Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
zan d’au lemo idona ya kai kan wata
farar enveloped. A zatona mantawa ya yi don haka ban ma bu’de ba na ajiye a gefe
ina jan kwalin exotic na fara d’addaka shi a cikina. Na tattare kayan idona ya sake
sauka kan enveloped da a bayansa na ga sunana b’aro b’aro. AYSHA IMAM KHALIL…
murmushi na saki ina tunanin ko wata kyauta Ustaz d’in ya bani don haka na jawo da
sauri na farke enveloped d’in da yake ta zuba k’amshin turarensa.
𝒜𝓈𝓈𝒶𝓁𝒶𝓂𝓊 𝒶𝓁𝒶𝒾𝓀𝓊𝓂.... 𝒩𝒾 𝒜𝒽𝓂𝒶𝒹 𝒮𝓊𝓁𝒶𝒾𝓂𝒶𝓃 𝒮𝒶ℯℯ𝒹 𝓃𝒶 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝓂𝒶𝓉𝒶𝓉𝒶
𝒜𝓎𝓈𝒽𝒶 ℐ𝓂𝒶𝓂 𝒦𝒽𝒶𝓁𝒾𝓁 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝒹𝒶𝓎𝒶 𝒷𝒶𝓉𝒶 𝒹𝒶 𝒾𝒹𝒹𝒶𝓉𝒶 𝒾𝒹𝒶𝓃 𝓉𝒶 𝓈𝒶𝓂𝓊 𝓂𝒾𝒿𝒾
𝓉𝒶 𝓎𝒾 𝒶𝓊𝓇ℯ......
Kasa k’arasawa na yi saboda yarda na ji numfashi na yana neman d’aukewa na dinga
ware ido ina jin zuciyata na wani irin bugu..
Tabbas NAGA RAYUWA Me yake shirin faruwa da ni ne? Saki a daren aurena daren da
muke d’oki da zakwa’din zuwansa ni da mijina ya da’de yana gaya min yana jiran
ranar da zai rungumeni dtazo saboda kiyeye dokar Ubangiji. Me na yiwa Ustazuna ya
sake ni? Na shiga uku!! Haka na furta a zuciyata..
To fa! ko me AYSHA ta yiwa Ustaz Ahmad ya zabga mata saki a daren aurenta? Duka
yana cikin littafin NAGA RAYUWA da zai dinga zuwa muku daga Alk’alamin…..
ℯ★
✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 2.
✍🏽
★
…..
Kuka ne sosai ya kufce min, irin kukan nan da kake jin d’acinsa har k’asan ranka.
Kuka mai sauti da Amon muryar karaya a cikinsa. Me Na masa? Shine tambayar da nake
wa kaina na kuma kasa lalubo amsar. Abinda zuciyata take gaya min nake k’aryatawa
ko nak’i ko na so dole ne na gasagata zuciyar tawa dole Butulcin d’a namiji ne ya
biyo ta kai na. Ko kuma ya yi haka ne don ya gwada mizanin soyayyarsa a zuciyata.
Amma ya rasa ta hanyar da zai gwada sai ta kalmar saki? Kai abinda kamar wuya Ustaz
da wayonsa ba zai yi wasa da saki ba Halak d’in da ya san Allah baya so, kuma idan
aka aikata shi ar’ashi tana girgiza. Dole ba don na so ba na amince da shawarar da
zuciyata take ba ni, na danganawa sashensa na je na tambayeshi abinda ke faruwa…
Tsam na mik’e na shiga laliben sashennasa, kasancewata bak’uwa a gidan bai saka na
sha wahalar gane k’ofar sashen nasa ba. Daga can corridor tsakanin k’ofar da zata
kai ka nawa sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa
baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a
kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim.
Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take
parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa.
Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin
motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda
idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo
ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya
lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na.
Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na
yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a
cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban
kuma fahimceka ba.”
Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin
yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a
shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin
nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don
haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….”
Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?”
Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani
ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son
dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa..
Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba
Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da
k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz
ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da
k’arfin gaske na fice daga d’akin.
Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina
mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da
ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa
sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min
sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya
mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya
san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na
t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba
wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba.
Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a
wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan
daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah
farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin
ga wa’dannan sune garkuwarki a gidan miji idan kika rik’esu kin samu makamin k’are
dangi.” Ina sallahr ina hawaye na kaiwa Allah kuka na, na bayyana masa rauni na na
kuma rok’eshi ya shige min gaba a dukkan lamari na.”
Ban tashi daga sallaya ba sai k’arfe uku da naji kaina ya fara ciwo abin mamaki sai
na ji na samu k’arfi da nutsuwar zuciya. Na ji komai ya faru gareni daga Allah yake
duk da tabbas Ustaz ya cuceni. Abu guda nafi buk’ata a yanzu na ji dalilin sakin da
ya yi min, sai dai na yi alk’awarin ni da kai na ba zan sake tambayarsa ba don ko
don ganinsa bana yi.
Barci ne sosai ya d’auke ni, kasancewar garin sanyi ne dare yana tsawaita don haka
sallar asuba sa daf da k’arfe shidda ake yi, shi yasa na samu barci sosai duk da ba
wai zance na yi isashshe ba ne. Ina sallame sallahr ko kayan sallar ban cire ba na
fice da su da sauri a jikina.
Shiru layin amma a haka na dinga tattaki har na je bakin titi. Allah kuma ya
taimakeni na samu adaidaita sahu. “Shara’da phase 2 kawai nace masa.
Har k’ofar gidanmu ya ajiye ni ta hanyar kwatance da na masa.
Duk da a tsorace nake da ganin Abbana hakan bai hana ni shiga gidan da k’warin
gwiwata ba. Y’an biki ko watsewa ba su yi ba, don wasu daga garuruwa daban daban
suka zo. Sai dai gidan shiru da alama kowa gajiyar biki ta saka ana sallah an
kwanta sai wa’danda suke aiki a bayan gidan ta can na dinga jin d’an hayaniya da
sautin kwanuka na tashi.
Jama’ar da suke kwance a
Parlor wa’danda duk k’annen Mami na ne da na Umma na suka dinga bi na da kallon
mamaki baki a sake. Anty Sharifa ta ce “Ke AYSHA lafiya?” Mami da fitowarta daga
d’akinta kenan itama hangame bakin ta yi tana ware ido ta furta “Ni Fa’dima me Zan
gani haka? Ke Aysha Uban me ya fito da ke da sassafe haka?” Ta fa’da tana jan
hannuna hankali a tashe ta furta “Ai dama sai da na gayawa Abbanku kin yi
k’ank’anta da aure, shekara sha bakwai don ko sha takwas d’in baki cika ba, yanzu
haka wani bak’on al’amari kika gani da yafi k’arfinki yasa kika gudo?” Anty Sharifa
k’anwar Umma ta ce “Ah haba! Sai kace ba y’ar yanzu ba, ai duk da take k’anwar Maza
na san ta san me aure ya k’unsa ko da ta hanyar k’awaye da karance karancen
littafine…” Mami ta d’an harareta “Me AYSHA ta sani? Karatun littafin take ita? Ko
k’awayen arziki AYSHA bata da su balle su sanar da ita aure da abinda ya k’unsa…”
Ta fa’da tana jan hannuna muka shige Uwar d’akinta.
Zaunar da ni ta yi a bakin gado, bayan ta koma ta rufe d’akin da key tana furta
“Bana son saka ido da munafunci yanzu duk ido zai dawo kan ki, kema kin yi wauta
Aysha. Me ya kai ki fitowa don kawai Mijinki ya kusanceki Ai shine auren muma duk
haka ake mana da haka kuma kowa yake sabawa… kowace macen aure da kika gani haka ne
yake faruwa da ita koda yaushe, don haka tun kafin sauran mutane da Ubanki su ji ki
tashi maza naje na mayar da ke, bana son na ji komai wannan sirrinki ne ke da
Mijinki. Maza tashi mu tafi kafin mutane su fara miki kallon mara wayo mai gudun
Miji.”
Hawaye ne suka fara zuba min, ganin ita Mami na inda take hange daban da abinda ya
kawo ni gidan. Na turo bakina ina furta “Ni fa ba wannan bane, ko hannu bai rik’e
min ba fa.”
Mami ta d’an bu’de idonta ta furta “To menene idan ba wannan ba?” “Ya sake ni…”
Wani irin ja da baya Mami ta yi idonta a waje tana kallona baki a bu’de ta shiga
shock sosai cikin wani irin yanayi ta furta “What? Ya sake ki Aysha? Shi Ahmad d’in
ne ya sake ki? A kwana guda da kika yi a gidansa to Uban me kika masa?” Hawaye ne
suka fara ambaliya a fuskata na gayawa Mami duk abinda ya faru ban b’oye mata komai
ba. Dariya Mami ta yi tana furta “Sharrin D’a Namiji! Ga abinda nake gudu ya zo.
Sai ki tashi mu je wajen Abbanki na bashi tukuicin alheri da Ahmad ya kawo masa, ya
mayar masa da y’a k’aramar bazawara Ahmad dai mai nagartattun halayen da Ubanki
yake faman b’ab’atu akai.” Ido na waro waje ganin tana ja hannuna “Tashi mu je
mana.” Na ja hannun ina girgiza kai “Mami, ba zan iya zuwa wajen Abba ba, Allah ina
tsoro, ban san yarda zai d’au lamarin ba.” Wani kallo ta min cikin b’acin rai ta
furta “Tashi na ce miki mu je ko? Iyakacinsa dai dake fa’da, tunda ba zai iya zare
miki ranki ba.” Ta fa’da a fusace ta kuma fincikeni muka fita wajen.
Abin haushi Jama’a an fito gaba d’aya kowa sai baza ido yake ana kallon mu. Kallo
guda Mami ta musu suka dinga bajewa suna ba mu hanya. Ban yi mamaki ba don ni da
kai na na san an samu topic.
Abba na zaune yana lazimin safiya. Umma ce a gefensa tana ha’da masa coffee da ya
saba sha duk safiya. Da alama shi bai san abinda ya faru ba. Balle Umma da tun
jiyan bata fita daga sashensa ba.
A razane duk suka zuba mana idonsu musamman Umma da har Cokalin hannunta yake
fa’duwa. “FATIMA lafiya kuwa? Naga Aysha da sassafe.” Umma ta fa’da tashin
hankalinta na sake bayyana a saman fuskarta.
Zama Mami ta yi a gefen Kujerar da yake kusa da Abba, ta saka ni a gefenta ta furta
“Lafiyar kenan Umma, sai dai d’an gaban goshin naku ya muku Aiken tukuicin
sakamakon alherin da kuka masa…”
Abba da yake laziminsa ya d’ago ya d’an zubawa Mami ido don ya san halin kayarsa
sarai danger ce wutar baya. Umma kuwa cup d’in ta ajiye tana sake furta “Me ya faru
to? amma fa Mammin Aysha ya kamata ki yiwa y’ar taki fa’da ta san fa ta girma, aure
kuma ba wasan yara ba ne. Idan ban da shashashanci menene na dako wannan Uban
sammakon, koma menene ba ga waya ba me yasa ba zata sanar miki ba? Sai ta d’ebo
jiki ta taho ta saka y’an biki su tafi da ita a bakin duniya tunda ko gama watsewa
ba su yi ba. Aa sam wannan wauta ce da shirme.” Mami wani kallo ta mata sai kuma ta
cije baki.
“Kamawa ta yi, ta dako uban sammakon babu gaira ba dalili ba abinda zai sakata
fitowa daga gidan Mijin da aka kai ta jiya.” Mami ta fa’da tana hura hanci da
jijjiga k’afa. Umma dai shiru ta yi don ba mamaki ta lura idan ta cigaba da magana
tata ce zata yi zafi.
Abbana yana jin su bai yi magana ba ya cigaba da laziminsa. Sai da ya idar sannan
ya ‘d’au coffee d’insa ya shanye ya zuba min kallon da na kusan jin kayan cikina
suna shirin fitowa. “Ke wace irin shashasha ce Aysha? Daga kai ki gidan Miji jiya
yau ki fito? Kin d’auka auren wasa ne? Me ya fito da ke?”
Madadin amsa masa jiki na ne ya dinga rawa kamar yarda zuciyata take bugawa. “Ba
magana nake miki ba?” Ya sake fa’da da Tsawar gaske, hakan da yasa har ban san
sanda na rik’e Mami da kyau ba ina makyarkyata “A’a Alhaji, kada ka sake hargitsata
Ai ba laifinta ba ne fitowar dole ne ta fito tunda ya saketa…..” Gaba d’aya bakinsu
a ha’de suka furta “Saki Fatima?” Ta jijjiga kai tana murmushi ha’de da furta
“Sakamakon halaccin da kuka masa ne, duk duniya kuna ganin ba wanda ya cancanta
kamar Ustaz Ahmad. Kullum zancenku nagartaccen mutum ne mai ilimin addini da ya
shahara a duniyar Malamai. Yau ga ilimin nasa nan ya fara nuna muku….” D’akin tsit
ya yi Abba jikinsa har rawa yake. Umma kuwa zama ta yi jab’ar a k’asa ta rik’e
kanta kawai jikinta na rawa….
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
NAGA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 4..
Da mamaki Umma take kallonta su Yaya Muhammad suma suka zuba mata ido. Ya Usman da
ya kasa shiru ya ce “Au ke kuma auren ne ba kya son ta yi? Shi yasa zata ke k’unshe
fuskarta, amma kamar wannan ba dabara ba ce..” Harara ta watsa masa tana furta “To
kanari Uban surutu, ni na ce maka bana son ta yi aure? Auren ne dai ba yanzu zata
yi shi ba sai ta yi dogon karatun da na tabbatar zata iya k’watar y’ancin kanta a
Wajen namiji sannan zan amince ta yi aure, haka kawai ba za’a aurar da ita da duhun
kai ba shikkenan ta zama sai kace baiwa wajen namiji…” Cikin mamaki suka zuba mata
ido, Umma kanta ta yi mamakin furucin Mamin, sai dai data tuna Mamin gidansu
gangariyar y’an boko ne sai bata yi mamaki ba ta saki ajiyar zuciya kawai tana
furta “Allah ya taimaka, ya nuna mana lokacin…” Yaya Muhammad gyara zama ya yi yana
tab’e baki ya furta “Amma dai wannan kamar ba shawara ba ce mai b’illewa, Saboda
kowa yanzu burinsa a ce y’arsa ta yi aure sai ta yi karatun a nata gidan Mijin….”
“Sai ka bari sai ka haifi taka y’ar Muhammad ba wannan ba…” ta fa’da a zafafe tana
nuna ni. Ta ja hannuna muka wuce samanta.
Tana banbamin fa’da har da rantsuwar nan gaba idan Muhammad bai yi wasa ba sai ta
mare shi.
A kashegarin ranar kuwa bayan na yi wanka Mami ta tsantsara min kwalliya cikin
shigar kayan hausawa da suka min matuk’ar kyau. Murna na dinga yi don kam dama ina
son su Mamin ce bata ba ni damar sakawa ba.
Sanda na fita tsakargida idanun masu aiki duk a kaina suke, sunan ta dariya ganin
kwalliyar da aka min. Har Iya ta kasa shiru ta ce “Lallai Aishatun Mami ta girma…
Ma sha Allah a yi shekaru irin na dabino.”
Abba da yake zaune daga can gefe shi da su Yaya Muhd, baki sake ya dinga kallona
yana furta “Inye Aishatun ba, irin wannan
Kwalliya haka? Waye ya siyo
Miki kayan hausawa…” ina dariya na zauna daf da shi an furta “‘Mami na ce, ita ta
siyo min su da yawa ta ce na daina saka wa’dancan kayan yahudun.” Jan hancina Abba
ya yi ya ce “Ai ke ce Yahudun.” Sannan ya juya yana kallon su Ya. Muhd ya furta
“Kun ga abinda na gaya muku ko? Na gaya muku kada ku tada hankalinku a kan yarinyar
nan Fatima ba zata yi sanadin gurb’acewar tarbiyyarta ba..Fateema mace ce data san
abinda take yi.” Shiru su ka yi suna cigaba da shan kununsu Ya Ali ne ya furta “Ba
shakka, to Allah yasa dai ba da wata manu…” wani kallo naga Umma ta masa sai ya ja
bakinsa ya tsuke yana dariya.
Tun daga ranar ya zama na saba saka kayan hausawa, kuma ko aike na waje za’a yi
Mami na bata bari na fita ba nik’ab har hakan ya zame min
Jiki. Sai dai a fuskar Umma
Wani lokacin ina kallon yanayinta kamar hakan baya mata da’di, sai dai ba yarda
zata yi ne. Duk inda na je kuwa sha’awar shigata ake, don kowa ya ganni ya san
d’iyar wacece? D’iyar mace mai mutunci wacce ta san ciwon kanta, kuma yake bawa
y’arta tarbiyya, ba wacce da kanta take saka y’a’yanta shigar banza ba don kawai su
kawo mata mazan aure ta dinga kuma zuga su da fa’din sun yi kyau.
Sanda na fara period kuwa, Mami hana aikena ta yi. Saboda wani irin kyau da na
dinga zubawa, mak’erin y’an mata na ji suna cewa ya fara k’era ni. Don haka ta
shiga taka tsantsan da ni. Idan Ya. Muhd ya yi magana ta hau masa masifa don haka
ya gani ya zuba mata ido kamar yarda kowa ya yi.
Sanda maganar aurensu ta bujiro da y’ay’an abokin Abba Mami na jin iya secondary
kawai suka gama. Ta dinga tab’e baki tana fa’din “Amma Sadik kun yi bak’ar dabara,
yanzu meye riba a auren k’wailayen mata?” Ya Muhd don takaici kasa mata magana ya
yi, Ya. SADIK MURMUSHI ya saki yana furta “Ai auren irinsu Mami ya fi riba, ko
bakomai zasu bi duk wani tsari da aka shar’anta musu..” Ta ja tsaki ta furta
“Mugunta zaku musu ba, ai shikkenan shi yasa duk bala’i ba zan yarda AYSHA ta yi
aure daga gama secondary ba dole ko degree sai ta yi, idan ma bata yi masters ba…”
Ya Muhd