Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
d’aura aure. Haka kika sake zuba kyau.” Na ‘dan yi dariya kawai ina kallon
Umma na, da ko kallona ba tayi ba sai dai murmushi sam ya kasa barin fuskarta. Na
da’de anan d’in kafin na zame jiki na koma sama, inda y’an uwan Mami suka cika
wajen. Suma da farin cikin suka tare ni. Mami kuma
Ta ware a cikinsu sai farin ciki take. Na zauna daf da ita na kwanta a jikinta
kaina a saman cinyarta na lumshe ido. Barci mai nauyin gaske ya ‘daukeni, na san
barcin da ban yi bane a daren ranar yake d’aukata.
Mami bata tashe ni ba sai daf da la’asar na ‘dan ware idona. Ina kallon wajen, ba
kowa sai Mamin da k’awayenta guda biyu. Duk suka zubo min idon da yasa har na ji
kunya na mik’e na bar wajen da sauri na shige ‘dakina.
Sallah na yi ina idar da sallahr na sauka k’asa wajen Umma. Har lokacin jira nake
na ji Ustaz ya kira ni amma bai kira ba. Kawai sai zuciyata ta dinga bani yana can
wajen amaryarsa. Don takaici har wata k’walla ce ta so zubo min. Na matse ha’de da
tura k’ofata parlorn Umma. Ba kowa a parlorn da alama duk bak’in sun tafi. Sai Umma
ita ka’dai da k’anwarta suka ‘dago suna kallo na. Umma ta d’auke kanta. Sai Anty
Zee ce ta ce “Shigo mana Aysha kin ci abinci?” Na ‘d’aga kai na “Na ci Anty.” Ta yi
murmushi tana fa’din amaryar da ba lalle, wannan aure naki Aysha Ai shine
bagatatan. Yaushe ya ce zaki ki gaida iyayensa?” Wani farin ciki ya shige ni don
abinda nake son na ce kenan, amma ba kasa gayawa Mami balle Umma. Na gyara zamana
ina furta “Yau ya ce Anty..” Ta saki murmushi tana fa’din “Kin ji ko Yaya, ai na
san wallahi kawai zan ce ne, ace kawai mutum ya auri mace sai ya zuba mata ido
alhali sabon shiga ne a aure a ce wani sai ta k’arasa karatu, karatun me Allah na
tuba a gidanta ba zata yi karatun ba, wallahi kada ki bi ta wani karatu ki tattara
y’a ki mik’a d’akin Mijinta….” Umma ta waro idonta tana furta “Rufa ni ki saya, ni
meye nawa da za’ace ni zan saka a kaita d’akin Miji, ki bar uwarta y’ar a lallab’a
da yaya ma aka samu aka shawo kanta a yau d’in. Shekara kamar yau ne, Idan Allah ya
kai mu.” Anty ta yi d’an tsaki tana kallon Umman ta ce “Allah ya kai mun, idan da
rabon an yi taron suna ne ba taron biki ba sai mu ce san barka…” Da sauri na mik’e
na fice daga ‘dakin cikin matsananciyar kunya. Na koma saman Mami. Bak’in sun tafi
sai ita ka’dai zaune ta zuba hannunta a k’unci. Har na zauna daf da ita ba ta sani
ba sai da ba dafa ta sannan ta juyo a razane tana d’an kallo na. Ta furta “Aysha
ce?” Cike da tausayinta na ce “Mami kin ci abinci?” Ta ‘d’aga min kai tana d’an
murmushi. Na yi shiru ina wasa da yatsuna na furta “Mami Ustaz ya rok’i alfarmar
yana son na je gidan su yau after magriba….” Mami ta ‘dago tana kallona, idanunta
suka bayyana tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Ta gyara zamanta tana sakin
ajiyar zuciya sai kuma ta kama hannuna murya a raunane ta ce “Ba zan hanaki bin sa
ba AYSHA, don yanzu duk duniya ba wanda yake da iko da ke sama da shi. Sai dai zan
rok’i alfarmar ki tsare jikinki, don maza mayaudara ne idan dama jikin naki yake so
da zarar ya kusanceki zai iya sakin ki tun kafin ki tare…. Ki min alk’awarin ba
zaki bari Ustaz ya kusanceki ba..” Na d’aga kai na, ina ji har a zuciyata na amince
da abinda Mamin ta ce. Ta sakar min murmushi ta furta sai ki shirya da wuri kada
yazo yana jiranki amma banda saka turare… na d’aga kai.
Da magriba ina idar da sallah Mami ta shigo d’akin hannunta d’auke da wata leda. Ta
zauna a gefen gado. Tana bu’de ledar wata doguwar Riga ce mai masifar kyau kalar
bak’a da stone golden ta yi matuk’ar kyau. “Ki saka wannan, sai ki je gidan nasu,
idan kin je kuma bana son rawar kai ki nuna musu ke mai tarbiyyace.” Na amsa ina
godiya. Bata amsa ba ta wuce ta fita.
Da wata irin murna na zura rigar a jikina na shafa powder sama sama, sai na yi
rolling. Ba k’aramin kyau na yi ba ni da kai na na sani. Sanda na fita parlor sai
naga Mami bata nan. Na san tana k’asa na sauka k’asan don Ustaz ya isheni da kiran
waya.
Yarda na zata kuwa suna tsaye a kitchen ita da Umma. Suka juyo suna kallo na. Anty
Small ta furta “Ma sha Allah, Allah ya yi halitta.” Mami ta dafa ni tana furta A
dawo lafiya, and take care AYSHA. Ga wata leda nan ki kaiwa Inlaw d’inki abinda ke
ciki…” Na d’au ledar ina murmushi na fita k’ofar gida don na san Abba yana
masallachi sai dai su Umma su gaya masa.
Cikin takun nutsuwa na isa bakin motar na saka hannu na bu’de k’ofar gaban motar.
Gaba na ya yi wani irin mugun fa’duwa ganin Habibteeyn Ustaz a gaban motar, ta sha
kwalliya ta yi masifar kyau tana zabga k’amshi. Murmushi ta ‘dan saki ni kuwa
fuskata a tsuke na juya da nufin komawa gidanmu don wallahi in dai da wannan za’a
ba zan je ba…. Kai bana jin ma zan iya kishi da zanka’ded’iyar mace irin wannan
habibteeyn ta Ustaz ba. Ta ko ina ta fi ni….
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 16.
16…
AYSHA! Na ji Ustaz ya fa’da cikin muryarsa da take bayyana ginshira. Na ja na tsaya
sai dai ban jiyo ba, Saboda bana son na jiyo d’in naga Habibteeyn Ustaz. Rufe
k’ofar Motar da aka yi ya tabbatar min da ya zo wajen. A daf da ni ya tsaya. Kafin
na juyo na ji hannunsa a cikin nawa hannun. Da kansa ya juyo da ni yana k’ok’arin
lalubar idanuna ni kuwa na ja na runtse idon. “Wuce mu tafi.” Ya ce cikin wani cool
voice da ta so ta saka raunin da yake zuciyata ya bayyana… “Ni ba zan shiga ba..”
“Me yasa?” Ya fa’da bayan jin abinda na ce. Na d’an turo bakina ina furta “Ka je
kawai, ka je ka kaita ni na hak’ura..” wani murmushi ya saki yana furta “Tafiya da
ita ne ba kya so?” Na d’aga kai na. “Me yasa zaka zo da ita?” Na fa’da hawaye suna
son zubo min. Ustaz murmushi kawai ya saki ya ce “Maza ki yi kuka a gabanta ta
raina ki.” Na matse hawayen ina kallon cikin idonsa da suke lumshewa kamar me… “Ku
je zan saka Ya Aliyu ya kai ni a motar Abba..” cute smile d’in ya sake yi yana jan
hannuna har kamar zan fa’da jikinsa. Ya furta “Yanzu dai ba kya son Third Party a
Cikin tafiyar mu ko?” Da sauri na d’aga kai. Sai naga ya saki hannuna yana murza
goshinsa a hankali. Kallon k’asan ido yake min kafin ya jefa min tambayar da ta so
saka ni zubewa a k’asa tsabar yarda jikina ke rawa. Cewa ya yi “Kina so mu
ka’daice, in har kika yarda muka tafi mu ka’dai zaki min deep kiss a cikin motar…”
ya fa’da yana murza hannuna. Da sauri na janye hannun ina furta “Mu je kawai, amma
ta koma baya tunda nice Uwargida.” “Done wifey ya furta yana dariya k’asa-k’asa.
“Hannunki AYSHA so soft, har bana son na daina tab’awa…” Da sauri na janye hannun
ina dubawa naga ko Maigadi ya ji, sai na ga ma baya wajen. Muka isa bakin motar
hannuna cikin nasa yana ta murzawa. Ja na yi na tsaya ina jin zuciyata kamar ta
buga, ganin yarda Ustaz ya durk’usa daf da ita yana gaya mata magana. Sai naga ta
‘dan ha’de rai ta fito tana min wani kallon banza ta shiga bayan motar. Murmushi na
saki ina jin duk wani bak’in cikina ya yaye. Na shiga gaban Motar cikin jin haushin
yarda da ta zauna a motar…
“Baku gaisa ba?” Muka ji muryar Ustza daga sama bayan
Mun fara tafiya. Shiru kowa ya yi har sai da ya sake furta “Ba kwa ji ne ina
magana…” Sannan ta furta “Ina yini?” A ciki na amsa don sai naga kamar ta fini
sauk’in kishi.
Wani irin wawakeken gate muka shiga, inda muka tarar da makeken fili. Ustaz ya yi
Parkin ina kallo ta fice cikin takun isa da son ta nuna min ita ta san gidan tunda
cousin ‘d’insa ce. Na d’an ha’de rai ina cije leb’ena idona suka kawo ruwa. Ustaz
ya sunkuya yana kallona ka’dan, tunda mu ba mu fita daga cikin motar ba. Ji na yi
ya kaiwa bakina sumbata ya kuma lashi d’an guntun hawayen da ya zubo min. “Kukan
menene?” Ya furta a cikin kunnuwa na. Da sauri na rintse idon, don na lura Ustaz so
yake ya kashe ni da salonsa. “Mu je mana Zauj, ko sai na d’aukeki..” na d’an turo
bakina ina furta “Ba ga shi can har ta wuce ba, so take ta nuna min lallai ta fi ni
iko da gidan ku.” Yatsa ya saka yana zagaye lab’b’ana. “Wato ashe bakin nan ya iya
tsiwa? Amma da kike kasa sak’at idan kin ganni a wuri. Mu je na raka ki kin ji
tunda ita ta nuna mana gidansu ne ta tafi ta barki.” Ya fita ya zaga ya bu’de min
mota. Zai rik’e min hannuna na janye ina d’an duban hanya na furta “Ka bari mana,
kada wani ya gan mu?” “And so what? Idan an gan mu Ai ba haramci muka aikata ba
ko?” Ya fa’da yana tsotsar bakina ka’dan. Na lura lips d’ina suna burgeshi. “Ke
halak d’ina ce Aysha, a yanzu ba wani shamaki tsakaninmu da ke, sai wancan karatun
da Maminki ta kafe sai kin yi,
Wallahi ba ruwana duk ranar da ta wayi gari ta ganki da ciki….” Da sauri na waro
ido jin abinda ya fa’da. Ya lumshe ido yana d’aga kai ya ce “Am serious Eesh baki
san yarda nake ji akan ki ba…” ya fa’da yana jan hannuna.
Da sauri na janye hannun nawa ganin yarda mutane suka fara fitowa daga k’ofofi
daban daban an ware ki’dan larabawa suka zagaye mu da Ustaz. Sai fa’dar Marhababuki
lale suke. Kana ganinsu kaga jinsin larabawa don farare ne k’al da su. Ustaz d’an
murmushi ya saki ya yi saurin zamewa ya bar ni da su. Matar mai kama da Ustaz kwabo
da kwabo ita ta k’araso inda nake ta kama hannuna tana ha’dani da jikinsa tana
fa’din “Marhababuki Ibnateey…” Wani irin sahihin k’amshi ne kawai yake fita ko ta
ina a gidan. Suka ja hannuna zuwa cikin gidan. Kaina a k’asa k’irjina sai bugu
yake, amma matar bata cika hannuna ba. Sai da muka isa cikin babban parlorn gidan.
Tabbas gidan su Ustaz ba k’arya ya ha’du kana ganinsa ka san sun ci sun tada kai da
naira, babu gami sam tsakaninsa da namu gidan. A kan kujera ta zaunar da ni, amma
sai na zame na zauna a k’asa. Ina gaishesu a kunyace.
Kishiya ta ce tazo kusa da ni ta zauna. Tana kama hannuna na ji kamar ta zubar
garwashin wuta a hannun, da sauri na janye sai na ji ta yi dariya ta furta “Am not
his wife, he was just joking… ni k’anwarsa ce the only Sis da yake da ita….”
Innalillahi na furta a hankali kunyar rashin mutuncin da na mata nake ji, dana sani
ya shige ni sosai. Ta yi dariya sosai ta fara bawa mutanen parlorn labarin acting
d’in da nake idan ta ce musu ni matar Ahmad ce. A raina na ji ba zan k’yale Ustaz
ba sai na rama, wannan ai ba wasa ba ne. Dariya sosai mutanen parlorn suka fara.
Mommy ce ta ce “Ahmad ba zai miki kishiya ba, ke ka’dai kin ishesa In sha Allah,
Son da Ahmad yake miki ba a kwatancensa Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a
d’ayyiba.” Ta juya tana kallon k’ofa. Ta furta “Ibnateey maza kirawo min shi, a yi
addu’a kafin a fara cin abinci..” Da sauri kuwa naga Habibteey ta mik’e ta nufi
inda zata kira shi.
Sai ga shi ya fito cikin wata jallabiya brown color yana shigowa da ni ya fara
ha’da ido. Na d’an turo bakina ina masa hararar gefen ido, kafin na sake jan mayafi
na rufe fuskata. “Ahmad kazo ka ciyar da matarka kamar yarda al’adarmu take at
first day of marriage.” Wata mai kama da Mommyn ta fa’da tana sake janyo Ahmad zuwa
inda nake. Zuciyata kawai bugu take ina tunanin ta yaya zai ciyar da ni? Daf da ni
ta zaunar da shi har jikina yana ha’duwa da nasa. Ta kawo masa kayan abincin
gabansa. Da kansa ya yi serving d’inmu. Kafin ya ‘dago yana kallon auntyn nasa, ta
‘d’aga masa kai “Oya ka fara mana, ina jira zan yi pic..” Hannunsa ya saka ya
‘d’aga mayafi na. Da sauri na runtse ido, ganin ya kai dabino guda baki na. A
hankali ya furta bu’de bakin…” “Amma ka san ba haka muke ba ko?” Anty ta fa’da
ranta a b’ace. Ina kallo ya d’an yi dariya, sai kuma ya mayar da dabinon bakinsa ya
gutsira ka’dan ya tauna ban yi auneba na ji bakinsa cikin nawa yana zuba min
taunannen dabinon. Jikina ne ya fara rawa da sauri na rik’e numfashina da yake son
d’aukewa ganin still YUstaz bai cire bakinsa a cikin nawa ba sai juya harshensa
yake cikin wani salo da lumsassun ido, sai da ya tabbatar na ha’diye sannan ya
janye yana ‘dan murmushi. Ihu da Kabbara suke kawai a gidan. Aka dinga mana hotuna
ni kuwa duk kunya ta saka jin jikina wani iri na sunkuyar da kaina kawai na kasa
ha’da ido da kowa. Anty ce ta ce Khadija ta tafi da ni d’akinta sai a kai min
abincin can tunda na kasa sakewa da su, su al’ada garinsu ce haka, ba abin kunya ba
ce, rana ce mai mahimmanci a wajensu da ake wa saurayin da bai tab’a aure ba, don a
ga yanayin da zai shiga a yi dariya idan an ga abinda zai yi a first deep kiss
‘d’insa. Ni dai tuni na bi bayan Khadija jikina na rawa muka isa ‘d’akinta.
Muna shiga ta janye mayafin fuskata tana dariya. “Bud’e fuskar Anty AYSHA na ganki
da kyau, tunda dai nan daga ni sai ke..” Knocking muka ji. Khadeeja ta furta “Yes
come in..” k’aninsu ne ya shigo yana d’an hararar Khadija ya furta “Mhmmn, I know
kina nan kin saka ta a gaba da surutu kamar parrot…” ta wani waro ido tana furta
“Ridwan am I play with you? Ni kake kira parrot iya get out from here…” Ya turo
bakinsa ka’dan yana furta “Aiken Mommy ne, ta ce ki rakata part d’in Yaya Ahmad su
ci abinci da shi tare…” Na wani irin waro ido, kamar na yi kuka nake kallon Khadija
na ce “Ki gaya mata na k’oshi don Allah…” Khadija ta waro ido tana furta “Ban kai
nan ba, idan ba so kike Ya Ahmad da Anty Danger su gididdiba ni ba..” tana jan
hannuna amma na kasa ta shi. Sai kawai ta fita sai gata ta dawo da wacce na
tabbatar ita suke cewa Anty Danger na ji ta ce “Anty Tasleem to gata nan, ki gaya
mata da kan ki.” Murmushi ta saki tana jan hannuna ta furta “Ta so Inlaw, yau
ranace mai muhimmanci ga duk mai son Ahmad, shima kuma yau rana ce da zai so ku
kasance tare tunda dai ba yanzu za’a kai ki gidan sa ba. Muje ku ci abinci ku yi
hira sosai.” A kunyace na mik’e na bi bayanta hannuna cikin nata, muka ratsa ta
wata k’ofa, Khadija na bin mu a baya, sai da muka wuce wani fili mai kyau kafin mu
dangana da wani d’an gini mai kyau duk da bai cika girma ba. Anty Danger ta saka
hannu a k’ofar ta yi nocking sai ga shi kuwa ya bu’de ina ji Anty Danger ta furta
“aka tabbatar ta ci ta k’oshi ka kuma bata gift mai tsadar gaske wanda ba zata
manta ba, na san ka san me nake nufi ko?” Hannuna na ji cikin nasa kafin ya kalli
Khadija ya furta “Ke bar nan..” Da sauri kuwa ta juya tana dariya ta furta “Su
Ya.Ahmad da mata Ai sai Allah. Anty Danger ma ta juya ya ja hannuna zuwa cikin
k’aramin parlorn mai masifar kyau na zata anan zamu tsaya sai naga ya shiga da ni
wata k’ofa da ta kai mu ainahin wani babban bedroom d’insa… muna shiga naga ya jani
jikinsa ya rungume sosai cikin wani irin sautin murya ya ra’da min “Bari na fara
baki gift d’in da surikarki ta rok’a na baki…” k’ok’arin zame jikina nake Amma ina
ji na yi kawai yana zame d’ankwalin kayana ya cusa hannunsa cikin gashin kaina a
kunnena na ji yana furta “Alhamdulillah Eesh komanki is beautiful ina fatan cikinki
yafi wajenki kyau….” Jikina rawa kawai yake shi kuma bai daina shinshina k’asan
wuya na ba.. “AYSHA ina son ki sosai ke ce rayuwata ki amince min yau d’aya
kawai….”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe:
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎18.
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 18.
Da sauri na kalleta kafin na girgiza kai na. Wasu hawaye na shirin zubo min, wanda
bana komai ba ne sai na jin haushin tsanar da Mami na ta yiwa Ustaz, alhali shi
yana sonta yana daraja ta, don kai tsaye zan iya cewa Ustaz kallon Uwa yake wa
Mami. “Zaki amsa min, ko sai kin gama k’are min kallo? Na ce kin mik’a masa kanki
ne?” Girgiza kaina na yi jin abinda Mamin ta ce. Sai naga ta saki wata ajiyar
zuciya da har ta bayyana ta saman k’irjinta. Tana kallona ta furta “To wankan me
kika yi? Ko da yake…” sai naga ta ‘dan cije leb’enta tana furta “Mhmn, ina ya kai
ki bayan gidansu? Don naga da’dewar da kika yi ta yi yawa, kin saka na kasa barci
fargaba ta d’aya kada ya mayar da ke cikakkiyar mace…•” K’asa na yi da kaina kurum.
Na ce “Gidansu kawai ya kai ni, kuma na da’de ne saboda duk y’an uwansa suna gidan
sun ‘dan ha’da Walima, wai su haka al’adarsu take, ranar da aka d’aura aure dole a
yi Walima ta nuna godiya ga Allah…” Ta ‘dan tab’e baki. “Bayan walimar sai kuka
zauna hira da mahaifiyarsa? A matsayinki na maras kunya ko?” Da sauri na girgiza
kai na ce “Wallahi a’a Mameey, kawai dai ina zaune da sisters d’insa suna jana da
hira…” na nuna mata kayan da suke kan gado na ce “Su