Author : Jidda Aliyu Category : Drama
ji a
zuciyata.
"Haba Teema.....haba wannan wane irin tashin hankali ne, har sai yaushe za ki
daina d'aga mana hankali a gidanan...?
Cewar Zee-zee tana girgiza kafand'u Teema.
Cikin muryar kuka Teema ta ce har sai lokaci da momma ta bud'e bakinta
tafad'awa duniya wacece ni, da kuma irin rayuwar da ta za6a min anan gaba.
Ta k'arashe magana had'e da ture su ta 6alla da gudu ta shige d'aki ta rufo k'ofa
har da su murza key.
"Cirko-cirko suka yi tare da kallon-kallon atsakaninsu, su Kalle momma ta
Kallesu Meena ce ta kawo k'arshen shiru nasu ta hanyar cewa momma me kuma kika sake
yi ma Teema?"
"Saida momma tayi ajiyar zuciya kafin ta ce "Ba abinda nayi mata matsiyata
iskokanta ne suka motsa, amma ni me zan mata.
"Wannan karo Zee-zee ce tayi magana kwata-kwata ban yarda da wannan al'amarin
naki ba momma, a koda yaushe iskokan Teema suka tashi duk yawan mutane gidanan ba
su tsinewa kowa sai ke, yau kuma da kunnena naji Teema tana miki Allah ya isa
kai.....ina momma wannan lamarin naki akwai lauje cikin nad'i Zee-zee ta k'arashe
magana tana girgiza kanta.
"Momma batasan abinda zata ce da su ba, gaba d'aya noti kanta ya kwance shiyasa
ta bi ta gefensu ta shige bedroom d'inta
***---***---****----**
Jirgin da Daddy ya biyo daga Lagos zuwa Abuja ya yi landing a Nnamdi Azikiwe
international airport Abuja, Daddy yana fitowa daga jirgi ya kira direbanshi ya zo
ya yi picking d'inshi suna cikin tafiya bisa hanyar zuwa gida message ya shigo
wayarshi sai kawai ya tsince kanshi da fad'uwar gaba, ya bud'e sak'on yayin da
gabanshi ke cigaba da fad'uwa *_idan har kanaso kasan wacece matarka Zaituna Ka yi
gaggawa ka zo western dreams hotel room 126_*
Rass....rasss....! Sautin da ke fita daga k'irjin Daddy zuciyarshi sai halbawa take
da k'arfin gaske, ya bud'e baki da kyar ya ce da direbanshi ya wuce da shi western
dreams hotel.
Jeeddah Aliyu.
[7/27, 12:25 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*38*
Barrister A tayi wanka ta shirya ta nemi wuri ta zauna tana jiran barrister z ta
kirata, ta ce sun iso tazo tayi picking d'insu har k'arfe 12 noon ya yi bata ji
daga gareta ba.
Ta kira wayarta yafi a kirga sai kawai taji matar nan mai zazzak'ar murya tana
fad'in wayar a kashe take.
"Da sauri ta mik'e tsaye tafito compound ta yafito Daniel da hannu ta tambayeshi
ina Sa'eed ya ce mata tun jiya yalla6ai Aliyu ya aike shi poultry house d'inshi da
ke suleja ya kai ma manager sak'o, jiya bai samu zuwa ba shiyasa yau ya tafi tun da
sassafe amma shima ya yi mamaki abinda ya hanashi dawowa har yanzu.
Sai kawai ta tsince kanta da fad'uwar gaba mai tsanani, da sauri ta juya flat
d'inta babban takaicinta bai wuce contact d'in Jamal da bata da shi ba.
Gani zata 6atawa kanta lokaci da fargaba yasa ta haura sama ta dauko handbag da
makullin mota, har tayi reverse ta fita daga gidan tana jin fad'uwar gaba kaitsaye
gidan Jamal ta nufa.
***---****----****--***
Direban Daddy yana danno mota a western dreams hotel.
Daddy ya jin fad'uwar gabanshi ya k'aru fiyye da farko, direban ya yi parking ya
fito ya bud'ewa Daddy k'ofa yayin da Daddy bai ma san sun iso hotel d'in balle
yasan direban nashi yana bude masa k'ofa.
Gani shiru nashi ya yi yawa yasa direban ya d'an sunkuya had'e da tura kanshi cikin
motar kana ya ce "Alhaji mun iso!
Firgigit......! Daddy ya yi kaman wanda aka tadda daga bacci ta hanyar watsa masa
ruwa musu masifar sanyi.
Cikin mutuwar jiki Daddy ya zuro k'afafunshi k'asa kafin ya yunk'ura ya fito da
gangar jikinshi waje.
"Batare da Daddy ya kalle direbanshi ba ya ce "Ka zauna a mota ka jirani ina
zuwa.
Yanda yake tafiya kawai zai tabbatar maka da baya cikin natsuwarsa, yana zuwa
bak'in k'ofar d'akin ya taka birki almost 3 minutes yana tsaye shi bai yi knocking
bai kuma juya inda yafito ba.
Can ya ga wankin hula zai kaishi dare ya yi kasada ya daura hannunshi, a jikin
k'ofar ya shiga knocking ahankali.
Jarumi da ke haye da ruwan cikin momma ya dakata da abinda yake yi, ya tsurawa
k'ofar idanu, yayin da Daddy bai fasa knocking d'in ba.
"Cikin tsanani gajiya Jarumi ya mirgina gefe ya kwanta yana sauke numfashi,
batare da ya kalle gefen da momma take ba ya ce "Zaituna ina gani room service ne
ya kawo abincin ki tashi ki kar6o.
Batare da ta furta uffan ba ta mik'e da kyar saboda ta gurzu a wurinsa ba k'adan
tsirara haihuwar uwarta ta mik'e, ta dauki bathrobe tasaka ta nufi k'ofa wacce har
zuwa lokaci Daddy yana cigaba da knocking d'in hankalinta a kwance tayi unlock d'in
k'ofar saboda sam bata kawo tunani yau ce ranar da zata kasance ranar tonuwar
asirinta ba, tana bud'e k'ofa idanuwanta suka sark'e da na Daddy wanda ke tsaye sai
faman tattara babbar rigarsa yake, ga kuma matsananci fad'uwa gaba da yasaka shi
agaba, saura kirisss.....numfashin Momma ya fita daga gangar jikinta yayin da duhu
ya mamaye gani Daddy kwakwalwarsa ta daina aiki ta tsaya cak.....tsananin rud'ewa
da tashin hankali marar misaltuwa ya sanya momma ja da baya, muryarta na rawa da
kyar ta had'a ruguwar jarumta da ya rage mata ta shiga had'a kalma da kalma tasha
bak'ar wahala kafin tasamu ta had'a. kalmar Al....ha..ji...!
Jarumi da ke kwance daga shi sai boxer saboda bayan tanufi k'ofa yasaka boxer d'in,
dalili kuwa yasan dole room service d'in ya shigo don haka bai kamata ya ganshi
naked ba.
"Cikin wani irin yana yi Daddy ya bi bayanta yayin da idanuwanshi suka sauka
akan Jarumi, cikin tashin hankali yake kallonshi gani haka yasa Jarumi ya mik'e
zubur.....da zumar ya ture Daddy ya gudu, cikin zafin nama Daddy ya cafke dantse
hannunshi ya kuma fizgo shi da k'arfi har ya yi nasarar tureshi bisa gado, Momma
wacce ke gefe tsaye ta kurma mashahuri ihu sakamako yanda taga Daddy yana dambe
cirewa Jarumi masks, kururuwa take yi da dukan k'arfinta shiru nata ya tsaya ne
cak....adai-dai lokaci da Daddy ya yi nasarar yaye face masks d'in, fad'uwar
gabanta ya k'aru a dalilin fuskar da take kallo wacce tsawon rayuwarta bata ta6a
koda mafalkinta ba, kafin tayi yunk'uri tambayarshi waye shi ya akayi ya rikid'e ya
zama Jarumi?"
Shin ko Jarumi yana canza launi ne ko kuma yana da sihiri da yake canza kamanu,
idan kuwa haka ne tabbas ya cuceta me zata cewa Daddy ta tabbata koda zata mutu
tasake dawowa duniya ta cewa Daddy abokin fasik'ancinta d'an uwanshi ne Suraj Ardo
ba zai ta6a yarda ba.
Daddy yana cire masa face masks ya koma gefe yana kallonsa da idanuwanshi da sukai
jajir, yayin da numfashinsa ya shiga daukewa yana dawowa ya misalta shekarun abokin
fasik'ancin momma wanda ko d'anta Aliyu ya girmeshi nesa ba kusa ba, saidai ya zo
tsaran Meena ba ma Zee-zee ba.
"Cikin mugun tashin hankali momma ta nufi wajen duplicate d'in Jarumi, kafin ta
aika masa tambayar da ke nuk'urk'usar zuciya da kwakwalwarta kafin tayi wani
yunk'uri 'yan Median suka bankad'o k'ofa suka cika d'akin kowane su yana k'ok'arin
daukar abinda zai watsawa duniya.
"Gani haka yasa Daddy ya k'ara firgita, numfashinsa ya tsaya cak....ya sulele
k'asa ya some.
Momma tafasa ihu tayi kanshi tana jijjiga shi yayin da press sai ya k'ara cika
d'akin suke, kamar turo su ake yi yayin da wasu nan take suka watsa akan social
Median, asirin uwargida M Ardo ya tonu an kamata tana fasik'anci da d'an cikinta,
wasu maganganu ba dad'i ji.
Yanda momma taga flash d'in camera yana shawagi ta ko ina akanta, yasa tayi suman
k'arya.
Ma'aikatan hotel d'in ne suka kira ambulance aka turo Daddy da momma akan gadon
daukar marar lafiya, sai lokaci direban Daddy yaga abinda ke faruwa.
Alokaci da ake k'ok'arin fitowa da Daddy da momma duplicate d'in Jarumi ya sami
hanyar guduwa.
Kaitsaye national hospital akai nufa da su har a can....basu tsira daga Median ba
saboda biye suke da su har lokaci da aka shigarda su d'akin taimakon gaggawa.
"Bayan kowa ya kama gabansa manager hotel d'in ya tsinto kayan momma ya rufe
d'akin.
Jin kad'an da fitarshi Jarumi uncle suraj ya fito daga ma6oyarsa bathroom, ya dinga
kwasa dariya kaman wani motsatsi.
Saida ya yi mai isarsa ya nufi k'ofar fita ya ciro key daga aljihunshi ya bud'e
y k'ofa, ya lek'a ya ga babu kowa a corridor ya fito abinsa zuciyarshi fara
tass....yau burinsa na daukar fansa akan d'an uwansa M Ardo ya cika dama burinsa ya
6ata masa reputation shi da iyalinsa.
"Lokaci da barrister A ta iso k'ofar gidan Jamal tayi horn batare da mai gadi
ya bud'e gate ba, ya fito gefen goshinsa sanye da plaster ya gaidata tare da sanar
da ita mutane gidan duka suna asibiti.
"Sosai tasake shiga firgici cikin tsoro da fargaba ta ce "waye ba lafiya a
gidan?"
Mai gidan da iyalinsa jiya daddare armed robbers suka shigo mana gida kalli
goshina, dukan bindiga ne suka yi wa maigida dukan tsiya suka yi awon gaba da
bak'in da suka zo jiya gidanan.
Barrister A ta dafe saitin zuciyarta da ke hal6awa da k'arfi kana ta shiga furta
"Innalillahi wa'inna illaihim raji'um.....!
Da kyar ta iya tambayarsa wane asibiti Jamal yake, sannan an sanar da Jami'an
tsaro.
Ehh.....an sanar da su ko d'azu sun zo sun sake bincike da yi min tambayoyi shi
kuma maigidan yana Nimzamia hospital.
"Cikin mugun tashin hankali ta tashi motarta, da zumar zuwa asibitin da Jamal
yake kiran Abbata ya shigo wayarta kaman ba zata dauka ba, sai kuma tayi tunani
tana buk'atar wanda zata yi magana da shi.
Tana picking ko gaisuwarta Abba bai tsaya amsawa ba ya ce "Minal wai meke faruwa ne
a family mijinki?"
saura kad'an tasaki steering mota, muryarta tana rawa ta ce "Abba wani ya sanar
da kai wani abu ya faru ne?"
Ba wanda ya sanarda ni gashinan yana yawo a kafaffen yad'a labarai da kafaffen sada
zumunta, abin ba kyau gani.
"Abba ni bansan komai ba wallahi.
Cike da takaici Abba ya ce "mother in law d'inki mijinta M Ardo ya kamata a waster
dream hotel she's having an affair abin takaici da k'aramin yaro, kuma wani kayan
haushi Median ta shigo cikin al'amari
sai yad'awa suke yi.
Kiyi gaggawa ki had'a kayanki ki zo Yola banaso press su yi wani rubutu akanki
matsayinki na daughter in law a gidan zai iya shafar career ki.
Idan babu flight ki nisanta daga gidan ki 6oye kanki zuwa gobe ki biyo jirgin
safe.
Girgiza kai tayi har ta bud'e baki za tayi magana sai ta laura ga mirror mota da
wani black van tun daga fitowarta gidan Jamal yake biye da ita, tunaninta ya bata
watakila hanya d'aya zasu bi kuma gashi ta tare musu hanya saboda sannu-sannu take
driving, gani haka sai ta d'an k'ara gudu sai kawai mai motar ya dinga yi mata wani
mahukacin horn.
Kawai tayi decided ta gangara gefen hanya tayi parking saboda zata fi samun natsuwa
ta fahimtarda Abba ya fahimci ita ma a yanzu tana d'aya daga cikin alhalin duk
abinda ya shafe su, ya shafata ko ta gudu ko ta tsaya ba abinda zai canza hakan.
Tana gama parking sai kawai van d'in ta zo da matsiyacin gudu, tasha gaban motarta
cikin tsananin tsoro ta ce "Abba ga wata black van tasha gaban mo.....
Kafin tak'arasa wasu mutane guda biyu suka fito daga van d'in d'aya daga cikinsu ya
d'aki glass d'in motarta ya tarwatsi da sauri ta duk'e gudu kada glass d'in yayi
mata rauni a fuska, da k'arfi ya fincikota daga cikin mota ya fito da ita waje sai
ihu take, ta wayarta da tafad'i Abba yake jiyo ihunta tana neman taimako, d'ayan ya
duk'a ya dauki wayarta ta ya yi switch off d'inta tare da jefawa aljihun black
lather jacket d'in jikinsa, tana ji tana gani suka jefata cikin motar tare da saka
mata blindfold suka kuma rufe mata baki da salatif, ba ka ji komai sai gurnaninta
doguwar tafiya suka yi saida suka fita garin Abuja k'auyen madallah suka nufa sai
da suka yi tafiya mai nisa kafin su nufi wani poultry house suka yi horn mai gadi
ya bud'e musu gate, bayan su yi parking d'ayan daga cikinsu ya sa6o barrister A a
kafad'arsa suka shiga da ita wani flat.
*****---****-----*****
Jamal da ke kwance akan gadon asibiti saboda yaran, Jarumi sun yi masa shegen duka
har da rauni aka matarsa Zulaiha ta shiga shafinta na Facebook sai kawai taci karo
da sabon labari, cikin mugun tsoro ta mik'awa Jamal wayarta. sosai shima ya firgita
da ganin labarin jikinsa yana rawa ya mik'e daga kan gado ya cire rigar asibiti
Zulaiha ta taimaka masa ya saka jallabiya, hannunta ya riko had'e da daukar handbag
d'inta wacce yake da tabbacin makullin motarta yana ciki, parking space suka nufa
ya mik'a mata handbag d'inta tare da cewa Zulaiha yi sauri ki ja mota mu tafi.
Ina za muje Jamal kai da baka lafiya?"
Nace ki ja mota mu tafi banso silly questions.
Yanda ya k'arashe magana cikin tsawa yasa babu gardama ta ja mota suka fice daga
Nimzamia hospital.
***--*----***-----*---***
*LAGOS NIGERIA*
Tun safe Aliyu yake conference hall yana meeting saboda wani contract na gina
manya-manya tituna da hanyoyin ruwa da kamfaninsu na contractual & building
material company wanda kowane kamfani irin nasu yake sa ran ya samu project d'in,
daga k'arshe kamfanin su Aliyu ne ya yi nasarar samun contract d'in.
"Saboda haka cike da farin ciki Aliyu ya fito daga conference hall direbanshi
ya bud'e masa mota ya shiga, sai lokaci ya yi switch on d'in phones dinshi da zumar
ya gira rabin ransa.
Da safe kafin ya shiga meeting da suka yi waya bai sake waya da ita ba gashi yanzu
har 1:27pm, ya yi dialling digit d'inta saidai wayarta ta a kashe kafin ya yi
yunk'urin kiran d'ayan layinta call d'in k'anwarsa Zee-zee ya shigo wayarsa, ya yi
picking tare da kara wayar a kunnenshi cikin matsanancin kuka Zee-zee ta ce "Don
Allah Ya Sultan duk inda kake duk abinda kake yi ka jinginar ka zo Abj muna cikin
tashin hankali wanda ba za mu iya jure shi mu kadai ba, muna buk'atar taimakonka.
Ya lumshe idanuwanshi tare da fad'uwar gaba mai tsanani ya ce Zainab waye ya
rasu?"
Ya Sultan ba wanda ya rasu amma wallahi gara ace rasuwa ce aka yi da wannan
iftila'i da ya fad'awa zuri'armu. Yaya Daddy ne ya kama momma a hotel tare da
k'aramin yaro wanda a shekaru ba zai wuce age mate din Meena ba they're having an
affair kuma gaba d'aya duniya ta dauka bansan ya aka yi median tasan abinda yake
faruwa a hotel din ba yanzu haka sai yad'awa ake yi musanmman a social median
saboda Abba Yusuf, ya biya wasu daga gidanje rediyo da talevision da su daina
yad'awa shiyasa abin ya yi sauk'i a kaffafen yad'a labarai
ta k'arashe magana tare da rushewa da wani sabon kuka har tana shed'ewa.
Innalillahi wa'inna illaihim raji'um!
Aliyu ya shiga maimaitawa har wani duhu-duhu yake gani da yana da d'abi'ar saurin
kuka da yau ba abinda zai hana shi rushewa da kuka, cikin wani yana yi na k'onar
zuci ya ce "Zainab ki daina kuka saboda ba abinda zai canza faruwar wannan
al'amari, ba'a fata sai ma ya haifar miki da wata matsala muyi hak'uri mu kuma
doshe kunneyenmu mu dauki wannan al'amari a matsayin k'addararmu, ke ce babba ki
rarrashi k'anneki kafin na zo kinji?"
"To Yaya tafad'a tare da share hawaye.
Ina Amina in tana kusa da ke ki bata waya nayi magana da ita.
Yaya batanan tun lokaci da al'amari ya faru na shiga apartment d'inta, masu aikinta
suka ce tafita kuma har yanzu bata dawo ba, duk da muna hospital na bar ma Daniel
sak'o idan tadawo ya sanar da ita muna asibiti.
"Shikenan Zainab ki kula da Daddy kafin na zo ki kuma kira uncle Suraj ki
sanar da shi abinda ya faru, ya sameki a hospital ba za ki iya hidimar asibiti ke
kadai ba.
"Yaya na kira shi yafi a kirga wayarshi switch off.
Aliyu ya dafe goshinsa damuwarsa ta k'ara k'aruwa.
"Ba damuwa ki cigaba da zama wajen Daddy ita kuma Meena da Fateema su zauna wajen
momma kafin in iso.
To....Yaya ta k'arashe magana had'e da hanging up.
Aliyu ya kira number wani friend dinshi da ke aiki a Airport ya ji ko akwai jirgin
da zai tafi Abj da rana, cikin sa'a ya ce akwai 2:30pm zai tashi ya ce ya siya
mishi ticket gashinan zuwa a cikin Airport din ya samu ya yi sallar azhar, yana
gama sallah saida ya sake gwada kiran number barrister still tana rufe hakan ya
k'ara jefa shi a damuwa saboda yasan bata da hearing a court, da kanta ta sanar da
shi lokaci da ya kira ta da safe ta ce yau tana gida ba zata fita ba.
"Oh.....ya rabbi ka taimake ni kasa ita ma ba wani mummunan abu ne ya sameta
ba.
har ya shiga jirgi bai fasa tunani da zance zuci ba yana cikin tunane-tunane
jirginsu ya d'aga.
***----**----***----**
Jarumi uncle Suraj yana hakince akan royal chair wacce ta k'awata masa falonsa, da
ke poultry house d'inshi ya yi crossing legs dinshi jikinshi sanye da farar shadda
hannunshi na dama rik'e da pistol yaranshi suka shigo d'aya sabe da barrister A a
kafad'arsa, ya direta gaban Jarumi tare da furta "mai girma Jarumi mun cika aiki.
Da pistol d'in hannunshi ya yi masa ishara da ya ja baya, ya tsare barrister A da
shegu idanuwansa kafin ya saki wani shegiyar murmushi ta gefen baki.
Ya kalli d'aya daga cikin yaransa ya yi masa alama da ya cire mata salatif d'in
bakinta, nan take ya cika aiki tana jin an bud'e mata bakinta ta dagargaje iya
k'arfinta ta kurma ihu wayyyo........don Allah ataimake ni wasu la'ananun Allah sun
satoni wayyo Allah....ataimakeni.
"Jarumi ya mik'e daga mazauninsa ya nufi wurinta ya shiga zagayata, jikinta ya bata
akwai mutum a kusa da ita ta juya da k'arfi ta shiga ja da baya tana kuma kici-kici
kwance igiyar da suka daure mata hannaye, tuntube tayi da center table tayi baya za
ta fad'a kanshi cikin sauri Jarumi ya rik'o hannunta ya daura bakinsa dai-dai
k'ofar kunnenta ya ce "welcome to my palace sarauniyata.
"Un.....cle....sur..raj!
Tafad'a cikin rawar murya. "Yesss.....sweetheart ashe