Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
nasa. Ban san sanda na wani irin mik’ewa da
sauri ba don ‘d’aukar Hijabin, sai ji na yi kawai ya jawo ni na fa’do jikinsa ya
saka hannu ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Idona a waje nake furta
Ustaz me ye haka? Ina matar taka?” “D’aya matar tawa tana gidansu Aysha, ga
uwargidan anan.” Ya fa’da min cikin wata murya a kunnena. Da sauri na wani kalar
Zillo na bar jikinsa ina kallo ya yi baya ya jingina da kujera idanunsa a lumshe
yana sakin ajiyar zuciya… ni kuwa kallonsa kawai nake ina mamakin jin abinda ya ce
da gaske an ‘d’aura mana aure shi? Kuma mu biyu da wata. Duk da na yi farin ciki
amma kishi bai barni na bayyana farin cikin ba. Zuciyata na sama da k’asa na dinga
kallonsa still idonsa a lumshe.. na furta “Wai da gaske aurena aka ‘d’aura ni da
kai da wata kuma?” Idanunsa a lumshen ya ‘d’aga kai. A zafafe na ce “Tab’di! Ni
Allah ban ce maka ina son mai mata ba…” “Aysha bana son surutu, ki tashi ki shirya
mu je gidanku, Abba yana jiranki abokai na suna jira su ga matata za su koma
garuruwansu. Ba lallai ku sake ha’duwa ba sai lokacin tariya.” Ya fa’da yana mik’o
min wata leda mai kyan gaske. Ledar na bi da kallo ina amsa ya jawo ni jikinsa.
Kissing ‘din lips ‘dina ya yi ka’dan yana jan karan hancina ya furta “Am sorry for
this, na da’de ina jiran wannan ranar. Sai ga shi Allah ya bani ku ku biyu… “ Turo
baki na na yi cikin matuk’ar jin kunya na sauka daga jikinsa. “Wa yace ki sauka?
Kin san dai ba haramun ba ne ko?” “Ni dai bana so, ka je wajen waccan matar.” Na
fa’da idona na zubar da hawaye. Murmushi ya yi yana furta “Don kuwa baki ga yarda
ta yi kyau ba, ta yi kwalliya sai zabga wani irin k’amshi take mai sanya tunani a
rai. Ke kuwa ko wankan bana jin yau kin yi, saboda kina
Cikin tashin hankalin kin yi rashin santalelen saurayi irina ko?” Turo baki na yi
na shige ciki da sauri. Ina jin sautin murmushin Ustaz.
Sai da na murza key a ‘d’akin don naga kamar Ustaz yau ya cire kunyarsa gaba d’aya.
Wankan na yi sosai har kamar fatata zata futa, don duk dole ina son nafi waccan
matar kyau. Ina cikin zura rigar lace a jikina na ji muryarsa a bakin k’ofa. “Bu’de
Aysha..” wani irin waro ido na yi na furta “Na bu’de na
Maka me?” “Idan ba zaki bu’de ba, answer your phone..” Sai sannan na kai idona kan
wayar naga numberrsa da na yi saving da Ustazu na, tana ringing. Amsa wayar na yi.
“Kada ki yi kwalliya, kada ki saka turare kuma don zaku gaisa da abokaina…” Ya
furta yana kashe wayar. Ban saka turare ba, amma na yi kwalliya don haka kawai ba
zan bari wata can ta fi ni kyau ba. Na fito tsaf da ni cikin laffayar da ta zauna
das a jikina ta fitar da shape ‘dina sosai. Idon Ustaz a kaina yake kallona ya
furta “Cab a hakan zaki fita?” Na ‘dan turo bakina “To ba kai ka kawo kayan ba?”
Mik’ewa ya yi ya isa kusa da ni, yana jana jikinsa da sauri na fara turjewa ya
rik’e ni sosai yana furta “Bana ce kada ki yi kwalliya ba, wa yace ki yi, tsaya na
goge jambakin nan.” Cak na tsaya a zatona gogewar zai yi sai na ji bakinsa a saman
leb’ena yana tsotsa a hankali. Da sauri na waro ido. Ya sake ni yana murmushi ya
bushe min idon da iskar bakinsa. Yana furta “Gobe ma ki sake k’in bin umarnina, ki
je ki sako Hijab, ba zaki fita da wannan abin ba, Ji k’irjinki ji yarda ta fitar da
zahirin Suffar Aysha…” Ya fa’da yana shafa gefen Hips ‘dina. “Anya Aysha zan iya
jira ki gama secondary ‘din nan, kamar yarda Abba ya buk’ata? Ba zan iya ba zan
wahala sosai wallahi, duk da dai ina da wata matar, amma kuma zuciyar tana nan…” Ya
fa’da yana ‘dage min gira ka’dan. Turo bakina na yi ina jin zuciya ta na shirin
tafasa na furta “Ni ka daina min zancen matarka.” Yatsansa ya saka yana zagaye
leb’ena da su, yana murmushi ya sake ba su sumbata sannan ya lumshe idonsa ya furta
“I like those kissable lips, na da’de ina mafarkin wannan ranar.” Shiru na masa ina
jin sauyawar yanayi tare da ni. Sakin ajiyar zuciya ya yi yana furta “Wannan
karatun boko…. Shikkenan maza ki je ki saka Hijab Madam, ana jiran mu.” Na juya
d’akin Anty Khadija. A drawernta na samo Hijab mai kyau da ya shiga da kayan na
saka. Ina fitowa na tarar Ustaz har ya mik’e yana waya k’asa k’asa na ji yana furta
“Ki jira na ce, zan zo yanzu ko Habibteey…” Wani irin duum na ji a raina. Ya mik’o
min hannu yana furta “Zo Aysha ku gaisa da Habibteey…” Banza na masa idona na
shirin zubo da hawaye na fice daga gidan da sauri. Sai ga shi ya biyo bayana na
kulle k’ofar. Banda ina son zuwa gida cewa zan yi ba zan bi shi ba. Ya shiga mota
ni ma na shiga fuskata a ha’de shima bai min magana ba ya ja zuwa gidan mu.
Sai da na ganni a k’ofar gida sannan hankalina ya dawo jikina na tuna da batun Mami
ko ta amince da auren? Gaba na ya fa’di sanin cewa ba lallai ta amince ba tunda ko
jiya da ta je gidna Ya Muhd ban ga alamar haka a tare da ita ba. Zan fita daga
Motar ya ja hannuna ya rik’e cikin nasa yana kallona. “Idan baki saki fuska ba zan
mayar da ke.” Na ha’diye tashin hankali na na furta “Ba wajenta zaka ba?” “Ina
ruwanki, ki yi abinda yake gaban ki, and kada ki sake ina magana ki yi gaba hakan
raini ne, kin ji ko? Idan baku gaisa kun saba ba sai yaushe zaku gaisa, idan na
gama da ke, zan tafi wajenta da daddare kuma ki shirya zan zo na kai ki wajen su
Mommy kafin su yagalgala nama na…” Yawu na ha’diye ina sauka daga motar bayan na
sake nik’ab ‘din fuskata don haka kawai sai na ji ina jin kunyar ha’duwata da
jama’ar gidanmu ban san kalar tsiyar da suka tanadar min ba.
Dariya Ustaz ya yi ganin yarda sam na kasa sake jiki na fita. Ya juya yana kallon
cikin harabar gidanmu. Kafin ya furta ko na kira miki Muhammad ya shiga da ke?” Da
sauri na ‘d’aga kaina. Don hakan zai fi kin sauk’i akan na shiga da kai na. Ina
kallo ya dannna wayar hannunsa ya kira Ya.Muhd. Bai ko d’au lokaci ba, sai ga shi
ya fito fuskarsa d’auke da murmushi yana kallo na. “Amarya..” Turo bakina na yi na
furta “Ya.Muhd, bana so, shine baka gaya min ba sai da aka d’aura auren.” Murmushin
ya sake yi ya ce “Ba gashi yanzu kin sani ba, gaya min are you happy or not?” Ya
kama hannuna muka nufi cikin gidan. Ina ji Ustaz yana fa’din idan na gama yana
jirana a sitroom.
Tsakargidan taf da mutane, ta cikin nik’ab ’dina na dinga ganinsu, y’an Uwan Umma,
Y’an Uwan Abba da y’an Uwan Mami sai hira ake cikin annashuwa da farin ciki. Har
sama Muhammad ya kai ni bai bari an ganni ba, ya shigar da ni parlorn Mami. Parlorn
nata shiru ba kowa. Sai k’arar Tv. “Ki shiga Mamin tana ciki, ki san yarda kika yi
kika kwantar mata da hankali, don tun safe ta k’i bari kowa ya ganta, ta yi fushi
sosai don har kuka yau ta yi a gaban Abba, ta furta Kalmar da ta tsayawa kowa a
rai, don an ga ita Allah bai bata haihuwa ba….Jikin kowa kam ya yi sanyi, don haka
ki rarrasheta..” Ya Muhd ya fa’da yana saka yatsansa guda a idonsa ya ‘d’auke
k’wallar da ta tarar masa a k’asan idon. Wani irin fa’duwar gaba na shiga, idona a
waje cikin tashin hankali na furta “Ba da sanin Mami ba, aka ‘d’aura min aure?”
Muhammad ya ‘d’aga kai “An yi kuskuren da kowa yake dana saninsa, don kam baa
kyauta mata ba, shi kansa Abban zan iya cewa ya yi nadama, amma ba hak’urin da bai
bata ba ta k’i saurararsa ta ce sai ya saketa tunda bata da wani amfani a wajensa…”
Wannan karan sai dana dafe k’irjina jin abinda ya ce na zube a kan kujera ina mayar
da ajiyar numfashi. Ina ji Yaya Muhammad ya fice yana sake jaddada min na aikata
abinda ya ce ‘din.
Na kai mintuna biyar kafin na daure na isa d’akin nata cikin tashin hankali na
mur’da k’ofar. Sai na jita a kulle, a hankali na fara nocking in kiran sunan Mamin
cikin tashin hankali.
Tsawon lokaci kafin ta bu’de k’ofar, na ‘dago idona ina kallonta hawaye ne yake
zuba a idon nata ya yi jajur, cikin tashin hankali na zube a jikinta, amma sai naga
ta janye ni tana min wani kallo da ya kusa ‘d’auke min numfashi na…..
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci
ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin da Tinysteps_ng ta yi muku na samun
duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin
buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki
ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng…
Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our
unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more
https://chat.whatsapp.com/
https://www.arewabooks.com/chapter?id=66a2a58ee86f6001e809b915
Akwai page 15 a arewa, ku duba ku Karanta a can. Gobe ina biki ba zan samu posting
ba. Na gode
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 15.
Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci
ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin da Tinysteps_ng ta yi muku na samun
duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin
buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki
ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng…
Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our
unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more
https://chat.whatsapp.com/
✍️
Idanunta zubar da hawaye kawai take, tana pointing d’ina da hannunta, bakinta na
rawa so take ta furta furucin da yake kan harshenta sai dai da alama harshen nata
ya kasa bata ha’din kai. Sai kawai na ji ta kamani ta min wata irin kyakykyawar
runguma tana sakin kuka kamar zata mayar da ni cikinta. Zuciyata da ta ta duka a
tare suke wani matsanancin bugu. Kukan kawai nake nima don na kasa jurewa. Ban san
tsawon lokacin da muka ‘dauka a haka ba. Sai da Mami ta gaji sannan ta ‘dago ni
tana share min hawayen ido na. Tana sakin wani guntun murmushi ta furta “Ina miki
murna AYSHA, ina wa iyayenki Murna….” Da wani irin zafin nama na rufe mata baki ina
girgiza kai. Muryata a shak’e alamar na ci kuka da yawa na furta “Kada kice haka
Mami, Wallahi bani da wasu iyaye bayan ke, ke nake wa kallon Uwa tunda ke na bu’de
ido na gani a matsayin uwata. Wannan auren nawa tabbas k’addara ce don Allah Mami
ki yi hak’uri, ki daina nuna fushinki, kada mutane su yiwa abin wata fassara…”
“Fassara?” Ta furta tana cije leb’en bakinta, sai kuma naga ta saki murmushi ta
furta shikkenan na san k’addara ce Aysha na kuma yarda da ita, In sha Allah zan
daure zuciyata, duk da na san ba zan tab’a iya kawar da damuwar da take zuciyar ba,
amma zan yi hakan musamman don idon mutane da kika ce..” Da farin ciki na rungumeta
ina sakin ajiyar zuciya. Ta ja ni jikinta ta bani kiss a gefen kumatu. Tana jan
karan hancina ta furta “Yanzu AYSHA ke matar aure ce ko? Ustaz zai raba ni da ke da
zarar kin gama secondary?” Sai kawai ta ciji leb’enta ta ja hannuna zuwa cikin
d’akin. Tana furta “Cire Hijabin nan, abin wani banbarakwai amarya da hijab. Cire
maza na gyara miki fuska mu fita a gaisa da mutane, idan da mai hoto a
Mana..”
Duk da ban manta da garga’din Ustaz ba haka na amince Mami ta zauna ta tsantsara
min kwalliya. Don Mami gwanar kwalliya ce. Sai ga shi na zuba wani irin fitinannen
kyau. Laffaya sabuwa dal ta ‘d’auko ta na’da min. Ta kuma saka min wasu irin
turaruka masu mugun k’amshi. Zuwa lokacin naga kiran Ustaz yafi nawa a wayata.
K’arshe da ya gaji sai ya turo min text. “AYSHA kina ina ne? Ki zo yanzu mun gama
cin abinci tafiya za mu yi. Ban da makeup banda turare pls!l” k’irjina ne ya d’an
buga ganin ya sake warning ‘dina a kan hakan, sai dai ban isa na bujirewa Mami ba.
Tana murmushi ta ja ni jikin mudubi ta rungumoni muka d’au hoto da wayarta, mun yi
masifar kyau sosai. Ta d’an ja hancina, tana furta “You look Gorgeous Ayshan Mami.”
D’an murmushi na saki itama ta yafa nata mayafin mai kauri muka fita tsakar gida.
Mutane suna ganinmu aka taho wajenmu da sauri ana muna gu’da a kai. Mami murmushi
kawai take tana amsa Allah ya sanya alherin da ake mata. Nan aka fara mata d’an
biki ana fa’din Mami girma yazo an samu suriki. Ya Muhammad ne ya shigo yana fa’din
Ina AYSHA take ne? Ke kizo in ji abokan ango. Na mik’e zuciyata na wani irin bugu
na ja hannun Asma da wata k’awarmu muka nufi sitroom d’in. Kaina a k’asa kawai
yake, ina jin ‘dan bikin da suke min, bayan amsa gaisuwar su Asma da suka yi. Sai
jin hannun Ustaz na yi a jikina yana ja na d’akin su Aliyu da yake cikin sitroom
d’in. Aka saka masa dariya gaba d’aya. Bai kula su ba sai da muka shiga cikin
d’akin ya kullo k’ofar da k’arfi ya zuba min tsumammun idonsa. Lumshe idon na yi
ina jin bugun zuciyata na tsananta don na san ni mai laifice a wajensa. Madadin na
ji ya yi magana kawai jin bakinsa na yi saman nawa yana tsotse jambakin bakina
kamar ya samu alawa. K’wace jikina nake son yi amma ya k’i bani dama don ya
rungumeni tsam a jikinsa. A kunne yake ra’da min cikin wata irin murya “Rashin
kunya ko? Da kunnen k’ashi, bana ce kada ki yi kwalliya ba kada ki saka jambaki, ki
kuma fito da hijabi shine baki ji ba kika yi kunnen uwar shegu kika na’do wannan
abin kika fito?” Ya fa’da yana zagaye hannunsa a shaffafen cikina zuwa saman
k’irjina “Ji fa Aysha, ji nan wajen duk sun fito tsaf a cikin kayan, kowane banza
ya kallesu kike so? Bayan mallaki na ne….” Tsaf na rufe idona, cikin matsananciyar
kunya, kamar yarda na Ustaz ‘din ma suke a rufe, Murya na rawa na ce “Ustaz ka bari
kai fa Malamin addini ne.” “Malamin addini baya soyayya? Baki san annabi ma ya yi
soyayyar da ta fi wannan ba?” Ya fa’da min cikin wata irin murya yana shinshinar
wuya na. “Turarenki Aysha yana jefa ni a wani yanayi ya sunan sa?” Kuka nake son na
saka masa don duk wani yanayi nake ji a jikina. “Pls Ustaz ka bari!” “I can’t
Aysha, na da’de ina jiran ranar da zan gan mu a haka, pls kice a gida kina so ki
tare zaki yi karatun a gida….” Ya fa’da yana bu’de lumsassun idanunsa da suke dawo
wata colour cikin nawa… “Your Love gonna make me crazy Aysha…” Ka’dan ya rage ban
sume ba, a yanayin da ya yi maganar….
Kasa furta ko kalmar ‘a’ na yi, saboda matsananciyar k’aunarsa. Na Dai d’an janye
jikina ina furta “Ustaz, mutane fa suna jiran mu.” ya min wani kallo kafin ya
girgiza kai “Ba zaki ko ina ba, a haka zaki wajen maza? Wa’dannan halittun nawa ne
ni ka’dai, Allah ni ka’dai ya mallakawa.” Daga haka ya fice da sauri yana jan
k’ofa. Ban San ya suka yi ba, ya dai lek’o yana furta min “Wifey zan dawo around
7:30, ki shirya.” Na ‘d’aga kai na. Ina kallo ya fice wani haushi ya cunkushe min
zuciya, na san ba mamaki wajen waccan zabiyar zai je… haka na ce a raina kafin na
mik’e a kasalance na fice daga ‘dakin jin su Asma suna kira na.
Saman Mami na sake hawa da su, suna ta min iya shege iri iri saman ma ba kowa da
alama Mamin ta sauka. Na zauna akan kujera ina kallon Asma da bakinta ya k’i
rufuwa. Ta furta “Wallahi lamarinku da Ustaz, AYSHA abin sha’awa, ta k’wayar idonsa
ake gane zallar k’aunar da yake miki.” Murmushi kawai na saki ina gyara zama na.
Sa’ada ma murmushin ta yi ta furta “Ke mai sa’a ce AYSHA, irin sa’ar da kowace mace
take son ta samu. Allah ya baku zaman lafiya amma na san yau fa kin tarwatsa farin
cikin y’an mata da yawa, don ko a Islamiyya Ustaz Ahmad ya tafi da zuciyar y’an
mata da yawa…” Haka dai muka yi ta hirarmu. Har nake sanar da su zamu fita da Ustaz
da daddare Amma ina tsoron na gayawa Mami. D’an waro ido Asma ta yi sai kuma ta
tuntsire da dariya “Mhmnm Fa Aysha, ba wai na ji ance ba yanzu zaki tare ba, kada
Ustaz…” Ta fa’da tana rufe bakinta tana dariya… Na yi tsaki ina dukanta a cinya na
furta “Ni y’ar yarinyata da ni, me Ustaz zai ‘d’auka a jikina…” “Abubuwa da yawa
mana, ai shi ya ga mai ya gani ya nace miki, Allah dai ya kai mu next year mu sha
biki…” Sa’da itama ta fa’da tana dariyar… shigowar Mami ce ta saka muka ja baki
muka yi shiru. Ta ‘dan kallemu tana murmushi ta furta “Aysha ki sauka k’asa, ku
gaisa da mutane…” na mik’e su Asma suka bi ni suka saka ni a tsakiya muka sauka.
Babban parlorn da ya kasance na Abba nan muka fara shiga, inda y’an uwan Abba suke.
Da fara’a duk walwala suke amsa gaisuwata. Umma Dijah ta kasa shiru tana furta “Ai
kin dace Aishatu, Ubangiji Allah ya sanya albarka a auren ya nuna mana ranar
tariya.” Kaina a k’asa na kasa amsa ameen ‘din sai wasa nake da zoben hannuna. Daga
nan muka shiga parlorn Umma. Zo kiga farin ciki yarda suka rungumeni suna ihun ga
amarya ga amarya. Murmushi kawai nake saki. Inna laddu kuwa k’anwar Babar Umma cak
ta saka ni a cinyarta tana furta “Ma sha Allah tubarakalla dole Ahmadu ya tubure
sai an