rabin ruwan duk ya zube mata a
jiki.
Cikin angry Voice ya ce ki shiga taitayinki da ni kinsani sarai banida mutunci,
bana d'aya daga cikin mutane da ke jure rainin hankalin tsohuwar kilaki irinki, don
haka ki natsu ki saurari irin hasara da ki ka janyo mana.
Ajiyar zuciya mai k'arfin gaske momma tayi, had'e da shafar wuyanta da ke ji tamkar
an daure mata shi da igiya, yayin da idanuwanta sun kad'a sun yi jajir.
Afusace Jarumi ya cigaba da cewa duk wurin malamin da na je magana d'aya ce,
tabbas sai Aliyu ya yi aure don haka ba mu da za6i illa mu kashe yarinyar bayan
aure.
Sai abu na gaba muddin kina so hakkar mu ta cima ruwa, dole sai kin hana Aliyu
kusantar yarinyanan malam ya gayamin muddin suka yi tarayya, komai na mu ya rushe
duk wani wahala na tsawon shekaru 28 ya rushe.
Hannunshi yasaka a pocket d'in rigar shaddar da ke jikinshi, ya ciro wasu bak'ak'en
layu ko kallonsu ka yi sai gabanka ya fad'i ya mik'awa Momma, ki binne su dai-dai
wurin da ki ka san Aliyu zai taka.
Hannunta na rawa ta kar6a ta shiga jujjuya su.
Sake dauko wata batta ya yi wacce aka lullu6e da fatar damisa, wannan kuma ki
turare shi idan ki ka san Aliyu zai shak'i k'amshinsa karki sake wani ya ji
k'amshinsa fa ce Aliyu, kinji ko?"
Gyad'a kai ta yi kafin ta gyara zama muryarta bata fita wtsosai saboda shak'ar da
ya yi mata, ta ce ba ka yi min gamsasshe bayani magani na menene?"
"Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba daga bisani ya zauna kusa da ita, ya dafa
kafad'arta ya yi kasa da murya tamkar mai rad'a ya ce amfanin wannan magani shine
mazakuta Aliyu zai mutum mutusss, koda tsirara ya ga mace ba zai ji sha'awarta ba.
Karki manta sihiri da ke jikinsa na tsanar aure ne da tsanar mata ba na sha'awarsu
ba, ki sani kasancewar Aliyu da wannan yarinya a waje d'aya dole wata rana zai ji
sha'awarta, idan har ya had'a shinfid'a da ita daga ni har ke kashinmu ya bushe don
haka ki kiyayye.
"Shikenan idan wannan ne Jarumi bakada matsala.
Da kyau 'yar gari sai ki tashi ki tafi, na gama magana Sai dai idan wani emergency
ya taso zai nemi ki.
Mik'ewa tayi tasaka rigarta da black shade d'inta, ta kuma zuba guzirin shed'an
d'in da yabata a handbag.
***---****----****
Da misali k'arfe 5 na yammaci Aliyu yana zaune a office d'inshi, ya duk'ufa akan
system dinshi aiki yake sosai.
Aka yi knocking k'ofa yes!
Yafad'a batare da ya kalli me shigowa ba,
Sakatariyarshi ce Ester.
Cikin girmamawa ta ce Sir Jamal ne ya zo kasan da zuwanshi a shigo da shi.
"Sai a lokaci ya d'ago darara idanuwanshi, masu masifar tafiya da imani 'ya mace
ya ce ki shigo da shi mana.
Okay sir!
Tafad'a had'e da juyawa.
Bata jima da fita ba Jamal ya shigo hannu ya mik'awa Aliyu suka yi musabaha kafin
ya ja kujera ya zauna, ya ake ciki abokina tun jiya yakamata mu tatttauna zance
barrister sai dai rashin wadattace lokaci ya hana mu?"
"K'ayattace murmushi Aliyu ya yi ya mayarda laptop dinshi gefe, ya kalli Jamal a
natse ya ce gaskiya ba laifi Barrister tana da kyau sosai kuma da alamu tana da
kyau hali, sai dai banji sonta ko k'ank'ani ya shiga zuciyata ba, kawai dai yanayin
shigarta da yadda take magana ya burge ni, matuk'a.
Amma a haka zan daure na aureta tunda an riga an mak'alk'alamin ita bani da za6i.
"Jamal ya yi murmushi tare da jinjina zance abokin nashi, ya gyara zamanshi yana
duban Aliyu cikin sanyaya murya ya ce ina gani tunda har ka amince wannan ba abin
damuwa bane duba da biyayya ce za ka yi ma mahaifinka,
"Inaso ka dauki zance da muhimmanci kada kayi halin ko oho da lamarin barrister,
ba mamaki ita ma biyayya ce za ta yiwa nata iyayyen ina rok'o ka abokina da kayi
abinda ya kamata.
"Ta6e baki Aliyu ya yi yana yatsine fuska "to ni miye nawa aciki?"
Daddy ya ce in shirya naje naga yarinyar na kuma je, bayan nadawo na shaida mishi
ta yi sai dai gaskiya ban nuna mishi bana sonta ba, yanzu dai lokaci biki kawai
nake jira.
"Ba damuwa abokina idan da rai da lafiya two months kamar gnbe ne, ya.zu yaushe
za mu sake komawa waJenta?'
# "Banaso a semi matsala daga gareka.
Cewa2 Jamal yana duban Almyu.
"Gaskiya yanzu bani da lokaci akwai d'inbin ayyuka agabana, kuma ma miye amfanin
zarya gun yar)nyar da banida ra'ayinta, ina ce sai in kana son mace ka ke d'oki da
rawar jiki son ganinta?"
"Gaskiya hakan bai dace ba abokina kadai duba, koda zuwa end of this month ne mu
kai mata ziYara wallahi yarinyar tana da kirki matwk'a.
"Shikelan Jamal zan dtba nagani amma a halin da ake ciki yanzu bani la |okaci, sai
mu jira zuwa k'arshen wannan watan.
Ba damuwa abokina kadai k'ok'arta.
Dariya Aliyu ya yi a ta{aice$ya ce naga alama kai da barrister ta ku!ta zo d'a}a.
Dariya Jamal 9a yi yana mai mik'a masa hannu suka kashe.
***----***---****
*YOLA*
Barrister Amina tare da Barrister Zarah suka jero suna fitowa daga magistrate
couru 3.
Barrister Zarah ta dubi barrister Amina ta ce bebs ya had'uwarku da(Aliyu ta
kasance hope guy ya yi miki?"
"Murmushi Barrister Amina tayi tace Ba laifi ya amsa sunanshi namiji yana da kyau
sosai da cikar kwarjini, ya had'u irin had'uwar da kowace 'ya mace take buk'ata.
Ya yi miki kenan?"
Ba laifi gaskiya karo na farko a rayuwata da naci karo da namijin da naji farat
d'aya ya kwanta min a rai.
Ta k'asara magana tana tunowa da fuskar Aliyu.
masha Allah!
Haka nakeso ji daga gareki bebs fatana Allah ya had'a kawunanku ya kade duk wata
fitina da ke ciki.
Amin! Bebs.
****----****-----****
A kwana atashi asarar mai rai yau gashi saura sati uku bikin Aliyu da barrister
Amina, zuwa wannan lokaci abubuwa da dama sun faru daga ciki akwai masu dad'i akwai
akasin hakan.
"Kud'ad'e masu kauri gaske Daddy ware ya ba k'anwarshi Salma ta je Dubai ta
had'owa Aliyu kayan lefe na gani na fad'a taci mutuncin naira ba kad'an ba.
Daddy bai saka momma cikin hidimomin bikin ba, asalima ma bata san da zance lefe
ba, sakamakon yadda ya ga tana nuna adawarta akan aure a fili, tun abin yana bashi
mamaki har yadawo bashi tsoro lokaci da ya sanarda Salma zance ita ce ta bashi
shawarar ya dinga 6oye Mata duk wani abinda ya yashafi zance auren na Aliyu, har
zuwa lokaci da za'a yi biki saboda basu san miye manufarta ba.
nan take Daddy ya yi na'am da shawarar Salma saboda shi kanshi lamarin na masifar
daure mishi kai.
"Akwati goma sha biyu Salma ta had'a har da tsaddadiyar mota akai kirar
cadillac, lokaci da aka kai lefen gidan Barkido ya yi fad'a sosai a cewarshi
bayason bidi'a da kyar dangi suka shawo kanshi ya amince aka kar6i kayan.
"Barrister Amina kwance akan gadonta ta yi zurfi a tunanin Aliyu abu d'aya ya ke
daura mata kai, ya kuma jefa zuciyarta cikin tunani shi ne tunda Aliyu ya zo sau
d'aya bata k'ara jin d'uriyarshi ba.
Sai kayan lefe aka kawo gidansu shin me hakan yake nufi?"
Anya kuwa Aliyu yana sonta?"
Wad'annan su ne tambayoyin da tarasa wanda zai bata amsar su.
"Mtsss....!
Ta ja tsaki ta dauki pillow ta matse gam a k'irjinta, ta d'an girgiza kanta cike da
haushin kanta ta tuna da halin da ta tsince kanta, game da Aliyu domin tun daga
ranar da idanuwanta suka ganshi, sai tunaninta ya canza zuciyarta ta bijiro mata
da wani al'amari mai wuyar fassarawa.
Tsundun ta tsunduma begen Aliyu al'hali shi d'in bai san tana yi ba.
Ba ko shakka tasan ta kamu da soyayyarshi mai zafin gaske, duk da tana da labarin
bai cika zama wurin d'aya ba, shi mutum ne mai yawan tafiye-tafiye ak'alla ace yana
kiranta a waya ko gaisawa su yi koda bai mata firar soyayya ba.
Yaushe ma ya ga numbernki da zai kira ki.
Wani bangare na zuciyata ya ce da ita.
Yanzu ahaka za su yi aure al'hali bai da lokacinta, kenan hakan za su yi zaman
aure?"
A karo na biyu tasake jan tsaki mtsss!
Cike da takaici zuciyarta sai rad'ad'i take mata, sosai take ji zafin kanta yadda
ta shiga damuwa akan mutume da bai ma san tana yi ba, asanyaye ta mik'e tashiga
bathroom sakamako kiran sallar magarib da aka fara.
***----****----*****
*LAGOS*
Aliyu na zaune a office dinshi da ke Lagos ayyuka sun masa yawa ba kad'an ba, duk
da yau ya sami sassaucin aiki, a matukar gajiye ya jingina bayanshi ga jikin kujera
da yake zaune akai a hankali ya zare sun shade glass din da ke manne a kwayar
idonshi, tare da lumsashe idanuwanshi wayarshi tayi ringing har ta tsinke bai d'aga
ba, a karo na biyu tasake ringing sai da ta kusan tsinkewa ya mik'a hannu ya dauka
batare ya bud'e idanuwanshi ba ya yi picking ya kara a kunnenshi.
"He...llo!
Yafad'a chan k'asan mak'oshi.
ka ci gidanku Sultan.
Ba shiri Aliyu ya ware idanuwanshi ya kuma gyara zamanshi, sakamakon muryar Daddy
da taki dodon kunnenshi.
"Dad ina wuni?"
Ban san inda yake ba.
Cikin shagwa6a Aliyu ya turo baki yana cewa Daddy....am sorry!
Duk da ban san laifi da nayi ba.
Fad'a sosai Daddy ya shiga yi mishi ta hanyar cewa karka maidani mutume banza
Gadanga, sau nawa ka je Yola wurin Amina bayan zuwanka na farko?"
"Tsuke fuska ya yi kamar Daddy yana ganinshi, ya ce Daddy am too busy ban samu
zuwa ba ayyuka ne suka yi min yawa.
Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:50 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*10*
Amma duk lokaci da na samu sassaucin aiki zan shirya in je, amma kuma Daddy sai
nake gani ko ban je ba zan iya aika P.A na kamal amadadi na, sai ta yi mishi list
na abunda take buk'ata ko nawa ne zan ba t.....
"To hell with you ka da kud'in naka Gadanga.
Daddy ya katse cikin fushi Daddy ya cigaba da cewa an gayamaka komai ne kud'i suke
iya siye, in fact yarinyarnan ba 'yar matsiyata ba ce ita kanta mai kud'i ce balle
aje ga iyayyenta.
Yadda ka ke tink'aho ubanka mai arziki ne ita ma nata uba mai arziki ne, inaso ka
jingine zance kud'i a gefen ka natsu kasan me ka ke yi, saboda kai ba k'aramin yaro
bane.
"Aliyu kamar zai fashe da kuka yake shafa sumar kanshi kafin ya ce kayi hak'uri
Daddy I don't mean to hurt you am just try to tell you how busy I'm but am so
sorry, zan yi k'ok'ari gobe na biyo morning flight nayi weekend a Yola.
"That's my favourite boy haka nakeso ji Gadangana.
kafin Daddy yasake magana ya katse kiran had'e da jefa wayar bisa file d'in da ke
gabanshi, ya tsurawa wayar ido yana girgiza k'afarshi, zazzafar ajiyar zuciya ya yi
had'e da jin haushin Daddy ganin da k'arfi da yaji yana so ya mak'alk'ala masa
auren yarinyar da baya jin sonta a zuciyarshi.
"Zuwa wannan lokaci yaci ace Daddy ya jinjina masa da namijin k'ok'arin da ya yi
na amincewa da auren, yaci ace ya yaba masa ya kyale shi yaji da k'unci da
rad'ad'in da zuciyarshi take mishi, ya Daddy yakeso ya yi da rayuwarshi ne?
"Shi mutum ne da bayaso damuwa ko kad'an sai gashi stress yana so ya yi mishi
yawa.
ya jima shiru yana nazarin abinda ya kamata ya yi, yasan tabbas bashi da mafita
dole yaje Yola, musanmman yadda ya daure kanshi har da wani cewa zai yi weekend a
can, ya zame mishi wajibi dole ya je ko baya so in dai yana so zaman lafiya
tsakaninshi da Daddy.
Ya d'ago kan ya dubi wrist watch d'in hannunshi sannan ya mik'e tsaye ya dauki
wayoyinshi ya bar office duk da yana da tarin ayyuka masu matukar muhimmanci.
****----****----****
*ABUJA*
Momma tafito daga apartment d'inta jikinta sanya da buba ta material black & golden
colour, kaitsaye apartment d'in eMaryam ta nufa dai-dai k'ofar shiga main parlor ta
tararda wata 'yar kyarmusasshiyar mata tana jiranta, barka da fitowa Hajiya!
Yauwa Ruky!
Shigo daga ciki ki ganta kwananan jikinta ya fara sauki sosai, momma tafad'a tana
wucewa gaba Ruky na biye da ita tun daga main parlor za ka fara ji gurnaninta,
tsaki momma ta ja mtsss!
wata k'ofa ta nufa ta sanya key ta bud'e wani irin masifafe wari ya bugi hancinta
babu shiri ta doshe hanci da tafin hannunta, cikin fushi ta shiga kwalawa inna
Laraba kira inna laraba.....inna laraba fa!
Da gudu tafito daga bedroom d'inta d'an kwalinta a hannu, cikin yanayi na tsoro ta
k'araso gani Hajiya.
Wannan wane irin wari ne ke fitowa daga d'akinan?"
Jikin inna laraba yana rawa ta shiga d'akin, Maryam na takure a jikin bango sai
fizgar gashin kanta take tana wani irin gurnani bakinta na fitarda miyau mai
yauk'i, k'afafunta da hannayenta daure da sark'a abin gwanin ban tausayi.
Cikin rashin tsoro Inna laraba tanufi wajenta, tashiga dubata tagano kashi ne tayi
d'agata tayi tanufi bathroom da ita ta tsaftattace mata jiki had'e da sauya mata
kaya ta fito da ita bisa gado ta zaunarda ita, ta dauki tissue ta goge inda kashin
ya6ata tayi mopping ta kuma fesa air freshner sannan fa momma da Ruky suka shigo
duk da haka sai wani yayatsine fuska momma take.
"Cikin daure fuska momma ta dubi inna Laraba ta ce inna ba mu wuri likita za ta
duba ta.
To!
Cewar inna Laraba tana mai ficewa daga d'akin.
Daf da Maryam momma ta tsaya ta d'ago ha6arta cikin zallan rashin imani ta dauke ta
da mari, sai da ta kai kwace, sai kawai ta rufeta da duka tana yi tana zurfa mata
zagi shegiya tsinaniya muddin ina raye kin dinga gani bala'i da masifa har karshen
rayuwarki.
Ba dai kin k'i mutu ba tsawon shekara ashiri da takwas ina azabtarda ke, da yake
ran kare ne da ke kin k'i mutu ki hutarda kanki nima in huta, to tunda kin kafe mu
zuba ni da ke d'a halak ka fasa, shegiya mai taurin ran tsiya.
Ta k'arasa magana tana huci.
Dafa kafad'arta Ruky tayi cikin sigar rarrashi ta ce don't worry Hajiya komai yana
da lokaci tunda ki ka iya jure zama da ita na tsawo shekaru 28 kisanta ba zai miki
wahala ba.
"Bana so na kasheta ne da kaina Ruky na fi so wahala ta kashe, ta kinga ba wanda
zai zargeni.
"Haka ne Hajiya you're too smart.
Dariya momma tayi cike da jin dad'i an ya6e ta.
Yi maza Ruky ki yi mata allurar haka kawai 'yan kwanaki nan da aka daina yi mata
allura tafara acting like normal mutane, kin ko ga ba abu mai sauki bane na barta
ta wark'e don haka daga yau kin dinga yi mata allura kenan.
"Murmushin mugunta Ruky tayi ta bud'e handbag tafito da wani Vaccination, saida
ta cika sirinji ta kama hannu Maryam wacce tun lokaci da momma ta jingeta take
kwance lamo kamar mai bacci, ga jijiyar hannu Ruky tai mata allura ko motsawa bata
yi ba cikin abinda bai wuce 30 seconds ba tayi bacci.