Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
kai ina sakin ajiyar zuciya a hankali. “Ba ni
wayar da ya baki?” Hannuna na rawa na mik’a mata. Naga ta danna wajen kashewa ta
kasheta tana murmushi “Bak’in mugu sai dai ka auri wata ba AYSHA ta ba…” ta fa’da
tana mik’ewa ta shige d’akinta “Ki je ki yi wanka ki kwanta, Maganar wannan mutumin
close har abada…” wani irin yawu na ha’diye da k’yar ina mik’ewa na ji kaina ya
sarawa na rik’e kan da k’yar na isa cikin d’aki, ina ji kamar Mami ta raba ni da
wani sashe ne na rayuwa ta..
Tun daga ranar na rasa duk wani farin ciki da walwala. Sai dai ina k’ok’ari sosai
wajen danne hakan don kada Mami ta gane. W
Ranar kwana uku da faruwar lamarin Mami ta fita, Umma ta hawo sama, ta shiga d’akin
da nake a kwance ta sameni idanuna na kallon ceiling ta tsaya a gefen gadon.
Ganinta ya saka ni yin firgitgit ina kallonta. Ajiyar zuciya ta saki ta zauna a
gefen gadon tana furta “Ta shi Aysha magana za mu yi, a matsayina na uwar da ta
haifeki na san kin kwana da sanin cewa ba zan cutar da ke ba.” Jikina a sanyaye na
mik’e na zauna idanuna na kawo ruwa sai na ji kawai ina son na yi kuka a jikin Umma
na. Fa’dawa jikinta na yi na saki kukan bata hana ni ba sai ma sake rungume ni da
ta yi a jikinta. Na yi kukan sosai kafin ta ‘dago ta share min hawaye ta furta “Me
ke damunki?” Girgiza mata kai na yi “Bakomai Umma.” Murmushi ta saki tana gigiza
kai “Ba zai zama bakomai ba AYSHA tabbas Akwai komai, ni na san kina son mutumin
nan Kuma kin amince da aurensa, me yasa kuma kwana biyu kika canja? Ga shi kullum
kina d’aki ba kya walwala, Aysha ina son ki bu’de kunne ki ji ni da kyau. Bin
Umarnin mahaifinki wajibi ne gareki, ki amince da auren nan kafin ki zo kina
nadama, me yasa ba kya amsa wayarsa alhali kin san baya gari? Ya kira Abbanku yana
tambayar lafiya idan ya kira wayarki bata yi? Ina wayar taki take?” Umma ta furta
tana min kallo mai cike da k’auna da rarrashi. A hankali na furta “Tana wajen
Mami.” Murmushi naga ta yi ta mik’e tana fa’din ki tashi ki yi wanka ki sauko ki ci
abinci bana son zaman ‘d’akin nan.” Na mik’e a hankali na shige toilet d’in. Umma
har ta tara min ruwa na shiga wankan sannan ta fita daga d’akin.
————
Kashegari da safe naga duk k’annen Abba maza sun zo gidan. Ban san me ake ba ni
dai na shirya na tafi makaranta. Da na dawo kuwa rigima na tarar a gidan wai ashe
ku’din aurena aka kawo da sa rana gaba d’aya..
Shine Mameey ta fito tana masifa a tsakargida na ganta da Umma tana janta da
akwatin ta tana furta “Wai Fateema meye haka kina cikin hankalinki kuwa? Saboda
za’a aurar da Aysha zaki bar gidan nan…” A zafafe ta janye hannunta. “Cika ni,
gwara na tafi meye amfanin zama na a gidan da baa san daraja da k’imata ba, ashe
dama kun bani y’ar ne don ku wulak’antani ku nuna min bani da iko da ita. Zan bar
gidan tunda ba Uban da na ajiye, ku je ku yi ta aurar da ita….” Da gudu na iso
wajen na zube a jikinta, jikina yana kakkarwa na furta “Please Mamy ba inda zaki,
ba Zan aure shi ba wallahi, tunda dai baki amince ba…” “Ashe kuwa sai dai idan ba
ni Iman ba ne na haifeki Aysha, aure ba fashi..” Mami ta juyo tana kallonsa “Kada
Allah yasa ka fasa Imamu, ga y’arka nan ka aurar da ita, amma ni na gama zaman
gidanka…” Hanya ya nuna mata yana juyawa a zafafe cikin parlorn sa. Mami ta
wancakalar da ni ta ja akwatin ta da sauri zan bi ta Abba ya daka min tsawa da
sauri na durk’ushe a wajen ina jin tashin motar Mamin. Na runtse idona da k’arfin
gaske, ina jin wani irin b’acin rai Yana dugunzuma zuciyata…
Wannan wani irin bal’ai ne tabbas zuwan Ustaz rayuwata ba abinda ya haifar sai
fitina a cikin gidan mu, abinda ban tab’a gani ba, sa’insa tsakanin Iyayena da
Abba. Ranar sam zuciyata bata da nutsuwa na ji a raina sam na shirya rabuwa da
Ustaz.
Nan da nan labari ya kara’de danginmu an bada ni an saka min rana. Aka yi ta zuwa
Allah ya sanya alheri. Mami kuma bata dawo gidan ba tashin hankalina kenan…
Ranar lahadi Ina zuwa makaranta naga motar Ustaz. Mamaki ya kama ni na fara tunanin
a yau d’in da ya dawo yazo kenan. A aji na same shi a zaune da wasu tsirari daga
cikin ajin. Ido ya ‘dago yana kallona sai naga kamar har rama ya yi a ido. Na
rusunar da idona kawai na isa wajen zama na na zauna.
Sai da ya gama karatu wanda duk rabi ba fahinta nake ba sannan ya ‘dago yana kallon
y’an ajin ya furta “Bissalam, ku je ku yi sallah.” Ni ce ta farkon fita.
Ana idar da sallah aka ce koda kowa ya mik’e, anan muke jin ashe yau ustaz zai yi
sallama da makarantar. D’alibai da yawa ba su so ba, musamman y’an mata da suke ta
maganar k’asa-k’asa. Ustaz ya yi alheri sosai ga makarantarmu. Sanda Malam Kawu ya
masa godiya a madadin y’an ajinsa na Ibn Kaseer ta cikin loud speakerr Ya furta
“Bayan jaddada kalmar godiyar mu, sannan ina son y’an makaranta su taya Ustaz Ahmad
murnar samun matar Aure da ya yi, a cikin makarantar nan. An saka musu rana da
hazik’ar mu, Hafizar mu Aysha Imam Khaleel, Head girl d’in mu ta wannan makaranta.
Duk da nik’ab ne a fuskata sai da jikina ya fara rawa musamman da kabbarar mutane
ta dinga shiga kunnuwa na. Na runtse idona a hankali. Ina hango yarda bakin Ustaz
ya kasa rufuwa yana ta sakin murmushi. Y’an mata kuwa duk fuskokin wasu ba walwala.
Har gaba na aka dinga zuwa ana sake taya ni murna. Ni dai kasa bu’de fuskata na yi
na samu na na silale na gudu…
Ina zuwa layin gidan mu naga yarinya ta biyo ni da gudu “Malama Aysha take ta
furtawa. Na tsaya ina kallonta sai da ta d’an yi haki na alamar gudun da ta ci
sannan ta mik’o min envelope ‘din mai matuk’ar kyau. Da tun kafin na bu’de na san
waye saboda k’amshin mayen turarensa. “Ba ruwana da fushinki, duk da na ji haushi
amma abu guda na sani dole a cika min alk’awarina zan zo shan ruwa gobe around
7:30pm.
Your’s Ustazun Aysha.
Ajiyar zuciya na saki. A raina ina tunanin ta inda zan rabu da Ustaz ba tare da na
saka shi a damuwa ba..
Kashegari nima tashi na yi da azimin kawai na samu kai na da son yiwa Ustaz d’in
girki, duk da ina ji a raina a ranar zan rok’e shi ya janye daga maganar aurena ko
don dawo da farin cikin gidan mu, kuma Mami ta dawo gidan mijinta. Girkin na masa,
Masa da sinasir sai miyar taushe na kuma yi kunun tsamiya da zob’o da ya ji kayan
k’amshi. Haka kawai na ji gwara na masa abincin mu na gargajiya. Umma dai sai
kallona take kafin ta gaji da shirun ta furta “AYSHA wa kike wa girki ne?” Kunyace
ta kamani na ce “Umma cewa ya yi zai zo ya sha ruwa.” Gani na yi ta yi murmushi ta
d’an’dana girkin da lemon ta girgiza kai ta furta “Kin yi k’ok’ari, sai ki ha’da
masa da zogale tunda naga harkar gargajiya kika masa. Ko ke fa? Ki rabu da Mami
zata dawo da ikon Allah, gobe ma Na ji Baffaninku suna za su je gidan…” Na d’aga
kai kawai ba wai don zan janye maganar rabuwa da Ustaz ba da na shiryawa a yau.
Daidai lokacin da zai zo kuwa sai ga Yaya Ali ya shigo d’akina yana kallona ya
furta “Bak’onki ya zo kandala.” Turo baki na yi ina fa’din “Kai Ya Ali me ye haka?
Kai ma ya kamata ka yi aure ka bar gidan nan.” D’alle min baki ya yi yana furta sai
ki aurar da ni, ashe dai kina son mutumin ji wani uban kwalliya da kika yi har da
su jambaki?” Harararsa kawai na yi na shige na sauka k’asa. Kafin na je ma har Umma
ta saka an kai masa abincin sitroom. Ina shiga yana zaune na same shi. Idonsa a
lumshe sai dai daga yanayin fuskarsa na tabbatar akwai abinda ke damunsa. Sallamar
da na yi bai saka ya bu’de idon ba ya dai amsa nima na ga haka ne ta hanyar d’aga
lab’b’ansa da ya yi. Tsawon mintu biyu bai bu’de idon ba duk da a jikina na ji yana
kallona da lumsassun idanun nasa. “Zuba min ruwan tea.ban sha ruwa ba dabino kawai
na ci.” Ya fa’da still idanunsa a lumshe. A daburce na fara ha’da masa shayin. Ina
shirin sake zuba sugar ya furta “Enough madam, wa ya gaya miki ana son maza su
dinga shan zak’i sosai?” Ya fa’da yana ware idonsa ka’dan a kai na. Maik’on
k’wallar ido yana k’arawa idonsa kyau. Hawaye naga sun d’an gangaro masa. Hakan ya
saka jikina ya yi sanyi. Na ajiye cup d’in shayin a kan table da ke kusa da shi.
“Na gode” ya furta cikin raunin muryar da ta saka har na ‘dago na kalleshi da sauri
na ce “Kuka ka ke?” Ya ‘d’aga min kai. “Kuka nake AYSHA, dole na yi kuka me yasa ba
kya so na? Kike wahalar da ni, kin san kalar azabar da kika bani a kwanakin nan,
Sana’a na je yi k’asar mutane amma na zama sam bani da nutsuwar da zan gudanar da
sana’ar na kira waya a kashe har na gaji na kira Abba. Amma still you don’t on your
phone why? Me na miki da na yi deserving this kind of purnishment a wajenki? Kin
san bana k’asar balle nazo na ji dalili. Ki gaya min gaskiya me ya faru kin daina
so na ne?” Da sauri na d’aga kai ina kallon sanda ya matse tea cup d’in hannunsa
duk da zafinsa na runtse idona. Sai na ji ya saki ajiyar zuciya ya ajiye cup d’in.
Ya furta “Na gode AYSHA, amma may I know the reason?” Ji na yi na kasa b’oye masa
na ce “Mami na bata son relationships d’inmu da kai, ta fi so na yi karatu…”
“Maminki?” Ya furta yana kallona kallon da yasa na ji wani mugun tausayinsa ya
kamani. Sai naga ya cije leb’ensa ya mik’e kawai ya ajiye cup d’in ya fice. Ji na
yi kamar na bi shi amma k’afafuna sun kasa sai b’alle war hawaye na ji daga cikin
idona. Ai kuwa na saka kukan sosai ina yi ina mayar da ajiyar zuciya….
Shikkenan na san na rabu da Ustaz idan ba’a yi wasa ba rabuwa ta har abada!
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢.
Kin fara karanta k’arfe a wuta kuwa? Kin ji da’din labarin Arfa da Viper? Idan
baki fara ba maza ki fara tunda ke kan ki kin san Alk’alamin Aysha cool baya rubuta
shirme. Rubutu ne take yi mai inganci wanda take rubuta abubuwan da suke faruwa
zahiran da hanyar warwaruwar matsalar. Kada ki manta marubuciyar k’anwar Maza ce
gaba da gabanta, cutarwa… maza ki fara ana kan free pages ina tabbatar muku ba zaku
yi nadama ba.
K’ARFE A WUTA……..
Don samun page 12 na Naga rayuwa ga wanda ba za su iya jira ba, ku duba arewabooks
an saka. Ga link d’in nan.
Nagode
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 10
Da daddare muna zaune a ‘daki ni da Mami. Kalba take min tana sake zuga ni akan
kada na yarda na auri Ustaz. Umma ta yi sallama ta tura k’ofar ta shigo. Idanunta
zube a kan mu. Mami kuwa tana ganinta ta tsuke fuska. Zama ta yi a gefen gadon
Mamin tana furta “Yanzu Fateema abin har ya kai haka? Ni ban ga abin d’aga hankali
a wannan maganar ba, har kike neman ki tsiro da wasu halaye na daban da ba masu
kyau ba. Wa’dannan abinda kike bakomai ba ne sai raina Abban su, kin koma san sarai
makomar macen da ta raina Mijinta. Ni ban ga aibun Abinda Abbansu zai yi ba. Kamar
fa gata ya yi muku ke da y’ar taki, auren namiji kamar Ustaz Ai duk uwa ta gari
zata so wa d’anta……” Kallon da Mamin ta mata ne yasa ta tsuke bakinta tana kallonta
da mamaki a fuskarta… “”Ke ce dai baki ga abin tada jijiyar wuya ba, ni na hango
shi, kuma kuka d’auki maganar nan k’arama ni na shirya fito na fito da duk wanda ya
ce zai mata aure a wannan y’an shekarun nata, wallahi ko Human right sai na kai
mutum, in dai da gaske har zuciyarku kun bar min y’ar, ai sai ku bar ni na yi
abinda zan yi da ita, sai dai idan nuna min za ku yi, ban isa da ita ba don ba ni
na haifeta ba….” “A’a Fateema, duk maganar bata kai ga haka ba, Allah ya baki
hak’uri.” Umma ta fa’da tana mik’ewa ta fice daga d’akin. Wani tsaki da ya tab’an
zuciya Mami ta ja tana furta “So kike ta yi zaman aure da gidahumanci kamar yarda
ke kike yi…” Sai na ji kalmar ta min girma a kai, na kuma samu raina da b’aci Umman
ce gidahuma kenan?
Sallamar Abba muka ji a kan mu bayan kusan mintuna 30 da fitar Umma, har a sannan
kuma Mami bata fasa zuga ni ba. Ido ya zuba mana cikin tsukakkiyar fuskarsa da ban
tab’a sanin yana da ita ba. “Tashi ki je sitroom kina da bak’o…” Mami ta ja hannuna
ta rik’e k’am. Ba zata je ba..” Ta furta idanunta cikin na Abba. Wani kallo ya
wurga mata mai cike da nuna zallar b’acin ransa ya furta “Kada mu yi haka da ke
Fateema, kada ki kai ni bango, abin ba zai mana da kyau ba. Cika mata hannu…”
Hannun ya fincike a nata hannun ya ja hannuna muka fice. Har d’aki ya raka ni. “Ki
shirya sosai ki same shi a sitroom, idan kin so ki watsa min k’asa a ido ki zubar
da martabar gidan nan…” Jikina kawai rawa yake, na kasa aikata komai sai share
hawayen fuskata nake. Ga Abba ya ce yana tsaye a parlorn Mamin yana jira na. After
dress kawai na zura akan kayan na fita duk zuciyata a furguce take ba ni da nutsuwa
ko ka’dan. Don ban manta kashedin Mami ba na kada na yarda da zuwa wajen Ustaz idan
kuwa na amince ta san na nuna mata bata isa da ni ba, kuma ba ita ta haifeni ba.
Wannan magana ita take firgitani nake kuma rasa nutsuwa tabbas sun saka ni a tsaka
mai wuya. Hannuna Abba ya sake ja, muka sauka ina kallon Mami da take tsaye ta saka
hannu ta share hawayenta sai na ji nima nawa hawayen sun zubo. Na d’an tsaya Abba
ya juyo yana kallona. “Kina son na b’ata miki rai AYSHA? Kada ki saka na d’aura
miki aure da shi yanzun nan…” Da sauri na girgiza kai. Sai da ya ga na shiga
sitroom d’in sannan ya juya ya koma cikin gida.
Zuciyata kawai bugu take, musamman da na ji k’amshin turaren Ustaz ya mamaye
sitroom d’in. Na yi sallama can k’asan mak’oshi. Shima a k’asan mak’oshin ya amsa
yana sakin ajiyar zuciyar da tasa na d’ago na kalleshi. Jallabiya ce bak’a wuluk a
jikinsa, yau bai saka Alkyabba ba. Kansa dai da farin Ihrami. Idanunsa sanye da
farin glass da ya k’ara fito da kyan fuskarsa. “Shigo ki zauna..” Kamar ba zan
shiga ba. Sai dai na shiga na zauna a kujerar da take nesa da shi. “Dawo wannan
kujerar bana son magana da k’arfi, I feel headache zuwan na dole ne..” Na kalli
kujerar da take kallon tasa na tashi na koma na zauna fuskata a tsuke ina wasa da
yatsun hannuna. Shiru ya yi kansa a k’asa kafin na ji muryarsa mai cike da rauni
yana furta “Ba gaisuwa AYSHA?” Sai na ji kunya ta kamani na d’ago kamar dole na ce
“Ina wuni?” Bai amsa ba, wani kallo kawai yake jifana da shi da yasa yanayin
jikinsa sauyawa, sai naga ya lumshe ido yana murza goshinsa ya furta “Gaya min
laifina Ayshatu? Kike hukunta ni da wannan sigar, na kira waya kin yi rejecting
text no answer, makaranta kin k’i zuwa, gaya min me ya faru?” Shiru na masa kawai
idanuna na zubar da hawaye da zan iya a lokacin kai tsaye zan furta masa ya janye
maganar aurena, amma wallahi na kasa ya min wani irin kwarjini da ba zan iya kallon
idanunsa na furta masa hakan ba. Gashi a k’asan zuciyata wata irin soyayyarsa mai
zafi ce take sake ragargazar zuciyar. Kallona dai yake kafin na ji ya sake kiran
sunana. Kiran da naji har tsakiyar raina. “AYSHA! D’ago ki kalleni ina son mu yi
maganar gaskiya, bana son k’unbiya k’unbiya kuma….
Zan baki tarihin kai na da baki tab’a tambaya ba, zan sanar da ke waye ni da
k’arfin soyayyarki a zuciyata, idan kin amince da aurena to, idan kuma kin ji ban
kwanta miki ba bayan sanin wanene ni sai na k’yaleki na yi fatan Allah ya ha’da
kowa da rabonsa….
Ahmad Sulaiman Saeed shine
Cikakken sunana, sunan da iyaye suka saka min, sunan da kowa ya san ni da shi. Sai
dai a yanzu a makarantar ku da gidanmu na ji sun canja min suna zuwa Ustazun
Aysha….”
Jin abinda ya fa’da ya saka ni saurin d’agowa ina kallonsa. D’aga min kai ya yi
“Banda tambaya har sai na gama, abu guda da na sani ina jin da’din Sunan da aka
canja min, ina kuma fata ya ‘dore har abada idan da alheri a cikin zama na da ke…
Mu uku kacal na gani a gidan mu, nima ban san dalilin da yasa suka zab’i su haifemu
mu ukun ba kamar a k’asar turawa duk da dai d’abiun turawan suke amfani da su… na
so a ce gidanmu muna da yawa kamar yarda nake sha’awar duk wani babban gida ya
kasance, sai dai hakan bata samu ba. Amma na ce alwashin duk matar da na aura sai
ta haifa min yara bila adadin ina son naga y’ay’ana sun kai hamsin…” waro idona na
yi ina kallonsa ya ‘d’aga min kai “Don haka sai ki shirya dafatan Allah ya bamu
masa albarka….” Runtse idona na yi saboda tsananin kunya a raina nake raya sai kace
nace masa zan aureshi?
Ahmad Sulaiman Sa’eed shine Babba, sai Khadija Sulaiman Sa’eed wanda kafin a
haifeta sai da na shekara goma cif. Itama tsakaninta da d’an autanmu shekaru goman
ne, shi yasa na ce miki su iyayena rayuwar turawa suke ko don a can k’asar masu
jajayen kunnuwan suka taso. Mahaifina ya da’de yana aiki a Canada kafin ya dawo
Nigeria ya kafa kasuwanci.
Mahaifina su Talatin ne a gidansu ba zan iya jero