Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 42

39K to 42K   out of 124.8K words

ya cika ta fita daga motar mutumin. Kamal ya ™arasa

wurin direban ya bashi ha™uri tare da cewa ™anwarsu ce. Shi ma ya bada ha™urin rashin yi mata bayani

wanda ya janyo wannan ruWanin.

"""Ga kayanta"" ya ce da yaga suna shirin tafiya."

Kwalaye ne madaidaita guda biyu. Šaya doughnut. Šayan kuma meatpie da samosa. Sai kuma ledar

youghurt wanda Hauwa ce da kanta tayi.

Anisa ce ta kula Hamdi bata da takalmi da ta zauna a baya. Za ta fita ta Wauko mata sai Taj ya ce ta zauna.

Shi ya Wauko harda wayar yana ta mamakin wannan coincidence. Ashe tana Abuja. Shi yasa baya ganinta a gidansu. Murmushi kawai ya dinga yi har su ka soma tafiya. Hanyar gidan da ba ganewa za ta yi ba shi ma Anti Labiba ce ta turo kwatance. Anisa ta ce ta gane. Idan sun isa unguwar za ta kira sai ta kwatanta

gidan.

"""Shhh"" Hamdi ta fara yi da baki saboda fitsarin da ya gama matsarta. Tun a na farko Taj ya ji. Hankalinsa"

gabaWaya yana bayan motar.

"""Step on it Kamal (™ara sauri)"" ya ce a hankali don kada taji kunya."

"Kamar a kunnen Anisa ya faWa sai cewa tayi ""eh kuwa. A matse take sosai"" tana kallonta."

Ko a jikin Hamdi. Burinta kawai a isa gida. ˜afafunta sun kasa zama waje guda. Komawa gidan tayi mata

nisa saboda uzurinta. Finally bayan ta gama gumi su ka shiga estate Win su Anti Labiba. A guje ta fita da

Kamal ya tsaya. Ta sake barin takalma da wayar da dama Taj bai mi™a mata ba.

Anisa ta bita cikin gidan su kuma suna waje. Anti Labiba da yara sun taso da murnarsu ta wuce su ta

shige banWaki. Bata ma kula harda maigidan ba sai da ta gama ta fito.

"""Washhh Allah na."" Ta furta da ta dawo hayyacinta. Sai kuma ta rungume Antin tana kuka."

"""Mene ne na kuka kuma? Ba gashi kin dawo ba."""

Ta kalli maigidan da su ke kira Uncle.

"""Na zata ba zan sake ganinku ba."""

"""Ke dai anyi matsoraciya."" Cewar Anti Labiba tana dariya."

"""Ko nice fa zan tsorata. Bata san wuri ba kuma an bi hanya daban."" Anisa ta kare mata."

Murmushi ta yiwa Anisan gami da bata ha™urin rashin cika al™awarin kai kaya.

"""Wa yake ta kaya baiwar Allah? Ai tunda dai kin dawo gida nima bu™atata ta biya."""

Kiran sallar magrib aka fara Anisan ta ce tare su ke da yayyenta. Uncle da kansa ya fita ya kira su cikin

falo domin su yi sallah bayan an kai musu ruwa sun yi alwala a waje.

Suna idarwa Anisa ta ce za su tafi. Anti Labiba dake kitchen tana haWa zoSo ta hana. Sai da ta haWa komai

ta kawo ta nemi Hamdi a falon ta rasa. Maigidanta ta tambaya ina take ya ce ai tun shigowar su sallah bai ganta ba.

Šaki Anti Labiba ta bita. Ta sameta zaune a bakin gado da zumbulelen hijabinta.

"""Ki zo ki sake yi musu godiya za su tafi."""

"""Anti rawar fitsari fa na dinga yi a motar. Ni dai wallahi ba za ni ba."""

"""Harda saurin rantsuwa?"""

"""Baki ganni bane"" ta faWi tana takaicin abin da tayi."

Falon ta dawo bata san Hamdin na bayanta ba. A bayan labule ta ma™ale ta Wan le™o da kanta. Hira

Uncle yake da su Taj inda a nan su ka gane su Win duka ´an Kano ne. Ya nemi su dinga zumunci domin an

zama Waya.

Ta bayan labulen ta sake haWa ido da Taj domin yaga tsayuwarta tun farko. Baki ta buWe don da wannan

kallon ta gane shi. Zuciyarta ma bata manta ba saboda irin harbawar da tayi da sauri. Ta sanya hannu ta rufe bakinta. Za ta gudu taji muryarsa da ta gane tun a wayarsu ta Wazu.

"""Kamal bani key na Wauko mata takalma da wayarta."""

Anti Labiba ta waiga ta hango shatinta a labulen.

"""Zo ki je ki karSo mana. Ko sai ya biyoki dasu kuma?"""

Sumi-sumi ta fito kai a ™asa. Kamal ya tsaya bawa Uncle numbar wayarsa. Ita kuma Anisa santin zoSo

take tana kuma wasa da yaran gidan.

Da faWuwar gaba ta isa bakin motar. Taj ya buWe ya Wauko mata takalman da wayar. Maimakon ya mi™a

mata sai ya jingina da motar yana kallonta.

"""Kin gane ni yanzu ko?"""

Murmushi tayi ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta.

"""Ashe nan ki ka gudu shi yasa ban ganki ba."""

"Kallonsa tayi a fakaice ""nema na kake yi?"""

"""Na san inda zan same ki Hamdi. Kawai ganinki ne ban yi ba a wajen."""

Shi mai maganar da ita da ake yiwa duk jikinsu tamkar anyi musu duka. Zu™atansu ke aikin wucin gadi na

tsananin murnar sake haWuwar bazata irin wannan.

"""Ina? Makaranta?"""

"""A gida."""

Daina Soye fuskarta tayi. Ta kalle shi da mamaki. Muryoyin su Anisa yaji sai ya bata kayanta.

"""Sai mun haWu a Kano. Take care."""

Motar ya shiga amma bai rufe ba har su ka iso. Hamdi ta sake yi musu godiya sannan su ka shiga mota su

ka tafi.

Daren ranar mutumin da bata san sunansa ba ne ya cika mata zuciya da tunani. Bata da wani aiki sai

murmushin da bata san lokacin da yake zuwa ba.

A Sangaren Taj kuma suna yin sallar isha ya ce bacci zai yi. Abincin da Anisa ta dafa Kamal ne kawai ya ci.

Shi kuma ya sanya snacks Win Hamdi a gaba. A take ya yanke shawarar sanyata a Sangaren snacks Win

restaurant Win shi wanda Kamal ya yiwa suna da HAPPY TAJ. Kuma ba shi kaWai ba. Kowa ya ci sai yaba daWin kayan.

Wayar da su ka dinga magana Wazu ya kira sai yaji muryar direban motar. Ba yadda ya iya. Godiya kawai

ya sake yi masa ya katse kiran. Kenan ba da wayarta su ke magana ba? Yayi guntun tsaki. Babu matsala tunda samunta ba zai yi masa wahala ba. Zuciyarsa wasai ya kwanta.

*

Tun asuba Taj ya faWawa Kamal cewa a yau za su koma Kano. Zai yi magana da Anisa kafin su tafi.

"Ba musu ya amince "" gara haka don zamanmu ma zai iya sanyawa ayi tunanin wata soyayya ku ke"

"bugawa fa."""

Da yake da wurwuri ta tashi ta haWa musu breakfast. Shi ya taimaka masa wurin samun ganinta da wuri.

Ta zauna a falo ta sunkuyar da kai ™asa. GabaWaya sai ya dinga jin babu daWi. Hajjo taje kawai ta sanya

mata rai.

"""Anisa."""

"""Na'am Yaya."""

"""Kinji haWin da Hajjo take son yi mana ko?"" Kai ta gyaWa da murmushinta."

"""Bani da abin cewa game da karamcin gidan nan naku sai godiya. Anyi min komai a lokacin da na rasa"

"soyayyar mahaifina."""

"Ta dube shi da tausayawa ""kayi ha™uri. Komai zai daidaita in sha Allah."""

"""Haka nake fata. Amma saboda halin da nake ciki Anisa bana son yin aure yanzu."""

A razane ta dube shi. Gabanta na faWuwa kada ya ce baya sonta. A ransa hakan yake son faWa ko don ta

bawa wasu dama. Amma yana gudun me zai je ya dawo.

"""Ina son lokacin aurena Alhaji ya halarta ba don anyi masa dole ba. Idan na sami ´a´a in kai masa ya yi"

"huWuba yadda yake yiwa ´a´an ´an uwana. Ya kuma sanyawa abin da na samu suna."" Yaja numfashi ""hakan ba zai samu ba yanzu saboda bai ha™ura ba."""

"""Kana nufin na nemi wani kenan?"""

Ta tambaye shi da sanyin jikin da ya sanya masa tausayinta.

"""Ina nufin mu bi komai a sannu sannan mu nemi zaSin Allah. Bana son in yi miki al™awarin da ba zan iya"

"cikawa ba."""

"Murmushi tayi ga ™walla ta taru a idanunta ""na fahimceka, zan kuma cigaba da yi maka addu'a."""

"""Nagode"" yaji zuciyarsa maimakon ta rage nauyi ™arawa tayi. Reaction Win Anisa na sau™in kai ya kwaSa"

masa lamari. Shawarar Kamal ta biyu zai bi. Ba zai yarda ya nuna mata kulawar da za ta saka rai da

samunsa ba. Amma abin da kamar wuya domin Hajjo ba za ta sakar masa mara ya sha iska ba. Shi ya san

da wannan.

***

Sati guda ya ™ara a Kano ya tattara ya tafi. Ayyuka ne har biyu su ka taso masa na bukuwan manya

wanda suka ™i yarda su nemi wani chef Win duk da baya nan. Sun tsara abubuwa da dama da Abba kafin tafiyar tasa.

"""Ka cigaba da training Win yaranka kafin na dawo. Idan sun yi passing test Wina zan yi retaining Winsu."""

"Abba ya ce ""shagon fa?"""

"""Ku cigaba da girkinku kafin a ™arasa wancan."""

Gidan Abba Habibu kowa ya yi farinciki da cigaban da ya samu. Wurin yanzu yafi na da komai da komai.

"Hamdi ce kaWai da labari yaje mata ba kunya ta ce ko waye Taj Winnan bai burgeta ba. Idan taimako zai yi ai da ya samarwa Abba wata sana'ar. Kuma da yake a idanunta wani matashin Wan daudun take gani, sai taji duk ta tsane shi tun kafin su haWu. Haka kawai ya zo ya yi amfani da halin rashin da suke fama dashi"

wanda ya hanata shiga jami'a ya sake dulmiya mata uba.

Har ta dawo Kano bayan wata uku da ko sau Waya bawan Allahn nan da ya gama da zuciyarta bai nemeta

ba. Tun tana damuwa don ta sa rai za ta sake ji daga gare shi har ta ha™ura. Sana'ar snacks ta kama ka'in da na'in wadda kuma Allah Ya sanyawa albarka. A Wan tsukin wajejensu tayi suna. Biki ko suna kowa Hamdi yake kai wa aikin kayan fulawa. Kuma tana yi Abba ya sayar mata a wurinsu. Kafin wani lokaci sai ya zamana su uku suke yi. Zee ta fi ™warewa a yin youghurt kamar ita Luciousbites ta koyawa. Abinsu

gwanin ban sha'awa.

Taj yana yawan kira ya gaishe da Yaya. Wani lokacin ta wayar Sajida. Idan aka yi mata tayin gaisawa da

shi sai tayi ta zillewa. Idan Yaya bata wurin kuwa wasu lokutan har tsiwarta yana ji ta wayar Sajida. Har

mamakinta yake yi. Idan ance masa tana da baki haka zai ™aryata saboda shi dai da fuskar salihai ya

ganta.

Su kuma ´an uwan nata komai su ka ji game da shi ko a hira ne sai sun faWa mata. Idan aka ce Kamal ya

zo kuwa bata yarda su haWu. Ita fa komai nasa akai kasuwa kawai. Ranar da Zee ta ce mata ya iya indiyanci babu irin sha™iyancin da bata yi ba. Da aka kwana biyu ya kira wayar Yaya sai ta Wauka. Amma bata saka a kunne ba. Kawai domin yaji haushi ya fita daga rayuwar gidansu tayi magana.

"""Yaya ga Salman Khan Winku ya kira."""

Taj ya kawar da wayar daga bakinsa ya gama dariya sannan ya ma™e murya ya kirata.

"""Hamdiyya."""

Tsigar jikinta ta tashi. Muryar bata yi irin ta mata sosai ba tunda bai saba ba. Amma dai ya kamanta don

ji tayi kamar ta yar da wayar.

"""Aap kaise hain?"""

"""Na'am?"" Ta ce da takaici. ˜ila ma har rawa da wa™a ya iya."

Ya sake maimaita tambayar wadda take nufin 'yaya kike?'

"Ta taSe baki ""zindagi choringe...ba dai shi ne indiyancin ba?"" Ta shiga falo da sauri ""Yaya ungo wayarki"

"Taj Winku ne."""

"""Zan ci mutumcinki akan yaron nan Hamdiyya. Ke da zaki ganshi sai kin raina kanki."" Yaya ta faWi ba tare"

da sanin Hamdin ta Waga kiran ba.

"Zee ta ™ara da cewa ""™ila ma ta ce tana son shi."""

"""Wuce nan wallahi. Wanda nake so namijin gaske ne."""

"""Lahhhh"" Yaya ta faWi tana jifanta da maficin hannunta ""ni kike faWawa haka ko mara kunya"""

Hamdi ta fice da gudu suna dariya ita da Zee. Šakinsu su ka koma su ka sami Sajida tana farinciki.

"""Me ya faru?"""

"Rungume ™annen nata tayi a tare ""Safwan zai turo ranar asabar."""

HaWuwa su ka yi su uku suna tsallen murna. Yayinda Yaya take waya da Taj wanda yake cike da nishaWin

jin muryar Hamdi.

RAYUWA DA GII 14

Batul Mamman

***

Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba

kullum. Har ta ha™ura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata WanWanonsa idan ta haWa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa'a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin

kwantai.

"""Yaya zan kai masa da kaina."""

Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s

Sau Waya ta taSa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata

"plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huWu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi ta™i jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler Win da"

ta sako meatpie Win mai hannu biyu ta kinkima ta ™arasa.

Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ™ofa ta kuma

tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.

"""Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi Wiyarmu ce don ga kama nan. ³an mata shigo daga ciki. Aunty"

"Simagade yau ana ta fama da ba™i."""

Gaban Hamdi ya yanke ya faWi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caSalSala

masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da Waurin ™irji. Kansa kuma ya yi Waurin ture ka ga tsiya da Wankwali irin zanin.

'Me ya kawo Wan daudu wajen nan?' Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ™uncin rai.

Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ™afafunta wani irin ba™inciki ya turnu™eta. Akwai kwastomomi da yawa

a ciki. Amma fa a yau dandazon ´an daudu sama da huWu ne su ke ta karakaina wajen Waukar odarsu da

kawo musu abinci. Muryoyinsu da ta™i jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna sha™iyanci. Ita

kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.

*

Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. ³ar Ficika ake

kiransa saboda ™an™anta da ™warewa a iya shege. Duk wani mai ji da haya™insa idan ya gamu da ³ar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haWawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ™warai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuWi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haWa abinci. ˜aryar mutum ya ce ya taSa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. ³ar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum.

"Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo ³ar Ficika ne ya biya masa rabin kuWin jirgi."

Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haWa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar

tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ™ar™ashinsa kaf babu Wan daudu. Maza ne kawai masu ra'ayin girki a dalilin rashin wata sana'ar. To yau kwana uku kenan da ³ar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ™afa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haWu da wanda

ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.

Abba bai Soye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. ³ar Ficika yaji ya kwaWaitu da samun darajar da ya

rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ™yama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa

Abba ya ce kuma zai buWe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa.

"""Šan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ™o™arina."""

"""Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka"

"sabon restoran Win sai na karSi wurin nan."""

Abba bai yi ™asa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin ta™aitaccen tarihin ³ar Ficika da

tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince.

"""Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake"

"dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau."""

"Taj ya ce ""haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya"

"take."""

Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaWi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk

lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daWi domin yau kasuwar ta buWe fiye da kullum. Ya ala™anta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wula™ancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman

wurin kafa sana'a da ya rasa wancan.

*

"""Kai, kai, kai...Tabarakallah."""

Hamdi ta waiga baya ta haWa ido da wani ™armasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi

yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. ³ar Ficika ya cigaba

da murmushi yana kallonta.

"""Wannan ma taka ce?"""

Yaronsa da ta haWu dashi a waje ne ya bada amsa.

"""Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ™amshi."" Ya faWi yana"

lan™waya hannu da juya idanu.

Wani irin Waci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ™yar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da

ya gabatar a matsayin abokan sana'arsa a Saudiyya.

"""Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama Waya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba."""

"""To"" ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje."

Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta Wauka Abba girki da abubuwa

na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu'amalanci mutane irin waWannan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin Wan daudu.

"""Hamdi"""

Sarai taji kiran da yake mata amma ta ™ara sauri. Kafin ta ™arasa titi ta dire coolar a gabanta ta Wagawa

wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faWa ciki su ka yi gaba.

Abba ya kalleta ya juya ya kalli ³ar Ficika da ya biyo shi.

"""Ba dai ganinmu bane ya Sata mata rai ba?"""

"Murmushi ya ™a™alo ""ahh haba dai. Sauri take yi."""

"³ar Ficika ya murmusa ""ko kai a gabana ka ™arasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na"

"saba gani?"""

Cike da jin nauyi Abba ya faWa masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu

mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da

14 / 42