Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   19 / 42

54K to 57K   out of 124.8K words

kada na saSawa Allah akan soyayya..."""

"""Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faWawa waWannan maganganun?"" Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin"

nauyi.

"""Ina sonta Alhaji."" Ya faWa kai tsaye abinsa."

"""Ita ´ar Habibun?"""

"""Eh."""

"""Zo ka zauna"""

Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daWe yana tunani kafin ya

"ce da Taj,"

"""Ka tafi gida ka jirani."""

"""Gidan Yayan za ka zo?"" Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi."

"""Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani."""

Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai bu™atarsa ita ce ya sami damar yin

auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Ha™uri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda

za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuWi.

*

Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba

"Habibu. Kafin isha'i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ´arsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faWa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ™arshe yadda ya fahimta wanda kuma da ™amshin gaskiya a ciki, auren ragewa"

Habibu ba™inciki Taj yake son yi.

Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaSi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai

nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.

*

Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A

gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.

"""Wace tsiyar ka ™ulla?"""

"""Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa."""

"A harzu™e Kamal ya ce ""ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. ˜arshenta ma harbeka zai yi."""

Taj ya ™yal™yale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj Win ne matsoraci.

Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A

gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.

"""Šanka ne ya Wauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe."

"Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana."""

Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.

"""Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a Waura."""

Godiya mara adadi Taj ya yi masa.

"""Ba sai ka faWawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da"

"kaina."""

"Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana"

biyu yasa bai ji ko War ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.

***

Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters' eve. Yau

shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ´an biki babu walwala sai

kowa ya sha jinin jikinsa.

Banda ´an mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar Waurin auren sai ´an uwansa maza. Su

duka mamaki bai hanasu haWuwa a masallacin juma'ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal

ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tu™osu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa

tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan Wanyan kai na Taj. Alhaji ba zai

barshi ya sha ba.

Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar Waurin aure kamar yadda aka faWa masa. An fara da Abubakar

Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya auki

kabbara.

Abba yana share ´ar ™wallar farinciki sai yaji an taSo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh.

Hayatu. Ba ™aramin ruWewa ya yi ba kuwa.

"""Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin"

"aurenta."""

"Abba baki ba rawa ya ce ""Yaya Hayatu..."""

"""Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta."""

"""Hamdiyya."""

Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faWawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka

sake sanarwa. An Waura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu

Wari biyu.

A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa

Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya Wuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.

"""Ni ne mahaifin Sabi'u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka ha™ura da abin da ya faru jiya"

"wanda bani da masaniya. Sai Wazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan Win ya yi min bayani."""

Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya Waura aure na uku. Safwan Sabi'u

Mamman da Sajida Habib Umar.

Allahu Akbar

Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.

RAYUWA DA GII 17

Batul Mamman

***

"""Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshi a ™asa a mi™a"

"godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ´an matanki a sa'a guda. Wannan farar juma'a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ´an dugwi dugwi iyalan Baba."""

Ba kowa bane da wannan aiki sai ³ar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka

amshe guWar su na yi. Yaya fitowa tayi daga Wakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.

Anti Zinatu ce kaWai ta san zaman me su ke a Wakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa

kaWai ke iya maganinsa.

Hamdi na jin muryarsa ta haWe rai bayan fitar Yaya daga Wakin.

"""Wai namiji kenan. Mtsewww."""

LulluSi Yaya tayi ta fita soron. ³ar Ficika ya wangale baki.

"""Sai muka ji abin arzi™i ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne."""

Ita ma takaicin Waga muryar tasa take yi. Ga za™in murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa

na jinsu a ciki.

"""Da ka Wan rage maganar saboda ´an biki ba su san auren Zee aka Waura ba maimakon Sajida. Sannan"

"kana cewa amare uku sai ayi zaton..."""

"""Ba zato bane Jinjin. ³a´an Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya"

"aurar dasu lokaci Waya."""

Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haWawa da wani. Sai kawai ta koma

ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.

"""Shirmen ³ar Ficika ne. Shi da ko wurin Waurin auren basu je ba?"""

Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ™arfinsa

saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma'ar unguwarsu har gida. Tafiyar

kimanin minti talatin. ˜afafunsa sun yi buWu buWu.

"""Yaya! Yaya!!"" Ya dinga ™wala kira kamar makaho na neman Wan jagoransa."

"""Kai Halifa lafiyarka kuwa?"" Wata ma™ociyarsu ta tambaye shi."

"""Ina Yaya?"" Ya faWi yana dariya."

"Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya"

tsallaketa ya rungume Sajida.

"""Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu"" cewar Inna Luba."

Murmushi ya yi yana duban ´an uwansa.

"""Yaya an Waura. Duka su ukun an Waura musu aure."""

Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.

"""Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?"""

"""Ya Sajida da Yaya Safwan."""

"Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna"

"sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa ""Alhamdulillah."""

"Anti Zinatu ta ce ""Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku."""

"Ya murmusa da farincikinsa ""a'a, sai Ya Hamdi da Happy."""

"Inna Luba ta ware idanu a tsorace ""Hafi? Mutum ne?"""

Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.

"""Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu."""

Cikin Hamdi wata irin ™ullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da

haka danne shi tayi da hannu biyu.

"""Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?"""

"""Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa Wansa aurenki."

"Sadakinki fa dubu Wari biyu. Cash in faWa miki."""

Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun

wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.

"Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa ""Ku ri™eta...Sajida kama hannun. A'a"

"rungumota kawai kada ta kai ™asa."""

Luuu haka taji ™afafunta suna narkewa su kaWai za su kaita ™asa. Kafin ta gama faWuwa aka tallafota

zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba.

***

³an uwa da abokan arzi™i dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al'amura su ka

kasance ma™iyi ne kaWai zai ce bai jidaWi ba.

"Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin"

da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ´arsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ™o™arin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ™yasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba.

A Sangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ´an uwansa. Kawunnai ne na Sangaren

"Alhaji shi kaWai sai ´an uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faWawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake"

´an uwansu maza da dukkanin abokansa.

Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. ˜aninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin

motocinsu.

"""Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?"""

"""Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?"" Ya amsa a wula™ance"

Daga nan gaban Taj ya faWi. Su ka haWa ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba

kuwa haWe rai ya yi.

"""Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar"

"dani jiya a ™urarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo Waurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi."""

"Alhaji ya yi murmushi ""bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar"

"al'umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina."""

Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko'ina ba ya gane shigo-shigo

ba zurfi Alhaji ya yi masa.

"""Alhaji don Allah ka tsaya"" Ahmad ya ro™e shi don baya jindaWin ganin manya su na sa'in'sa."

"""Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?"" Ya nuno Abba"

da yake tahowa inda suke da ´an abokansa.

Abin ban sha'awa babu Wan daudu ko Waya. Dama su ³ar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin

Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su Waurin auren ba don kada a sake samun matsala.

Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya mi™awa Yaya Babba gami da rissinawa

sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri.

"""Yaya barka da rana?"""

"Fuskarsa shi ma a sake ya ce ""Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai."""

"Abba ya murmusa ""ina ni ina surukuta da ku Yaya? ³a taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa"

"gida."""

Ragowar ´an uwan Alhaji su ka ™arbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buWe musu hanya. Ransa fari

™al ya sake rissinawa ya mi™a hannu ga Alhaji.

"""Yaya Hayatu ..."""

Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ™arfin a kira shi na wula™anci. Sai dai a ce ™as™anci. Domin ba ma da

duka ™wayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama

lalacewa da bleaching ba. Knuckles Win (gaSoSin yatsu) duka ba™a™e ™irin. Ragowar hannun kuma fari da Wigo Wigon ba™i.

Yawu mai Waci Taj ya haWiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun

kawai ya mayar ya ™ara du™awa.

"""Barka da rana."""

"""Kaga tashi don Allah. Bana son wannan Wabi'ar taku ta gaisuwa kamar maro™a."""

"""Alhaji"" Taj ya kira sunansa da Wan ™arfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me"

yake aikatawa a gaban mutane.

Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai.

Ba tare da nuna Sacin rai ba Abba ya mi™e yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu.

Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa.

"Alhaji ya ce ""Ina son ganinka yau bayan Isha'i. Ai ka san gidana ko?"""

"""Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu."""

"Alhaji ya yi irin murmushin nan na Sacin rai. Yana magana ciki ciki ""na manta yanzu kai ne uban. To kada"

"ku wuce Isha dai."" Ya kalli Taj ""kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne."""

Mota ya faWa abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana Wagawa motar hannu tare da faWin

"""Allah Ya kiyaye hanya."""

"Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje ""Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake"

"nema."""

Sai da ya tafi ´an uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda Sacin rai. Ya dai

dinga gyaWa kai kawai. Yaya Babba ne ™arshen yi masa magana.

"""Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya"

"zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaWinsa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba."""

Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi.

"Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa ""mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan."

"Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani."""

Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ™ullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina

damuwa.

"""Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?"""

"""Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za"

"su Saci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haWu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka"" cewar Abba wani sarkin"

zuciyar.

"Bishir Wan salihin cikin mazan ya ce ""Šauko sun dai ya dace ayi su haWu a gidan Yaya ko gidan Yaya"

"Babba."""

Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ™urewa kuma ba su sami matsaya ba.

"""Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaWai"

"ne sai mu je mu yi musu bayani."""

Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A

hanya Ahmad Win duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran

sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka

kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haWu su je gida wuraren biyar na yamma.

*

"Kamal na tu™i ya Wan kall Taj ""Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban"

"jama'a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wula™anta Abba."""

Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya.

"""Me yasa idan na zo da abu baya bani zaSi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya Wauki hukunci mai"

"tsauri a kai."""

"""Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka ha™ura"

"da gaggawar nan amma ka ™i."""

"""Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma"

"ya Wora laifin naka a kaina."""

"Kamal ya haWe gira ""akan me zai Wora maka?"""

"""A dalilin kafi kowa kusanci dani mana."" Taj ya bashi amsa."

Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma

mamakin da ya ™yale shi ya buWe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba.

Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi.

"""Happiness, ba fa zan bari ya wula™anta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai"

"tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin."""

Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun

ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen.

"""Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaSar wanin mahaifinka."""

Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa.

"""Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taSa bani zaSi ba. He just pushes me away and gets angry"

when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faWa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni.

"Da cewa ya yi in zaSi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taSa barinku ba. Ba don Amma..."""

Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya dam™i hannun

daman Kamal dake ri™e da sitiyari tunda yafi kusa da shi.

"""Kamal...ya zan yi? Amma.

19 / 42