Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NAGA Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel by Nazeefa NASHE

Author :  NAZEEFA NASHE Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 15

42K to 42.5K   out of 42.5K words

da k’arfi ya turo k’ofar shima idanunsa akan Umma ya furta wai menene?” Nan
Umma ta shiga ba shi labari Mami dai bata ce komai ba illa ficewa da ta yi tana
hawaye. Madadin Abba ya yi fa’da sai naga ya girgiza kai ya kalli su Ya. Muhd ya
furta “Ku tafi masallaci Muhammad an yi sallah.” Suka fice a hankali. Umma ta
dubeshi yana zama yana danna waya ta ce “Amma ka barsu suka fita baka wa Umar
fa’dan abinda ya yi ba?” Jingina ya yi da kujera yana lumshe idonsa ya furta “Nima
ina tunanin da Umar yake….” Ba shiri Umma ta zauna tana furta “A’a Abban Aysha kada
ka fara irin wannan maganar don Allah…” wani kallo ya mata kafin ya cije bakinsa.
Ya furta “Ina zargi na ce, kuma tabbas idan na tabbatar da zargina wallahi sakinta
zan yi, ina jiran feedback d’in Ahmad, mun yi waya da mahaifinsa ya gaya min su
basu san labarin sakin ba, amma sun yi waya da Ahmad ya sanar masa yana airport
d’in Abuja zai wuce egypt, amma Babansa ya dakatar da shi ya ce ya juyo lalle a
daren nan zai zo ya gaya mana koma menene…” Umma jikinta a salub’e ta mik’e tana
furta “Allah ya kyauta.” Ta bar ‘d’akin. abba ya sake d’agowa a karo na biyu yana
kallona ya furta “Kin tabbata baki san komai ba?” Na d’aga masa kai na. Ya girgiza
kansa shima ya mik’e ya fice daga d’akin. Tausayin kaina ya sake kamani. Kuka nake
sosai ba wanda ya sake bi ta kaina, tun bayan da Umma ta shigo ta kawo min tea ta
rutsa ni sai da na shanye. Sannan ta fice daga d’akin.


Har dare gidanmu tsit ba wani mai walwala, y’an biki tuni suka watse bayan an sanar
musu ba wani abu bane, Ustaz ne tafiyar gaggawa ta same shi.


Bayan Isha’i Iyayen Ahmad suka zo, Abba ya saka aka shiga da su parlorn sa na cikin
gida. Ni dai gaba na kawai fa’duwa yake. Ba su wani da’de ba suka tafi. Sai ga
Ya.Umar ya shigo da gudu yana furta “Umma fito Abba ba lafiya jikinsa rawa yake…”
Da wani irin sauri Umma ta fito nima ban san sanda na fito daga d’akin Abba ba, na
bi bayansu sitroom d’in Abban. Da wani irin tsawa Abba ya ce min “Fice Aysha
haihuwar ki ba ta min rana ba, ku d’auka ku dubi hotunan nan ku ga irin b’atancin
da cutarwar da ta yiwa nagartar gidan nan…..”


K’afafuna na rawa na zube a wajen ina kallon takardun da Ya Muhammad ya zubo min,
ido na ware ganin ba abinda ya b’uya a hoton daga tsiraicina komai na a waje,
k’irji and everything gefe guda wani mutum ne zaune kusa da ni yana shafa
k’irjina…. Na zunduma wani Uban ihu, ina jin numfashina na neman barin gangar
jikina…




Kash! Ina mai baku hak’uri, anan Book 1 ya k’are, sai dai ba zan yi jumurin kawo
muku shi a kullum ba ta kafar whatsapp saboda wani dalili mai girman gaske, zan
mayar da posting Litinin talata laraba da alhamis. Wato sau hu’du a sati. Sauran
ranakun zan dinga posting a arewabooks. Y’an Arewabooks zasu dinga samu kullum In
sha Allah. Dafatan za’a min uziri. Na gode sosai.


Masu so arewa ku yi searching @nazeefah ko kuyi searching sunan Book d’in. Labari
yanzu aka fara AYSHA bata ga komai ba sai nan gaba. Akwai book 2 akwai Book 3.
Ganin rayuwar yana gaba…



𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢 ✍️

15 / 15