Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
‘dan tsuke ya furta “Morning…” Daga haka bai sake
magana ba ya mayar da kansa kan abinda yake na daddanna waya. Principal ya mik’e
min wasu files “Maza ki kaiwa Emeka, ki ce masa ya yi signing before a fita
break..”
Na amshi files d’in ina d’an durk’usawa. Na fita raina a b’ace. Zuciyata cike da
mamakin kallon da Ustaz ya min kamar bai sanni ba. Sai na ji sam ban ji da’di ba.
Haka dole na koma Islamiyya ba don raina na so ba, sai don zuciyata ta kasa
dauriyar rashin ganin ustaz. Ranar ma ko kallo ban ishesa ba, ya yi karatunsa ya
fita fuskarsa a d’an tsuke.
Ina komawa gida na tarar da abinda ya kusa fasa min zuciya. Tun daga bakin gate
nake jiyo hayaniya a cikin gidan mu. Muryar Mami a sama take sake furta “Wannan ma
ai zance ne, kuma ba mai yiwuwa ba, Ayshan nawa take da za’a d’auko maganar aurenta
yanzu, to wallahi in dai ina numfashi ba mai aurar da ita a wannan lokacin..komai
zai faru sai dai ya faru….
Gabana ne ya yi wani irin mugun fa’duwa na waro ido a hankali na furta “Aure kuma?
Ni Ayshan za’a yiwa aure yanzu?” Murya a sanyaye na yi sallama, gaba d’aya suka
zubo min ido, kamar sun samu Tv. Take na gasgata abinda zuciyata ta gaya min. Aurar
da ni za’a yi. Gefe na ja na zauna idanuna tuni suka fara bulbular da hawaye ina
kallon Mami na na ce “Mami aure za’a min?” Mami da itama nata idanun suka yi jajir
suna son zubo da hawayen, ta furta “Kul Aysha! Kada ki sake ki zubar min da hawaye
anan, wannan maganar ki ‘dauketa tatsuniya wallahi in dai sunana Fateemah y’ar
halak kuma cikin iyayena sai na cika burina a kan ki… babu wanda ya isa ya aurar da
ke a wannan k’ananan shekarun sai kace a karkara. Ko su karkarar yanzu an daina
irin wannan auren. Wuce ciki ki zauna…” Na kasa wucewa cikin zuciyata sai kakkarwa
take, ni na san halin Abba yana da kafiya da naci akan abinda ya saka gaba, ba
wanda ya isa ya canja masa ra’ayi, baya ma tank’waruwa ko ka’dan, irin mutanannan
ne da ake cewa taurin kai kamar mutanen farko. Don haka ban san sanda na kece da
wani irin kuka ba musamman da na tuna shikkenan son da nake wa Ustaz ya zama tarihi
kenan, ba zan aureshi ba? Mami hankalinta ya sake tashi, ta ja hannu da k’arfi muka
hau sama cikin b’acin rai da k’unar zuciya take furta “Ba zai yiwu ba, ki gaya masa
ma tun farko kada ya yi abinda zamu zo muna samun sab’ani da shi.
“An da’de baa samu sab’anin ba, aure ne dai ba fashi sai dai ki yi duk abinda za ki
yi. Haka kawai ba zan ga samu naga rashi ba. Nagartaccen mutum irin wannan ya zo
neman auren y’ata ko a primary take tsigeta zan yi na ba shi…” muka ji muryar Abba
a sama yana fa’da yana tsaye a k’ofar shigowa…
Mami ta juya a fusace tana furta “Kada mu yi haka da kai Abban Aysha….
Tsaki ya ja kawai ya shige parlor jin ana kiran sallah.
Bayan Sallahr Isha, a al’ada irin ta gidanmu bazuwa ake, a tsakargida kan tabarma a
ci abinci. Yau d’in ma haka ce ta kasance sai dai ni ina daga wani d’an lungu a
zaune kamar yarda Mami ta umarce ni. Abba ya juya yaga kowa bai ganni ba. Ya kalli
Mami ya ce “Ina Aysha?” “Ina zaka ga Aysha anan? Alhali ka birkita mata kwanya tun
d’azu take kuka..” “Ta shirya fara na jini, don aure ba fashi, ki kuma sanar da ita
k’arfe takwas bak’onta zai zo. Don Allah ki sata ta wulak’anta martabar gidan nan
kiga abinda zan
Aikata.. Babban mutum ne da ba zai juri rashin kunya ba…” Daga haka bai saurari
surutun Mami ba ya wanke hannunsa ya saka a cikin tuwo ya fara ci…
Ina tsaye ina jin k’afata na rawa. Babban mutum nake ta nanatawa a zuciyata it
means mai iyali dattijo. Na runtse idona ina jin wani zafi a k’asan zuciyata. Ina
jin yaro ya yi sallama aka amsa masa ya ce “Wai akwai bak’o a waje…” Na ji zuciyata
ta wani irin hantsilawa har sai da na dafe k’irjina. Muryar Abba na ji yana cewa
“Kai ALIYU jeka ka shiga da shi sitroom, kai kuma Usman jeka ka kira min Aysha… Ji
na yi kai na ya wani irin sarawa. Usman da ya nufo inda nake ya tsaya yana kallo
na. “Au da kina tsaye kina ji?” Hawayen idona na d’auke na d’aga masa kai na. “Ki
je in ji Abba kina da bak’o… Saura ki je masa da wannan banzan hawayen shashasha
tun baki san wa ne me neman aurenki ba kin sakawa kan ki damuwa…” Ban bi ta kansa
ba na nufi inda Abba yake. Mami kuka take tana sake rok’onsa ya janye maganar sa.
Kallona Abba ya yi ya ce “Ki je ki shirya ki je sitroom kina da bak’o saura ki je
ki nuna masa rashin tarbiyya…” Na juya jikina a sanyaye madadin na je na canja
kayan Wucewa na yi wajen haka idona a damalmale da hawaye na tura k’ofar, muryata
cike da k’unci na masa sallama.. k’amshin turaren Ustaz na ji ya baibaye hancina
zuciyata na bugu nake son d’agowa naga ko shine ban dawo daga tunanin da nake ba,
na ji ya ce “Aysha Imam ya gida?” Ko daga barci na tashi na san muryar Ustaz na yi
saurin d’ago kaina idona ya sark’e cikin nasa, yana zaune yana matse yatsunsa cikin
na juna fuskarsa d’auke da murmushi…..
Cikin mamaki na furta “Ustaz!” Ya d’aga gira yana murmur ya furta “Ayshatu….
𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 8
Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
Kasak’e na yi ina kallonsa, shi kuma sai sakin murmushi yake ya firta “Kin yi
mamakin gani na ko? Koda yake na san ba lallai ki yi mamakin ba don tini zuciyarki
ta sanar da ke zan zo d’in ko ina so ko bana so, haka ne?” kallonsa kawai nake
kafin na
Ankara da abin kunyar da na so aikatawa na runtse idona ina jin yarda zuciyata ke
harbawa da k’arfin gaske. Bana son na bu’de idona balle na tarar da
Mafarkin da na saba ne.. “Ki yi hak’uri nazo gidanku ba tare da saninki ba, ban
kuma nemi amincewarki ba ko? Na yi hakane saboda koyi da sunnar manzon Allah s.a.w,
na fara
Neman izinin iyayen yarinya kafin ita yarinyar. Na san tuni ki fuskanci manufata ba
ke ba ma wasu da dama a ajinku sun san inda zuciyata da ruhina suka karkata, kema
kuma a idonki na gano zallar son Ustaz da k’aunarsa…” Da sauri na waro idona ina
kallonsa. Ya ‘daga min girarsa guda da ta bada wani shape mai kyan gaske. Yana
lumshe idon. “Don't pretend Aysha na san kina so na, albushir guda da zan miki ina
miki so ninkin miliyoyin naki…” wani sanyi na ji yana ratsa zuciyata ban san sanda
na saki wata siririyar ajiyar zuciya ba. “Ba ki ce komai ba?” Na sunkuyar da kai na
wani murmushi da ban shirya zuwa masa ba yana kufce min. Cikin siririyar murya na
furta “Me Zan ce Ustaz…” “Ki ce I love you too…” Da sauri na saka tafin hannu na
rufe fuskarta, ina ji Ustaz ya saki ajiyar zuciya ya furta “Yawaitar kunyata a
idanunki ya tabbatar min da zazzafar soyayyata a ranki. Amma naga kafin ki fito
kamar kin yi kuka ko dai baki so fitowar ba ne?” “Ai ban san kai ba ne…” Na yi
saurin toshe bakina jin abinda bakin ya furta.
Murmushi Ustaz ya saki ya furta “Ni na sani ai, da kin san ni ne kwalliya mai kyau
zaki cab’a min ki fito kina iyayi irin yarda budurwa take wa Habibinta ko?” “Kai
Ustaz!” Na furta ina d’an satar kallonsa “Kai ko gaskiya, next zuwan da zan yi dama
ki tabbatar kin fito min a y’an matanki caras a bu’de min kuma jiki tunda ya
halatta ko sau d’aya ne kaga matar da zaka aura ki saka min kaya mai kyau.. Kin ji
ni ina ta surutu ban tabbatar ma ana so na ko a’a ba…. AYSHA d’ago ki kalleni…” na
d’ago a hankali ba don zan iya kallon nasa ba, sai don bana son na masa gaddama.
“Kina so na za ki aure ni?” K’asa na yi da kai na in furta “Kana da mata?” Wata
irin dariya ya yi da har sai da ya bayyana wasu points a gefen hancinsa. Ya furta
“Kishi kumallon mata, kada dai ace AYSHA na da kishi?” Girgiza kai na yi “Ni ba ni
da kishi, ni dai kawai ba zan auri mai mata ba..” Dariya ya yi sosai ya furta
“Mhmn, ba amsa kenan, don wannan amsar bata cika gamsashshiya ba.” In a serious
tone ya furta “I have a wife AYSHA da yara biyar…” wani irin waro ido na yi,
k’walla na taruwa a k’asan idon nawa. Na girgiza kai. Ustaz kuwa idanunsa ya kafa
min yana sakin murmushi k’asa k’asa. “Gaskiya na gaya miki, ki je ki yi shawara zan
dawo jibi idan kin amince sai ki gaya min. Ko ta cikin waya ne.” Ya fa’da yana
ajiye min wani kwali a cikin leda “Idan kin kunna akwai layi a ciki, na yi setting
komai, ban amince da Instagram da duk wasu tarkacen Social media ba sai whatsapp
kawai. I repeat Whatsapp only AYSHA…. Anjima zan kira na san a waya dai may be zaki
amsa min sosai ba za’a dinga min maganar bebaye ba, mai rowar murya kawai…”
Murmushi kawai na saki ha’de da fa’din “Na gode.” Cikin sanyin murya don kam Ustaz
ya sanyayar da ita, tunda ya gaya min yana da mata. “Numberta kawai, Sai Siblings
d’inki da parents ban da su bana son ganin any number.” Na ce “Toh!” Ya ‘dan kalli
table ya tab’e baki “Budurwar k’auye ba ruwa ba lemo haka ake saukar saurayi ko?”
Da sauri na girgiza kai ina y’ar dariya ka’dan. Na lura Ustaz sam bai da bak’unta.
Komansa free yake. “Ki gaida kowa na cikin gida sai na dawo.” Ya fa’da yana ficewa
daga d’akin. Sakin ajiyar zuciya na yi, ina lumshe ido. A wata duniya na dinga ji
na, mai girman gaske. Da na san Ustaz ne yazo wajena ba ta yarda za’a yi na zubar
da hawaye na a banza, tunda Burina ne dama burina zuwan wannan ranar. Abu guda ke
fa’dar min da gaba Mami na! Ban san yarda zata fuskanci lamarin ba. Ni kam ina son
Ustaz kuma na shirya Aurensa koda Ba Abba ne ya ce ba, balle shi ya ce.
Na ‘d’au kwalin wayar, ba kowa a tsakargida shiru gidan, dama Mami ce mai son hirar
tsakargida da alama tunda bata da sukuni a zuciyar ta sai kowa ma ya kama kansa.
Umma dai itace da girki na san tana wajen Abba. Step na fara hawa ina jin tsoro na
yana sake yawaita. A hankali na tura k’ofar parlorn Mami, Kamar yarda na zata tana
zaune tana kallon tashar Arewa24. Ta amsa sallamar ba tare da ta kalleni ba.
Jikina a sanyaye na zauna a gefenta ina nazarin fuskarta na ji ta furta “Yaya kika
ganshi? Wani dattijo ko? Mai gemu buya-buya tunda na ji ance Ustaz ne, yanzu haka
ma k’azami ne..” Kallon Mami ina mamakin kalamanta, tabbas bata san Ustaz ba, da
bata yi wani furucin ba, ba mamaki da zata gan shi taga kamanninsa itama ta so ya
zama surikinta.. ina cikin ko a cikin maza millions za’a tsame Ustazu na a matsayin
wanda yafi kowa kyau da tsafta.. Mami ta zaci in dai ance mutum Ustaz ne sai ya
zama wani mara fasali. Ai yanzu Ustazai akwai d’aukan wanka da kwalliya sosai ma.
Ban san me yasa ba sai na ji wasu siraran hawaye suna zubo min, wanda na san ba
hawayen komai ba ne sai na zallar farin cikin cikar burina, tunda na ji sanyinsu
har k’asan raina da cikin jikina..
A zaton Mami kukan bak’in ciki nake. Ta mik’e tsam daga kujerar ta ta dawo inda
nake ha’de da dafa ni, ta furta. “Daina zubar da hawayenki a banza Aysha, in dai
ina numfashi babu mai miki wannan auren tozarcin ko me ma zai faru ya faru… wani
irin tsalle zuciyata ta buga, na ‘dago da sauri ina kallonta na furta “Mami, kada
ki ce haka, Mu yi hak’uri kawai mu yarda da k’addara, Saboda ba mu san abinda Allah
ya b’oye ba….”
“Rufe min baki Aysha…” Ta furta cikin wani irin zafin rai, da har huci take fesar
wa. “Kada kice min zuciyarki har ta amince da wannan mutumin? Wato har kin ji a
zuciyarki zaki iya aurensa? So kike ki ba’da min k’asa a ido? Duk da yak’i da
hak’ilon da nake na nema miki y’anci a wajen iyayenki da ba su san mutuncin ki ba?
To bu’de kunnenki ki ji da kyau, ko son sa zai kasheki ba zaki auresa ba…” Ta fa’da
tana fancakalar da hannu na ta mik’e a zuciye ta shige d’aki. Shiru na yi zuciyata
na harbawa na zubawa hanyar da ta bi ido. Ina mamakin duk furucinta. “Anya Mami
tana cikin hankalinta kuwa?” Ras take” zuciyata ta bani amsa tsabar son boko ne da
ak’idar bokon yaja mata haka.
Na d’an tab’e baki ba ina tunanin tabbas za’a samu matsala, don yarda nake son
Ustaz bana jin wani hargitsin Mami zai saka na rabu da shi. Na shige d’akina. Ina
bu’de ledar da ya ajiye min. Waya ce mai kyau IPhone 13 sai turaruka masu kyau guda
biyu. Na shinshina turaren d’aya irin turarensa ne sak, a jikinsa ya rubuta “For
Night only…” Murmushi na saki, ina tunanin sabida me zai ce sai dare kawai zan
saka.. Na san Abba ya kwanta, don haka sai da safe zan kai masa wayar ya gani, idan
ya amince sai na cigaba da rik’ewa idan kuma bai amince ba sai na mayar wa Ustaz.
Wanka na yi na saka sleeping dress sannan na fesa turaren da Ustaz ya sanar da ni
sai dare kawai zan dinga sakawa. Sai da na kwanta sannan na gane dalilinsa na cewa
For Night d’in. Don k’amshin sosai ya dinga tuno min da Ustazun. Na dinga sakin
murmushi ni ka’dai. Kafin na ji wayar na vibrating. Idona na kai kan screen d’in
wayar sai ga hoton Ustaz a ciki yana sakin murmushi an rubuta “Farhatul K’alb..”
(Farin cikin zuciya) ina sallama ya saki ajiyar zuciya kafin ya amsa ya furta
“murya mai da’di…” shiru na yi “Ba gaisuwa AYSHA? Me ya hanaki bacci k’arfe d’ayan
dare?” Da zan iya cewa zan yi Tunaninka. Sai dai na ji na kasa na furta “Bakomai…”
“Gaskiya ban yarda ba.. ni na san me ya hanaki barci..” “To menene?” Na fa’da cikin
sanyin murya. “Cewa zaki yi To menene Habibeey?” Ya fa’da yana koyan muryar y’an
mata dariya ya bani sosai na dinga yi kuwa ba k’akkautawa “Tunanin D’an Ugly
saurayinki ko?” Na ware ido.. “Ba zaki amsa ba. Zaki iya vedio call please.” Da
sauri na girgiza kai ina cije leb’ena na furta “A’a” “Me yasa?” Duban jikina na yi
na ce “Ni dai bana so…” “Mhmn..” Ya ce cikin wata irin murya “Allah ya baki
hak’uri, amma ki saka Hijab mana mu yi, wallahi son ganin ki kawai nake ko zan iya
barci, kin bi kin rufe idona ke kawai nake gani.” “Shikkenan ma, kaga ba sai ka
ganni ba kenan…” Dariya ya saki ya ce “Aysha!” Sunan da na ji ya tsarga har
k’aramin yatsan k’afata “Kin san sunana?” “Uhm” na ce masa. “Okay fa’da na ji
please, ni dage sai fa’dar naki nake kamar ni na ra’da miki. Ya sunana?” “Ustaz!”
Na fa’da cikin muryar da ni kaina ban san na iya ta ba. Shiru ya yi tsawon seconds
Hamsin har na zata ko ya kashe ne. Na furta “Hello..” ya saki ajiyar zuciya yana
firta “Ina jin ki Aysha… kin tafi da numfashi na ne, Allah ya baki wata irin murya
da zan yi kishin wasu mazan su gaba da jinta in dai za su yi feeling abinda nake ji
yanzu… Ba zan iya ba, ki tashi ki yi sallah yanzu ki rok’a mana dukkan alheran da
suke cikin neman auren nan kin ji?” “Toh” na amsa “Kina sallahr ai ko? Ko ba kya
sallar dare?” “Ina yi.” To maza ki yi sallahrki zan kira da safe na ji feedback
akan maganarmu.” Ya fa’da yana kashe wayar bayan ya furta “I love you…” cikin k’asa
da murya. Sai da na ware ido ina tunanin Anya kuwa Ustaz ne.. ashe Ustazan nan suma
ba baya ba wajen bawa soyayya hakkinta? In dai kuwa haka ne tabbas na dace..
Sallahr na yi na dinga rok’on Allah musamman akan Mami da niyyar Allah ya karkato
mata da zuciyarta ta amince ta kuma so auren nan.
Da sassafe na tashi, cikin matuk’ar karsashi da wani farin ciki da ya kasa b’oyuwa
a fuskata.
Idona kawai zaka kalla ka karanta abinda yake k’asan raina na zallar farin ciki.
Kasancewar lahadi ce na fita Parlorn Abba inda anan ake zama duk ranar lahadi a
karya.
Tun daga tsakargida masu aiki suke bina da kallo har na isa parlorn. Su ma su Abba
da mamaki suke kallo na ganin yanayin sauyin fuska a tare da ni ba kamar jiya ba da
na tashi fuskar kamar hadarin kaji. Mamaki ya ishi Abba ya kasa shiru har sai da ya
furta “Ayshan Mameeyn ta, ta samu ne naga kina wani farin ciki.” Sunne kaina na yi
ina dariya da girgiza kai. Na mik’a masa kwalin wayar hannuna don na b’oye
turarukan. Wayar ya bi da kallo yana furta “Wannan fa Aysha?” Cikin k’asa da murya
ina kallon Mami da take min wani kallo na furta “Mutumin jiya ne ya ba ni.” Abba ya
‘dan ware ido yana furta “Ma sha Allah, labarin zuciya a tambayi fuska. Fateemah ya
naga haka kuma? D’iyar take da alama ta yi na’am da zanka’de’den mijinta, ke tun
baki tsaya kin ji waye ba kike kumfar bakin ba kwa son sa. Ustaz Ahmad Sulaiman
Sa’eed babban Malamin nan, yaro da kwanyar manya shine fa yake son ta…” Cikin wani
yanayi Mami ta ‘dago idonta tana furta “Ustaz!” Da mamaki a idonta, ta furzar da
wani huci tana furta “Shine ma abinda ba zai yi wu ba cab’di! Kama sake nazari….”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎