Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   26 / 42

75K to 78K   out of 124.8K words

fi tausayawa. Sai ya musgunawa Wayan kuma? Duk da haka ya ™udurce

ajiye abin a ransa har ya gano yadda aka yi taji zancen.

Bayan sun kammala wani emergency order na taro an fitar da abincin ya tafi wurin Kamal. Mutumin da

"kullum idan ya shiga shagon nasa har mita yake masa na rashin hutu yau a zaune ya same shi yana gyangyaWi. Ya kan ce masa mene ne amfanin ´an zaman shagon dake nuna kaya da waWanda ke wurin biyan kuWi. Shi kaWai ya yi nan, ya yi can. Sai gashi hayaniyar kwastomas bata hana shi baccin ba. Yana zuwa hannu ya kai ya taSa wuyansa da goshi. Abin da ya farkar da Kamal Win da sauri don ji ya yi kamar"

an Wora masa ™an™ara. Tsigar jikinsa har tashi tayi ya buWe ido a firgice.

"""Happiness kaji jikinka kuwa? Tashi mu koma asibiti"" Taj ya ce yana kai hannu gefe ya Wauko masa"

wayarsa.

"Hamma Kamal Win yayi ""bacci ne fa. Bari na shige ciki na kwanta"" ya nuna nasa office Win."

"""Kada ka raina min hankali mana. Bacci ne yake kawo zazzaSi? Muje don Allah."""

"Wasa ya mayar da maganar ya ce ""Sai dai in kai ka. Dama na faWa maka yau Wanin motarka zanyi. A"

"adaidaita sahu ma na taho saboda son banza."""

"""In ka bari mu ka je asibiti Allah zan yarda mu yi musanye. Saboda na san kai mayenta ne na saya."""

Wani irin kallo Kamal ya yi masa. Taj is just selfless akan duk abin da ya shafi Kamal. Abubuwan da ya yi

masa iyayensu basu sani ba ba za su ™irgu ba. Ciki harda bashi jarin da ya gina boutique Winnan. Ya rufa masa asiri a lokacin da Alhaji ya bashi miliyan goma yaja jari. Allah Ya haWa shi da ´an damfara su ka wanke shi. Abu kamar rufa ido. Ya shiga ™uncin rashin sanin yadda zai tunkari Alhajin. Kawai sai Taj ya ce ya sayar da filinsa da su ka saya tun da daWewa. Filin da Mama take jira a fara gini. Filayen biyu su ka kama miliyan shabiyar. Ko ™wandala Taj bai karSa ba duk yadda ya so hakan. Ya kuma so ayi rubutu idan

ya samu zai biya nan ma Taj ya ce kyauta ce. Baya fatan har abada a sake tada zancen.

"""Tashi mana"""

Muryar Taj ta dawo dashi daga duniyar tunani. Mi™ewa ya yi cikin dauriya ya ce masa mura ke son kama

shi. Shi yasa yake zazzaSin.

"""Ni kuwa sai nake ganin kamar kana Soye min wani abu Happiness. Kwanakin nan kamar fa baka nan."

"Komai ni kaWai nake yi."""

"""You are married Happy. Ya kamata mu fara rage wasu abubuwan. Da banyi tunanin ba sai da Abba ya"

"ankarar dani."""

"Taj ya taSe baki ""yanzu zancen Mal. Sule har wani abin Wauka ne?"""

"""Ai kuwa dai ya fi mu gaskiya. Nan gaba kaWan sai kaji ana Malama hide my ID. Brother Win mijina kullum"

"suna tare. Ko unguwa zamu sai ya kira Wan uwansa. Bamu da wani lokaci irin na mata da miji saboda ya kankane komai. Don Allah a bani shawarar yadda zan Sullo musu ba tare da mijin nawa yaji haushi ba."""

Dariya sosai Taj ya yi.

"""Kamal mai malaman ig. Wato har salon tura sa™on ka iya. DaWinta dai ba Hamdi bace za ta yi wannan."

"Daga ji Doctor ce ta fara ™orafi. Tell her I'll make myself scarce in kun yi aure. Ayi soyayya lafiya."""

Daga nan sai zolayat juna. Kamal ya dage va zai je asibiti ba wai yunwa ma yake ji. Cikin Happy Taj su ka

"koma. Kamal ya yi odar shinkafa da gasasshen kifi. Kamar yadda Taj ya koyo, yawancin abincim Asia duk da hannu ake ci. Masu zuwa ko sun so gayu suna fara ci sai kaga an yi yadda yake a hoto da bidiyo da"

suke a lungu da sa™on wajen ana ci da hannu hankali kwance.

"""Kawo masa kaza"" Taj ya ce da waiter Win."

"""Ban gane ba. Ka dai sanni da kifi ko?"""

Wani article Taj ya nuna masa sannan ya tura masa a waya. A ciki anyi bayanin yawancin abincin dake

"kawo allergy. Akwai gyaWa da dangoginta. Kifi, kayan da aka sarrafa daga madara, ™wai, kantu da kayan"

fulawa.

"""Za ka daina cin duka. A hankali sai mu dinga gwada Waya muna gani. Wanda a kansa reaction Winka ya"

"dawo kaga mun san shi ne. Nima zan daina ci don ma kada ka ce mugunta na shirya maka."""

Yawun bakin Kamal Waukewa yayi. Ya shiga damuwa amma dole ya mayar da ita dariya. Sam baya

jindaWin Soye Soyen nan. Amma yanzu da zarar sun sani ™arshen duk wani farinciki na gidansu ya ™are.

Baya son ya zama silar daina walwalar kowa akan lafiyar da kuWi kawai ba za su iya saya masa ba.

Abincin da yake masa WanWanobda magani saboda rashin jindaWin abin da yake yi ya dinga tutturawa

harma yafi Taj ci.

***

Office Win an rubuta Dr. Kubra Hayatu a jiki. Wani private asibiti ne mai tashe na mata da yara da su ka

buWe ita da ™awayenta biyu. Wurin yana samon mutane fiye da zato saboda ™warewar aikinsu musamman akan mata. Zaune take tana harhaWa wasu takardu kafin ta fita don ta gama shift Winta taji bugu a bakin ™ofar. Umarnin shigowa ta bayar inda wani matashi ya shigo ya gaisheta. ˜aramin kwali da

aka yi wrapping ya mi™a mata.

"""Ban sayi komai ba. Bana tsammanin delivery."" Ta ce masa."

"""Ance na wani Kamaluddeen Hayatu ne amma ke ake so ki fara gani."""

"""Wa ya aiko ka?"" Ta tashi tsaye."

"""Idan kin duba ciki za ki gane. A tashi lafiya"""

Fita ya yi kafin ta sake yin magana. Ta Wauki kwalin taji babu nauyi sai Wan girma. Ta jijjiga taji abu kamar

magani. BuWewa tayi da sauri sauri. Sunayen magungunan da hotunan dake jiki su ka sa ta kusa yanke jiki ta faWi.

"""Kamal? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."""

Waya ta Wauka za ta kira Alhaji. Har ta shiga sai tayi saurin katse kiran. Duk yadda aka yi likitarsa ce ta

turo sa™on. Kuma da alama hakan yana nufin tana son ganawa da ita domin tayi mata bayanin da ya

dace. Kiran Alhajin ne ya biyo bayan nata. Ta Waga wayar a firgice.

"""Doctor yaya? Haihuwar Nabila (™anwarta mai ciki) ce ta tashi?"""

"""A'a Alhaji. Kira nayi mu gaisa kuma sai network ya katse kiran."""

Kwantar da hankali ya yi su ka taSa hira sannan ta tashi. Kao tsaye asibitin da Kamal ya kwanta ta nufa.

Aka sanar da ita Dr. Mubina sai litinin za ta zo. Nambar wayarta ta nema a reception Win aka sanar da ita

bata ™asar ne. Ta tafi Ghana amma ranar lahadi za ta dawo. Haka nan ta tafi cike da zulumi da fatan

gaggawar zuwan litinin Win.

***

Wato ´an gidan Alh. Hayatu gwanaye ne wajen son shagali. Duk abin da zai sa su taru a gida komai

™an™antarsa basa raina shi. Daga su har ´a´ansu. To iyayen ma dai ba a barsu a baya ba.

Akan maganar zuwan Hamdi sai ka rantse bikin ne ya taso. Mama ce ta kira Yaya ta nemi izini tunda har

yanzu a gida take. Bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta.

"""Suna na Haj. A'i kuma Mama a gida."""

"""Allah Sarki Hajiya. Da fatan kuna lafiya."""

"Da jindaWin yadda Yaya ta tarbeta Mama ta ce ""Alhamdulillahi. Allah Yasa Taj ya yi muku Wan bayanin"

"gidan namu."""

"""Sosai. Ya ce Hamdi surukarki ce ke da Wayar maman tashi ta Abuja."""

"""˜warai kuwa. To muna bada ha™uri tunda mace ita ya kamata a bi. Yanayin gidan namu ne Masha Allah."

"Muna da yawan da in muka zo za sai ´an unguwa sun fara tunanin ko biki ake baki gayyace su ba."""

Yaya ta kama dariya. Da alama barkwancinsu Taj ba a ™asa su ka Wauka ba.

"""Allah da gaske. Shi yasa mu ka ce gara ta zo. Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba. Ai kin"

"san wacce ce Inna a cikinmu ko?"""

"Yaya tayi murmushi ""na gane."""

"Mama ma dariyar tayi ""tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne. Ina fatan zuwan nata babu"

"takura."""

"""Wace irin takura kuma ku da abar ikonku? In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu'a."""

Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana. Taj zai Waukota bayan azahar.

***

Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta ta™ar™are tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan

Sajida.

"""Allah ™adiran ala mayyasha'u. Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin? Lallai Sajida rakiya tayo a"

"gidan nan ga ´ar so nan kin saka a gaba"" ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi ""kema ´ar rakiyar ce"

"ko za ayi miki?"""

Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo. Hamdi da Zee su ka yi ta dariya. Da ™yar Hamdi ta yarda

ake yi mata. Wai cikin mutane za ta je. Bata son a rainata ta. Zee ma nata kwaSin yana gefe. Ita kuma sai

yau Baballe zai zo. Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren. Yaya ta ce gara a ga ´a´an nata a

yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci. Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu.

"Falon ya bita ""dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira."""

"""Kankara kuma don Allah kamar wata faso?"" Ta faWi tana ´ar harararsa cikin wasa."

³a´an da irin wannan abu ba ba™onsu bane su ka tattara su ka barsu a falon. Zee ce ta™arasa mata ita

kuma ta yiwa Zee Win.

"""Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?"" Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lulluSin"

™aton zani kowacce ta zauna akan kujera.

"""Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba. In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida"

"gobe."""

"""Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce? Ni fa na rasa ma me zan ce. Haka kawai yanzu shige ds fice"

"na sai in bin wani bayan a gidanmu nake"" cewar Zee."

"""Na ma manta da tambayar. Zan dai gwada. In na kasa in rubuta a text."" Shawarar ta yiwa Zee. Ita ma a"

text Win za ta rubuta.

Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya. Jinkirin fita na Waya daga cikin

abubuwan dake saurin kawo saSani tsakanin ma'aurata. Ita dai nata to ne. Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida. Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana

son ji daga babbar yaya.

*

Biyu da kwata Taj ya iso. ˜ememe Kamal ya™i rako shi. Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda

shi a waje zai tsaya. Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi. Haka nan ya tafi yana mita. Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka.

Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama.

Ya juya a hankali su ka yi sa'ar haWa ido. Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa Winki irin na matasan zamani. Ruwan toka ne kamar kullum an ™aranta adon. Very classy and

elegant. Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi.

Ita kuwa cikin Winkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar Waurin aure. Riga da

siket ne mai adon ja da shuWi mara turowa ne a jiki sai ba™i. Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin

wannan. Light make up. Komai cikin tsari babu hayaniya. Tayi Waurinta a karkace kaWan ta Wora shuWin

mayafi daga rabin Wan™walin. Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a Waya. Šayan

kuma agogo ne na silver.

"""Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?"" Yaya ta ce da taga kallon ya™i ™arewa. Taj ya ma manta inda"

yake da alama. Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take.

Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu. Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfala™i.

Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai. A idonta dai

jeep ce tunda tana da tudu. Fara ™al da tambarin BMW a jiki.

BuWe mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai. Gilasan masu duhu ta kalla ta ™ara jin

wannan tsoron. ˜amshin daWin da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake. Taj na zama a

mazaunin direba ta kama kanta. Šan waigen ™auyancin ya ™are. Ya tada motar ya kunna AC sannan ya

fara ribas.

"""Šan tsaya."""

Hamdi ta faWi tana Wora hannu a ™irji.

"Burki ya taka da hanzari ""Me ya same ki?"""

"Idanunta har sun tara ™walla ta ce ""Gabana ke faWuwa wallahi."""

"""Saboda me? HaWuwa da ´an gidanmu?"""

Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi.

Yana son honesty Winta. Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce

"""Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?"""

"Tana jindaWin yadda yake girmama mahaifinta sosai. Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi ""na"

"sani ko ka fara yau. Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje."""

"""³ar ™auye zan ce miki ko matsoraciya? Amfanin wannan tint Win ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji"

"ya kamata..."" Wauke ido ya yi daga titi su ka kalli juna."

"""Ya kamata me?"""

"""Will you let me kiss you idan mun dawo? Ko yanzu in sami wurin parking?"""

"""Ya Taj???"" Idanunta su ka firfito."

"""Na'am. Ashe kin san suna na. Na zata Salman Khan za ki ce. Har na tanadi wa™arsa da zan miki."" Ya yi"

maganar yana dariya.

Bakin tsiwa ya mutu murus. Ya Wan kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo. Shi da ya tsammaci ta

bashi amsa.

"""Hamdi? Yaya? ZazzaSin ne yau ma?"""

"""Uhmm"" ta gyaWa kai harda shafa wuya da goshi."

"""Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai."""

"""Allah da gaske nake. Jikina babu ™wari ma."" Ta Waga hannu ta sake shi yaraf."

"""Kinga mun kusa zuwa gidan. Ki rufa min asiri yanzu don za ki haWu da ´an jarida masu tambayar tsiya."

"Akwai ´an bugun ciki ma waWanda za ki iya faWa musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba."""

"A tsorace ta ce ""da gaske?"""

"""Da wasa"" ya furta a hankali yana yi mata murmushi."

A bakin gate Win wani ™aton gida taga sun tsaya. Ya Waga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso.

"Tsoron nan bai barta ba ta ce ""ba za ka shiga ba?"""

"""Alhaji bai yi min izini ba."" Ya amsa mata da murya mai rauni."

Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka.

"""Kada ki Sata min kwalliyar nan tun kafin na biya kuWinta don Allah."""

"""Ni ba don kai nayi ba"" ta ce da tsiwar nan."

"""Mala'iku suna jin ki dai."""

"Da sauri ta ce ""Astagfirullah."""

Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi. Hannunta mafi kusa dashi ya kama

ya sar™e yatsun ya lan™washe su.

"""Wa ki ka yiwa kwalliyar? Suna ji dai kada ki manta."""

Tsuke baki tayi tana jin yadda Wumin hannunsa ke shigarta. Ita kam ta shiga uku. Wannan aure ta son ya

Wore. Allah na tuba ta faWi a zuci.

"""Hamdi?"" Ya Wan matsa hannun."

"""Kai na yiwa"" murmushi ya soma yi ta ™ara da cewa ""amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi."""

"""Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki..."""

Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki.

"""Kaga fa Ya Kamal ya fito."" Ta kalli gate Win a firgice."

Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya ri™e shi da Waya hannun.

"""Idan ya ™araso sai na ce ya tayani ro™onki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long."""

Kamal har ya ™araso. ˜wan™wasa gilas ya yi ta Sangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas Win ™asa.

"""Happiness ta™i yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar"

"sako min ita."""

Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake ri™ewa.

"Kamal dariya yayi kawai ""Mrs Happy haka za mu yi dake?"""

"""Shi za ka zaSa?"""

"""Da me kike tunani? Ya zaSeki a kaina?"""

"""Naga wai ni ce ™arama"" tayi kicin kicin da fuska."

A take Kamal ya canja she™a.

"""Happy buWe mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can."""

"""To wallahi tayi al™awari a gabanka"" Taj ya sha kunu da ya yi maganar."

"""Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira."""

"""Nayi."" Ta faWa don idanun ´an uwan su biyu sun hanata sakat."

Sama Taj ya yi da gilas Win ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma

ranta don kunya.

"""Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan"

"an Sata miki rai ki fara faWa min kafin su Abba. Zan baki ha™uri a madadin ko waye. Kin ji?"""

Murmushi tayi har zuci. Ta Wan matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita.

Kamal na buWe gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana.

"""Ya Kamal basu iso bane?"""

Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata

amarya.

"""Salwa? Saukar yaushe?"" Ya ce babu wani jindaWi a tare da tambayar."

"""Šazun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo"

"gaishe da su Hajiya."""

"""Gata ku gaisa."" Ya faWi yana kallon yadda shigarta gabaWaya ta saSawa sanin da ya yi mata a baya."

"""Sannu amarya."" Ta ce tana yin gaba ""bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito."""

Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buWe ™aramar ™ofar gate Win ta fita.

Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta.

RAYUWA DA GII 22

Batul Mamman

"This page is sponsored by _Scentmania_ by Sana. A Kano take, amma ™amshi babu ruwansa da gari ko"

"™asa. Wuyarta ciniki ya faWa. Za ku sami undiluted oil perfumes Winku a duk inda ku ke. Bayin Allah babu cika baki. Talla ne daga abin da na gani, na gwada kuma na amince dashi. Gashi babu ruwanki da jiran sai asusunki ya cika ya tumbatsa kafin ki shiga jerin mata masu aji. Da dubu biyar ma za ki haWa kwalabe daban daban ki gigita waWanda ya halatta su ji ™amshin jikinki da yawan tambayar wane irin turare ne wannan.

26 / 42