Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 42

9K to 12K   out of 124.8K words

ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel Win makarantarsu, Osmania University ya"

tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta.

***

Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci

karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ™irgu

ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan.

Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura

layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya ha™ura da shigar ya kama zagayen ™ayataccen ginin yana mai son ganin iya faWinsa. ˜amshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ™arar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas Win wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ™o™arin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaWi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an

"taSa kafaWarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ™asar."

Da sauri ya juya yaga wani Wan dattijo sanye da t-shirt da wando ya Waure ™ugunsa da apron mai

tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana

amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ™iyasin idonsa zai yi sa'an Alhajinsa.

"Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa ""I'm sorry. Sorry. Sorry."""

Hanyar komawa yake nema don tsoronsa Waya kada mutumin ya haWa shi da security a ce me ya kawo

shi nan.

"Murmushi mutumin ya yi ya ce ""hungry?"" Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko."

"""Come inside"" ya umarce shi da yaga yana neman guduwa."

"""Am sorry Sir. Please. I won't come again."" Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ™irjinsa."

Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya ri™e hannun ™ofar da ya biyo ya fito zai koma. BuWewarsa ke da

wuya wani jibgegen mutumi ya tare ™ofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa.

Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za

su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba.

˜uttt ya haWiyi yawu sannan kamar mai taka iska ya bi su ciki. ˜ofar na rufewa gabansa ya sake faWuwa.

"Sai dai duk wannan tsoron ya kau lokaci guda da ya ™arewa kitchen Win kallo na kurkusa. Aiki kowa yake yi da sauri-sauri ga magana ana yi wadda ya fahimci karanto odar masu jiran abince ce ko bada umarni. A gefe guda kana iya ganin wasu suna ta jere plates Win da aka gama haWawa a wani abin turawa za a fita da shi. Ga masu girki sun du™ufa suna yi. Wuta da mai da cokula sai chuu...chauuu su ke. Ganinsa ya ™are akan masu yanke yanke kamar inji. Wasu su na yanka albasa, caras, da ma nau'ikan kayan lambun da bai taSa gani ba. Wani haWaWWen murmushi ya saki sai ga ™aton mutumin ya dawo da tray sha™are da"

kwanukan abinci.

"""Eat."""

"Mutumin tsoro yake bashi amma duk da haka ya faWa masa gaskiya ""Am not hungry."""

"""Taste our food and we talk, okay?"""

Juyawa ya yi yaga dattijon farko ne ya yi magana. Musu ma wuri yake samu. KarSar tray Win ya yi babu

shiri ya zauna a inda aka nuna masa. ˜amshin abincin ya tafi da tunaninsa. Shinkafa ce da kaza. Ga kuma

"wani haWin albasa, cucumber da tumatir da wani ganye mai tsami tsami da daWi kamar kunne zai fita. Wani Wan kwano mai zurfi a gefe kuma miyar naman sa ne wanda ya dahu ya yi luguf. Sai wani abu kamar bread ko gurasa mai faWi. Abu Waya ya kula shi ne babu cokali. Ya Waga kai ya tambaya dattijon"

nan shi kuwa ya ce masa.

"""We eat with our hands here."""

Taj ya gyaWa kai ya mi™e yace zai wanke hannu. Sink ya nuna masa ya wanko ya dawo. Yana zama ya yi

"Bismillah ya fara ci. Miyar ya Wauka zai zuba a shinkafar da wani Sangaren nata ya yi jaja-jaja, wani fari- fari, wani kuma yellow. Mutumin ya nuna masa ai gurasar nan ake ci da miyar. Shinkafar kuma ya zuba salad ya dinga haWawa da nama. Ya tambayi sunan abincin aka ce masa chicken biryani ce da kuma"

chappati da beef curry (miyar).

Tunda ya saka hannu bai cire ba sai da abincin ya rage Wan kaWan. Yana ture plate kawai yaji mutanen

kitchen Win suna ihu harda masu rungume juna. Ashe duk sun ankara da tsayuwarsa tun farko. Shi ne

ogansu mai wurin ya shigo da shi. Farincikin fuskarsa a matsayinsa na wanda su ke da ya™inin ranar ya

fara cin abincinsu ne yasa su murna.

Sai da kowa ya nutsu aka cigaba da aiki sannan mutumin ya tambaye shi sunansa da dalilinsa na le™ensu.

"""Kenan kana son girki"" ya tambaye shi da turanci bayan ya yi masa bayani a ta™aice."

"""Sosai."""

"""Ka taSa yin makarantar girki ko ka koya daga wani professional?"""

"""A'a."""

"""Muna da makarantu a nan inda za ka iya yin degree."""

Taj ya yi murmushi da ya hango fuskar Alhaji idan ya je gida da kwalin degree a fannin girke girke. Sanar

dashi ya yi cewa karatu zai fara kuma banu damar canjawa.

"""Idan ka tabbata kana da ra'ayi ni zan iya koya maka a nan. Ka je ka duba tsarin karatunka. Ranakun da"

"baka da aji ka zo nan kayi aiki."""

Baki ya buWe da tsananin mamaki.

"""Aiki?"""

"""Baka so ne?"""

Da sauri ya ce yana so. Ya dai yi mamakin samu ne kafin ya nema.

˜aton mutumin nan ya sakar masa fuska ya ce.

"""Dukkaninmu a haka yake Waukar mu aiki. Ra'ayin yi kawai zai gani daga gareka sai ya Wauke ka yaronsa."

"Wurin nan nasa ne. Idan ka bada himma tabbas za ka ji daWi. In kuma yaga baka da ™wazo a wata Wayan farko zai sallame ka."""

Kamar wasa daga wannan rana Taj ya fara karatu kuma yana zuwa koyon aiki a ROYAL CUISINE. Abin

farinciki shi ne kasancewar dattijon da ake kira Paaji (Wan uwa ko yaya) musulmi. Yawancin ma'aikansa musulmai sun fi yawa ma. Komai na wurin halal ne. Sai da ya yi wata guda cur babu abin da ake koya masa a kwana ukun da yake zuwa duk sati sai sanin sunaye da amfanin kayayyakin abinci da kayan

™amshi (spices). Hancinsa ya aikatu don ko abu na kama da Wan uwansa idan bai tantance ba maimaici za

ayi ta yi. Wasu abubuwan kuma a ido su na kama amma a zahiri Waya nada amfani Wayan kuma guba ne.

Dole suma sai ya gane bambancinsu don kada a bashi a kasuwa ya cutar da masu sayen abinci.

Bayan nasararsa a wannin fanin kuma aka koma koyon Sare tafarnuwa da yankanta ™anana. Kan kace

"meye wannan hannunsa ya cika da plaster. Irin wannan yankan na mugun sauri ake so ya iya. Da ™wararre a wurin aka haWa shi. Daga nan aka koma albasa. A haka, a haka ya ™ware a yankan kayan lambu da kayan marmari. Yankan nama ma zaman kansa yake. Sai da ya koyi haWa mince meat ko babu na'ura da wu™a kawai da ´ar muciya. Shekara guda ko mai ba a taSa bari ya soya ba sai da ya zama"

zakara a fannin ™ananan ayyukan da su ne ™ashin bayan kowane girki.

Bayan an dawo hutu wanda yaje gida ya yi da kyakkyawan sakamakon ™arshen shekara ta farko aka kai

"shi gaban wuta. Zo ka ga farincikinsa da na abokan aikin. Mutane ne ´an asalin garin Punjab masoyan duk wani abu na farincikin al'umma. Su dai ayi nishaWi a zauna lafiya. Shi yasa Taj ya saje cikinsu. Happy Taj su ke kiransa tun ranar da ya yi skype da Kamal su ka ji yana kiransa Happy. Da yake anfi samun ´an ™abilarsu mabiya addinin musulunci a Pakistan, shi yasa Paaji duk inda ya sami ´an uwansa musulmi"

yake basu aiki. Taj da wani Uygur Chinese (wata ™abilar musulmai a China) Aynur kaWai ne ba™i.

A cikin shekara ukun farko Taj ya ™ware a girke girke da dama na yankin Asia. Banda na Indiyawa an koya

musu na Larabawa da duk wani yankin Asia da su ka yi fice ta fannin abinci. Duk kuma wannan bada™ala ko sau Waya Ahmad bai taSa sani ba har ya gama ya koma gida. Taj ya ci karensa babu babbaka ya haWa riba uku a zaman nasa. Bai manta da ™udurinsu na bitar hadda ba shi da Kamal shi yasa ya shiga wata makarantar ™arshen mako da ake yi a masallaci. Kamal ne kaWai ya san me yake ciki kuma ya bashi goyon

baya tare da nanata masa mahimmanci barin abin a matsayin sirri.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Taj da Kamal sun ™ar™are karatunsu a cikin shekara uku da ´an

"watanni. Kowanne akwai taron convocation da za ayi a makarantarsu. Kamar yadda aka fara kai Kamal, ranar nasu taron ta zo sati uku kafin na su Taj. Alhaji sai ya Wauki Hajiya da Umma su ka tafi Dubai."

"Satinsu biyu a can su ka koma gida tare da Kamal Win. Bayan kwana huWu ya juya da Ahmad, Mama da"

Inna zuwa India.

***

Gagarumar gasar girki ce Culinary Academy of India ta saka domin samun zakarun da za ta bawa tallafin

yin karatun degree na tsahon shekara uku a fannin Catering Technology and Culinary Arts. Makarantar

reshe ce ta Jami'ar da ya kammala wato Osmania University. Kuma Walibanta ta buWewa gasar masu

ra'ayin girki waWanda ba ´an asalin ™asar ba. Paaji na samun labari ya saka shi a gaba a gaban kwamfutar

restaurant Win nasu ya cike komai online. Abokan aikinsu su ka yi ta murna domin da fari har ya soma yi musu sallamar komawa gida da zarar an yi convocation.

A kwana biyar za ayi komai a gama. Taj bai san da tahowar su Alhaji ba kamar yadda Kamal bai san ya

shiga gasa ba. So ya yi ya yi surprising Wan uwan nasa. Wanda kuma da ya faWa masa zai gargaWe shi da tahowar tasu. Duk wayarsu da gida ana ta Soye masa don an san ba ™aramin farinciki zai yi ba idan su ka

zo. Tahowar Ahmad kawai ya sani saboda zai zo registration na masters tunda ya gama bautar ™asa.

Sun iso ™asar awa guda kafin a shiga gasar a rana ta huWu wadda ta kasance alhamis. Zuwa yanzu team

Win Taj da aka haWa da wani banufe Wan Nigeria mai suna Wakili su ne su ke jan ragamar mu™ami na biyu. Wasu wa da ™ani ´an Indonesia kuma a sahun farko. Wayarsa Ahmad ya kira ya faWa masa sunan hotel

Win da su ka sauka.

"""Yaya ka daure ka ™araso Uma Nagar cikin Culinary Academy."" Ya ce da farincikin isowar Wan uwansa."

Don dai yau Waya yana ganin ba komai bane idan an sani. A tunaninsa nasararsa ta karatun da Alhaji

yake so za ta sa ya bashi damar cika nasa burin.

"""Me ake yi?"""

"""Gasar girki na shiga."""

Gefe Ahmad ya matsa hankali a tashe.

"""Ashe ba ka da hankali Taj? Tun yaushe Alhaji ya soke maganar nan?"""

"Da yanayi na ban tausayi Taj ya ce ""Yaya ina so wallahi. Domin neman amincewarsa na dage sosai a"

"makaranta. Kana ganin yanzu ba zai sauko ba tunda nayi karatun da yake so?"""

"""Baka da hankali."" Ahmad ya sake faWi yana jin zufa na karyo masa."

Duk abin da yake yi hankalin Alhaji dake magana da su Inna yana gare shi. Sauke wayar daga

"kunnuwansa ke da wuya yaji ya ce masa,"

"""Me ku ke Soyewa da har za ka tashi ka dawo nan?"""

"""Babu komai Alhaji. Ya ce min baya hostel ne."""

"Rashin gaskiya ya gani ™arara a fuskar Wan nasa shi yasa ya ce,"

"""Kai ni inda yake!"""

RAYUWA DA GII 5

Batul Mamman

"""Alhaji..."""

"""Zan saSa maka."""

Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huWu suka kama hanya. Mama da Inna ba su

san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj Win da su ka shiga bai Wauka ba. Da tambaya su ka ™arasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ™udaje. Basu wani sha wahala ba su ka hango tebura huWu na ™asashen da su ka rage a gasar. A yau za a fitar da wani team Win sai ya rage uku.

"Washegari idan an yi na ™arshe a fitar da na Waya, na biyu da na uku."

Cikin wata irin nutsuwa da tsantsar ™warewa Taj yake aiki. Shi da Wakili girkinsu cikin tsari yake kamar

"sun manta da lokacinsu na tafiya. Wannan nutsuwar ita tafi burge al™alan gasar. Masu sauri saurin cimma lokaci kuwa daga kwano ya faWi ya fashe sai ka ji su na washhh, mai ko ruwa mai zafi ya fallatso mu su saboda garaje."

Tunda Alhaji ya yi tozali da Wan nasa wani abu mai masifar Waci ya sami wurin zama a ma™ogaronsa. Taj

yake gani sanyi da dogon wando ba™i da riga yellow mai tambarin makarantar sai apron fari tas Waure a

™ugunsa. APRON!?

Inna kuwa tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi. Tunda ta nunawa Mama shi bata sake iya cewa komai

ba. Maman ce ma ta iya yin magana da ™yar.

"""Ahmad me idona yake gani?"""

"""Gasar girki ce"" ya bata amsa a sanyaye."

"""Ku zo mu koma."" Alhaji ya ce da matansa ""Kai kuma ka jira ya gama ka taho min da shi."""

"Ahmad ya so raka su amma ya nuna masa yawo a ™asar da ba tasu ba, ba ba™on abu bane gare shi. Haka"

su ka tafi babu mai cewa komai. Da isarsu Alhaji ya Wauko magungunansa na hawan jini ya watsa sannan ya ce kada wanda ya tashe shi sai Taj ya iso. Dama Waki uku ya kama musu. Sai su ka koma Wayan.

"Ido cike da ™walla Inna ta ce ""Yaron nan so yake ya jaza mana tashin hankali ko me?"""

Kallonta Mama tayi ta girgiza kai.

"""Matsi da takura yaro bai fiye haifar da Wa mai ido ba. Taj ya yi masa biyayya an sami abin da ake so."

"Mene ne aibu don ya Wan waiwayi burinsa? Don fa mun haife su ba yana nufin dole su rayu kwatankwacin tamu rayuwar ko ra'ayi ba."""

"""Kayya dai Mama. Rayuwar yara sai da nuna hanya daga iyaye."""

"""Nima ban musa ba. Amma babu inda addini ya bawa iyaye damar tauye ´a´ansu akan abin da bai"

"saSawa addinin ba. Baki ji malamai suna faWin ko sakin aure indai ba bisa adalci ba, iyaye basu da hurumin tilasta shi ba? Girkin nan kuma maza nawa ke yi? Mene ne aibu a ciki tunda ba daudu yake ba?"""

"Inna dai duk a tsorace take ta ce ""tunda mahaifinsa ba ya so sai ya ha™ura ko don neman albarka."""

Mama gani tayi cigaba da nunawa Inna illar takura tayi yawa ga Wa mai biyayya bata da amfani ba sai

taga Innar ta kasa fahimta. Idan ta matsa kada abin ya yi kama da tana son sanya shi yin bore. Zaman jiran tsammani su ka yi har bayan Isha.

*

Sakamakon gasa yau dai da su Taj ya tashi. Cikin nasara da taimakon Allah su ne su ka yi na Waya. Yawan

makinsu idan an haWa da na kwanakin baya ya basu damar iya yin na Waya gobe in sun dage. Banda ihun

"murnar ´an Nigeria da su ke makarantar ba ka jin komai. Yanzu ya rage teams uku. Gobe za a fitar da na Waya, biyu da uku. Da su ka fito za su tafi Wakili ya tare shi da godiya."

"""Ban san a ina ka koyi girki wanda yasa talent Winka ya zarce na kowa a nan ba. Your are truly amazing."""

"Taj ya yi murmushi ""ai ban kai ka ba."""

"""Magana ta gaskiya ake yi. Idan muka yi nasara na san albarkacinka na ci. Saboda haka ina ro™onka don"

"Allah gobe ka dage fiye da kullum. Samun karatun ya fiye min akan kuWin da za a bawa na biyu ko na uku."""

Murmushi Taj ya sake yi da al™awarin in sha Allahu gobe zai yi bakin ™o™arinsa.

Da tallafin gwamnati Wakili ya sami tahowa karatu. Ya gama degree kamar Taj amma yana tsoron

"komawa gida yanzu. A ™auye su ke. Gashi samun aiki yanzu ya koma wa ka sani, wa ya san ka. Tunda yana aiki a wani gidan abinci a nan yana samun abin turawa mamansa da ™anne ba zai so ™arewar visa yasa shi komawa gida a sake naWe hannuwa ba."

*

Murnarsa ta koma ciki da Ahmad ya faWa masa tare da su Alhaji su ka zo akan hanyarsu ta zuwa hotel Win.

"""Yaya don Allah kada ka sanar dashi zancen competition Win nan."""

Cije leSe Ahmad ya yi wanda yasa Taj tambayarsa ko ya faWa hankali a tashe.

"""Tare mu ka shiga inda ku ke girkin. Ya riga ya gan ka."""

"Bayan karanto duk wata addu'a da ya sani ta neman sau™i, bai sake cewa komai ba har su ka isa hotel Win."

Kai tsaye Wakin Alhaji su ka je su ka tarar da Inna da Mama a zaune jigum. Jikin Alhaji har ya soma tsananta saboda damuwar da ya sanya a ransa.

Wuri ya samu kusa da Mama ya zauna jikinsa a matu™ar sanyaye. Shiru yana jira a fara yi masa faWa

amma babu wanda ya yi magana. Cike da fargaba ya rarrafa gaban Alhaji kai a ™asa.

"""Don Allah..."""

Tassss. Alhaji ya tsinke shi da marin da ya gigita shi. Inna tsam ta mi™e ta fice daga Wakin don ba za ta juri

gani ba. Ko da ta koma Waya Wakin fashewa tayi da kukan da bata san na mene ne ba. Tana tausayin

Wanta. Tana kuma son ya sami damar cikar buri sannan kuma tana so ya yiwa mahaifinsa biyayya.

Sake Waga hannu Alhaji ya yi zai kuma marinsa cikin zafin nama Mama ta ri™e hannun da sauri.

"""Ka dubi Girman Allah kayi ha™uri."""

"""Ki sakar min hannu"" ya mi™e tsaye da fushin da yafi na farko yana mai fincike hannunsa."

"""Haba Alhaji. Mene ne aibun girki a wurin namiji da har za ka kasa bawa yaron nan damar cikar burinsa."""

"""Buri? Buri fa ki ka ce A'i?"" Ya nuna ™irjinsa ""Wan

4 / 42