Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
suka bani.” Ko kallon kayan
bata yi ba, ta fice da sauri daga ‘dakin tana furta “Ina ruwana da wasu kayansu,
tunda dai bai kusanceki ba Ai shikkenan, ki gaya masa kuma fita an yi ta farko an
yi k’arshe ba zai ya bu’dar miki da ido ba, ya zuba miki karatun da sam bana son ki
fahimceshi a yanzu…” daga haka ta ja k’ofar da k’arfi ta bar ni da bu’dadden baki
ina kallonta. Na saki ajiyar zuciya kafin na zura kayan sallah ta na tada sallahr
isha’i da ban yi ba. Bayan na gama tunanin irin rigimar Mami, tabbas idan ka
fahimci halinta tana da da’din zama amma kafin ka fuskanceta zaka saka ta a
b’angaren mutane masu bau’dadden ra’ayi.
Sanda na kwanta kuwa kiran wayar Ustaz ne ya isheni, kunyarsa da nake ji na
abubuwan da suka wakana a tsakaninmu ne ya hana ni d’aga wayar, sai da ya yi kira
ya kai biyar sannan na saka wayar a kunnena. Wata ajiyar zuciya ya saki. Yana
furta “Na kasa barci Eeesh, kina ta yi min gizo duka surar jikinki ta baibaye
tunani na, da na san haka ne da ban fara janyowa kaina ba….wani feeling nake ji mai
zafin gaske AYSHA, na kasa controlling kaina na samu barci… please ki amince min
even once… na kusanci halak d’ina..” K’it na kashe wayar ina mayar da numfashi.
Lamarin Ystaz yana neman ya girmi kaina. Kiran duniya ban amsa ba. K’arshe ya turo
min msg. “Shikkenan tunda ba zaki amsa ba, I really missed your cutable lips…. And…
boo….” Sai ya yi alamar murmushi bai k’arasa ba. Wani irin waro ido na yi a fili na
furta “Na shiga uku me yasa Ustaz sam bai da kunya, amma idan ka ganshi a fili ba
zaka zaci zai aikata haka ba. A lumshe idona yake Amma duk wasu feeling ina jinsa
nima kamar Ustaz d’in kawai daurewa nake don ban san ya zan yi ba idan ba dauriyar
ba, na san ko giyar waje na sha ba zan amincewa buk’atar Ustaz ba, idan ba so nake
Mami ta yi yaga yaga da nama na ba.
Da safe sanda na isa makaranta ashe labari tuni ya baza makarantar kunya ta dinga
isata jin ana ta min Allah ya sanya alheri. A islamiyya ma kasa katab’us na yi duk
da dai da nik’ab a fuskata.
Tunda aka d’aura aure sai gidanmu ya zama nasu Ustaz, don in dai yana gari baya
jure rashin iya zuwa. Mami kuma ta kasa ta tsare don k’iri k’iri wani lokaci da ya
tambayeta zan raka shi unguwa ta ce “Ahmad, ka saurareni da kyau ba zan amince ka
dinga fita da AYSHA bata tare ba.” Ya ‘dan ware ido yana kallonta ita kuwa ba
abinda ya dameta ta mik’e ta shige bedroom d’inta. Ustaz ya ‘dan dubeni yana sakin
ajiyar zuciya. Na mik’a masa lemon da na ha’da masa, don anan saman Mamin muke
zance da kanta Kuma ta buk’aci hakan. Ranar da yazo bayan d’aurin aure da kwana
biyu zan fita sitroom ta ce “AYSHA hau da shi sama na, ai ya zama d’an gida, bai
kyautu a dinga barinsa a parlorn waje ba, sai kace wanda yazo zance.” Gaba ‘d’aya
wajen ba wanda bai d’ago ya kalleta ba, hatta Abba sai da zancen ya bashi mamaki.
Ita kuwa ta maze tana murmushi ta ce “Da ne nake adawa da auren AYSHA, banda yanzu
da k’addara ta Riga ta tabbatar da hakan. Allah ya sanya musu albarka a auren.”
Abba murmushinsa ya kasa b’oyuwa kamar yarda bakin Umma ya kasa rufuwa.
Shikkenan tun daga ranar Ustaz ya samu sake, mafi yawan lokuta ma tare ake zama a
ci abincin dare da shi. Ya d’auki iyayena kamar nasa kamar yarda nima kullum muke
gaisawa da Mommynsa a waya idan har na sha’afa ban kira ba, da kanta take kira na.
Khadija kuwa ta zama uwa k’awata tsabar shak’uwar da muka yi, duk da ta girme min.
Gefe guda al’amarin Mami na bani mamaki a zahiri a gaban kowa ta hak’ura amma a
ba’dini ni ka’dai na san yarda muke zaune da ita, musamman duk ranar da Ustaz zai
zo ta dinga ha’de rai kenan tana min masifa komai na yi kuma laifi yake zama a
wajenta. Ban gayawa kowa ba, don bana son kowa ya sani balle a ji haushinta. Mafi
yawan lokuta idan Umma ta fara mata zancen da ya rage na watannin tariyata tsam
take mik’ewa ta bar wajen.
Wannan abu yana tab’a min ruhina har na ji sam ban ji da’din abinda take yi d’in
ba. In dai batun karatu ne, da bakin Ustaz ya mata alk’awarin sai nayi karatu a
gidansa har sai nace ya isheni, tunda shima ta wani fannin d’an boko ne da ake
damawa da shi a bokon.
June-july, shine watannin da muke saka ran zamu gama makaranta. Kwanci tashi sai ga
shi lokacin har yazo. Ina ji ko mu da zamu zana jarrabawar bamu kai Ustaz lissafa
kwanakin ranar graduation d’in mu ba. Wata rana muna waya. Ya ce “AYSHA, na k’agu
ki gama wannan makarantar na sauke buk’atar da ta min cunkoso a jikina….” Waro ido
na yi kafin na furta “Wace buk’ata kuma?” Sai da busar da iskar da take bakinsa,
har na ji sautin ta ta cikin waya sai na ji ya ce “Kashe mu yi vedio call, zan gaya
miki buk’atar…” “Ni dai A’a, na yafe.” Na fa’da a shagwab’e. Ya saki murmushi kafin
ya furta “Ashe kin san buk’atar tunda kina jin kunyar na gaya miki, bari na miki ta
Malam bahaushe, wallahi AYSHA na gaji, gangar jikina tana buk’atar maha’dinta, ina
son jin d’umin Aysha zahirinta ba tare da shamakin tufafi ba…” da sauri na kashe
wayar ina mayar da ajiyar zuciya. Ni da kaina na san Ustaz ya yi hak’uri gashi
yanzu ko rungumar baya samu ya yi min Mami ta kasa ta tsare, sau tari sai muna
zance sai ta shigo parlorn da niyyar d’aukar wani abin. Wani lokacin Ustaz kasa
sakin jiki yake yi. Shi yasa yace min sau da yawa shi yasa baya zaman Nigeria yake
tafiyarsa wata k’asar ya kwana biyu.
Burina kawai na fito da A1 a duka subject d’in da nake, don haka na dage da karatu
Ka’in da na’in. Ustaz ma a wannan lokacin ya mugun d’aga min k’afa sai dai ya kira
ni a waya. Har rama na yi saboda bani da isashshen lokacin kaina ko waya a gaggauce
nake amsa masa, sau tari sai ya nuna fushin sa sannan nake bashi lokaci na.
Ranar da muka gama makaranta, rana ce mai matuk’ar mahimmanci a wajena. Duk da
Ustaz ya hana ni ko saka kwalli a ranar, hakan bai hana ni zuba wani Uban kyau ba
na kwatance. Wata doguwar Riga mai masifar kyau na saka wacce Mommyn Ustaz ta kawo
min. Da takalmi half cover wanda zai matching da adon rigar golden brown. Na yi
rolling kaina. Sanda Ustaz yazo zamu tafi hararata ya dinga yi yana tsaki k’asa
k’asa. Muna isa wajen ya kulle motar yana zuban narkakkun idanunsa. Kafin ya kaiwa
bakina sumbata ya furta “Me yasa? Me yasa ko baki kwalliya ba sai kin yi attracting
idon mutane..” Murmushi kawai na masa. Sai naga ya bu’de dashboard ya ciro nik’ab
Sabo fil a leda da kansa ya saka min nik’ab d’in yana furta “fuskar Matata haramun
ce ga dandazon maza.”
Ustaz ya kasa ya tsare ta dole ya nunawa mutane ni matarsa ce, don bai ji kunyar ko
su Abba ba sanda za a bani kyauta ya rik’e hannuna muka hau kan step. Shi ya karb’i
kyautar da Mataimakin governor ya bani sab’anin sauran matan da suka dinga amsa da
kansu. Tafi aka dinga yi da wani irin ihu.
Da aka tashi bai barni na yi hotuna ba, ya saka ni a mota yana furta “Is enough
kuma, idan ba so ake Ustaz zuciyarsa ta yi bombing ba..” ya tada Motar yana jan
hannuna da yake saman cinyata yana murzawa a hankali ya furta “Saura 2 weeks na
mallaki komai da komai na jikinki Ayshatu na, har nan ko?” Inda hannunsa ya sauka
ne ya saka ni ware ido ina runtse su da sauri da k’arfi. Sai naga ya daki sitiyari
yana murmushi ya furta “na godewa Ubangiji da ya mallaka min kamilar mace, da nake
jin In sha Allah nine nan d’an mukullin wancan abin da ake killacewa, I love you
Ayshatu na….ina son ki fiye da son da nake wa ruhina, I wish to spend the rest of
my life with you…” ya fa’da yana d’an jan hancina. “Na kusa cire kunyar nan gaba
d’aya. Just 2 weeks za’a saka, a haka ma ni ba haka na so ba na so a ce 1week after
Graduation kawai, amma ya zan yi Mommy ta kafe basu gama shirye shirye ba.”
Gani na yi kawai ya ja gefen hanya ya yi parking. Ya kwantar da kujerar yana
kallona da wasu lumsassun idanunsa. Tsigar jikina ce take tashi kawai. Iya zallar
kallon Ustaz yana canja min yanayi inaga ranar da zan ganni da ga ni sai shi a
matsayin ma’aurata. “Say something AYSHA, ko da yau ka’dai ne kice Ustaz I love you
na ji sanyi a raina…” Lumshe idona na yi, Karon farko na ji yau ina son shayar da
Ustaz mamaki. Murya a sark’afe cikin wani irin sauti na furta “I… Love…You Ustaz
with All my heart Ustazu na.” Jina kawai na yi a jikinsa yana bani wasu zafafan
kiss. A kunne ya ra’da min “Me kika tanadar min a ranar da zamu tare?” Na runtse
idona. “Kada ki ji kunya My Eesh ba kunya tsakanin Miji da Mata say it…. Kin
tanadar min duka kan ki…” na d’aga kai na na ji ya bani sumbata a forehead d’ina da
tsinin hancina. Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya mayar da seat d’in yarda ta ke
ya ja muka tafi.
Sanda muka isa gida, na hau sama Mami na tarar tana cika tana batsewa a cikin
parlornta, idanunta sun ka’da jajur tana kallona kafin ta zauna ta rik’e kan nata.
Jikina a sanyaye na yi hanyar da zata kai ni d’akina, na ji muryar Mami a kaurare
ta ce “AYSHA! Zo nan!” Cak na tsaya kafin na juya a hankali na isa inda ta ke. Na
zauna a gefenta. Ta nuna min cards… “Ga cards d’in bikinki nan, burinki da na
iyayenki ya cika, ina muku murna, ba zan b’oye miki ba AYSHA sam bana farin ciki da
aurenki, zan kuma amince da aurenki ne idan kika amince da wasu shara’di da zan
baki…. As from today zaki dawo kwana a d’akina ba kuma naso ki gayawa kowa, sannan
ban amince ko gayawa kowa wannan shara’din nawa ba, sannan ki sanar da shi daga yau
ba waya tsakaninku sai mesaage…….
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA 17.
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 17.
Jikina na rawa na kauce fuskata daga sumbatar da yake kai min. “Ustaz shine ka min
k’arya?” Na fa’da ina janye jikina daga nasa na zauna a kan kujera. Zaman dirshan
ya yi a gabana ya zuba hannunsa a kan cinyata yana kallona cikin wani yanayi ya
furta “AYSHA k’arya kuma? K’aryar me?”
Magana yake cikin wata irin murya da na kasa tantance a wani mahalli zan sakata.
“Kace min Khadija matarka ce.” Na fa’da ina yin k’asa da idona don bana jin zan iya
jure wannan kallon da yake min. Wani murmushi ya saki da har ina iya juyo sautinsa
da numfashin da ya sakar min ya ratsa fuskata. Yana dariyar ya furta “D’ago ki
kalleni…” na k’i d’agowar da ba zan jure ba. Hannuna ya kama ya matse cikin nasa. A
hankali ya furta “Ranar da kika ce ba kya so na, kin fasa aurena hankalina tashe na
taho gida. Ni da kaina na tabbatar ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida, Saboda
tashin hankalin da zuciyata take ciki.
Sanda na isa gida ko ciki ban shiga ba kamar yarda na saba. Na shiga part d’ina na
zauna hankalina a tashe. Duk na ji duniyar bata min da’di. Ashe Mommy taga
shigowata ta camera ta aiko Khadija taga ko lafiya ban shigo ba kamar yarda na
saba. Yanayin da Habibteey ta ganni ne ya sata zubewa cikin tashin hankali a
gabana tana kama hannuna ta furta “Subhanallah Ya Ahmad lafiya kuwa?” Na ‘dago
idona da suka yi jajir na zube a kanta sai kawai na ga ta ru’de ta fara magana “Ya
Ahmad ka yi magana me ya sameka?” Ajiyar zuciya na saki cikin wani irin rauni na
sanar da ita dukkan damuwata. Madadin naga ta cigaba da damuwar sai naga ta
tuntsire da dariya ta furta “Ya Ahmad wallahi AYSHA na sanka, kawai dai akwai wani
dalili da yake nema ya mata Katanga da son naka zai kuma iya togaceku daga aure
idan baka yi gaggawar sakawa a d’aura muku aure ba ina tabbatar maka nan gaba zaka
rasa AYSHA…” shiru na yi ina murza goshina kafin na ce “Khadija ta yaya kike zaton
Iyayenta zasu yarda su aurar da ita a S.S 2.” Ta sake murmushi ta ce “Ka je musu da
buk’atar auren kawai banda tariya idan yaso idan ta gama secondary school sai ku
tare…” Shiru na yi ina nazarin zuciyata duk gwiwata ta yi sanyi don na san
mawuyacin abu ne Abbanki ya yarda da abinda zan je masa, ni kaina ina tunanin yarda
zan yi aure na kuma zuba miki ido bayan auren a zuwan sai an tare na kusanceki ko
ba so akwai sha’awa balle ke da nake so nake kuma mafarki kullum
Akan wancan gwadaben sai na ji abin da kamar wuya. Gefe guda kuma ina jin tsoron ko
kin daina so na don ba zan iya auren matar da bata so na ba, don haka kai tsaye na
ce da Khadija “Idan kuma bata so na fa?” Dariya ta yi sosai, dariyar da ta dinga
saka min wani irin d’aci a zuciya, a zafafe na ce “Khadija wai meye haka? Ya nazo
miki da matsalata zaki saka ni a gaba kina dariya?” Dariyar ta sake yi kafin ta ce
Tabbas Ya Ahmad na yarda kai sabon shiga ne a fagen soyayya, duk mutumin da zai
Soka da farko ya dawo ya k’i ka da k’arshe to ba k’in ka yake ba sai dai idan akwai
wani dalilin da zai saka ya janye soyayyar… ka bincika kuma zaka ce na gaya maka.
Kana so ka gane tana sonka ko bata son ka?” Da sauri na ‘d’aga kai, don shi na fi
buk’ata. Ta gya’da kai ta furta “zan baka hotona, ka kaiwa AYSHA a zuwan ni ce
matar da zaka aura, idan har kaga ta shiga tashin hankali to tabbas tana son ka,
idan kuwa kaga bata damu ba to gaskiya sonka bai je ko ina ba a zuciyarta.” “Good
idea!” Na furta cikin jin da’di.
Da k’yar na bari kashegari ta yi, kafin na kai kaina gidanku, sai dai me? Ina zuwa
aka ce min kina gidan Yaya Muhammad. Wani farin ciki na ji. Na saka aka min
kwatance sai gidan Muhammad. Sanda na baki hoton Khadija, lab’e wa na yi ba tafiya
nayi ba, ina son naga reaction d’inki. Wani farin ciki ya mamaye ni ganin yarda
kika nuna damuwa da hoton da kika gani. Ya Muhd shi ya sanar da ni komai da abinda
ake ciki game da Maminki. Hakan shi ya bani k’warin gwiwar zuwa na tari Daddy na da
zancen son zuwa a nema min aurenki. Da fari bai amince ba sai da na masa rantsuwar
zan amince na barki ki yi karatu sannan ya yarda zai je nema min aurenki da
shara’din idan Abbanki bai amince ba zan hak’ura. Na yarda da hakan.
Kashegari kuwa aka je nema min aurenki, abin mamaki take Abbanki ya ce ya amince
banda ma yana tausayawa Maminki kada zafin ya mata yawa da yace na tare da matata
kawai. Bokon me? Bokon Ai ba fa’dar Allah ba ce. Na ji da’din wannan labarin na
tabbatar na auri y’ar babban gida irin matar da Manzon Allah ya kwa’daita mana mu
aura. Muhd ne ya bani shawarar zai ‘d’auke ki ya kai ki gidansa har sai bayan an
‘d’aura auren don ya lura kamar damuwar da Mami take ciki ne yake neman tunzira
zuciyarki. Ki bujirewa auren. Wannan shine abinda ya faru My Eeesh dafatan zaki
yafe min?” Na lumshe idona kawai ina jin yarda yake murzar min hannuna a hankali.
“Ana ahubbuki kaseer kaseer Eesh.” Murmushi kawai na saki ina janye hannuna na ce
“Ustaz mu tafi gida kada dare ya yi.” Sumbata ya kaiwa hannun yana furta “wani gida
kuma Aysha? Kina da gidan da ya wuce nan ne?” Idona na ne ya kawo ruwa na zare
hannuna ina furta “Please Ustaz! Kada mu yi haka da kai mana..” Shiru ya yi yana
sake matsar da hannuna saitin bakinsa idanunsa a lumshe yake sumbatar yatsun yana
furta “Shshsh, idan kika cigaba da min magiya you will spend your night anan…” na
waro ido. Jin abinda ya ce bai fasa kissing hannun nawa ba. Sai da ya gaji don
kansa ya janye hannun yana sakin ajiyar zuciya ha’de da kallona da burkitattun
idanunsa ya mik’e naga ya shiga wata k’ofa da na tabbatar toilet ne, bai wani jima
ba naga ya fito da rigar wanka a jikinsa yana goge jikin. Da sauri na runtse idona
na ji ya saki dariya mai k’aramin sauti ya furta “Idan baki wasa ba zaki shafa min
mai….” Ai ban san sanda na isa bakin k’ofa ba, ina sakin haki na tsaya a bakin
k’ofar da zata fitar da kai daga parlorn. Tsawon mintuna biyu sai ga shi ya fito
sai zabga k’amshi yake fuskarsa very fresh. Ina ganinsa na yi saurin murza handle
d’in k’ofar zan fita sai dai hakan bai samu ba don key ‘din na hannunsa ya k’araso
daf da ni, kansa a saman wuya na ya rungumeni ta baya yana sakin ajiyar zuciya, a
kunne ya ra’da min. “Kin saka ni wankan dole Ayshata…” wani irin runtse ido na yi
na furta “Please Ustazu Ka Bari am too young fa..” naga ya d’an yi murmushi kawai
ya kaiwa bakina sumbata ya furta “Mu je kafin Maminki ta k’arar da charging wayarki
ta miki missed calls ya fi hamsin…” waro ido na yi ina kallon wayar da Ustaz yake
mik’o min, a raina na furta shikkenan na ka’de yau har ganyena….
Da zan tafi Mommynsa da Aunty’s d’insa suka ha’da ni sha tara ta arziki. Tabbas a
idanunsu na hango sun yi na’am da ni.
Sanda muka isa k’ofar gida, da sauri na kai hannu zan bu’de k’ofar sai na ji ta a
kulle gam. Na juyo ina kallon Ustaz na ce ya haka?” D’an lumshe ido ya yi yana turo
min lab’bansa “I need kiss AYSHA in dai kina son ki fita, ina son ki min abinda zan
dinga tunawa da shi da zarar na rufe ido da niyyar barci…” “Allah Ustaz ba zan iya
ba…” Ji na yi