Author : Jidda Aliyu Category : Drama
picking call d'in.
"Suna gama gaisawa ta shiga bata labari duk abinda yafaru daga ciki har da
yadda Aliyu yafara nuna mata kulawarshi.
"Sosai barrister z ta shiga tayata murna da k'ara k'arfafa mata gwiwa, da haka
suka yi sallama.
***""****""""***
Momma ta fito daga bathroom dai-dai kiran Jarumi na shigowa wayarta, cikin zumud'i
ta d'aga kiranshi Hello.....Jarumi ya zan kiraka jiya nafad'a maka akwai matsala,
sai kawai kayi picking ka k'i magana daga k'arshe sai ma kashe wayarka kayi, wato
sai yanzu kayi lokacina.
"Dakata Zaituna!
Ya daka mata tsawa duk da ga waya ne saida momma ta tsorata, cikin hargowa ya ce
"ubanwa kika fad'awa sirrina?"
Saboda jiya banga kiranki a wayana ba.
Sosai momma ta girgiza da jin kalamanshi atsorace ta furta nashiga uku
Jarumi....idan ba kai bane waye ya d'aga wayar?"
Uhm.....Zaituna kin gama da ni kin rusa min plans, nasha gayamiki ki daina
kirana sai in nine na kira ki da yake kwakwalwar kifi ne da ke, bakya ganewa
to....gashinan garin shirmenki kin janyo mana masifa, saboda bansan waye ya d'aga
wayar ba.
Ban kuma san iya adadin abinda ki ka fad'a ba, amma ba komai ki zo ki sameni a
mahad'armu dole na sauya plans.
"Ya katse kiran tuni momma tafara sweating kaman ba Aircon a room d'in.
**"""***"""***
Aliyu ya d'ago da kanshi ya dubi wall o'clock yaga lokaci ya tafi sosai, ya mik'e
da sauri ya shiga tattara files d'in ke kan desk yana zubawa a locker daga bisani
ya dauki wayoyinshi yafice.
Isah direba yana gani yafito ya janyo mota ya bude masa k'ofa ya shiga, saida ya
biya k city restuarent ya yi mata take away sannan ya nufo gida.
"Koda yashigo tana upstairs bedroom kaman yadda ya umarceta tana kwance sai zugi
hannunta yake mata, ya turo k'ofa dauke da sallama ta mik'e zaune da sauri saboda
bata yi tsanmani ganinshi a wannan lokaci ba.
"Cikin sanyi murya mai had'e da rad'ad'in ciwo ta amsa mishi sallama, ya k'araso
kusa da ita yana fad'i ya hannun naki hope baya miki zafi sosai?"
murmushin k'arfi hali tayi kafin ta ce "da sauki yana zafi saidai ba sosai ba.
Hannun ya rik'o gani yadda ya yi, yasa zaro idanu duk yabi ya tashi hankalinshi sai
cewa yake tashi maza ki shirya mutafi hospital, shiyasa tun farko naso mu je
hospital kika kafe akan lalle hannu baya miki zafi kalli garin sakarcinki za kiyi
min wasa da lafiyarki.
"Ba abinda ya firgita barrister A ya kuma jefata a tarkon tunanin kaman
faruncinshi na k'arshe, duk da tana jin hannunta yana mata zogi bai hanata
murmushin jin dad'i ba.
Wanda sautinshi yafita hakan yasa shi d'agowa ya kalle cikin idanuwanta ya ce
"ke lafiya ina magana kina murmushi wato ga shasshasha ko?"
"Girgiza kai tayi kafin ta ce kayi hak'uri Yalla6ai naga duk ka bi kad'aga
hankalinka akan d'an k'ank'anin abu.
"Mtss.....yaja wata shegiyar tsaki mai cike da nuna jin haushi, ya ce "abeg my
friend tashi ki sauya kayan jikinki karka 6atamin lokaci yana gama magana yafice ya
barta sake da baki tana kallon bayanshi.
"Yana rufo k'ofa ta sauko daga kan gado tadaka tsalle had'e da furta
Alhamdullilah......!
Wani shegen zafi ya yi ma hannunta ziyara bazata da sauri ta runtse idanunta, saida
taji hannun yalafa mata sannan ta sauya kayan jikinta.
"A downstairs parlour ta iskeshi tsaye yana jiran fitowarta, yana ganinta yafice
ta bishi abaya.
"Kai tsaye Nissa hospital suka nufo bayan sun ga doctor, gaba d'aya saida aka
d'aye fatar hannunta sai runtsa idanuwa take hawaye na zuba, bayan ancire fatar aka
wanke ciwo sannan akayi dressing wurin.
"Yana rungume da rabin jikinta suka fito daga cikin reception na hospital d'in
hannunshi rik'e da hannun nata mai ciwo har suka iso gida yana mata sannu.
A main parlour ya zaunarda ita ya nufi kitchen ya dauko plate ya juye mata abinci
da ya shigo da shi, a baki ya shiga bata duk da bata jin yunwa sai ta tsince kanta
da bude baki, ita kanta tayi mamakin yawan abincin da taci da kyar ta iya bude baki
ta ce da shi ta k'oshi, ya bata maganinta tasha.
"Har zuwa lokaci she can believe Aliyu ne shin me ya kawo wannan sauyin da sauri
haka?"
Ta Kalleshi irin kallon mai ratsa jini da 6argon jiki ta motsa pink lips dinta with
so much excitement ta ce thank you so much my humble husband for caring.
D'an hararanta ya yi yaja karan hancinta ya ce banaso shirme duk abinda nayi
miki tamkar kaina nayi ma don haka karki sake godemin.
"Sai kawai tayi murmushi.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:14 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*27*
Momma tafito cikin shirinta na zuwa ganin Jarumi.
sai sauri take yi kaman mai shirin bari gari, tun kafin ta k'arasa parking lot tayi
unlock d'in motarta da car key da ke rik'e da hannunta.
Ta shiga motar tayi reverse ta nufi gate maigadi ya bude mata gate tafice da wani
irin gudu na ban mamaki, western dreams hotel ta nufa saida tayi 6ada kama ta
hanyar saka face mask za ka dauka saboda cutar corona ne, yasata amfani da shi ta
rufe kwayar idanunta da black shade, sannan tafito daga mota ta shiga reception
shigowar text message taji a wayarta _ina room 247_
Tana gama karanta text message d'in ta nufi corridor da zai saddata da d'akin.
"Tun kafin takai da yin knocking ya bude mata k'ofa, tashigo yau d'inma fuskarshi
a rufe take da face masks mai siffar lion tana shigowa ya maida k'ofa ya rufe.
Tana dosana bombon d'inta gefen gado tana jin saukar wani mushirikin mari, saida
tanemi ji da ganinta tarasa kafin tayi wani yunk'uri ya tureta tafad'i kwance akan
gado ya bita ya haye ruwan cikinta.
"And then....he started removing her clothe ya yi mata naked ya tsaya yana
kallon nakedness d'inta.....he wearing a wicked smile duk lokaci da yaso yaci
zarafinta kwanciyar wulakanci yake da ita cikin muryar kuka momma ta ce don Allah
Jarumi kayi hak'uri....don't treat me like this"
"Ya d'ago da fuskarshi da ke lullu6e da masks ya ce "you made a huge mistake na
sanarda wani sirrina don haka ina da damar da zan yi treating naki yadda nakeso.
"Tana ji tana gani ya shiga sarrafata kuma irin na mugunta d'inan ga momma jiki
yafara nauyi dama makeup ne yake 6oye tsofanta....lol.
Haka ya Jarumi ya cigaba da shagalinshi ita kuma tana kwance kaman gawa saida ya yi
son ranshi, sannan ya barta abin takaici ta tashi ta tsinto tufafinta da ya zubar a
k'asa tasaka.
"Cikin kaukausar murya yafara magana wato yanzu na fahimci reni yafara shiga
tsakanina da ke Zaituna, kin manta waye ni da Kuma abinda zan iya aikatawa idan
mutum ya kuskure min.
Zan miki gargadi na k'arshe wallahi.....wallahi Zaituna kinji na rantse idan kika
sake plans dina na tsawon shekaru masu yawa ya rushe ki saka aranki kin zama gawa.
"Da mugun tsoro momma take kallonshi, shi kuwa ko a jikinshi ya cigaba da
zazzaga mata ruwan bala'in.
Tunda na fahimci kwakwalwarki batada amfani na canza plans d'ina ba kuma zan
sanarda ke ba, saidai na baki umarni ki bi idan kuma kika kuskure sai na lahira
yafi ki jin dad'i tashi maza ki 6acemin da gani tsohuwar banza tsohuwar kilaki.
"Ta tashi jikinta yana rawa ta dauki car key d'inta tafice cikin wani irin
tafiya kaman wacce tayi tangard'e.
"Tana shigowa main parlour ta iske Daddy tare da Teema zaune yana sauraren
shirmeta, suna arba jikinta ya dauki mugun rawa kaman daga sama taji sautin
muryarshi yana cewa "Zaituna daga ina kike?"
"Cikin rawar murya tafara magana abinka da marar gaskiya Du.....biya.....
Dubiya?"
Ya tambaya sounding very angry momma ta gyad'a kanta.
"K'arya kike yi Zaituna ba daga dubiya kike ba, koma daga ina kike Allah yana
ganinki.
Daga haka bai k'ara furta uffan ba ya dawo da ganinshi akan Teema.
"Momma tayi shiru saboda babu bakin magana, jikinta sanyi lak'asss.....ta nufi
upstairs yayin da Daddy yabi bayanta da kallo yana jin wata irin tsanarta tana
haurowa a k'asan zuciyarshi.
*****---****----*******
"Tun daga dowawarsu daga asibiti yake zaune a gida bai sake fita ba, sai kulawa
ta musanmman yake bata.
"Ko motsi kadan tayi sai ya tambayeta hannu ne?"
Ita kuma ta gyad'a kanta har wani sabuwar shagwa6a ta tsiro da shi ta dinga matsar
hawaye k'arya.
"sallah kadai ke fitarda shi daga gidan, lokaci da ya dawo daga sallar isha'i
ya bi ta flat d'in momma domin ya sanarda ita barrister A ta k'one.
"Koda ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya nufi bedroom d'inta da ke upstairs ya
sanarda ita, ba yabo ba fallasa tayi mishi fatan Allah ya bata lafiya ba.
Falon Daddy ya wuce ya isa ga kujera ta kusa da wacce Daddy yake zaune ya zauna
yana gaidashi "Daddy barka da hutawa!
"Ya amsa da yauwa sultan ya jikin matarka?"
Taji sauki Daddy!
Madallah ka kula da ita sosai.
"Insha Allah Daddy!
Daga haka suka yi shiru yayin da Aliyu yake karantar yanayin mahaifin nashi, sai
yaga kamar akwai damuwa atattare da shi ya ce "Daddy naga kamar akwai abinda ke
damunka, musanmman lokaci da na shigo sau uku ina sallama kafin ka ji kayi nisa a
tunani "don Allah Daddy meke damunka?"
Asanyayye Daddy ya yi murmushi ya kalle d'an nashi ya ce "ba komai sultan gajiya ce
kawai.
Kallonshi kawai Aliyu ya yi amma ba don ya yarda ba, ya mik'e had'e da cewa sai da
safe Daddy!
Har ya kai bakin k'ofa Daddy ya kirashi sultan...!
Na'am Daddy amsa had'e da juyowa.
Zo nan.
Daddy ya yafitoshi da hannunshi na dama.
''Dawowa ya yi ya zauna inda ya tashi yana kallon mahaifin nashi atsanake.
"Sultan inaso kayimin wani alk'awali ko bayan raina bazaka warware shi ba.
"Inajinka Daddy!
Cewar Aliyu cike da fargaba jin abinda mahaifin nashi zai fad'a.
Sultan inaso kayi min alk'awali komai runtse bazaka rabu da matarka ba, za ka zauna
da ita cikin dad'i ko akasin hakan.
Murmusawa Aliyu ya yi yana shafar gemunshi ya ce "Daddy idan wannan ne bakada
matsala da ni, nayi maka alk'awali komai wuya komai dad'i ina tare da Amina.
"Masha Allahu.....yarona naji dad'i wannan furuncin naka Allah ya yi maka albarka,
ya baka ikon rik'e alk'awali.
Aliyu ya amsa da ameen summa ameen!
Cike da farin ciki Daddy ya ce tashi ka tafi ka gaida min da ita, kafin na shigo da
safe na dubata.
Za taji Daddy!
Ya tashi yafice.
Lokaci da ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya wuce d'akinshi ya yi wanka, ya
shirya cikin pyjama saidai bai rufe bottoms d'in rigar ba sai uban k'amshin dolce &
gabbana perfume yake yi kai tsaye bedroom d'inta ya nufa alokaci har tayi wanka
tana sanye da cotton night gown mai d'an siriri hannu wacce da kad'an ta wuce
cinyoyinta.
"Yana tura k'ofa ta d'ago suka had'a idanu ya yi tsaye jikin k'ofar, yana aika
mata da shu'umin kallo.
Kasa jure kallon nashi tayi sakamakon wani irin bugawa da zuciyarta ke yi.
Ya k'araso ya iso gabanta ya durk'usa, ta shak'i dadd'add'en k'amshin turarenshi
wanda gaba d'aya ya lullu6e k'ofufin hancinta ta lumsashe idanuwanta. Hannunta mai
ciwo ya rik'o yana kallon ciwo, kafin ya dawo da ganinshi akanta cikin tattausan
lafazi ya ce "ya kike jin hannu yanzu?"
Rausayarda kanta tayi tana kallon wani gun daban, ta ce da sauki.
"Murmushi ya yi had'e da mik'ewa tsaye batare da dauke idanuwanshi akanta ba ya
ce "tashi muje kici abinci.
Nagode Yalla6ai amma bana jin yunwa.
Tafad'a had'e da sadda kanta k'asa.
"Ya 6ata fuska sosai alamar ranshi ya6aci, duk da haka sai ya tsince kanshi da
controlling anger nashi ta hanyar sassauta murya alamar rarrashi ya ce "ki daure
Amina ko kad'an ne kici idan baki ci ba, bazan zan ji dad'i ba.
Yadda ya yi magana ya yi masifar burgeta tayi murmushi had'e da mik'ewa ya wuce
gabanta ta bishi abaya.
"Da kanshi ya yi mata serving da yake ga hannunta na dama ta k'one sai ta rik'e
spoon da hannun hagu, saidai bata taji dad'in rik'on spoon d'in ba.
"Gani haka yasa ya kar6i spoon daga hannunta ya shiga feeding d'inta, goganyar
taku ta bud'e ciki ta narki abinci kaman ba ita bace ta ce ta k'oshi.
ragowar abinci da ta rage ya ci sai faman kallonshi take yi idan ya d'ago suka
yi four eyes, tasake mishi murmushi shima ya mayar mata da martani murmushin nata.
Yana kammalawa ya tattare plates ya kai kitchen.
Ya nufo cikin falo idan ya hangota zaune maganinta ya dauko da bottle d'in ruwa, ya
bata tasha sai faman yatsine fuska take yi shi kuma yana mata sannu.
Around 10:30pm tayi mishi sai da safe ta nufi bedroom d'inta bata jima da
kwanciyar ba, bacci ya yi awon gaba da ita.
Aliyu ya jima zaune har lokaci kwanciyarshi bacci ya yi, ya mik'e ya koma bedroom
dinshi saidai sam ya kasa bacci sai faman juyi yake yi, nan take tunanin ya fad'o
mishi bai kamata ya barta ita kadai ta kwana ba, dole ya kasance tare da ita karta
falka tsakiyar dare ta buk'aci ruwa ko wani abun daban. daga k'arshe ya tashi ya
nufi d'akinta ya tasaki sa'a bata rufe da key ba.
Yana murd'a handle k'ofar ta bud'e ya kutsa kai, duk da d'akin yana dauke da diff
light hakan bai hanashi gani kyakyawar fuskarta ma'a6ociya kwarjini ba.
"Sam bai yi tunanin kwanciya kusa da ita ba ya dauki two pillows ya jefa kan rugs
carpet ya kwanta, sai dai kuma ya kasa bacci domin wannan shine karo na farko da ya
kwanta ad'akinta, ya jima sosai kafin ya samu bacci ya dauke shi.
"Can tsakiyar dare ta falka don ta gyara kwanciyarta ta shak'i k'amshin
turarenshi da ya gauraye d'akin, ta tashi zaune ta hango shi kwance kan carpet da
sauri ta yaye duvet da ke rufe da jikinta ta zuro fararen k'afafunta k'asa, sannan
ta mik'e tsaye ta isa wurinshi ta durk'usa tashiga bubbuga hannunshi had'e da kiran
sunanshi.
A hankali ya bud'e idanuwanshi ganinta a durk'ushe yasa ya tashi zaune yana
murtsuke idanunshi asanyaye ta ce "Yalla6ai don Allah tashi ka koma kan gadon ka
kwanta.
Ya girgiza kanshi ya ce "ki barni anan ya isa yana k'ok'arin komawa ya kwanta, Ta
marairaice murya kaman za ta fashe da kuka, tasake cewa don Allah yalla6ai ka tashi
ba don ni ba.
Ko dai kana tsoro kar na dameka da snoring ne...?ni sai na kwanta k'asa sai kai ka
hau gado.
"Murmushi ya yi batare da ya furta uffan ba ya mik'e ya hau gadon ya kwanta,
yayin da tayi tsaye tana kallonshi.
"Zo ki kwanta barrister banaso kallon nan naki mai kama da na tuhuma.
"Tayi murmushi batare da ta musa ba ta isa kusa da shi ta kwanta, yaja duvet ya
rufa musu ya shak'i k'amshin turarenta ya lumsashe idanuwanshi bayan ya sauke
zazzafar ajiyar zuciya.
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:17 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*28*
Cikin kwanaki k'alilan shak'uwa ta ban mamaki ta shiga tsakaninsu, tun barrister A
tana gani abin kaman al'mara har ta zo tafara sabawa.
"Gani yadda ya dauki komai nata da mahimmanci yasa tak'ara zage dantse wurin
kyautata mishi, duk da har yanzu ba abinda ya shiga tsakaninsu ko abisa kuskure bai
ta6a gwada koda sum6atar ta ne ba.
Tun bayan fitar Aliyu office take ji gidan so bore, sai kawai ta tsince kanta da
son fita compound, tasha fresh air mik'ewa tayi tasaka flip flops a k'afarta.
Jikinta sanye da palazzo trouser had'e da split flutter sleeve ta yane kanta da
scarf shigarta ta, tak'ara fitowa da ainihin kyauta.
Ta nufi k'ofar fita daga main parlour tana fitowa tayi tsaye a barranda flat
d'inta, tana kallon shige da fice na ma'aikatan gidan.
"Abinda ke daure mata kai ya k'ara jefata duhu, bai wuce flat d'inan mai dirty
tsiya ba. musanmman yanzu da take tsaye tana kallon yadda ma'aikanta gidan suke
tsaftace harabar gidan.
Hatta da ganye flowers da idan ya fado sai sun tsince shi, to amma meye dalilin da
yasa suka bar waccan flat d'in da dirty.....?"
Rashin sani amsar tambayarta yasa ta yanke shawarar yau dai sai taje wurin, koma
menene zata gani da idanuwanta.
"Har ta isa flat d'in ba wanda ya ganta da yake kowa aikin gabanshi yake yi, tana
shiga barrandar mamakinta ya k'aru sakamakon k'arar sautin television da taji, tayi
shiru na wasu 'yan seconds kafin ta nufi k'ofar ta shiga knocking....shiru ba'a
bud'e ba kasa hak'ura tayi ta cigaba da knocking da k'arfi tabbas yau sai taga
abinda ke cikin wannan flat d'in.
"Ta dauki dogon lokaci tana knocking batare da tagaji ba.
ba'a kuma bud'e mata k'ofar ba.
Har ta yanke hukunci ta zagaya backyard tunda akwai windows awurin ta lek'a koma
menene zata gani sai taji footsteps ana zuwa, da sauri taja da baya kad'an ta kuma
k'ara ware idanuwanta yadda zata ga me zuwa.
bud'e k'ofar akayi wata tsohuwa ce wacce ak'allan shekarunta na haihuwa zasu kai
sittin a duniya ta baiyana, kallon-kallo suka shiga yiwa junansu.
"Barrister A ce tayi k'arfin halin cewa sannu baaba.....!
Yauwa 'yar nan ko kece likita da Hajiya Zaituna ta turo?"
kafin barrister A ta bata amsa ta cigaba da cewa da yake ban wayeki ba waccan 'yar
k'armusasshiya nasani, mai siffar marasa imani amma ke da ganin fuskarki kina da
burbushin imani duk da abin ba'a fuska yake ba.
Shigo daga ciki ki dubata da yake kwana nan kamam tafara dawowa hankalinta.
Duk surutu da baaba laraba keyi barrister A tsaye kawai take tana kallonta.
"Gani ta ra6e ta bata hanya yasa tayi shahada ta kutsa kai, baaba kuma ta maida
k'ofa ta rufe da key had'e zare shi.
Ta wuce gaba barrister tana bin ta abaya, cikin d'an k'ank'ani lokaci ta k'arewa
falon kallo gaba d'aya cushion d'in da ke cikinshi sun tsofa irin sun zama old
model muryar baaba laraba