Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
da yake tsaye ya tura hular sa goshi yana furta “A dai rage dogon buri,
idan yarinya ta yi girma da yawa yanzu mazan ma gudun aurenta suke, don sun san
tafi k’arfinsu…” Yana ji ta k’unduma wani zagi ya shige d’akinsu yana dariya.
Haka kuwa aka yi, bayan wani lokaci aka gudanar da bikin Ya. Muhd da Ya sadik. Muhd
da Khadija, Yaya Sadik kuma da Nafisa a lokacin ina Js 3. Amma duk wata cika ta
matantaka ta bayyana a surar jiki na.
✍️
Ina SS 2… al’amarin ya faru. Mun taso daga Islamiyya ni da k’awata Asma’u, muna
tafe muna hira a hankali cikin nutsuwa. Ranar ganin ba kowa a layin sai na ‘dage
hijabi na. Asma’u ta kalleni da mamaki ta ce “Yau kuma Aysha? Lallai kina son idan
Mami ta ji labari har ni ta ha’da ta ci mutunci na kenan?” Tab’e baki na yi, ina
yamutsa na fuska na ce “Ai layin ba kowa….kuma ma waye bai sanni a layin nan ba?”
Cigaba ta yi da bani labarin wani series da ake yi a Mbc bollywood wanda na yi
missing ban kalla ba, sabida girki da Mami ta saka ni a daidai lokacin.
Murmushi kawai nake saki… Zuciyata ce ta wani irin bugawa daidai lokacin da muka
ha’da ido da shi yana tsaye a gefen wani gida da ake gini ba’a k’arasa ba…” Da
sauri na ja nik’ab d’ina na mayar ina jin yarda sautin bugun zuciyatta ya tsananta.
Tabbas na san fuskarsa a sunna t.v matashin Malamine da yake tafseer a duk azimi.
Ba wanda bai san Ustaz Ahmad ba. Saboda yarda yake d’an gayu komansa mai kyau ne
yana kuma ji da tashen Naira. Asma’u ta furta k’asa k’asa “Ke AYSHA kamar Dr. Ahmad
sulaiman ko?” Ban amsa mata ba, k’irjina dai ya cigaba da bugu. Sam zuciyata kasa
cigaba ta yi da saurarar labarin da Asma take bani saboda wani yanayi da na fa’da
mai girman gaske..
Tabbas tunda nake ban tab’a ganin mutumin da jallabiyya ta yiwa kyau kamar wannan
mutumin ba. Ga wani azababben k’amshin turarensa da ya maye wajen gaba d’aya. A
kallon da na masa sai naga ashe har ya fi kyau a fili. Yana da haske sai dai ba
sosai ba. Idanunsa farare tas kuma mayalwata. Cikakkiyar gira ce da shi da gashin
ido kamar yarda gashin kansa yake cikakke kuma bak’i si’dik. Duka wannan na gani ne
a guntun kallon da na masa.
Asma tana shiga gida nima na fa’da gidanmu da sauri tunda mak’ota muke da su. Shi
kuma Ustaz gidan da yazo gidan yana kallon gidanmu.
Ban bari kowa ya ji shigowata ba na haye sama da sauri na shiga d’akina. Haka kawai
nake don sake ganinsa don na san windown d’akina yana kallon gidan da yazo. Ina
d’aga labulan kuwa na hango shi yana tsaye still suna magana da Lawal da ya kasance
d’an mak’otan mu. Idanunsa na ga ya juyo yana kallon gidan mu kamar mai nazarin
wani abu… Daidai lokacin Mami ta shigo tana k’wala min kira. Da sauri na saki
labulan windown alamar rashin gaskiya bayyane k’uru k’uru a cikin idanuna. Ba ta yi
min magana ba sai takowa da ta yi zuwa gaban windown ta d’aga labulan tana furta
“Uban me kike kallo anan d’in?” Idanunta ya sauka akan Ustaz da sauri ta juyo tana
kallona baki sake ta furta “Namiji kike kallo Aysha? To Uban me ya ha’da ki da
shi?”
Hantar cikina ta ka’da… bakina na rawa na furta “Babu komai Mami….
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
Wancan group d’in ya cika Wanda Bai samu Shiga group 1 ba ya Shiga 2. Amma don
Allah idan kana group 1 kada ka Shiga 2 don duk Abu d’aya ne.
A shiga group, ba Zan juri posting a kowane group ba, ba kuma Zan juri a dinga cewa
Na tura daga farko ta private ba. Hankalinka kwance ka shiga group kawai.
Nagode[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 5.
Mami ta zabga tsaki tana sakin labulan tana kallo na ta furta “Idan ma shi kike
kallon, ki tsaya ki saurareni da kyau.” Ta fa’da tana jan kunnena “Koda wasa kada
ki sake ki saka wani namiji a ranki, a yanzu dai kam don ko me zai faru ba zan bari
a aurar da ke ba, sai na cika burina na kin zama wani abu a fannin ilimin boko.”
D’aga kai na na yi, ina lumshe idona. Ta fice da sauri ina jin b’acin rai ma ya
mantar da ita abinda ya kawo ta.
Bu’de idona na yi a hankali ina sakin ajiyar zuciya. Ba tare da damuwa ba na sake
yaye labulan d’akin. Daidai lokacin da Ustaz ya d’ago yana sake kallon gidan mu,
ban damu ba na tsaya na kalleshi sosai don na san ba zai ganni ba, glass d’in yana
da duhu daga waje ba’a ganin wanda yake ciki.
Na saki ajiyar zuciya ina kallon sanda ya shiga motar sa yana sake bawa Lawal hannu
suka yi misabiha. Ya ja motar ya bar wajen. “Allah ya yi halitta…” Na furta a
hankali ina kai wa saman gado na zauna. Har a lokacin yanayin bugun zuciyata bai
koma daidai ba.
Shikkenan na samu abin yi tun daga ranar da na gan shi, ban sake komawa daidai ba.
Kullum cikin tunaninsa nake da burin sake ganinsa koda sau ‘d’aya ne a rayuwata.
Ranar da sati ya zagayo ranar wata lahadi still mun dawo Islamiyya da Asma’u kamar
wancan lokacin. Asma ce take ta surutunta ni kuwa bakina shiru, don wani irin
yanayi nake ji a zuciyata ga bugun zuciyartawa ya sauya. Muna doso layinmu na ji
mayataccen k’amshin turarensa wanda ba zan tab’a mantawa ba. Da sauri na sauke
Nik’ab d’in don kuwa na tabbatar shine duk da bayansa kawai na gani still sanye
yake da jallabiya mai kyau brown kansa da hula tashi ka fiya nace mai tsadar. Muna
doso ta inda suke zamu wuce don dole sai ta nan d’in na ji k’afafuna sun fara rawa
kamar ba zasu d’aukeni ba. Duk da nik’ab ne a idanuna na ga ya ‘dago yana kallon
inda muke sai kuma suka yi shiru da hirar da suke. Da k’yar na saita kaina na nutsu
muka shige su. Sai da na shiga gate d’in gidanmu sannan na saki ajiyar zuciya a
hankali ina furta “Ya rabbi! Me ke faruwa da ni ne?”
Bayan kwana biyu ina zaune a ajin mu ja Islamiyya. Aka aiko kirana. A matsayin da
nake kai na shugabar makaranta na san ba wani abu bane don an aiko kirana d’in,
amma wannan karan sai na ji zuciyata ta buga sosai. Ido na tsurawa mai kiran nawa.
Har ya ji haushi ya furta “AYSHA magana fa nake.” Da sauri na amsa da “To gani
nan.”
A Office d’in Headmaster na tsaya ina knocking a hankali. Muryar Malam d’in na ji
yana furta “Bismillah Ayshatu…” Na yi sallama na shiga, k’amshin turarensa ya doso
hancina har ban san sanda na ware ido ganin Ustaz a zaune ba idonsa akan wani
littafi da ke hannunsa. Wallahi Allah ne ya yi ba zan fa’di ba, Saboda zallar
rashin nutsuwa. Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da yatsuna. Har Malam ya gama
rubutunsa ya d’ago yana kallona “Gaisuwa fa Ayshatu?” Da sauri na juya na kalli
Ustaz da ya yi kamar bai san da ni ba a wajen. “Ina yini?” Bai d’ago ba na ji dai
ya masa murya a k’asa “Lafiya..” D’an tab’e bakina na yi duk da na ji haushinsa, na
mayar da hankalina kan Malam. “Ki je maza ki sanar da duk ajujuwa akwai assembly
idan an idar da sallah..” Na amsa da sauri don burina fita daga office d’in kafin
halin da nake ciki ya bayyana…”
Haka kuwa aka yi, ana idar da sallah ba wanda ya tashi daga babban filin harabar
makarantar. Kowa ya zauna ya kuma nutsu ana jiran fara assembly. Duka Malaman
makarantar suna zaune sun kame akan kujerunsu. Mu kuma muna tsaye don lura da masu
surutu. Wajen tsit baka jin saurin komai. Malam Kawu ne ya nuna ni da nufin nazo
wajensa. Ina isa ya furta “Ki fara karatu, Yanzu Malam Babba zai zo.” Na mik’e na
d’au speaker d’in ina fara karatu ya yi daidai da shigowarsu. K’asa kawai na yi da
kai na na cigaba da karatuna kawai cikin muryar Shureim da na k’ware da karatu da
ita. Ina kallo Ustaz kawai ya lumshe idonsa yana jijjiga k’afa a hankali.
Sai da nace sadak’allahul azeem sannan ya bu’de idon nasa ya sauke su a kaina. Ji
na yi tsigar jikina ta tashi. Da k’yar na ja jiki na koma inda nake na zauna don
kam ba zan juri tsayuwa ba.
Malam Ahmad ne ya fara jawabi da sanar da su babban cigaban da makaranta da ta samu
na zuwan Ustaz Ahmad da son d’aukar wani darasi a makarantar…” Kabbara da ihu
d’aliban suka saka cikin matuk’ar murna da farin ciki.
Bayan ajiye loudspeaker d’insa Malam Kawu ne ya d’auka ya ‘dan yi barkwancinsa
sannan ya sanar da cewa ya barwa Ustaz abinda har zuwa sanda zai bar makarantar.”
Ta cikin nik’ab na ware ido jin abinda ya ce don ajin Malam kawu nan ne ajin mu,
gefe guda kuwa na zuciyata wani irin farin ciki ne mara misali a cikinta. Haka aka
tashi zuciyar kowa cike da farin ciki. Ina ji y’an mata suna ta yaba Ustaz haka
kawai sai na ji raina ya b’aci tsananin haushi ya shiga zuciyata, ban sani ba ashe
wannan shine kishi.
Kashegari da wani irin ‘doki na yi shirin makaranta, karo na farko har da mutstsika
Lipstick a lab’b’ana sai naga na yi kyau da sauri na saki nik’ab d’ina tun kafin
Mami ta gan ni da jambaki ta min masifa.
Sai dai na makaro ina d’aga kai na hangota ta cikin mudubi fuskarta a ha’de take
kallona. Ta iso inda nake zuciyata ce ta dinga harbawa da k’arfi. Saka hannu ta yi
ta cire nik’ab d’in, ta kuma saka yatsa tana zagaye lab’b’ana tana sakin murmushi
ta furta “Jambaki AYSHA? Jambaki kika saka zaki makaranta? Me kike son b’oye min
ne?” Lumshe idona na yi ina jin zuciyata na bugu da mugun k’arfi. “Kada ki fara
AYSHA, kada ki fara abinda zamu zo muna k’aramin yak’i da iyayenki a gidan nan.
Goge shi tas idan baki yi wasa ba tsaf zan cireki daga Islamiyyar na samu Malamin
da zai dinga koya miki…” Da sauri na rik’e hannunta “Don Allah Mami kiyi hak’uri
kada ki raba ni da makarantata, In sha Allah ba zan sake sakawa ba. Kuma wallahi
bana kula kowa ko Asma ki tambaya…” Murmushi kawai ta saki ta janye hannunta. “Zan
bincika..” Daga haka ta fice bayan ta saka ni na goge jambakin dama ni ko kalli
bana sakawa ina da kwallina daga indallahi. Na saki ajiyar zuciya ina fita daga
d’akin.
Shiru makarantar da alama ni da Asma ne muka fara zuwa. Muna shiga aji Asma ta fice
don itace da Duty ranar. Sai na zauna ni ka’dai na bu’de kur’ani na soma tilawa.
Don dokar Tahfiz ce duk wanda ya fara zuwa shi yake fara karatu a lokacin….
K’amshin turarensa da sallamarsa ne ya saka ni yanke karatun cikin fa’duwar gaba.
Na kuma kasa bu’de baki na amsa sallamar…
Tsaye ya yi yana kallona bai shigo ajin ba, ga shi nik’ab d’ina a d’age yake. Na
saka hannu zan ja nik’ab d’in k’asa ya furta “Ba kya amsa sallama ne Malama…”
Wallahi jin muryarsa ka’dai sai da ya razanar da zuciyata. Muryata na rawa na ce
“Alaykassalam…” Murmushi ya d’an saki ya isa wajen zamansa. Sai da ya zauna ya
furta “Ina sauran y’an ajin? Ni fa bana son makara, don haka dole a kiyaye…” shiru
na masa don bani da nutuswar da zan iya cigaba da amsa masa. “Cigaba da karatunki…”
Ji na yi kamar na zunduma ihu. Ta ina zan iya karatu wallahi ba zan iya karatu daga
ni sai shi a yanayin da nake ciki ba… d’ago ido ya yi ya d’an kalleni ya sake furta
“Cigaba na ce….” Ji na yi kamar na zunduma ihu. Allah ya taimake ni sai ga Asma ta
ranga’da sallama cak ta tsaya ganin sabon Malamin. Gaisheshi ta yi ya amsa mata
yana d’an tsuke fuska. “Kin makara ki juya…” Da sauri ta ce “Wallahi Malam ba
makara na yi ba, na je duty ne ka tambayi AYSHA ma ka ji…” “AYSHA?” Muka ji ya
fa’da, wanda yasa na yi saurin d’aga kai don a zatona kirana ya yi, sai naga kawai
ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce “Ku bu’de Manhajjul Muslim… A ina kuke?” Asma
ce ta amsa ni kuwa sam hankalina baya wajen…
Tunda ya fara karatun bai ‘dago ya kallemu ba y’an aji kuma duk wacce tazo sai ya
tsayar da ita ya ce ta makara… ga karatun da yake mana mai mugun saka kunya don
karatu ne akan yarda ake wankan janaba da abinda yake sabbaba shi..
“Yanzu kun gane yarda ake wankan ko? Da kuma sabbabinsa?” Asma ce kawai ta ‘d’aga
kai, ya juya yana d’an kallo na.. “AYSHA kin gane menene janaba, sababinta da kuma
yarda ake wankanta?” Runtse idona na yi jikina har ya fara rawa musamman idanunsa
duka ya zubesu a kaina. “Ba kya ji ne? D’auke wannan bak’in k’yallen ki min
cikakken bayani….” “Ya ilahi na furta ina jin kamar na zunduma ihu ta ina zan fara
wannan abin kunyar…. “Ke samo min ruwa a office mai sanyi, ke kuma ina jin ki?”
Ina kallo Asma ta fice tana dariya k’asa-k’asa. Ji na yi kamar na ruga na gudu
musamman da ya jawo kujerarsa daf da ni, ina sake shak’ar Mayen turarensa… “AYSHA”
ya fa’da cikin wata irin husky voice “D’ago ki kalleni..” Da k’yar na d’ago sai dai
na kasa kallon nasa. Kallona yake shi kuwa kamar ya samu Tv fuskarsa d’auke da
murmushi ya furta “Answer my question before na ha’da duk makarantar nan ki musu
lecture akan haka…. menene janaba? Hukuncin ta a musulunci da yarda ake wankanta?”
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
Albishirinku! Albishirinku!!
Yau ne fa! Yau ne litattafan Bright pens za su fara zuwa muku da izinin Ubangiji….
1.K’arfe a wuta. AYSHA cool marubuciyar k’anwar maza.
Hadarin gabas Nazeefa Sabo Nashe. marubuciyar Me Zan Yi da ita?
Mutallab daga harzik’ar marubuciya Nimcyluv
Zaytoon zai zo daga Alk’alamin Malamar Adabi Zee kumurya.
Za’a fara sakar muku K’arfe a wuta kafin zuwan sauran In sha Allah.
Don samunsa a sauk’ak’e ku yi joining wannan link d’in…
Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/FTFuiA4woYJCgNQrcBYGX4
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Page d’in kacokam naki ne k’anwata Nimcyluv hope na goge lefina Masoyiya 🤣
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 6
Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
Ji na yi zuciyata ta cigaba da bugu, na kasa amsa masa tambayar ya bi kuma ya tsare
ni da ido. Hannayena kawai nake matsawa don ban san me zan ce masa ba. “Ba ki ji
ba? D’age wannan bak’in k’yallen don ban sani ba ko hararara kike..” K’iris ya rage
na fashe da kuka saboda yanayin da ya saka ni, ga mayen turarensa ya bi ya hana ni
sukuni… “ki d’aga na ce, Are you dumb?” Hannuna na rawa na saka na d’age nik’ab
d’in. Na runtse idona saboda har ga Allah ba zan iya cigaba da kallonsa ba… ina ji
ya sauke ajiyar zuciya yana furta “Kin yi passing wannan Oya tashi ki fita sallah…”
Tun kafin ya kai k’arshe na mik’e da sauri ban san yarda aka yi na isa bakin k’ofa
ba, ni dai na gan ni a waje. Na tsaya ina sauke numfashi hannuna dafe da k’irjina
da take matsanancin bugu… Ina jin k’amshin turarensa alamar nan yake tahowa na zuba
sauri har da ‘dan gudu don kada ya riskeni a wajen…
Yanayin tsarin karatun nasa ya saka y’an aji aka daina makara saboda ana son
karatun nasa sosai. Na san wasu y’an matan da yawa ba don Allah suke zuwa da wuri
ba. Ga shi su cab’o Uban kwalliya a fuska a baza k’amshin turare ana yi ana zuba
iyayi duk don Ustaz ya yaba. Shi kuwa sam baya kulasu idan zai shigo ma bak’in
glass yake sakawa ya rufe idonsa…
Wata rana da ta kasance ranar Talata ce. Sam kasa yarda na yi na je makarantar
saboda da na duba maddar da zamu yi sai naga fik’hu ce. A rayuwata ina kunyar Ustaz
shi yasa sam ba zan iya zama ya karanta Fik’hun a gaba na ba, kada a yi irin ta
ranar da muka karanta Babul janabati… Don haka yau ina duba littafin naga za’a yi
bayani ne akan ruwa kashi uku da yake fitowa daga gaban mace na ji sam ba zan iya
zuwa ba. Sanda Asma ta biyo min ta shiga d’akina tana kallona ta furta “AYSHA me ye
haka?” Nima kallon nata na yi nace “Me kika gani?” Ta saki tsaki tana kallon agogo
“Yau kuma wani sabon abu zaki tsiro da shi, makara? Abinda ba halinki ba. Kin san
dai Ustaz Ahmad ya jaddada rashin son makara ko?” D’an yamutsa fuska na yi “Ke
makarantar ce fa ba zani ba.” Ta waro ido “Dalili?” “Bana jin da’di ko na je ba
fuskantar karatun zan yi ba. Ki ba shi uziri na.” Asma ta ‘d’au jakarta tana furta
“Allah ya baki lafiya, amma kamar ciwon naki bai kai inda ba za’a iya zuwa
makaranta ba..” Ban mata magana ba har ta fice daga d’akin. Na saki ajiyar zuciya
duk ina son zuwa makarantar ko don naga Ustaz wannan karatun da zai yi yau ne zai
hana ni zuwa. Allah ya san ba zan iya zama yana zayyano min karatun nan me saka
kunya ba…
Kashegari da wuri na shirya musamman ganin maddar Hadith da Tajweed ne da mu. Asma
ta biyu muka tafi..
Ajin har ya cika y’an mata sai baza k’amshi suke. Muka shiga muma muka bi ayari
muka zauna. Ina ji wata sanda Ustaz ya shigo k’asa k’asa ta saki ajiyar zuciya
“Wallahi Zahra mutumin nan ya gama sace zuciyata..” Zahran ta harareta tana furta
“Ke ka’dai? Ai kowa nan da kike gani yana fatan ya taya shi…” Wani abu ne ya tsaya
min a zuciyata. Na d’aga idona na kai duba na gare shi duk da idona a cikin nik’ab
yake ina kallon yarda ya tsuke fuskarsa ya shigo ya ja kujera ya zauna. Fuskar a
yamutse ya furta “Kada na sake ganin wata da