Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 42

78K to 81K   out of 124.8K words

Scentmania by Sana, na Naana Hauwa'u queen of oil perfumes. Domin neman ™arin bayani a"

tuntuSeta a wannan layin 07065525409.

Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate Win. Kamal ya yi mamakin

ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta Wan jira shi. Ko

kallon Taj Win bata yi ba domin ranta a Sace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu.

Kafin Kamal ya ™arasa gate Win sai ga Firdaus. ³ar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da

Hamdi.

"""Anti Hamdiyya Habib Umar"" ta kirata da ™arfi cikin murna."

Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta

ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ™arya. ˜aruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta

rungumeta.

"""Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki Webo"

"ba. Uncle Taj is my favourite."""

Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso

da sauri.

"""Ke matsa min. ˜anwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita."""

"""To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow"

"me..."" wata ™anwarsu ta janyeta ""sannu da zuwa Sis"""

"""Meye haka jama'a? Ba babba babu yaro?"" Umma tayi magana daga ™ofar Wakinta. Kowa sai ya sami"

"nutsuwa ""Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?"""

Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame

jikinta ta koma ™asa. Akayi akayi sam ta™i komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da

zuri'ar Abba Habibu ta Sace Sat.

Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ´an uwansa

Waya bayan Waya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaWai sun ishi juna gayya.

"""Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu."" Yaya Kubra ta faWi."

Tana cikin waWanda Hamdi ta ri™e sunansu saboda kana kallonta kaga ´ar gayu ajin ™arshe. Gashi ance

likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna.

Kai ta gyaWa har lokacin ta kasa buWe fuskarta da kyau. Hira ce ta Sarke kowa da irin tambayar da yake yi

mata.

"""A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah."""

"""Hajiya ai so muke ta buWe bakinta."""

"""Baki zai buWe ne babu abinci?"" Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara Wauko kwanuka."

"""Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?"" Wadda tayi maganar ta fara buWe food flask."

"Akwai fried rice wadda taji kayan haWi da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau'ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro,"

kodayake taron ne tunda yawa garesu.

"Kai a ™asa ta ce ""Na ™oshi."""

"""Kada na sake jin zancen ™oshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau"

"dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu."" Umma tayi magana tana hararar ´a´an nasu ""daga"

"cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa."""

Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta

lura kusan sa'anni ake haWawa a tray guda. Firdaus ta nace a haWasu a tray guda amma fir aunties Winta

su ka ™i. Wai matar aure ba sa'arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ™ila na ™arshe.

"""Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare."""

Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma

su kwashe da dariya suna hailing Winta. Harda masu karambanin Wauko plate za su zuba musu.

"Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce ""Bismillahir Rahmanir"

"Rahim."""

WaWanda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu

maganinta. Inna ma murmushi tayi.

Abinci ya yi daWi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na ba™unta.

Su na ci ana kiran sallar la'asar. Šakin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ™ofa ba.

"""Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haWu da wata ´ar uwar taku ma a bakin gate mu"

"ka gaisa. Naga kamar ta tafi."""

"""Kai anya kuwa. Kowa na nan fa."""

"Ba don bata ri™e sunan ba ta ce ""sunanta Salma ina jin."""

"""Salwa ko?"" Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce ""Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan."""

Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita

dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaWa wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba.

"""To ku kira ta mana. An duba banWakuna? Ko bacci ya Wauketa a wani Wakin?"" Cewar Hajiya."

"Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun ´an gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruWanin ina ta"

shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta.

"""Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan."""

"""Da shirin fita ki ka ganta?"" Anti Zahra ta tambayi Hamdi."

Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama.

"""A'a, cewa tayi za ta je wajen shi..."""

"Yaya Hajiyayye ta ce ""shi wa?"""

"""Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?"" Yaya Zulaiha ta tambayeta."

Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan bu™ata ba. Tayi

kaWan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daWi ba.

"""Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki"" Anti Zahra ta faWi hankalinta a tashe."

Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko

abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taSa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki.

Kamal Win aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo.

"""Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?"" Umma da ta kira wayar ta tambaye shi."

"""Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu."""

Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke

"wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haWawa ake yi."

Hamdi ta auro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiWa mata abin sallah.

Shigarta ta kamala ta burge Mama. Ta™i jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko

hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma Wa'a ga

addini ba.

Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar.

"""Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji."""

Gaban Hamdi ya Wan faWi. Ko faWa mata zata yi ta fara shirin zama bazawara?

"""Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da ala™arsa da mahaifinsa?"""

"""Na sani"" ta amsa kai a ™asa."

Mama ta numfasa ta ce

"""Kullum burinmu shi ne ™ila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ™addara masa aurenki. Wannan"

"ma ya ishi mai hankali tunani."" Ta kamo hannunta ta ri™e ""a halin yanzu mutumci da martabar"

"mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da Wabi'ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da Worewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili."""

Jin an taSo Abbanta ne yasa ™walla cika mata ido. Wani Sangare na zuciyarta yana ™ara tunatar da ita

laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani Sangaren kuma yake

kare Abba a matsayin an Adam ma'asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana

tubansa.

"Da ™aramar murya ta ce ""Me ya kamata na yi?"""

"""Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaSin da Allah Ya yiwa Taj."" Mama ta"

"faWi tana yi mata murmushi ""Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ™uruciya su ke samun wannan ™warin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ™watarwa kanki ´anci. Sai abin yafi ™arfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ´a´an Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ´a´a ta kowacce fuska. Na ™arshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ™aunarsu dasu da sana'ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da"

"zama ´ar da shi ko wani zai kasa ™auna a matsayin suruka ba."""

A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko

ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a Wan dun™ule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken Wan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya

gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa.

A ta™aice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun

da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ´a´ansa. Sannan sana'ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi

fushi da Wansa.

Godiya tayi mata da al™awarin kamantawa da yardar Allah.

"""In kin kula gidan nan babu ´an ubanci tsakanin ´a´anmu. Duk da Alhaji ne ya Wora mu akan turbar"

zaman lafiya to amma fa akwai ™o™ari matu™a daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ´a´a maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina Worawa kaina laifi domin kuwa ni na ™arfafa masa gwiwar girki. Fatana da

"raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya dam™awa mahaifiyarsa."""

Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun

shigowarta komai na jama'ar ciki yake burgeta su ma da nasu.

"Šakin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaWai zaune akan abin sallah. Suna"

"shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta Waga hannuwa tana addu'a, Hamdi sai ta Waga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin."

"Umma ta zolayeta da cewa ""Wato kin ji ina ro™a muku ´an bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta"

"cewa amin ko?"""

"Kunya kamar ta nutse ""Allah ban san ita kike yi ba."""

"""Janye Amin Win za ki yi?"""

"""Eh"" Hamdi ta faWi da sauri, kunya duk ta ishe ta."

"""Yanzu addu'ar tawa ce ba kya so?"""

"Sake daburcewa tayi ta ce ""A'a ban janye ba. Yi ha™uri don Allah"""

Umma tayi dariya sosai.

"""Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna."""

Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu Saraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin

da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ´a´a tunda ba a raba siblings da ´an rigingimunsu. Amma dai

duk inda aka je aka dawo su Win tsintsiya ne masu maWauri guda.

"""Hamdiyya don Allah ki ri™e mijinki ri™on da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraWa kunya."""

"""In sha Allahu Umma."""

"""Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaWai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake"

"so kuma ke ya zaSa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ™i ji. Ki gani, ki ™i gani."

Babu wata rayuwar auren da take Wari bisa Wari. Amma indai kun ri™e juna amana za a sami nutsuwa da

"rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure."""

Wani tunani ne ya Warsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita Wakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san

shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ´an uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba'in da Woriya suna gina ´a´ansu akan turba mai Sullewa. Ba za su taSa maraba da abin da zai kawo

rabuwar kai tsakaninsu ba.

"""Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki."

"Haka ne?"""

Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaWa a

hankali.

"Hajiya ta dafa kafaWarta da kulawa ""Inna ce kaWai cikinmu bata sani ba sai kuma ´an uwanku da shi Taj"

"Win. Ko kin faWa masa?"""

"""A'a."""

"""Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu"

wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ´an uwansa su ka karSeki hannu bibbiyu. Innarsa da

"danginta kuwa ..."" ta kasa ™arasawa. Ha™i™a wannan karon akan Taj yayyen Inna da ™annenta da su ke"

duk maza sai Sarin kuWi suke yi.

Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da

Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an Wauke musu. Lefen da ´an uwansa ke haWawa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin

babansa haka su ma can yake yi musu.

Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ™asa a gwiwa ba ta ce

"""Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar."""

"""Hamdiyya addu'a nake so ki yi. Ki ro™i Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin"

aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai Saci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arzi™i bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa'adin zaman ne bai ™are ba

"amma da tabi ta ´an uwanta da ta daWe a gida."""

"""Subhanallahi"" Hamdi ta faWi cike da tsoro."

"""˜warai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama...Haj. A'i da ki yi sallah a Wakinta ma tafiya za ta yi. Saboda"

"kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki."" Ya dubi Hamdi da kyau ""a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da"

"muka Sata muna gina ´a´anmu akan soyayyar juna da zumunci?"""

"Murya na rawa Hamdi ta ce ""Hajiya aikin ya yi min nauyi."""

"""Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa."""

"""Abbana...Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?"""

"""Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri'arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki."""

"""To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?"" Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me"

su ke so ta™amaimai.

"""Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ™are kafiya da taurin kai"" Hajiya ta faWi"

tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi.

"""Duk ya bi ya Sata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa"

gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane Wansa da baban

"naki da yake ™i basu ragu da komai ba akan sana'arsu. Allah Yasa kin fahimceni."""

"""Na gane Hajiya. Amma..."""

"""Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai ha™uri bai iya"

fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. ³a´a ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya

"zamu yi?"""

Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana Waya su ke yi mata. Ina ita

ina Waukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taSa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani.

Hajiya tashi tayi ta ce mata su je Wakin Inna. Sun sameta da yawancin ´an matan jikokin nasu. Zolayarta

su ke son rai tana biye musu.

"""Ku zo ku fita."" Hajiya ta nuna musu ™ofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat Win Ahmad da ya dage ba"

zai fita ba.

"""˜yale shi Hajiya"" Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi ""iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha."

"Nawa kawai tuni ne akan ki ri™e maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taSa haWaku kuwa?"""

"""A'a"" Hamdi ta

27 / 42