Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NAGA Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel by Nazeefa NASHE

Author :  NAZEEFA NASHE Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 15

21K to 24K   out of 42.5K words

miki su ba, sai dai na san
mutanene masu zumunci masu son kuma auren zumunci, nima bijirewa na yi na musu
tsallen baka’dai na gaya musu AYSHA kawai zuciyata take so. A d’akin su Abba na
akwai Umma Amina itace Babba sai Umma Jamila, Daddynmu sai Abba Kabeer, Abba Ali,
Abba Naseer da Umma Shatu.. autarsu kenan kuma mate d’ina ce mai sunan Ayshata…

A gidansu Umma na kuwa su Ashirin ba biyu ne, sai dai a d’akinsu su biyar ne kacal.
Ramla Mahaifiyar Ahmad Sulaiman, sai Saudat Tasleem, Taiba da Nihad. Nan fa wai su
mahaifiyarsu balarabiya shi yasa ta sakawa yaranta sunan larabawa don Kakata
buzuwar Yamen ce.. sai kin hankali da su idan muka yi aure don mutane ne masu
felek’e da iyayi na gaske.


Duka karatu na tun daga matakin yarinta har na girma, na yi su ne a lebanon school,
sai da na gama secondary sannan na tuburewa Daddy na ce Jami’atul Madeena za’a kai
ni. Ya so ya bujire don shi burinsa na zama iyalen Elizabeth ni kuma na ce nawa
burin na zama dangin King Fahad ne, an kai ruwa rana kafin ya amincewa buk’atata na
tattara na tafi Jami’atul Madeena ban kuma dawo ba sai a waccan shekarar… Ina isowa
Nigeria na tsunduma aikin k’wadago ina ha’dawa da noma da kiwo da kuma safara daga
can k’asashen waje zuwa tamu k’asar.


Ranar da na fara ganinki, rana ce mai matuk’ar girma a wajena, da ba zan manta da
ita ba. Kamar ba zan fita daga gida ba saboda hadari da ya lullub’e sararin
samaniya sai dai wayar da Kabeer yake min ta isheni na zuwa ganin wani gida da Zan
gani a layinku. Na mik’e na shiga wanka kamar ba zan yi kwalliya ba sai dai na samu
kaina da tsara kwalliya ashe zan ha’du da matata ne…
Ina tsaye da abokina na dinga jin zuciyata na wani irin harbawa. Mamaki ya isheni
na juya don ganin dalili sai idona ya fa’da kan wata zuk’ek’iyar yarinya doguwa
fara mai suffar larabawa. Numfashina ne ya kusa d’aukewa duk da na Yi matuk’ar
daurewa wajen yi miki kallon da shari’a ta amince da shi kallo guda. Sai da kika
wuce sannan na saki ajiyar zuciya ina kallon Kabeer na furta “Wacece wannan?”
Kabeer dariya ya yi sosai yana cewa “Ai kuwa in dai sonta ka ke ka dace da macen
k’warai, Saliha managarciya da kowa ke so.. duk layin nan ba nutsuwar yarinyar can
wallahi…” na d’an yi dariya ina furta “Dalilinka na cewa haka Kabeer?” “Saboda kai
daga gani shigarta ka san ta ha’da duk qualities d’in da ake son mace ta gari ta
zama..” ya furta yana kallona cikin son tabbatarwa. Dariya na yi nace “Idan kuma
Basaja take fa?” Kabeer ya ware ido ya ce wallahi ba wani Basaja idan baka amince
ba kuma ka yi bincike..” “Bincike ya zama dole Kabeer, don aure nake son mu yi ta
zame min Uwar yara na kaga kuwa dole na binciki sahihancin tarbiyyarta..” Kabeer ya
jinjina min kai. “Ina tabbatar maka Ahmad duk binciken da zaka yi akan yarinyar nan
magana guda zaka samu Mai tarbiyya ce…” Na saki ajiyar zuciya ina d’aga kai na
windownku na hango kamar ana lek’e jikina kuma ya bani ke ce ko?” Waro ido na yi
ina kallonsa. Ya saki murmushi yana d’aga min gira. “A jikina na san ke ce, na san
kuma kema kin fa’da soyayyata daga yanayin yarda idanunmu suka sark’e da juna…”

Daga ranar na kafa d’anbar bincike ka’in da Na’in. Shine dalilin da yasa na je har
makarantarku neman koyarwa. Kuma daga ranar kullum a kan idona kike tafiya
makaranta duk da ba na bari ki ganni, na kuma lura duk sanda kika zo wucewa sai kin
dinga d’an juyowa kina dubawa. Ina sane na dinga miki duk tambayoyin da nake miki a
aji sai na samu kina da matsananciya kunya. Wannan ma ya sake k’ara miki k’ima a
idona.

Hakan yasa kai tsaye naje gida da buk’atar azo min neman izinin fara zuwa zance
wajenki. A take Abba ya ce wallahi in dai nine nake sonki ya ba ni ke, sai dai zai
rok’i alfarmar a barki ki gama secondary saura shekara guda. Ba wanda ya ja da
haka sai dai ni ba haka na so ba, na so a ce a yi bikin cikin wata biyu idan yaso
ki k’arasa makarantar a gida na. Mommy ce ta dinga tausata. Abin kamar almara
kullum Aysha k’ara min wutar sonki ake.. Yau da na ganki kina kuka a makaranta da
k’yar na k’arasa musu karatun da nake musu. Allah ne ka’dai ya kai ni gida. Na
dinga rok’on Daddy yazo a d’aura aure kawai amma ya k’i ya ce dole a bi maganar
Abbanki ko shine ba zai aurar da y’arsa bata gama secondary ba. Still yanzu ma nazo
naga kina kuka, AYSHA ki gaya min gaskiya ba kya son auren ne?”

Ajiyar zuciya na sauke a hankali na d’aga kai na. Waro ido ya yi har yana mik’ewa
ya iso gaba na a tsayen da yake hannayensa a k’irji ya furta “Ki gaya min gaskiya,
da gaske ba kya so na, idan Kika sake tabbatar min zan hak’ura…” Jikina ne yake
rawa na sake d’aga kai na.. Zama ya yi yana rik’e kansa naga sai murza goshinsa
yake. Sai kuma na ji cikin sark’akkiyar murya ya furta “Ki furta da bakin ki, cewa
ba kya so na…” Na d’aga leb’ena a hankali ina kallon k’wayar idonsa muryata na rawa
na furta “Na ba yanzu zan yi aure ba sai na yi ko degree ne, am too young to
marry…..”



Ga mai son next page ya duba shafina na arewa zai samu page d’aya ko biyu bayan
wannan.



Page 11 @ ArewaBooks Danna link d’in nan Zai kai ka har page 11.


https://arewabooks.com/chapter?id=669d122dc1b845b878dad215
Saboda yawan complain d’inku yasa na yi haka… dafatan za’a ni ha’din kai.
Group 1 and 2 ya cika ga group 3 nan wanda bai samu ba ya shiga.


𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

𝒫𝒶ℊℯ 12




Kashegari na lallab’a na yi shirin makaranta, don kawai na zame na je gidan su Mami
na. K’arfin hali kawai nake don ko barcin kirki ban samu na yi ba. Don ma a ‘d’akin
Umma nake kwana tunda Mami bata gidan. Ganin juye juyen da nake ya yi yawa, hakan
yasa ina ji Umma ta saka baki ta kira suna na. “Mik’e AYSHA ki shiga toilet ki yi
alwala ki yi sallolin nafila tunda barcin ya gagara. Na mik’e kuwa jikina a sanyaye
na aikata abinda ta ce d’in, sai naga na samu sauk’in abinda nake ji a cikin raina.


A kitchen na sameta tana dama kunun gya’da. Na furta “Umma zan tafi.” Ta ‘dago tana
kallona kafin ta mik’o min cup d’in hannunta mai cike da kunun gya’da mai zafin
gaske. “Shanye shi tas kafin ki tafi, kina nan kin sakawa kan ki k’wazzaba duk kin
bi kin rame.” Ban mata musu ba na sha kunun don ni da kaina ina ji a jikina na
matuk’ar ramewa don har kamar iska zata kwasheni.

Ina shiga motar na ce da Baba Driver “Gidan su Mami zaka kai ni ba makaranta ba
Baba.” Ya juyo yana kallona ya ce “Yau ba zaki makarantar ba Ayshatu?” Na d’aga
masa kai, sai bai ce komai ba ya ja mota ya nufi da ni court road don anan gidan su
Mamin yake.



Shiru gidan har na shiga cikin harabar gidan ba kowa, don gidan sam ba yara sai
Maman su Mamin duk an musu aure mazan gidan kuma wasu suna k’asashen waje karatu.
Na shiga Parlorn gidan da yake k’asa inda anan step d’in benen yake.
Mama ta dubeni tana bu’de baki. “Yarinyar Mami ce a gidan nan da safe haka, ina
makarantar?” D’an murmushi na saki ban yi mata wasan da na saba mata ba ni jika da
kaka. Na zauna a gefenta ina furta “Mama ina kwana?” Ba zan amsa ba Aysha, kin ga
yarda kika dawo kuwa? Wace irin masifa ce kuka jefa kan ku haka ke da Uwar taki,
ita ba nutsuwa ke ba nutsuwa, ku wato ba zaku yarda da hukuncin Allah ba kenan,
dole sai kun ja da mahaifinki alhali dukkanku a k’ark’ashinsa kuke, ai ni ya min
daidai wallahi wani Sokon Uba ne shi da alheri na binsa zai saka k’afa ya doke
saboda wani bokon banza da wofi… ai idan nice a ranar da aka zo neman auren ma zan
d’aura auren kowa ma bai ji ba bai gani ba. Mutum kamar Ustaz Ahmad da yake burge
kowa, a cikin lafazin karatunsa zaka gane mutum ne mai nagarta…” idanuna ne suka
kawo k’walla na yi shiru kawai ina jin zancenta. Ina ma y’arta zata zauna ta gane
abinda Maman take fa’da. Amma Ai mun bari gini tun ran Zane, ni na san Ustaz ya yi
zuciya ya bar ni daga yanayin kallon da ya min jiya. Ai shi ba k’aramin mutum bane
da zai zauna ina masa walagigi da hankali. “Tashi ki je can wajen Uwarki, kada ki
min kuka anan ba zan wani lallasheki ba, don ni bana bayan rashing gaskiya..” Na
Mik’e kawai ina harha’da hanya na hau saman don na san a can zan samu Mami har
yanzu yaran gidan kowa da d’akinsa.

Na tura k’ofar na shiga, Mami tana kwance a saman carpet idanunta a lumshe kamar
mai barci. Ta bu’de ido tana kallo na. Da sauri na isa wajenta, mik’ewa ta yi zaune
tana bu’de min hannunta alamar na shiga. Na kuwa shiga ta Mayar ta rufe i ruf tana
sakin ajiyar zuciya. “I missed you Mami na.” Ta lumshe ido tana furta “I mish you
too Baby na.. Ina school d’in baki tafi ba kika biyo nan.” Hawaye na fara yi. Ta
saka yatsa tana wasa da hawayen fuskata tana sakin murmushi a hankali ta kai min
sumbata a gefen k’unci. “No more crying Baby na..” “Zaki koma gidan? Ni na yarda ba
zan aure shi ba.” Ta saki murmushi ta ja hannuna ta matse cikin nata ta furta “Zan
koma Aysha, don ba zan iya rayuwa ba tare da Baby na ba..” Murna na fara yi ina jin
abinda ya tsaya min a zuciyata yana tafiya. So nake na tambayeta ta amincewa
alak’ata da Ustaz amma sai na ja baki na yi shiru don bana son b’acin ranta. Ina
kallo ta shiga wanka ta fito ta shirya a gabana sannan ta zura hijab d’inta muka
sauka k’asa. Mama bin mu ta dinga yi da kallo ganin yarda nake jan akwatin Mamin.
Murmushi kawai ta furta “Lallai Fateema, yanzu ba wanda bai rarrashekiba aka dinga
baki hak’uri kika k’i komawa gidan mijinki sai yanzu da Aysha ta zo? Ai shikkenan
Allah ya kiyaye hanya..” Mami murmusawa kawai ta yi muka fice daga gidan. Muka
shiga cikin motar Mamin sai gida.


Umma tana tsakargida tana ware kayan miya da naman da za’a saka a freezer ta ji
sallamar mu. Da mamaki ta ‘dago tana kallonmu. Mami murmushi ta saki tana furta
“Kallon fa?” Umma ta ce “Ba dole na kalleki ba Fateema, yanzu ba wanda bai je biko
ba har ni kishiya, amma kika k’i dawowa Mahaifinki ma ba yarda bai yi da ke ba,
shima kika ja kika kafe sai yanzu kawai naga ficilar yarinyar ta dawo da ke..” Mami
Murmushi ta saki. Ta ce “Hakan zai nuna muku mahimmacin ta gareni a rayuwa ta…”
Umma ta ce “Ba shakka, To Allah ya kyauta na gaba…”


Daga ranar da na furta masa ba zan aure shi ba, bai sake nemana ba har tsawon
kwanaki biyar. Zuwa lokacin duk na fige na lalace sai kace wacce ta yi watanni tana
ciwo. Ba wanda ya sake bi ta kaina balle a min zancen Ustaz.



Da yamma sai ga Yaya Muhammad ya shigo gidan muna tsakargida duk muna aiki. Ya d’an
dubi Mami yana sosa kai ya furta “Hajiya Mami, Aron Aysha zaki bani, Khadija na
fama da laulayi ni kuma tafiya kaduna ta kama ni zan kwana biyu a can…” Mami ta
masa wani kallo kafin ta furta “Muhammad bana son jaye jayen magana, ita ina y’an
gidansu ba za’a kai mata su ba, sai Aysha? AYSHA ce zata je ta mata wahalar
laulayin kenan? To ba sai yiwu ba ka samar mata y’ar aiki idan ma bata da y’an uwan
da zasu zauna mata.” Muhammad ya d’an rusuna, duk da ba wani girmansa Mami ta yi
ba, bai fi 2 yrs ta bashi ba, amma yana girmamata a matsayinta na matar ubansa. “Ki
taimaka, ko don nan gaba idan Aysha ta yi aure bata da y’an uwa mata itama fa y’an
uwan Mijin ne zasu kula da ita.” Mami ta girgiza kai “Wallahi don dai kai ne, amma
da Umar ne Allah ba zata gidansa ba..” Dariya Muhammad ya yi don ya san Mami da
Umar sam basa shiri haka ma Usman. Ya dinga dariya yana kallona ya furta “Ke d’ebo
kayan da zasu miki kwana biyar, ki yi sauri ina mota ina jiranki…”


Na mik’e na hau sama, a raina sam bana son zuwa saboda ina yawan fita da yamma naga
ko zan ga Ustaz amma bana ganinsa. Na shirya kaya na na bi Yaya Muhammad gidansa.


A parlor na samu Anty Khadija daga yanayinta na hango tabbas laulayin take.
Gaisheta na yi ta amsa tana murmushi na mata sannu. Da kanta ta raka ni ‘d’akin da
zan zauna. Hijab d’ina na cire na fito parlorn ba mayafi a jikina sai hula. Tas na
gyara gidan don ya yi k’ura ka’dan. Kafin na shiga kitchen na tuk’a musu tuwon
semovita da Yaya Muhammad ya ce shi ka’dai take iya ci.

Tsaf na shirya musu table d’in duk zuciyata ba da’di balle ganin tunda suka shige
d’aki basu sake fitowa ba wai bata son k’amshin kayan miya. Mijinta sai wani
lallab’ata yake. Haushi ma abin ya bani don haka bayan na yi wanka kawai na fita
k’aramin parlorn na kwanta. Ina kallon wani Korean series. Anty Khadija da Ya Muhd
suka shigo hannunsu sark’afe cikin na juna sai wani janta yake a jiki, ita Kuma
tana sake narke masa. Kunya da takaicin su ma duk suka ha’du suka sake jagule min
zuciya ta. Khadija na kallona ta furta “Sannu Aysha..” na amsa mata ina mayar da
kaina na kwanta. “My love wallahi duk jikina ciwo yake, so nake ka yi min tausa…”
Gani na yi kawai ya sunkuya ya ‘dagata cak tana Zillo tana komai ya fice da ita
kamar Babyn roba.
Lumshe idona na yi ina tunanin dama nice da Ustaz a haka, da na tabbata ba wani da
zai kai ni farin ciki a duniya. Sai kawai na samu kaina da zurarowar hawaye.
K’amshin turarensa da na dinga ji yana sake yawaita ne ya saka ni bu’de lumsassun
idanuna…. Da wani irin sauri na mik’e ganin Ustaz ne da Ya Muhd a parlorn. Ustaz
d’in a zaune idanunsa akan wayarsa. Hula ce kawai a kaina, itama ta zame don haka
gashi na ya bayyana sosai. Kayan jikina kuwa T.shirt ce da ta d’an kamani ka’dan
sai siket. Ido na dinga warowa ina k’ank’ame jikina. Sai na lura Ustaz ko kallona
bai yi ba, ya cigaba da hirarsu da Yaya Muhd, kamar ma basu san ina wajen ba. “Bari
na kawo maka ruwa” Ya Muhd ya mik’ewa yana ficewa. Sai sannan na furta “Ya zaka
shigo ba sallama, ai dai ba kyau shiga gidan mutane ba sallama, ga shi nan ka shigo
ko Hijab babu a jikina…” Wani irin kallo ya min. Kafin naga ya ‘d’auke kansa ya
mayar kan waya ya furta “Ba wajenki na zo ba, kuma mai gidan ne ya bani izinin
shigowa.” Raina ne ya sake b’aci a kufule na ce “Sai ka tashi ka fita, ina son zan
wuce cikin gida…” “Na hanaki ne?” Ya furta yana zuba min narkakkun idanunsa.. Turo
bakina na yi sai ga Ya Muhd ya shigo yana kallona “Tashi ki samo masa snacks a
kitchen Malama…” Ji na yi kamar na yi ihu. Na kalleshi na ce “To ka bani Hijab
d’ina a cikin gida…” Tsaki Ya Muhd ya yi kafin ya fice sai ga shi ya dawo da Hijab
‘din ya hurga min. Ina kallo Ustaz ya ‘dan tab’e bakinsa na zura Hijabin na fice da
sauri. A kitchen na tsaya ina mayar da ajiyar numfashi dafatan Allah yasa Ustaz
aurena yazo sake nema.. Ban dawo daga hayyacina ba sai da Ya Muhd ya shigo kitchen
d’in yana wurga min harara ya furta “Ki zuba abinci ki kai masa Malama ki ha’da da
snacks.” Ya fice da sauri.


Na sauke ajiyar zuciya. Na ha’da abincin da snacks d’in sannan na shiga d’akin da
yake zuciyata na wani irin bugawa. Har na ajiye abincin bai d’ago ba. Na ja na
tsaya don na kasa fita daga sitroom d’in. “Zuba ka’dan.” Ya furta cikin wata irin
husky voice. Kamar ba zan zuba ba, sai dai na zuba tunda neman sulhu nake. Na ajiye
akan table ya d’ago yana kallona kafin ya d’au abincin ya tab’e bakinsa. Na rasa
dalilin wannan tab’e baki don haka na fara kallon jikina ko wani abin ya gani ban
ga komai. Don haka na koma kujera na zauna. “Ki tashi ki koma ba wajenki na zo
ba..” Da wani irin zafin rai na ‘dago ina kallonsa sai naga shi ko kallona ba ya yi
tuwonsa kawai yake ci. Haushi ya kamani na mik’e da sauri zan fice daga ‘dakin. Na
ji muryarsa a waya yana furta “Aysha, zo ku gaisa da zab’in alheri da Allah ya min,
ga matar da za’a aura min aure da ita jibi….” Wani irin rawa jikina ya fara na juya
da sauri don ganin matar da yake nuna min a vedio call. Zuciyata ce kawai bata fito
ba, Saboda tashin hankali. Ya mik’a min wayar ba tare da ya kalleni ba. Take
hankali yazo min kada a yi abin kunya na karb’e wayar ina kallon kyakykyawar
yarinyar a cikin waya sai sakar min murmushi take. Yarinya kamar ita ta k’era kanta
fara jajir da ita. Idan ma zata girmeni da ka’dan ne. “Sannu Aysha..” ta furta
cikin zak’in muryarta. Kokawa na dinga yi da numfashi na na ja iska da k’yar na
fesar ina k’ak’aro murmushi na ce “Sannunki…” ta lumshe ido tana furta “Yaushe zamu
ha’du ki taya ni shirin biki?” Ji nayi kamar na k’unduma mata zagi. Na ha’diye wani
abu da ya tsaya min a mak’oshi na ce “Ki yi hak’uri ina school ba ni da time, Allah
ya sanya alheri..” Daga haka na mik’a masa wayar da sauri, ina jin zuciyata na wani
irin hantsilowa. Bai karb’i wayar ba ya nuna min gefensa “Ajiye min anan, kin ga
zab’in da Allah ya yi min ko? Wani baya auren matar wani, she is my cousin jibi
za’a d’aura mana aure don a shekaruna ba zan iya jiranki wani degree ba, duk sanda
kika gama degree d’in idan kina da niyyar aure na the door is open…” Ya fa’da yana
kurb’ar lemo da min kallon

8 / 15