Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Rayuwa DA Giɓi Complete Hausa Novel by BATUL Mamman

Author :  BATUL MAMMAN Category :  African Stories & Novels

Chapter   17 / 42

48K to 51K   out of 124.8K words

zaton zamu iya gamawa da anyi magariba."""

"""Bari na kira Kamal ko sun gama. Motarsa ai za ta ishe ku ko?"""

"Abba ya yi dariyar jin ana tambayarsa ko mota za ta ishe su ""Adaidaita Waya ma yana isar mu. Zee a sama,"

"Halifa a kusa da direba. Mu uku a tsakiya."""

"""A sama kuma? Saman nan dai na bayan seat?"""

"""Eh mana."""

"Abin Waure masa kai ya yi ya ce ""Ninke ta za ayi ko lan™wasawa?"""

Abba ya dinga dariya. Har su ka gama Taj na mamakin zancen zaman sama. Da su ka fito sai yaga har

gara wurinsu. Boutique Win Kamal ya cika da samari da ´an mata. Mu™ullin motarsa ya karSa ya ce masa zai kai su Abba gida.

"""Za ka iya dawowa kuwa?"""

"""Me ka mayar dani ne? Zan dawo mana."""

"Kamal ya yi dariya ""a dinga haWawa da in sha Allahu dai."""

Da ya fita shima Abba tambayar da ya fara yi masa ita ce ko zai gane hanyar dawowa. Ya nuna babu wata

"matsala sai su ka tafi. Abba na gaba, ´a´ansa na baya. Hamdi tana ta faman kumbure kumbure don ita bata son ma a gaba ace suna cin arzi™i."

Waya Abba ya gama da Yaya ya sanar da ita suna hanya. Ya duba missed calls.

"""Ashe kin yi ta kira bayan wadda na Wauka Hamdi? Ban ji ba ne."""

"""Ai Abba ™iris ya rage ka fito kaga tana kuka. Ka san yadda bata son zuwa taro."""

Saurin kallon madubi Taj ya yi kamar ta sani kuwa ita ma ta kalla. Maimakon taji kunyar ™aryar da tayi

masa sai ta juya idanu ta murguWa baki.

"""Kin yi kyau."" Ya furta idanunsa har lokacin a kanta ta madubin."

"""Wa?"""

Abba ya faWi yana kallonsa. Su Sajida ma duk sun zuba masa ido su na jiran amsa.

"""Wata mota ce ta wuce yanzun nan. Ba don motata ta kusa isowa ba da ita zan saya."""

A haka zancen ya mutu. Lokaci lokaci suna haWa ido ta madubi tana harararsa. Sai bai damu ba. Zuciyarsa

tana raya masa tabbas ya yi mata laifi ne. Laifin da yake ganin ba zai wuce na rashin nuna mata ya santa ba lokacin da su ka haWu a Abuja.

Ya kai su gida lafiya amma komawa ta gagara. ˜arshe sai Abba ya kira saboda rashin dacewar neman ´an

mata sha Waya da rabi na dare. Da kwatancem Abban ya fita daga unguwar. Yana tafiya a hanya yana nanata 'in sha Allah ba zan kuma Sata ba.'

***

Satin farkon buWe Happy Taj lokaci ne da Taj da Kamal ba za su taSa mantawa dashi ba. Sun sami ciniki

da yawaitar al'umma fiye da tunaninsu. Taj gani yake hakan ba ya rasa nasaba da addu'ar da Alhaji ya zo ya yi musu daren da za a buWe wajen. Da kuma ta iyaye. Sai kuma saukar karatun da su ka yi shi da Kamal da sadaka domin neman Allah Ya sanya musu albarka. Kuma Ya tsaresu da wurin kansa daga zamewa

al'umma fitina.

Duk da ya yi sanarwar gama Waukan ma'aikata to amma fa har lokacin mutane basu fasa kawo takardun

"neman aiki ba. Ya rufe ido ya ™ara Waukar masu shara da wanke toilets. Da kuma masu wanke-wanke da shara. Irin aikinka, irin uniform Win da za a Winka maka da suna idan an Wauke ka. Bakery ne kawai ya bar space Win Hamdi. Da gaske yana son yin aiki tare da ita. Ya yabawa iyawarta sannan yana kusancinsu zai taimaka masa ya sami soyayyarta."

Baya son yin garajen fara nuna mata soyayya a yanayin da ake ciki. Bai san yadda Abba ma zai Wauki

maganar ba don ya kula yana da gudun rigima. Balle kuma Alhaji. Idan ya ™yaleta haka kuma tabbas zai ji

"labarin wani ya yi masa shigar sauri. Da wannan shawarar ya tunkari gidan ranar wata lahadi, ana saura kwanaki huWu kamun Sajida."

Cikin gidan ya fara shiga su ka gaisa da Yaya. Bayan sun Wan taSa hira ya tashi ya ce ta turo masa Sajida.

Kuma sarai ya san Sajidan bata nan. Tun zuwansa aka ce tana wajen gyaran jiki. Zee kuma ta tafi karSo

Winki.

"""Daddawar Waka ce kawai a gidan."""

"Kamar bai san wa take nufi ba ya ce ""gaskiya a ™annena babu daddawa."""

"""Ashe baka san Hamdi ba. Kana kallo dai tun shigowarka ta shige Waki. In ba kiranta nayi ba kuma da"

"wuya ka sake ganinta har ka tafi."""

Daga Wakin Hamdi ta zumSura baki da kwance zanin da Yaya take yi mata.

"""Sai ki fito don na san kina jina."" Yayan ta Waga murya."

Taj bai ji ta amsa ba har ya isa zauren ya tsaya. Ya sa rai za ta jima sai gashi bai fi minti biyu ba ta fito.

Bakin nan a gaba.

"""Kya hua Hamdiyya?"" Ya zolaye ta."

Shi yake yaren ita take jin kunya.

"""Ba na jin indiyanci."""

"""Na ga mata suna son movies Winsu. A nan ku ke tsintar kalmomi. Sisters Wina dai na san haka su ke."""

"""To banda ni. Ba na kalla. Kuma namiji mai gani ma ba kula shi nake ba."""

"""Allah Ya so ni kenan."" Taj ya ce yana neman haWa ido da ita amma ta ki yarda."

"Mamaki ya bata don bata yarda da furucinsa ba ta ce ""Ba ka gani?"""

"""Ko Salman Khan Win da ki ka kirani rannan ban sani ba."""

"""Allah ban yarda ba"" ta ce kai tsaye."

Taj ya yi dariyar da amonta ya zauna daram a zuciyarta. Bata sani ba ko ana kiran maza cute. Ita dai da

yana dariyar nema ya yi ya sauke mata bangon da take ginawa a tsakaninsu. Shammatarta da ya yi da tambayar da fito daga bakinsa ce ta yanke mata shagalar da ta so yi.

"""Laifin me nayi miki ne da ya zamana tsakaninmu babu kallon kirki sai harara? Ko don ban faWa miki na"

"san ki ba a Abuja?"""

Shiru tayi. Ya sake maimaita tambayar amma sai ta kawar da kanta. Bai yi fushi ba ya ajiye girma da

matsayinsa ya faWa mata abubuwan da su ka wakana tun lokacin da Firdaus ta faWa masa sunanta da biyota gida da ya yi.

"""Dalilinki na zo gidan nan amma yanzu ba don ke kaWai na nemi kusanci da Abba ba. Ina ji a jikina zamu"

"amfani juna in sha Allah."""

Kasa magana tayi. Sai tunani da yawa da take fama dasu. Da yaga tayi shiru ne ya nemi jin ta bakinta. Sai

ta faWi abin da bai taSa tsammani ba.

"""Da Abbanmu ya rasa wajen sana'arsa nayi murna ni dai. Na so ace wata sana'ar ya samu ba komawa"

"girki ba."""

Taj yaji tamkar ta watsa masa ruwan zafi.

"""Kema ba kya son namiji mai girki ne? Ko kuwa wanda ya taSa rayuwa irin ta Abba?"""

"""Mene ne maraba? Duk namijin dake girki ba Wan daudu sunansa ba? Har yanzu ba sunan da ake kiran"

"Abbanmu kenan ba saboda ya™i yin wani aikin sai na mata."""

"""Daina magana irin haka Hamdi"" Taj ya kwaSeta ""yanzu har za ki iya aibata sana'ar da mahaifinki yake yi"

"miki komai cikinta kuma wadda Allah bai haramta ba?"""

"Kuka ta saka masa ""Baka ji muryarsa ba? Idan yana tafiya meye marabarsa da ma..."""

"""Ya isa..."" ya kaWa kai yana mamakinta ™warai da gaske ""indai za ki iya waWannan maganganu akansa to"

"waye a waje ba zai yi ba? I thought idan kowa ya ™yamaci mahaifin mutum shi yana son abinsa."""

"""Nima ina son sa. Amma wallahi bana son sana'arsa."" Ta kalle shi ido cikin ido ""kuma bana son duk"

"wanda zai taimaka masa akan cigaba da sana'ar girki."""

"Tunowa da Alhaji ya dinga yi da kalamanta masu Waci. Cikin Sacin rai ya ce ""nima ban ce ina son ki ba. So"

"kada ki yarda ki min rashin kunya akan sana'ata. I am a Chef and I love what I do."""

"Bata san ta Waga murya ba ta ce ""to wa ya hanaka dama? Meye na sanya Abbana a ciki?"""

A ganinsa bata ma cancanci ya faWa mata kuWurinsa na taimakawa Abba ya rage ko bai daina duka

"abubuwan mata ba. So yake ya nuna masa zai iya sana'arsa cikin nutsuwa ba tare da ya yi koyi da mace ba. Shi yasa ya Wauki ri™a™™un maza waWanda ko magana su ka yi sai an san namiji ne na gaske aiki. Girki daban, daudu daban. Wannan abin yake so hausawa masu fahimta irin ta Alhaji da wannan mara kunyar"

yarinyar da yake jin soyayyarta har yanzu su gane.

"""Saboda na isa."" Ya faWi don taji haushi."

"""Me kake nufi? Abbana yaronka ne?"""

"""Uba na Wauke shi mai sawa ya hana. Wanda kuma da ni ya haifa ba zan guje shi ba."""

"""Na ce maka ina son Abbana. Girkin ne bana so."""

"Ya zata yi ya fahimceta? Indai Abba bai daina sana'arsa ba, gani take ba zai taSa rabuwa da Wabi'un da ya"

"koyi girki cikinsu ba na daudanci. Idan mutum yana abu maras kyau a ganinta nesanta dashi, shi ne yafi alkhairi."

Shi kuma Taj so yake ta gane cewa sana'ar ba ita ce ta mayar dashi haka ba. HaWa biyun da mutane su

"ke yi, shi ne musabbabin da yasa mazan dake son girki da dama a ™asar hausa su ke karkacewa su yi koyi"

da jinsin mata. A ganinsu kamar girki ba zai cika ba sai da waWannan Wabi'un.

Ran kowa a Sace su ka rabu. Don ko amsa bai iya sake bata ba ya fice abinsa. Ita kuwa tana shiga gida

taji saukar lafiyayyen mari daga wajen Yaya.

"Huci take rai a Sace ""ki ka ce ba ki son duk mai taimakon mahaifinki akan sana'arsa Hamdi? Saboda kin"

"tashi duk runtsi duk wuya bai taSa ™in kawo abin da za a ci a yi sutura ba? Ashe baki dawo daga rakiyar zuciya ta ™yamar babanki ba?"""

"Hannunta akan kumatu tana jin zafi har ranta ta ce ""Yaya ku daina yi min irin fahimtar nan. Ina son Abba"

"mana. Girkin ne kawai...Yaya har yanzu muryar mata gare shi fa"""

Sai kuka mai cin rai. Yaya ma kukan take yi. Duk cikin ´a´anta dama kafiya da sanya abu a rai babu

"wanda ya kai Hamdi. Kowa na zaton rigimarsu da Ummi ta kashe mata waccan ™iyayya. Ashe har yanzu bata son sana'ar. To amma wacce take so ya yi? Bayan mutane suna da wuyar uzuri da ™arSar kuskure. A yanayi da Wabi'unsa, duk inda ya sanya ™afa neman taimako ko son fara sana'a sai ace Wan daudu ne."

Girkin ne kaWai idan ya yi sai an bishi an saya. Da shi kaWai yake tsaye a ™afafunsa. Banda wauta da ™uruciya me zai sa ta ´arsa ta zauna ta faWawa wanda ya killace mata uba daga gaban murhun da kowa yake ganinsa a da. Yanzu sai ya gama ya dawo iyakarsa kitchen. Ba a ganshi ba balle ma a aibata shi.

Kuma saboda duka kitchen Win maza ne har ya fara ™o™arin gyara tafiyarsa.

"""Kin bani kunya wallahi."""

"""Yaya..."""

"""Tashi ki bani wuri."""

Šakinsu ta shiga tana kuka kamar ranta zai fita. Soyayyar da take yiwa Taj ta Wauki sabon salo. Haushinsa

kawai take ji. Ba ma ta son shi. Kuma ba za ta taSa son nashi ba.

"""Aikin banza. Meye abin burgewa a namiji mai girki? To da me matarsa ma za ta burge shi?"" Ta ayyana a"

ranta duk cikin kukan.

Shi a ranar kasa gane kansa aka yi a Happy Taj. Da yaga komai ™an™antar abu sai ya yi faWa sai ya koma

office Winsa kawai ya rufe ™ofa. Kan 3 seater yaje zai kwanta ya tuna Hamdi ta taSa kwanciya a kai sai ya tashi yana tsaki.

"""Ashe yarinyar nan bata da kunya? Na iya ha™ura ma da Alhaji ya koreni balle wata ™aramar yarinya?"""

Daga inda suke kowannensu ya dage yana sauke fushinsa ta hanyar ™ara faWawa zuciyarsa girman laifin

Wayan. Shi dai Taj baya son wadda ta kasa ganin ™o™arin mahaifinta a matsayin da Allah Ya ajiye shi. Ita

kuma Hamdi gani take tsabar mugunta ce ma za ta sa ya cigaba da ingiza mata uba akan hanyar da babansa ya kore shi a kanta.

***

An yi Kamun Sajida ranar laraba cikin farinciki da taron dangi. Hamdi tuni ta ajiye wani Taj ana ta sha'ani.

Wannan karon ko ciwon kai bata ce tana yi ba saboda tsananin farinciki. Sajida ta sami wanda take so kuma yake sonta ba tare da ya taSa goranta mata ba. Damuwar su Yaya da tsoron ´an matansu ba za su

auro ba ta kau. Komai nasu na rufin asiri sun yi domin fitar da juna kai kunya.

Alhamis aka yi sisters' a wani event centre. Ranar dai har rawa Hamdi tayi tunda taron mata ne. Sai da

Anti Labiba ma ta janyeta saboda ko gajiya bata yi. Ana canja kiWa take komawa.

"""Wannan ko ke ce amaryar sai haka."""

"Wata ´ar uwarsu ta kare mata ""barta tayi. Ranar nata auren ai ba yi za ta yi."""

*

Ana can ana shagalin biki wasu motoci biyu masu kyau su ka yi parking a ™ofar gidan Abba. A tsaye yake

da Kamal da Taj. Kamal ne ya zo bashi tashi gudunmawar wadda ta kasance ta kayan abinci. SaSanin ta Taj da ya bashi kuWi. Yana ta cewa sun yi yawa da almajirai na kaiwa cikin gidan waWannan motoci su ka

tsaya.

³ar Ficika ne ya fara fitowa daga motar gaban yana murnar ganin Abba a ™ofar gida.

"""WaWannan mutanen ne su ka zo nemanka nace musu ai ka tashi daga wurin. To sai..."" ya juya ya nuna"

"wani Alhaji da ya nufosu yana takawa kamar baya so ""wannan Alhajin ya nemi in kawo shi wurinka. Har za mu je restoran Win sai na tuna Wazu ka ce min kana gida."""

"Abba ya yi murmushi ""ai da ka sa wani ya rako shi ma."""

"""Yaran nawa duk basu san nan Win ba."""

Abba ya mi™awa mutumin hannu domin su gaisa sai ya ™i Waga nasa. Kallon wula™anci kawai yake yiwa

Abban. Shi da ragowar mazan da su ka firfito daga motocin har su biyar.

"""Kai ne Habibu Simagade?"""

"Abba ya Wan murmusa ""a da kenan."" Ya kuma mi™a hannun mutumin bai karSa ba dai."

"""Ni ne uban Safwan mahaifi."""

Mamaki ya bayyana a fuskar Abba. Tabbas ga kama nan. To amma ba wani abu bane tunda da ana

neman aure kawunnansa ne su ka zo.

"""Allah Sarki. Bari nasa ayi shimfiWa a ciki."""

"""Barshi. Zuwa nayi na faWa maka cewa idan ka kuskura aka Waura aurensa da ´arka gobe sai na Waure"

"duka mutanen gidan nan."""

"""Alhaji me ya faru?"" Abba ya ce da fargaba. Taj da Kamal ma hankalinsu tashi ya yi."

"""Meye ma bai faru ba? Ya faWa min yana son wata yarinya nasa aka bincika aka ce ubanta Wan daudu ne."

"A ranar na soke maganar. Shi ne ya haWa kai da wan uwarsa aka zo aka nemi aure da komai a bayan idona. Suna ta Soye Soye basu san na sani ba. Dama bari nayi sai goben in ci muku mutumci duka a wajen Waurin auren. Sai yayansa ya shiga maganar"" ya nuna babban Wansa ""shi yasa na zo yau. In kun je"

"an Waura za ku ga abin da zai faru. Zuriata tafi ™arfin haWa jini da irinku. ata gari, lalatattun mutane"""

Banda Innalillahi babu abinda Abba ke faWi. ³ar Ficika kuwa ihu ya saka kamar mace yana ta jan

jallabiyarsa sama yana tumamin wai sun shiga uku.

Baban Safwan ya kalle shi cikin takaici da ba™incikin anyi asarar namiji. Ha™uri Abba ya fara bashi ya

dakatar da shi. Kamal da Taj su ka saka baki ya ce babu ruwansu. Ba su yi aune ba Abba ya dire

gwiwoyinsa a ™asa zai fara ro™o mutumin ya juya abinsa bayan ya yi tsaki.

"""Alhaji ka yiwa Allah kada ka hana auren nan."""

Da sauri Taj ya kama hannunsa zai Waga shi amma ya™i mi™ewa.

"""Abba don Allah ka tashi."""

"""Idan auren nan bai yiwu ba gabaWaya gidana laifina za su gani. Sajida bata taSa saurayi ba sai akan shi."

"Sun saka rai Taj, kowa ya saka rai. Duniya za ta zage ni. Duniya za ta min dariya.."""

"Babu wani tunani ko hangen nesa Taj ya ce masa ""Abba indai ka amince za ka bani Hamdiyya, in sha"

"Allahu gobe za ka aurar da ´a."""

"""Taj?"" Kamal ya kira shi gabansa na faWuwa."

"""Ina son ta Abba. Saboda ita na zo gareka."""

Abba Habibu rasa bakin magana ya yi. Ido kawai ya zubawa Taj har motar baban Safwan ta bar layinsu

bai sani ba.

RAYUWA DA GII 16

Batul Mamman

_Ya Rabbi. Ya Zhuljalal wal Ikhram. Allah ´a´anmu sun koma makaranta. Ka duba mana su da dukkan

"abokan mu'amalarsu da sauran ´a´an bayinKa. Ya Allah Ka tsare su daga dukkan sharri. Ka kare su daga zamewa kowa sharri. Allah Kada a kai ™ararsu, kada su kai ™arar wani. Ka basu ilimi mai albarka da amfani. Kasa aci moriyar abin da ake nema na boko da addini. Ya Sami'ud du'a Ka fimu sanin mawuyacin halin da ™asarmu take ciki. Ka horewa iyaye abin da za su ciyar da iyalansu daga halali. Ka makantar"

damu akan haram. Duk uzurin da zai taso Ya Allahu kada Ka sa mu ro™i kowa. Ka buWa mana. Ka albarkaci

nema da samun mu. Ya Rabbi Ka kawo mana sau™i da sassaucin rayuwa. Ka azurtamu daga taskarKa

wadda bata da iyaka. Amin_

***

Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ™auna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya mi™e tsaye

ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.

"""A duniya bayan iyayena da matata da kuma ´an uwana da ba su guje ni ba da kuma ™alilan cikin abokai,"

"kai ne mutum na farko da jini bai haWamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata."""

Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da Wanyen aikin da Taj ya Sallo.

"""Abba..."""

Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.

"""Kada ka damu Kamal. Ba zan taSa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu"

"ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ™ara nesanta uba da Wansa ba."""

"Daga Taj har Kamal ba ™aramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,"

"""Abba, Alhaji ya daWe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai ..."""

"Kamal ya katse shi da hanzari ""wallahi zai ™ara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su"

"Inna ne?"" Ya mayar da idanunsa ga Abba ""ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba."""

Abba jinjina zumuncin ´an uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faWa musu.

"""Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko sha™i™an da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba."

"Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida ha™uri. Na san za ta yi min uzuri."""

"""Sai dai idan ni ne baka son bawa ´arka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta."""

"""Har a yaushe ka santa?"" Kamal ya tambaye

17 / 42