Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gidan Rina Complete Hausa Novel by Jidda Aliyu

Author :  Jidda Aliyu Category :  Drama

Chapter   4 / 26

9K to 12K   out of 76.6K words

fuska tayi kamar za tayi kuka ta zuro k'afafunta k'asa farare tass....da
su, tayi mik'a gani hakan yasa Ummi ta nufi k'ofar fita tana mai k'ara jadadda mata
tafito yanzu nan.
"Ummi na ficewa tasake komawa ta kwanta zuciyarta cike da tunani tafara
described d'in Aliyu, gajere ne bak'i mai k'ato ciki hancinshi chan sama, da sauri
ta tashi zaune tana zaro idanu daga bisani ta girgiza kanta dogon bak'in gashinta
ya warwatsu akan gadon bayanta, hannunta tasaka ta tattare shi ta dauko d'an
k'aramin band k'ark'ashin pillow ta daure gashin, murmushi tayi had'e da d'an dukan
k'eyarta.
"Akaro na biyu tasake zuro k'afafuwanta k'asa ta sauko daga bisan gado 'yar
yaloluwar rigar barcinta light pink a bayana, bathroom ta wuce ta bata dauki dogon
lokaci ba tafito daure da towel hannunta rik'e da rigar da tacire ta jefata cikin
laundry basket.
"Agauggauce ta shafa mai had'e da zura fitted gown na shaking material, bata
daura d'an kwali ba sai tasaka hula irin na yadin hijab ta fice.
kaitsaye kitchen ta wuce Asabe ta samu tana had'a plate da spoons d'in da za'a yi
breakfast.
"Ina kwana lauya?"
cewar Asabe har da d'an runsunawa.
Lafiya qalau Asabe...antashi lafiya?"
Lafiya qalau lauya.
Asabe Yau zan yi bak'o me kike gani za'a shirya masa wanda ya kamata?"
"Cikin murmushi Asabe ta ce Minal kenan ya za'a yi nasan abinda yake so amma me
kike tunanin ya kamata ayi masa, shi kadai ne ko suna da yawa?"
Ta6e baki Minal tayi kafin ta ce wannan ne ban sani ba, kawai mu shirya abinda ya
kamata.
Bari nafara fiddo kaji a freezer kafin ki k'arasa naki aiki.
Ta juya tanufi wajen freezer yayin da Asabe ta cigaba da aikinta.
***----****---****
*ABUJA*
*11:24am*

Aliyu yafito cikin shirinsa cikin farare kaya as usual, farar shadda gezner tana
walkiya da daukar ido takalmin k'afarshi cover ne suma farare, yayin da ya lullu6e
kwayar idonsa da farin eyes glass wanda ake iya hango brown eye balls d'inshi,
Jikinshi na fitarda fitinane k'amshi.
kaitsaye falon momma ya wuce gani bata falon yasa ya nufi bedroom d'inta, ya tura
k'ofa ya shiga tana zaune gefen gado sanye da cotton night gown, tana waya ganinshi
yasa ta katse waya tana wuk'i-wuk'i da idanu kamar marar gaskiya.
"Da murmushi akan fuskarshi ya zauna kusa da ita ya aza kanshi akan shoulder
ta, cikin shagwa6a ya ce momma na fito ki yi min addu'a.
Ya motsa fuska ta yi kafin ta ce Allah ya kiyayye hanya, yasa yarinyar tayi maka.
"Kai momma wannan addu'a duk ni kadai?"
"Eh mana yaron momma ko tayi kad'an ne na k'ara ma da wata?
A'a....momma ta yi ta farkon zan amsa miki da Amin.
Ta biyu ce ba zan amsa ba.
"Dad'i ne ya lullu6e momma tasaki dariya har Aliyu yafice daga bathroom din tana
dariya.
"Sitting room d'in Daddy ya nufa Daddy na zaune da newspaper a hannunshi yana
dubawa, shigowa Aliyu yasa ya ajiye newspaper d'in ya tattara hankalinshi akan
Aliyu.
"Ina kwana Daddy?"
Cewar Aliyu yana mai runsunawa.
"Lafiya qalau Sultan hope shirin tafiya Yola ne.
yana magana yana nuna kayan jiki Aliyu da yatsanshi.
"Eh.....Daddy sallama na zo nayi maka.
Madallah.....Allah ya kai ku lafiya, ka kuma kiyayye banaso a sami matsala daga
gareka ka ji ko?"
"Na ji Daddy insha Allahu zan kiyayye.
Shikenan je ki Allah ya tsare.
Amin....Daddy.
Daga haka yafice direbanshi Isah yana zaune a mota yana jiran fitowarshi, kafin
Isah ya bude masa k'ofar mota har ya budewa kanshi, ya zauna a back sit Isah ya ja
mota maigadi ya bude musu gate, Zone 2 suka wuce suka dauki Jamal sannan suka dauki
hanyar Nnamdi Azikwe Airport, bata dauki dogon lokaci ba Jirgi yad'aga.
*****-----*****-----****
*YOLA*

Barrister Amina tafito daga wanka daura da towel iya cinyarta, ta nufi wurin mirror
ta dauko hand dryer ta jonata a socket ta shiga busar da dogon bak'in gashinta.
"Bayan gashin ya bushe tashiga shafe shi da mayuka gashi kala dabam-dabam katon
band tasaka ta daure gashin.
Kafin tafara shafe lallausar fatar jikinta da body lotion yayin da skin d'inta sai
glowing yake.
Simple makeup ta yi ta bude closet dinta ta fito da Arabian gown royal blue in
colour, mai adon stones sai walki'ya da daukar ido suke.
"Bayan tasaka inner wears ta zura rigar d'an k'aramin red veil ta yi rulling da
shi, perfumes na Amani da Azaan ta mulke rigar da shi nan take ta dauki wani
mushiriki k'amshi, ta yi tsaye agaban mirror looking herself don gani yadda ta yi
kyau yasa tasaki sanyaye murmushi ba yabon kai ba duk d'a namiji mai
ingantattaciyar lafiya ya yi arbani dole ya so ni.
"Barrister Amina tafada a k'asan zuciyarta, kai ta girgiza cike da nishadi ta
dauki d'aya daga cikin Shoe dinta da ke jere akan shoerank tasaka ahankali tanemi
gefen gadon ta zauna, phone d'inta ta dauko ta yi calling Barrister ladan a vidoes
call Barrister ladan tana yi picking tasoma yi mata tsiya gani yadda ta yi kyau
yayinda Amina sai sakin murmushi take, daga bisani Barrister Ladan tashiga bata
good advised, turo k'ofar da aka yi yasa Barrister Amina juyawa Rahma ce tashigo ta
ce Ya Minal Ummi ta ce ki fito bak'i sun iso.
"Ras....ras...sauti da ke fita daga k'irjin Barrister Amina kenan har batasan
time d'in da ta dafe chest d'inta da hannunta ba.
Da kyar ta hadiye yawu ta ce je ki ki ce ganinan fitowa.
Rahma ta fice barristers Ladan ta ce tashi ki tafi bebs kinsan wani bayaso jira
idan sun tafi za mu yi waya, batare da Barrister Amina ta yi magana ba ta katse
kiran ta mike tafice daga d'akin

Jeeddah Aliyu
[7/26, 11:46 PM] Jiddah Aliyu: *HASKE WRITERS ASSO.*πŸ’‘πŸ’‘

*DA D'UMID'UMINSU...Daga Alk'aluma shida*

_INA MASOYA? YAU GA RANARKU...._

_DADINA DA GOBE SAURIN ZUWA, TABBAS INKAJI KIRA SAMU NE SANNAN IDAN KAJI WANE TO BA
BANZA BA,HAKANNE MA YASA SHAHARARRIYAR KUNGIYAR NAN TAKU MAI FARIN JINI MAIYI
DOMINKU DOMIN FARANTA ZUK'ATANKU TASAKE ZUWAR MUKU DA MASU D'UMI KUMA HASKAKKUN
LITTATTAFAI GUDA SHIDA RERAS WADANDA TAYIWA LAKABI DA,DA D'UMI D'UMINSU DAGA
ALK'ALUMA SHIDA GARABASA....ME KUKE JIRA? MAZA KU GARZAYA KU NEMI NAKU TUNDA
DUMINSU DOMIN FASIHAI HAZIKAI SANNAN MASU NAZARI KAFIN SU RUBUTA SUNE SUKA HADA
KARFI DA KARFE DOMIN NISHANTAR DAKU,MASHA ALLAH RIGIJI GABJI DAGA JI KASAN AKWAI
MAGANA, MARUBUTAN DA ZASU NISHANTAR DAKU SUN HADAR DAπŸ‘‡πŸ»_

*JIDDAH ALIYU*πŸ‘‰πŸ» _GIDAN RINA_!

_DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR_ *NIDA YAYA HABEEB* _DA_ *SONKI NE SANADI*

*A'ISHA DANSABO*πŸ‘‰πŸ» _BURIN ZUCIYA_!!

_DAGA SHAHARARRIYAR_ _MARUBUCIYAR_ *LAIFIN BOYE* _DA_ *HURAYYAH*

*KHADIJA AHMAD KDEEY*πŸ‘‰πŸ» _DA CIWO A ZUCIYATA!!_

_DAGA SHARARRIYAR_ _MARUBUCIYAR_ *Y'AR* *BABBAN GIDA* DA *ABU IRFAN*

*RAHMA MUH'MD RUFA'I NALELE*πŸ‘‰πŸ» _RAYUWATA_!

_DAGA SHAHARARRIYAR_ _MARUBUCIYAR_ _LITTAFIN_ *LIKITAN ZUCIYA* _DA_ *SAMARIN
BANA*

*SLIMZY*πŸ‘‰πŸ» _IZZA TA!!_

_DAGA SHARARRIYAR_ _MARUBUCIYAR_ _LITTAFIN_ *ANYI WALKIYA* DA *TAK'ADDAMA* _WANDA
YAKE ZUWA MUKU A KYAUTAπŸ‘ŒπŸΌ_
*SAFIYYA GALADANCHI* πŸ‘‰πŸ»_TANA K'ASA TANA DABO!!!_

_DAGA SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR_ _LITTAFIN_ *RUBUTACCIYAR KADDARA* _WANDA_ _YAKE
ZUWA MUKU YANZUN HAKA A_ _KYAUTA... πŸ‘ŒπŸΌ_

*_WANNAN SHI AKE KIRA DA INBAKAYI BAN WURI,KUMA DADIN DADAWA ZAKU SAMU WADANNAN
KAYATATTUN LABARAN AKAN FARASHI MAI SAUKI DAIDAI DA ALJIHUNKU KUDAI KAR KU BARI
ABAKU LABARI,GANI YA KORI JI,HASKE MAGANIN DUHU,RUBUTUN MU YA BANBANTA DA SAURAN._*
*ZASU FARA ZUWA MUKU RANAR SALLAH DA KWANA UKU, MUN KAI SHI HAKA NE SABODA AZUMI
LOKACIN JAJURCEWA GA IBADA, GA DUK ME BUQATA ZAI IYA BIYA YANZU, SAIDAI LOKACI NA
ZUWA KAWAI YAGA ABINSA, IDAN KO SAI SALLAR NE MA DUK D'AYA MUDAI MUNA MARABA DA
MASOYAN MUH*

*DAN HAKA GAME BUKATAR SIYAN WAD'ANNAN KAYATATTUN LITTATTAFAI WADANDA MUKA YIMUSU
LAKABI DA D'UMID'UMINSU SHIDA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL 500 MAISON GUDA DAYA ZE
BIYA 200, ME SON 2 ZE BIYA 300 MESON UKU ZE BIYA 350 MESON HUDU 400 MESON BIYAR 450
ME BUK'ATAR DUKA KUMA ZE BIYA 500 KAMAR YANDA MUKA FADA A SAMA. kU TUNTUBEMU KAMAR
HAKA*πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»

_FIRST BANK_
3120641551
_SAFIYA MUSA GALADANCI_
_SHEDAR TURA KUDINKA GA WANAN NUMBER_ πŸ‘‰πŸ»08103943903

πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»
_ZENITH BANK_
2255398727
_AMINA JIBRIL_
_SHAIDAR BIYANKA GA WANAN NUMBER_ πŸ‘‰πŸ»08166177830

_IDAN KUMA KATI NE SHIMA ZAKI IYA TURAWA WANAN NUMBER KATIN MTN GA NUMBER KAMAR_
_HAKA:_ 08039424298 SHEDAR BIYAN KATINKA GA 07084161619


Jeeddah Aliyu

*7*


Lokaci da Jirgin su Aliyu ya yi landing uncle Suraj ne ya dauko su daga Airport,
akan hanyarsu ta zuwa gidan uncle suke tattauna zance business da yake uncle Suraj
shi yake handled din business d'insu na Yola.
Gidan uncle suka fara yadda zango bayan sun huta suka ci abinci had'e da sallar
azhr, sannan uncle ya had'a su da direbanshi yakai su gidan Alhaji Abdullah Barkido
Misali k'arfe 2:52pm direban da ya dauko Aliyu da Jamal ya Parker mota cikin gidan
Abdullah Barkido, Khalid ne yafito ya tarbe su had'e da yi musu jagaro zuwa falon
bak'i.
"Jamal ne yafara zaunawa yayin da Khalid ya fice.
Ahankali Aliyu yake nazarin falon kafin ya zauna yana shak'ar Air freshener & odour
neutralizer din da aka sanyawa, falon sosai ya yi masa dad'i sanyayyar ajiyar
zuciya ya yi, sannan ya d'an sosa gefen kuncinshi da yatsanshi, zuciyarshi ta afka
tunanin saboda bai san yadda zai ga yarinyar ba, ko yaya kamanunta suke bashi da
mafita dole ya aureta domin ya farantawa Daddy rai.
'Tunaninshi ya katse sakamakon sallamar da ta bugi dodon kunnenshi, alokaci d'aya
shi da Jamal suka dubi k'ofa Asabe mai aiki ce tare da Rahma suka shigo dauke da
kayan abinci, had'e da drinks Jamal ne ya amsa musu sallama, sai da suka ajiye
kayan sannan suka gaida su nan ma Jamal ne amsa saboda Aliyu bakinshi ne kadai ya
motsa ko Jamal da ke zaune kusa da shi ba lalle bane ya ji abinda ya ce ba.
"Bayan Asabe ta bar falon Rahma ta ja tai tsaye tana kallonsu, Jamal ya ce Baby
ya sunanki?"
kusa da shi ta nufa da yake Rahma akwai d'an banza surutu kamar parrot ta ce sunana
Rahma Abdallah Barkido, kaine za ka aure Ya Minal ko wannan da baya magana?"
Takarasa magana had'e da nuna Aliyu da baki.
"Aliyu ya d'ago fuskarshi dauke da lallausan murmushi, da yake sosai maganar
Rahma ta bashi dariya shiyasa ya murmusa, Jamal ya yi 'yar dariya ya ce bani bane
wannan ne ya nuna Aliyu da yatsa.
"hannunta Aliyu ya rik'o yana murmushi ya ce Rahma yakike ya karatu?"
Lafiya qalau....kaine za ka dauke mana Ya Minal?"
"Gyad'a mata kanshi ya yi yana cool smile ko ba za ki barni na dauke ta ba?"
Turo baki ta yi kafin ta ce zan bar ka saboda kana da kyau amma duk da haka saidai
katafi da mu duka gidanka.
Jamal ya kyalkyale da dariya yayin da Aliyu yak'ara fad'ad'a murmushinsa har kana
iya jiyo sautinsa ya ce na amince Baby Rahma, ya zura hannu cikin pocket dinshi ya
fito da bundle na 'yan five hundred ya mik'a mata gashi Baby Rahma tasha ice cream.
"Girgiza kai ta yi ba zan kar6a ba Ya minal za ta dokeni, haka ranar abokin
aikinta ya zo ya bani kudi na kar6a bayan ya tafi ta zane ni.
"Kwatarda murya Aliyu ya yi ya ce kar6i kawai ba zan barta ta dokeki ba, kinmanta
ni ne zan aureta?"
Washe hak'ora Rahma ta yi tasaka hannu biyu ta kar6i kudi ta yi mishi godiya ta
fice da gudu tana murna.
"Bayan fitar Rahma Jamal ya dubi Aliyu ya ce duk da ak'oshe mu ke amma yakamata mu
ci koda snacks ne da drinks gudu kada su ji babu dad'i.
Uhmm.....Aliyu ya fad'a had'e da daukar samosa guda d'aya ya kuma tsiyaya Juice a
handle glass cup, yana kur6a juice d'in a hankali.
Sautin tafiyar takalminta ne yafara isa musu da sak'on zuwanta, kafin ta tura
k'ofar falon ta shigo k'amshinta ya mamaye k'ofufin hancinsu, cikin sanyayeyar
muryarta mai matukar dad'i da gard'i ta yi sallama.
[7/26, 11:47 PM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU...DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I
NE IDAN KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
08103943903
*SAI KA TURA SHAIDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KI IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYAN KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMIND'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA```
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELE*:-```RAYUWATA```
*SLIMZY*:-```IZZA TA```
*SAFIYA GALADANCHI*:-```TANA K'ASA TANA DABO```


*GIDAN RINA*


*8*



Cikin fara'a Jamal ya amsa mata sallama, sai da ta zauna sannan ta gaida su Jamal
ne yasake amsawa yayin da Aliyu yake k'are mata kallo ta k'asan ido.
Jamal ya gyara zamanshi ya ce sunana Jamaludeen Muhammad, tare muka taso da Aliyu
tun muna yara ko zan iya sanin sunan amaryar ta mu?
Sai da ta yi lallausan murmushi cikin sweetness voice d'inta ta ce sunana Barrister
Amina Abdallah.
Wow! masha Allah ashe amaryar ta mu lawyer ce?"
Uhmm.....tafad'a had'e da sadda kai k'asa.
Da fatar mun samu kar6uwa a wurin Barrister?"
Cewar Jamal yana mai kallonta.
Da kyar ta d'ago saboda kunya kunsan mu fulani da kunya duk wayewar mu da gogewar
mu, za ka sami wasu daga cikinmu da kunya....lol.
Ba k'aramin namijin k'ok'ari ta yi ba ta hanyar furta, insha Allahu daga gareni ba
bu wata matsala fatana anan Allah ya had'a kawunan mu.
Amin summa Amin Barrister.
Jamal ya fad'a cike da jin dad'i maganarta ya mik'e ya kalli gefen da Aliyu yake
zaune ya ce king bari na ba ku wuri ku fahimce juna.
Kafin Aliyu ya yi magana har Jamal ya fice, shiru suka yi na tsawon lokaci yayin da
kowane su da abinda yake sak'awa a zuciyarshi.
"Aliyu ya gyara zamanshi ya tattaro hankalinshi gareta sam bai dauka haka zai ganta
ba, ya yaba da irin shigar da tayi sai yaji ta burge shi, karo na farko a tarihin
rayuwarshi da shigar wata 'ya mace ta burge shi ba ko shakka dole ya rubuta wannan
a diary shi.
"Cikin husky voice d'inshi yayin da fuskarshi ke dauke da murmushi, ya ce
Barrister Amina ya gida?"
Ta cire kai da kyar ta kalle shi wani irin shock ta ji ya jata, a hankali ta bude
baki ta ce "Lafiya qalau, ya hanya da su mommy?"
'Alhamdullah!
Yafad'a yana kallonta suna had'a ido ta yi sauri sadda kai k'asa.
Daddy ya gayamin ke lawyer ce mai zaman kanta, kenan idan mu kayi aure anan za ki
zauna ko za ki bi ni Abuja?"
"Sai da ta yi murmushi kafin ta ce duk Inda ka za6a mana.
Ya fad'ad'a murmushinsa har lokaci idanuwanshi na kanta ya ce, gaskiya na fi zama a
Abuja da Lagos idan ki amince sai mu zauna a Abuja ko ya ki ka gani?"
"Ba laifi hakan ya yi.
Tafad'a Cikin sanyi murya.
Shikenan Allah ya nuna mana lokaci.
"Da kyar ta iya furta Amin.
Daga haka suka yi shiru.
Aliyu ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta dai-dai ita ma ta d'ago ta sace kallon
nashi, karaf....suka had'a ido da sauri ya dauke kanshi, jimm....ta yi tana kallon
gefen fuskarshi yana juyowa ta kauda kanta.
Ya duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunshi sai ya mik'e tsaye yana cewa mu
je ki rakani mu gaisa da Mama.
Ta mik'e tsaye ta wuce gaba yana bin ta, a farfajiyar gidan suka hango Jamal tsaye
yana waya, alama Aliyu ya yi mishi da hannunshi.
"Hakan yasa Jamal ya katse wayar ya kuma nufo su, har Falon Ummi ta shigar da su
ta ce ku zauna bara na kirata bayan ta kira Ummi suka gaisa sannan suka yi mata
sallama har compound ta raka su idan direban uncle ke zaman jiransu.
"Tsaye suka yi suna facing junansu, kafin ya yi magana wayarshi ta yi ringing ya
fito da waya gani momma ce mai kiran nashi yasa ya kalli Amina ya ce please 2
minutes.
Uhmm.....Tafad'a tana mai wasa da zoben hannunta.
Nesa da ita ya yi ya amsa wayar, yana receiving ya kara wayar a kunnenshi
hello....momma!
Ya hanya yaron momma?"
"Alhamdulillah....momma mun iso lafiya har muna shiri wucewa sai ga kiranki.
"Uhmm!
Da fatar yarinyar ta yi maka?"
Murmushi ya yi mai sautin gaske had'e da shafar sumar kanshi, ya ce momma za mu yi
magana idan na dawo gida lokaci yana k'urewa kada mu yi missing flight d'inmu.
"Daga haka ya katse kira saboda yasan halinta sarai sai tasake, watsu masa wata
tambaya.
Daga chan gefe kuma Barrister Amina ta k'ura masa ido tana nazarinsa daga sama har
k'asa, tabbas ya amsa sunanshi cikkake namiji domin ya mallaki komai na cikar
halitta, ta d'an namiji wanda kowace lafiyayyar mace za ta yi burin mallakarshi a
matsayin life partner.
"Ganin ya juyo gareta yasa ta yi gaggawar kauda kanta, ya k'araso daf da ita shi
ma kallonta ya yi sosai sannan ya yi gyaran murya tare da kiran sunanta
Aminaaa......!
Yadda ya ja sunanta yasa tsigar jikinta tashi yarrrr.....
Ta d'ago ta kalleshi ya ce mu za mu wuce saboda yau za mu koma Abuja, gashi ban yo
miki tsarabar komai ba, sai wani lokaci idan Allah yasake had'a mu.
"Murmushi ta yi wanda yak'ara mata kyau ta ce ba komai, nagode da ziyara Allah
yakai ku lafiya, ka gaidamin da su mommy.
"Amin...
Ya furta chan k'asan mak'oshi.
Ta juya wajen Jamal ta ce malam Jamal nagode Allah ya kiyayye hanya ka gaida iyali.
"Mu ke da godiya barrister.
Cewar Jamal.
Daga haka ta juya ta nufi cikin gida.
Yayin da Aliyu da Jamal suka shiga mota direba ya ja aka bude musu gate direct
Airports ya kai su, ko gidan Uncle Suraj ba su koma ba.
****---****----****
*ABUJA*

Momma zaune akan sofa abin duniya ya taro ya yi mata yawa, tun jiya da Aliyu ya
dawo daga Yola har zuwa yau bai bari ta had'u da shi ba.
Yau tun da sassafe ya fice kuma har yanzu yamma lis bai dawo gida ba, ta kira phone
d'inshi yafi a kirga saidai ta ji P.A shi ya dauka ya ce yana meeting.
"Mtss...ta ja tsaki daga bisani ta dauki wayarta ta yi dialling, d'aya daga
cikin contacts d'inta sunanshi ya bayyana akan wayarta, kamar haka Jarumi!"
Wayar ta shiga ringing kamar ba za'a dauka ba saboda saida ta yi kusan tsikewa, ya
yi picking Hello....
Yafad'a ahankali.
"Cikin rawar murya momma ta ce Jarumi akwai gaggarumar matsala da ke shirin
tunk'aro mu, idan har mu ka yi sake ta afku shikenan mafalkinmu ya zo karshe.
"Har ta dasa aya a zance ta Jarumi yana saurareta, huce ya yi ya fesar da iska
mai zafi daga bakinshi, cike da tafarfasar zuciya ya ce duk abinda yake faruwa
nasani kema kuma kin san nasani, yanzu haka ina cikin garin Abuja domin mu nemowa
kanmu mafita.
"Ki zo Ina westerns dreams hotel room 402, saboda wannan magana ba ta waya
bace gudun kada wani ya jiyo ki lokaci da mu ke magana.
Yana gama magana ya katsi kiran.
A gurguje momma ta nufi bedroom d'inta ta shirya key motarta ta dauka had'e da
handbag, ta nufi k'ofar fita kicibuss....ta yi da Tima zaune a k'ofar fita daga
main parlour ta wargaje gashi kanta, ya rufe mata fuska.
"Gaban momma ya fad'i....rass!
Cikin

4 / 26