Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
da na tabbatar na rainin hankali ne. “Ba wani aurenka da
zan yi, ce maka aka yi ni kuma kwantai zan yi da zan auri Mijin wata, ragowar wata
Allah ya kiyaye Mijina zan samu Wallahi nima dallele na aura…” na furta ina huci
kamar wacce ta yi tsere. Murmushi ya saki yana yamutsa fuskarsa ya furta “Allah ko?
Amma dai kin san ba zaki samu wanda ya fi ni ba… Idan haka kika zab’a Ai shikkenan,
ina fatan ita dai kin ganta idan bata fi ki ba, ke ba zaki fita ba…” Ya ‘d’au key
d’insa yana furta ki turo Min Muhammad zan ba shi Invitation card d’in Abba ya kai
masa…..” “Ba zan turo shi ba ‘din…” na furta kai tsaye idona na cikin nasa, duk
wata shakkarsa da nake ji ranar ta kau, Saboda tsananin kishi da ya rufe min ido
na. Murmushi ya saki ya furta “Bakomai, bari na kira shi a waya…” Cije leb’ena na
yi ina ji yana furta “Muhammad idan ba damuwa d’an fito na baka cards d’in Abba na
d’aurin aure na special guests…..” Daga haka ya saka kai ya fice ya bar ni a tsaye
kamar statue gaba d’aya naji duniyar na juya min na runtse idonsa sai ga wasu
k’walla masu turiri sun fara zubo min.. fuskar budurwarsa still a cikin
Idanuwana……
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe:
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 13
Tabbas bata inda zan ha’da kaina da matar da zai aura, ta fi ni komai kyau ilimi
wayewa, da kuma gata, daga ganin gidansu inda ta d’au hoton in dai ba y’ar feck
life ba ce to na san Ubanta yafi Abba ku’di nesa ba kusa ba. Me ya ja min? Na ce na
fasa auren Ustaz gashi nan na jawowa kai na sakiyar da ba ruwa.
Da k’yar na mik’e na fita cikin gida, daidai lokacin da na ji Motar Ustaz ta fita
daga gidan a guje. Na lek’a ta window sai naga Yaya Muhd ya shigo gidan . Fuskarsa
a ha’de yake kallona. Kafin naga ya yi k’aramin tsaki ya shige bedroom d’insa. Da
alama haushina yake ji ta yarda nayi watsi da duk abinda suke so na zab’i farin
cikin Mami fiye da nasu. Wayata na jawo na fara kiran Ustaz da sauri amma wayar na
ringing Ustaz bai ‘d’auka ba. Na ja tsaki ina cilla wayar kan kujera tare da zama
dab’ar ina rik’e kaina da naji yana sara min da k’arfin gaske. Idona na lumshe amma
still Ustaz da Amaryarsa nake hangowa a wani yanayi na soyayya. Zuciyata ta dinga
bugu da k’arfin gaske. Wasu hawaye masu zafi suka dinga zubo min. Ban san sanda na
ja wayar na danna masa msg ba. “Ka ‘d’aga wayar magana za
Mu yi….” In seconds ya dawo min da amsa “It’s too late, ki yi barci zan yi magana
da safe, yanzu muna discussing da amaryata ne.” Na yi cilli da wayar ina jin wani
d’aci har a mak’wagoro na. Cije leb’e na kawai nake yi ina mamakin wulk’ancin da
Ustaz yake son ya fara min.
Da dai naga babu sarki sai Allah, sai kawai na mik’e da sauri na nufi bedroom ‘din
da nake, direct washroom na shige na sakarwa kaina shower da kayana a jiki da
komai, burina naji abinda nake ji ‘din ya ragu. Sai dai ba abinda ya ragun daga
zafin zuciya da nake ji. Na ‘d’auro alwala na shiga sallah ba ji ba gani…
Kashegari da k’yar na tashi na hau gyaran gidan don duk kawai na kawar da abinda
nake ji a raina. Da yamma sai ga Mami na tazo gidan. Da sallama ta shigo na yi
saurin ‘d’aga kai ina kallonta. Zama ta yi tana tana jikinta ta furta “Ke Baby!
What happened to you na ganki so pale haka?” Daurewa na yi ban sakar mata hawayen
da suke son zubo min na ce mata bakomai…” Sai sannan ta amsa gaisuwar da Khadija ta
mata. Tana fa’din “Ina Muhammad ‘din?” Anty Khadija ta ce “Ai bai dawo ba..” Gani
nayi Mami ta girgiza kai ta ce “Yaushe ya ce zai dawo daga Kadunan?” Khadija ta ce
“May be gobe.” Ni mamaki nake yi don dai Yaya Muhd yana nan a cikin gidan nan me
yasa Anty Khadija zata ce bata nan… Mami ta ‘dan ja tsaki ta furta “D’an bamu waje
Khadija zan yi magana da ita…” Kamar jira take tayi saurin mik’ewa ta fice. Mami ta
saki ajiyar zuciya tana jawo wata leda a jakarta. “Dama yana dawowa ki dawo gida, a
goben, kin ji na gaya miki.” Na ‘daga kaina ta zaro wata roba mai cike da wani abu
kamar rubutu tana furta “Bu’de ki shanye, ban yarda da lamarin wancan mutumin ba..”
Na karb’a hannuna na rawa na bu’de na sha duk da sam hankalina ya kasa yarda da
rubutun, abu ne da na sani a gidan mu Abba d’an izala ne shi yasa baa ta’ammali da
rubutu, zan iya cewa tun tashi na ma ban tab’a ganin rubutu a gidan ba. Yana dai
yin tofi. Ina shanyewa ta saki ajiyar zuciya sannan ta ciro wani turare a jakarta
ta shafa min. Turaren sam ba shi da da’din k’amshi. Daga haka ta mik’e bayan ta
bani chocolates da ta siyo min da biscuit da yawa ta ta ce “Zan tafi AYSHA na gaya
miki ki taho yana dawowa gobe..” Na ‘daga kaina ko sallama bata yi da Khadija ba ta
fice.
Sai ga Yaya Muhd ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya zuba min ido yana
kallona. “Me ta baki kika sha?” Na waro ido ina furta “Bakomai fa…” “Bakomai d’in
Uwaki, ba ina kallo ta baki abu roba kika shanye ba…” ya furta yana tsare ni da
ido.
Yana bu’de k’ofofin hancinsa da alama k’amshin turaren yake shak’a. “Wannan wani
irin turare ne kamar na y’an bori? Tashi kije ki yi wanka don Ubanki shashasha da
bata san ciwon kanta ba…” Yaya Muhd ya furta a zafafe kamar ya mangare ni. Da sauri
na shige d’aki ina turo bakina alamar na ji haushin abinda ya yi min ‘din. Ina ji
ya zabga tsaki.
Da na yi wankan, zama na na yi a ‘d’aki fuskata a ha’de don na ji zafin abinda ya
yi min. Sai gashi ya shigo d’akin yana kallona ya furta tashi magana zamu yi
AYSHA….” Na mik’e na zauna still fuskata a ha’de. “Haushi kike ji ko? Baki da
hankali yarinya har yanzu baki san me duniya take ciki ba, ina sane na kawoki nan
don ban yarda da wannan matar ba…” Wani irin waro ido na yi na furta “Mamin nawa?”
Harara ya zuba min,
Yana fa’din “Saura kuma don Ubanki ki je ki gaya mata, na ce ban yarda da ita ba,
tunda da alama ta shanye miki zuciya har kina k’ok’arin gasa taki zuciyar saboda ki
sanyaya tata, kan ki
Kika cuta ba wani ba na tabbatar ko gama karatun kika yi ba zaki samu kamar Ustaz
Ahmad ba, shi na daban ne ina gaya miki, gashi nan kin cuci kanki zai yi aure ya
bar ki, saboda ko farantawa wata k’atuwa rai shi kuma Abba da hakkin ki masa
biyayya yake kanki kin bak’anta masa nasa ran a matsayinsa na mahaifinki,
Kin nunawa duniya bai isa da ke ba. Ina sane na kawo ki nan amma nan ‘din ma sai da
ta biyoki. To wallahi ki kiyaye kan ki na gaya miki bakomai zata sake baki ki yi
amfani da shi ba. Ki ‘dau waya kuma ki kira Ustaz idan ya amince yazo gidan nan sai
na tayaki bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura ya aureki.” “Ameen” na furta ba tare
da na san ameen ‘din ta fito ba. Ya Muhd ya bi ni da wani irin kallo kafin ya yi
murmushi ya ce “Shashasha, kina so kina kai wa kasuwa..” Na sunkuyar da kai ina
d’an dariya. Ya furta “Ki kira shi yanzu.” Ya fita daga d’akin.
Sai da na yi addu’a sosai sannan na kira shi, Ringing ta yi sosai kafin ya ‘d’aga.
Cikin Husky Voice ‘d’insa ya ce “Assalamu Alaiki, K’anwata AYSHA ya aka yi?” Wani
irin waro ido na yi raina ya b’aci da sunan da ya kira ni da shi. Wai k’anwata ina
ma laifin Habibteeyn… da yake fa’da. Ba dai ji haushi ba na furta “Ina yini?” Sai
da ya yi ‘dan jum sannan ya furta “Lafiya lau, Babyn Mamy me ya faru na ji muryarki
so weak…” Hawaye na ji sun silalo min na yi k’ok’arin tsayar da su ina furta “Zaka
zo yau please…” “Ina zan zo?” Ya furta a hankali cikin k’asa da murya “Gidan Ya
Muhd please Ustaz…” Sai da ya ja fasali sosai sannan ya furta “Me Zan zo na yi? Ko
kin shirya amincewa aurena ne?” Shiru na masa zuciyata na bugawa da sauri na ce “Ni
dai kazo don Allah…” ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya. Yana fa’din. “Sai dai
gobe yau a gidan su Habibteey zan sha ruwa..” wani irin wuntsilawa zuciyata ta yi
don haka naja baki na tsuke ina hucin da na tabbatar yana jin sa ta cikin waya..
“Kada ki fashe, don naji fushin ya bayyana har ta numfashinki, zan zo Amma ina son
a min irin funkaso da masar rannan ki saka man shanu a cikin miyar.” Ya furta a
hankali. Wani farin ciki naji na ce “Ai baka ci abincin ran nan d’in ba, ta ya aka
yi ka gani? Bayan baka bu’de ba…” Y’ar k’aramar dariya ya saki ya furta “Little
girl, bayan kin gama kuka a sitroom na saka Drivernku ya ‘dauko min Warmers ‘din na
tafi gida da su, ranar duka kowa a gidan mu sai da ya ci abincin AYSHA Momeey na ta
mamakin iya girkin ki da murnar ki zama surikarta ashe ba zaki zama ba….” “Wa yace
ba zan zama ba?” Na furta da sauri. Na ‘dan Jim ya yi bai ce komai ba, kamar ma ba
zai ce ‘din ba sai kuma ya ce… “Ke kika zab’i rabuwarmu Aysha… Ga shi Yanzu it’s
too late, koda yake sai nazo za mu yi magana, take care ki ha’da min zob’o bana son
kunun aya…”Ina ji ya kashe wayar. Nima ajiye wayar na yi cikin sanyin jiki, ina
runtse idona wasu zafafan hawaye suna zubo min..
Na dubi agogo naga akwai sauran lokacin da zan iya masa da funkaso, tunda sai a
lokacin ma 3:30 ta yi. Da sauri na mik’e na isa kitchen ‘din Anty Khadija.
“Alhamdulillah” na fa’da ganin duk abinda nake buk’ata akwai shi a kitchen d’in.
Nan da nan na fara shirin girki, don kam Alhamdulilah Umma da Mami sun hora ni da
girke girke iri-iri, don haka duk inda na je basu da fargabar a bani girki. Sai
shidda daidai na gama girkin. Gidan sai zuba k’amshi yake. Wanka kawai na yi na
samu kaina da tsantsara kwalliya ta fitar hankali, wai duk don na kamo matar Ustaz
a kyau. Amma still walainiyar fuskarta kawai nake gani. Don haka na saki tsaki na
goge makeup ‘din tas hawaye na bin idona. Sanda aka yi sallah kuwa dabino kawai na
samu na ci, don nima na yi azimin. Zaman dafi’an na yi akan sallaya. Ina ta lazimi
da addu’ar Allah ya ‘dorani akan Ustazuna ya janye batun auren waccan yarinyar mai
kama da zabiya, idan har ya amince ni na yarda ko kashegarin ranar ne a ‘daura min
aure da shi. Daga baya zan san yarda na yi muka shirya da Mami.
Ina zaunen akan sallaya Ya. Muhd ya shigo, ‘Dan duba na ya yi sai kuma naga ya
tab’e baki ya furta “Ki taso Malama, bak’onki ya zo.” D’aga kai na yi gabana na
cigaba da matsanancin bugu. Na mik’e cikin mutuwar jiki da kasala. Dama na jera
masa komai a sitroom ‘din.
Fuskata fayau ko kwalli babu na fita wajensa cikin shigar doguwar riga bak’a da na
yi rolling da mayafinta. Jikina ruf ba inda ake gani sai fuskata don hatta k’afata
a rufe take.
Da sallama na shiga parlorn yana zaune ya tank’washe k’afa suna hira da Ya. Muhd
har ya fara cin abincinsa. Ya ‘dago kai ya kalleni ya mayar kan abincinsa. Ya. Muhd
mik’ewa ya yi ya fita. Ni kuma na zube a k’asa daga gefensa ‘dan nesa da shi
ka’dan. “Ina yini?” Ya ‘dago yana kallona. Kafin ya furta “Lafiya Lau Ukhteey..”
Turo baki na yi, na ce “Ni ba y’ar uwarka ba ce..” ware idonsa ya yi ka’dan ya
furta “Then ke mecece?” Sunkuyar da kai na na yi ina wasa da yatsun hannuna. Ustaz
bai bar kallona ba don ina ‘d’agowa muke sake ha’da ido da shi. “Amsa min mana ke
mecece? Tunda kin ce ba kya so na, ni yanzu kallon k’anwa nake miki..” Idona ne ya
kawo ruwa na zuba masa idanun nawa da naga ya k’ank’ance nasa idon ya saka cikin
nawa ya Kuma lumshe su. Cikin wata irin murya ya furta “Matsayin Yayan ma ba zaki
bani ba kenan?” D’aga kai na yi. Ya yi dariya sosai har wushiryarsa na bayyana ya
ce “Shikkenan nagode. Matsayin me zaki ba ni? Gaya min AYSHA?” Mutsu-mutsu na fara
yi shi kuma ganin hakan bai saka ya d’auke idonsa ba. Kallona yake kawai yana
murmushi yana kuma kurb’ar ruwan zob’onsa. “Ba zaki gaya min ba? Ai shikkenan bari
na tashi na tafi Habibteey na jira na, na gode da girki ya yi da’di sosai mijinki
ya ji da’dinsa Wallahi na masa murna. Nima Allah yasa dai Habibteey ta iya girki…”
Turo bakina na yi na furta “Ni ka daina min zancen zabiyar nan…” ware idonsa ya yi
yana furta “Habibteeyn ce zabiya? Lallai ma, to idan ita zabiya ce ke kuma mecece?”
Ban san sanda na harareshi ba. Na furta “Allah ya sawwake ni Ai fari na ba irin
nata ba ne. Fari na yafi nata kyau…” Ya tab’e baki yana dariya ya ce “Ko dai kishi
ne? Idan banda haka kiga yarinya zubin larabawa ki ha’da kanki da ita. Zan tafi ta
ce ma
Na gaisheki, amma kafin na tafi ina son na san matsayina sannan don Allah a min
alfarma ki halarci event ‘dinmu ko guda ‘d’aya ne….” “Wallahi ba zani ba…” Na furta
da sauri, har muryata na sark’e wa saboda tsabar takaici da bak’in cikin da
zuciyata take ciki. Na lura ba k’aramin so yake mata ba kuma duk ni na jawowa kai
na. Da sauri na fice daga ‘dakin ina sake fa’din “Ba zan je ba, sai kace wata mara
zuciya…” Ban san sanda hawaye ya dinga rigegeniya a kan fuskata ba…
Ranar kam ba barcin da ya ‘daukeni, ko b’arawon ma hak’ura ya yi ya k’yaleni.
Da safe kam da ciwon kai na tashi. Kuma ko shara ban yi ba. Ina kwance a ‘d’aki
Anty Khadija ta shigo tana kallona ta ce “AYSHA kin tashi, naga yau ko fitowa ba ki
yi ba. Ki je in ji Yayanki.” Ban amsa mata ba, don haka kawai na samu kaina da
k’uncin zuciya da jin haushin kowa ma. Na mik’e da rigar Barcin da take jikina na
fita parlorn. Kaina ko gyara babu. Idona ya yi k’ozai-k’ozai.
Zuba min ido Yaya Muhd ya yi kafin ya furta “Ke baiwar Allah, lafiya kike? Kinga
yarda kika dawo kuwa?” Kallonsa kawai nake ban amsa ba ganin yarda yake walainiya
cikin sabuwar shadda fara k’al da ita. Ya tab’e baki ganin bani da niyyar amsawa ya
ce “Allah ya kawo sauk’i, ke Khadija mu je na sauke ki a asibitin tunda ita bata
shirya ba, balle ta raka ki, ni zan wuce wajen d’aurin auren Ustaz… Hararar gefen
ido kawai nake watsa masa, ina ganin Ya Muhd d’in kamar wani gagarumin mak’iyina.
Ganin ba zan amsa ba ina kallo Suka fice shi da matarsa suka rufo min k’ofa…
Na cusa hannuna cikin gashin kaina ina jin zuciyata na wata irin suya. Hawayen ma
k’in zubowa suka yi. Kawai wani irin kuka nake na zuci. Ban san iya lokacin da na
‘d’auka a kwance a wajen ba, sai ji na yi wata ta yi k’ara na duba naga msg d’in
Ustaz ne ya shigo wayata. Tsaki na zuba kamar ba zan karanta ba sai dai na bu’de
sai naga ya saka “Alhamdulillah an ‘d’aura aure na, ina jiran fatan alheri daga
k’anwata…..
Duum naji na daina ji da gani…
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our
group for updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots
more
https://chat.whatsapp.com/FuUV3xjAcKgDaquGHnOnjw
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 14
14…..
Tun daga kwanyata nake jin wani irin zafi, har k’asan zuciyata. Jikina ya yi sanyi
sosai kukan ma ya kasa zuwa sai wani b’acin rai nake ji mai dugunzuma zuciya, ya
raunata gabban jiki. Da k’yar na sulale na zame na kwanta a k’asan carpet ina
lumshe idona. Tafarfasar da zuciyata take yi yasa na dinga jin kai na yana neman
yin tsawa. Gashin kaina na burkita gaba d’aya ina jan gashin da k’arfi kamar shi ya
min laifin. Kuka nake son yi amma kukan ya k’i zuwa. Rigar barci ce a jikina ban
kuma damu da na cireta ba, don bata wankan nake ba. Sai yanzu na ji ina jin haushin
biyayyar da na yiwa Mameey, kamar na cuci kai na kamar ni na jawowa kai na.
Ina kwancen cikin tafasar zuciya idanu na a kulle. Na ji kamar wani na tsaye a kai
na. Da k’yar na dinga bu’de lumsassun idanuna sai na ga Ustaz ne a tsaye sake mayar
da idon na yi na kulle don ina tunanin imagination d’in da na saba ne.
Daf da ni na dinga jin k’amshin mayataccen turarensa, don haka na ware idona sosai
na zuba su a kansa. Yana zaune daf da ni idanunsa a kaina yana sakar min murmushi.
Da sauri na mik’e cikin razana ina neman ko Hijab ne da zan suturce jikina don
rigar barci ce a jikina itama iya gwiwa mai santsin gaske, sanda suka tafi na ji
abin duniya ya min zafi ban san sanda na wancakalar da Hijabin can gefe ba. Hijabin
yana daga can bakin k’ofa. Ga shi sam ba zan iya tashi ba. Na takure gefe guda ina
rufe jikina duk da na san ba abinda bai gani ba, don ban san tsawon wani lokaci ya
‘d’auka a wajen ba. Murya a sark’e na furta “Ya zaka shigo min haka? Ba sallama ka
bani Hijab ‘dina…” Still kallona yake yana murmushi kawai bai kuma mik’o min Hijab
d’in ba. “Please Ustaz, ka bani Hijab ‘dina….” Na furta kamar na yi kuka. Muryarsa
a sark’e ya lumshe ido… ya furta “Idan na k’i fa?” A tunzire na furta “Amma dai ka
san haramun kake kalla ko?” Sake k’ura min ido ya yi kafin murya can k’asa ya furta
“Da jikin da Mai jikin yau duk mallaki na ne, Matar Ustazunta…” wani irin ware ido
na yi don ni duk ban fuskanci manufarsa ba. “Tashi ki ‘dau Hijabin naki…bari na
rufe ido na..” Ya fa’da yana rufe idon