Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NAGA Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel by Nazeefa NASHE

Author :  NAZEEFA NASHE Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 15

39K to 42K   out of 42.5K words

Anty Surayya mai Bojuwa herbals ba k’arya ba ne, suna da amfani
k’warai a jikin mutum. Zan kuma baki numberr wayarta don ki dinga tuntub’arta don
samun ingantattun magani na gyaran zamantakewar aure…. Ta mik’e sai gata ta dawo da
wata roba. Zuba y’an k’wayoyin maganin ta yi a hannunta ta ha’da min da dabino tace
na taune. Sauran kazar sababi tace a satinnan zata kawo miki. Na san komai don haka
kunya ta kamani don ina karatun litattafai saboda haka na san magungunan da Umman
ta bani da dalilin ba ni su. Da Mami ce ba zan ji kunyarta ba kamar Umman don ita
Umma sam bata saki jiki da ni ba. “Gyaran jiki dai ba kya buk’atarsa don fatar ki
mai kyau ce ba abinda kike buk’ata, sai zuwa saloon a miki predicure da manicure
zuwa jibi ki shirya ki je.” Na d’aga mata kai. Daga haka ta mik’e ta shige kitchen
na san ba kunya ce ta saka ta barin wajen. Na d’an saki murmushi kawai ina jin
soyayyar Umman da wani irin tausayinta a raina. Ni kenan y’arta mace amma ta iya
kyauta da ni ta kuma d’auke kanta a kaina. Lallai Umma ta cika fulanin k’warai masu
kunya kara da d’auke kai.


Sai dare sannan bak’i Mami suka tafi. Ina shiga parlorn naga sun yi kaca kaca da
shi. Tab’e baki nayi na shige mai aikin da take gyarawa.



Wata litinin abubuwan suka fara faruwa tsakanina da Ustaz, litinin d’in ana saura
kwana hu’du a fara bikin. Na san anan yake shan ruwa in dai ya yi azimi. Shirin
bikin bai hanani tashi na fara shirya masa abin shan ruwa ba, duk da yinin
Ranar sam bai kira ni ba. Nima kuma na shiga busy shi yasa ban kira shi ba. Azimin
ne nima a bakina, amma haka na daure na fara shirin yi masa abin bu’de baki. Kunun
kwakwa nake son masa, rashin ganin flavour ya saka ni fitowa daga kitchen d’in zuwa
d’akin Mami. A bakin k’ofa na tsaya ganin ba Riga a jikinta tana shafa mai. “Shigo”
na ji ta ce. Kamar ba zan shiga ba sai kuma na shiga kaina a k’asa. Tsaki ta zabga
tana furta “wani munafuncin kuma kika tsuro da shi na tsayawa a bakin k’ofa?”
Girgiza kai na nayi na ce “Aa naga kina saka kaya ne..” ta d’an yi tsaki kafin ta
ja towel ta rufe k’irjinta “Yau kika saba gani na ba riga?” Na girgiza kai.
“Flavour nake so Mami zan saka a kunun kwakwa..” na furta don son barin d’akin.
“Yana gidan Uban Ahmad…” Mami ta furta cikin wata irin murya mai bayyana tsananin
b’acin rai. Na d’ago ina kallonta idona yana kawo ruwa, ta iso gaba na cikin b’acin
rai ta ce “Kike kallo na, na ce yana gidan Ubansa Sulaiman Sa’eed ba, ko da abinda
zaki yi?” Hawaye ne kawai suka shiga zuraro min na saka k’afa da sauri na juya na
bar d’akin jikina har rawa yake yi. Da k’yar na koma kitchen na k’arasa girkin a
gaggauce na fa’da wanka. A raina ina jin ko me Mami zata yi ba zan rabu da Ahmad
ba, amma fa zuciyata sai suya take yi.

Shima bayan magribar da yazo sai naga fuskarsa sam ba annuri, kallona kawai yake da
k’yar ma ya amshi cup d’in da ba zuba masa Kunun, naga yana kurb’a a hankali kamar
yana shan magani, idonsa da suka jirkita zuwa brown colour a kaina. Kawai sai na
samu kaina da rushewa da kuka. Bai hana ni kukan ba kamar yarda bai fasa kallona
ba, abin mamaki shima sai naga gangarowar hawaye a nasa idon. “Me ya sameki?” Ya ce
cikin wata irin murya da yasa na d’ago ina kallonsa… ban amsa masa ba illa cigaba
da kukan da na yi, ya saka hannunsa ya mik’o min “Zo ki gaya min…” Ji na yi ba zan
iya masa musu ba na isa wajensa jikina a sanyaye na zube a gabansa. Durk’ushe wa ya
yi a gabana ya d’ora cup d’in kunun a bakina.
A hankali na fara sipping. “Gaya min damuwarki?” Ya furta min a hankali. Na ce “Kai
zan tambaya Ustaz, kai zan tambaya ji fa k’walla a idonka. Kana cikin damuwa yau
gaba d’aya fa ko kira na baka yi ba…” ya saka hannunsa a goshina yana murzawa a
hankali bayan ya jani jikinsa bakinsa ya saka a saman nawa yana lasar lips d’ina.
Kafin ya lumshe idonsa yana cigaba da shafa goshin nawa ya furta “Ki yi shiru baki
da lafiya ga kanki nan yayi zafi jijiyarsa ta tashi.” Ni da kaina na yarda ba ni da
lafiya sai dai shima na ji nasa hannun shima ya ‘d’au zafin. Tafin hannunsa na kama
na rungume a fuskata ina shak’ar k’amshin turarensa na furta “Ustaz kai ma jikinka
zafi.” Idonsa a lumshe ya d’aga min kai. “Bani da lafiya ne AYSHA, wani irin ciwo
zuciyata take min, ina kika je jiya da daddare, na kikkira wayarki baki d’aga ba?”
Girgiza kai na yi ina mamakin furucinsa na furta “Ina zan je ban gaya maka ba,
kaima ka san ba inda zan iya zuwa.” Still idonsa a lumshen ya sunkuya ya sunbaci
tsinin hancina ya janye ni daga jikinsa sai naga ya mik’e yana kallona ya furta
“Good night, idan kinga baki ji sauk’i ba ki fa’da a gida a kaiki asibiti..” Da
mamaki na ce masa “Baka ci abincin ba ai?” “Am okay.” Ya fa’da yana fita da sauri
kamar har a lokacin da k’walla a idonsa. Na mik’e zuciyata na bugawa na shige cikin
d’aki duk hankalina a tashe.


Tun daga ranar Ustaz ya canja gaba d’aya, baya kira na sai dai na kira shi. Khadija
ma har waya take min ta ce sun rasa kansa a gida. Amsa guda nake bata nace nima
anan d’in ban san me ke damunsa ba. Sau tari ma idan na kira shi cewa yake yana
busy ya kashe wayar. Tun jikina na bani bakomai har nazo na yarda tabbas akwai wani
abin da Ustaz yake b’oye min.


Mami kuwa hankalinta kwance cikin zallar farin ciki take gudanar da shiryen shiryen
bikin. Dukiya yake kashe min bata wasa ba, lamarin har ya fara firgita tunani na.
Kullum kulawa take bani ta musamman. Na yi wani irin fitinannen kyau da kowa ya
gani sai ya tanka.


Ranar da za’a kamu, sanda aka min kwalliya wallahi idan ba fa’da aka yi ba zata
zaka yi India ce, Saboda fitinannen kyan da na yi a cikin Indian dress d’in da aka
min complete kwalliyarsu. Jikina a rufe yake ruf. Duk da fuskata da walwala sai dai
sab’anin zuciyata da take cike da takaicin Ustaz na rashin kulawa da ya kamata ya
bani, musamman a irin wannan lokacin da amarya da ango suke buk’atar zuwansa.


Mai kwalliya na gama min Mami ta shigo wajen. Wani irin bu’de baki ta yi ta furta
“Wow! Ya subhanallah Ayshata haka kika dawo? Fatabarakallahu Ahsanul
Khaleek’in, Tabbas Allah ya yi halitta…” murmushi kawai na saki ina kallon yarda
Mamin ta rungume ni a jikinta ana d’aukarmu hotuna ko ta ina. Na so ace Ustaz ne a
madadinta.

“Sai ki kirashi ku tafi.” Mami ta furta fuskarta a d’an tsuke kamar ba ita ta gama
dariya yanzu ba. Wayata na d’auka na fara kiransa ta dinga ringing bai d’aga ba
kamar yarda ya saba a kwanakin nan. A fusace na ji ya yi furucin “Wai menene?”
Mamaki ya kamani jin tambayar rainin hankalin da ya yi min, na dinga kallon wayar
ina son na tabbatar da gaske daga shine. “Na gama shiryawa” na furta a hankali. “Ki
ce Mami ta kai ki.” Ya furta yana katse wayar. Ido na d’an ware kafin na sake danna
wayar na tura masa text “Amma dai ka san kai ya kamata ka kai ni ko?” Ban zaci zai
dawo min da amsa ba, sai naga ya turo min da “To ki jira…” na d’ago ina kallon Mami
da suke magana da mai kwalliya ta kalleni itama ta ce “Ya taho?” Na d’aga kaina
kawai ina furta “Eeh ga shi nan.”


Tun a mota nake kallon yanayin Ustaz d’ina tamkar ba shi ba, fuskarsa murtuk babu
annuri ko ka’dan a cikinta, na zata zai yaba kwalliya ta sai dai ko kallona bai yi
ba. Ya ja mota muka tafi bayan Asma ta shiga. Hankali ne tashe nake kallonsa na ce
“Baka da lafiya ne Ustaz?” Bai ko kalleni ba balle ya amsa min, ya cigaba da
driving zuwa inda ake gudanar da shirin. Shiru motar tafiya kawai muke kamar kurame
sai sautin k’ur’an da yake cikin motar cikin suratun nisa’i.

Muna isa wajen Dinnerr Asma ta fita. Ni kuwa kasa fita na yi ina bin Ustaz da kallo
da idanuwana da suke kawo ruwa. “Ya dai?” Ya furta yana d’an Cijan bakinsa da kawar
da kai, na san kwallar da ke idonsa ce baya son na gani. Hannunsa kawai na kama
k’am cikin nawa. Na furta “Gaya min ustaz, gaya min ko laifi na maka na baka
hak’uri bana son irin wannan horon da kake min zuciyata ba zata ‘dauka ba…” cigaba
ya yi da danna wayarsa idanunsa duk sun ka’da sun yi wani iri. “Baka da lafiya ko?”
Na fa’da ina son lalubar k’wayar idonsa. A fusace ya ce “K’alau nake Ayshatu, just
go and live me alone….” Kallonsa nake yi idonsa a runtse kafin na janye hannuna a
hankali na fice daga motar idona na zubar da k’walla ban damu da b’acin kwalliyar
ba damuwata sanin wani laifi na yiwa Ustazun Aysha..




𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️NA GA RAYUWA…21.
Ina neman alfarma Don Allah da Manzonsa 😭 don Allah ku shiga link ɗin nan ku yi
mana voting MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
https://www.facebook.com/share/p/ChZaudpRhnBicHZ5/?mibextid=C7JYKg

Idan kun shiga zai nuna requesting ana yin approving sai ku danna mini don Allah.



Masoya Ustazun Aysha. A nuna mata kara… Daga kungiyata abar alfaharina. In dai kuna
son na cigaba da rubutu cikin da’din rai…




Ganin irin yawan mutanen da suka zo wajen kamun biki na, ya wanke min duk wani
b’acin rai na da bak’in cikin dake nuk’urk’usar zuciyata. Wani farin ciki ya
ziyarce ni, da na tuna duka wa’dannan mutanen sun zo ne saboda ni. Zuciyata ta yi
haske walwala da fara’ar fuskata suka dawo. Mai hoto ce ta dinga d’aukata duk inda
na saka k’afa, har zuwa sanda na isa wajen zama na. K’awayena suna bina a baya. A
haka na zauna ina ta sakin murmushi. Ki’dan larabawa ne kawai yake tashi a wajen,
da wani irin k’amshin turaren wuta masu da’din gaske. Ba’a rawa kowa yana wajensa a
zaune sai mai gabatar da shirye shiryen bikin ce kawai a tsaye a filin wajen, tana
ta yiwa manyan bak’i barka da zuwa. Kowa yana zaune cikin aji kai daga gani ka san
mutane ne masu aji da wanda ilimi ya ratsa su suka halarci wajen. Ba wani hayaniya
kowa yana zaune a inda aka tanadar masa ya zauna ya hanyar ganin Table no. D’insa a
card d’insa.

An ci an sha, kowa ya yi nak, an kuma yi barkwanci Malamai mata suka yi wa’azi
sosai. Bayan tsawon lokaci aka tashi daga wajen. Dangin Ustaz ma sun zo sun kuma yi
min kamu akan ku’di masu daraja. Ustaz ne ya mayar da ni gida bayan an tashi sai
dai ko kallon arziki bai ha’dani da shi ba balle magana ta fatar baki. Tattarashi
na yi na watsar don ni sam ban san wani laifi guda da na yi masa ba.

Sai sha biyun dare na kashe wayata saboda naga da gaske dai Ustaz bai kira ba.

Da Asuba kuwa ina kunna wayata kiransa ya shigo. Na saki ajiyar zuciya na saka
hannu na amsa kiran cikin matuk’ar farin ciki, don rabon da ya yi min kira irin
wannan har na manta. “Hello Habeeby…” Na kira shi da sunan da ban tab’a kiransa da
shi ba. Madadin ya amsa sai ji na yi ya yi k’aramin tsaki ya furta “Ina ki ka je
jiya da daddare, ba kira wayarki a kashe?” Zuciyata ta wani yunk’oro da tsananin
b’acin rai na ce “Ina kuwa zan je da daddare? Wace irin tambaya ce wannan barci
nake ji shi yasa na kashe wayar na kwanta… na san ba kira zaka yi ba shi yasa ban
ma saka a kai ba.” “Kada ki raina min hankali mana, ki mayar da ni wani sokon
namiji wanda bai san abinda yake yi ba, ke…….”
D’if na kashe wayar da sauri, jin mamakin furucinsa, a muryarsa nake jin wani
b’acin rai wanda na tabbatar har k’asan zuciyarsa yake. Ba zai yiwu na cigaba da
waya da shi ba, don nima tawa zuciyar a hassale yake shi yasa na kashe. Na runtse
idona ina jin wayar tana ta ringing kuma na san Ustaz ne don ringing d’insa daban
ne. Hannu na saka na d’au wayar ba rubuta masa gajeran sak’o.

“Allah ya huci zuciyar manya, ka yi hak’uri Habibeey idan zuciyarka ta yi sanyi ka
kira ni. Ina tura masa na kashe wayar gaba ‘d’aya cikin wani irin tashin hankali
naji hawaye na zubo min daga idona. Me na yiwa Ustaz me zafi haka da nake hango jin
haushina a tsakiyar k’wayar idonsa?
Ranar ne aka yi Dinnerr bikina a AMANI… Shima tsaf aka tsantsara min kwalliya ta
cikin Black material wanda zab’in Ustazuna ne, kwalliyar ta min kyau matuk’a da
gaske. Stone peach ne a jikin material d’in don haka aka min amfani da Shoe and
clutch peach sai sark’ar wuyana ta zallar Zinare zubin English golden. Baa min
kwalliya ba ranar saboda hawaye ya k’i barin idona ba kuma hawayen komai bane, sai
na rabuwa da gidanmu Abba na Ummana, da Mami na. Ga su Ya Usman ma duk wai yau zamu
yi ban kwana, zan tafi rayuwar da kowa yake gaya min sai hak’uri. Zuciyata ta yi
rauni sosai musamman da aka kai ni wajen Abba mu yi sallama. Abba ya d’ago cikin
jarumta ya saki murmushin da na tabbatar na k’arfin hali ne. Hannu yasa ya ya fito
ni jikin sa. Muryarsa cike da k’arfin hali ya ce “Matso AYSHA ta….” Na matsa kuwa
jikinsa na kafa kaina a saman cinyarsa ina zubar da wani irin hawaye. Hannu ya saka
ya bubbuga baya na alamar rarrashe cikin wani irin furuci ya ce. “Ki yi hak’uri
Ayshatu na, haka kowace mace ta gada kuma shine abin alfaharin ta. Aysha, ina son
ki yiwa mijinki biyayya kwatankwacin biyayyar da Rabi’atul Adawiyya ta yiwa
Mijinta, ko ki samawa zuri’ar gidanku k’ima da daraja a idanun Mijinki. Ba na son
AYSHA ki yi abinda Mijin ki zai tsaneki har ta kai ga yazo yana dana sanin aurenki.
Alhamdulillah ina alfahari da iyayenki mata ina so kuma ki yi koyi da su. Na fi son
a fito min da gawar Ki daga gidan Ahmad Aysha, haka shine cikar burin Uba na gari,
musamman da ke ke ka’dai ce d’iyata Mace da Allah ya bani. Soyayyar da nake miki ce
ta saka na aurar da ke da k’ananun shekaru ba k’iyayya ba, Saboda na san Ahmad
mutum ne na k’warai zai kuma rik’e min ke tsakaninsa da Allah. Ki kiyaye Ayshan
Mami Allah ya miki albarka.” Ameen na ji jama’ar parlorn sun amsa Daga haka Abba ya
ja hannuna ya damk’a min Alkur’ani ya saka min wata jaka mai kyau a gefena.
“Alk’ur’ani ya zamo abokin hirarki, sallaya ta zama inda zaki sujjada ki kaiwa
Allah kukanki, bana son kawo k’ara, mutuniyar kirki bata fiye kai k’arar Mijinta ba
gudun b’ata masa suna. Kin ji ko?” Na d’aga kai ina jin zuciyata kamar zata tafasa
saboda tsananin b’acin rai.


Ranar kam Ustaz k’in zuwa ya yi ya kai ni wajen dinner, kiran duniya ya k’i d’agawa
k’arshe ma sai ya kashe wayar tasa gaba d’aya. Jan bakina na yi na tsuke ban gayawa
kowa ba sai su Mami ne suka tafi dani wajen dinner.


Wannan shine labari na da duk wata soyayya da muka gudanar da Ustaz.

Hawayene ya gangaro daga idona na mik’e daga saman kujerar da nake ina bin d’akin
Abba na da kallo. Tunani ne ya shiga yi min suntiri a zuciyata so nake na gano
dalilin da yasa duk son da Ustaz yake min ya riki’de ya koma zazzafar k’iyayyar da
ta kasa b’oyuwa a ransa har ta kai shi ga furta min kalmar saki a daren auren mu.
Daren da Ustaz ya da’de yana gaya min ya ci buri iri iri a kansa. Burin ganin
Aysharsa a zahirin Aysharsa ba tare da shamakin tufafi ba. Sai ga shi daren yazo
mana a wani irin hagunce da namu burin. Menene sila? “MAMIN KI!” Na ji zuciyata ta
amsa min a tsawace..
Da sauri na runtse idona ina girgiza kai da k’arfin gaske. Daidai sanda aka bu’de
k’ofar d’akin aka shigo. Na dawo hayyacina ina binsu da kallo cikin dishi dishin
idona. Yaya Muhammad, Ya Sadik, Ya Umar, fuskarsu a murtuke ba fara’a suke zubo min
ido. Suka shigo cikin wani irin taku da yake nuna zallar b’acin ran da suke ciki.
Zuciyata ta shiga bugu da k’arfin gaske na dinga bin su da kallo ina kallon yarda
suka dogara k’afafunsu akan kujerar suka zagaye ni da idanunsu…
Wani irin kallo suke jifana da shi, wanda na rasa a mizanin da zan saka kallon
nasu. Na san dai kallo ne na Allah wadaran halinki…


Sautin zuciyata ya sake bugu da k’arfin gaske jin Ya.Muhd ya kira sunana da
sark’akkiyar muryarsa. “AYSHA! Gaya mana laifin me kika yiwa Ahmad ya sake ki a
daren farko? Kada kice mana bakomai don hakan ma kin san ba zai yiwu ba. Ba auren
k’iyayya aka muku ba, Ustaz kuma bai d’ora miki iddarsa ba balle a ce auren
d’and’ano ya yi da ke? Me kika masa?” Ya fa’da a tsawace.
Hawaye ne kawai yake kwarara daga ido na. Na shiga masa rantsuwa da a idonsa ka’dai
na san rantsuwa ta ba inda ta je. Na ba shi labarin abinda na sani dangane da canja
min da Ustaz ya yi a kwanaki ka’dan da Suka rage na bikin mu.

“Mak’aryaciyar banza, wa kike tunanin zai yarda da wannan tatsuniyar taki? Ta yaya
kike tunanin mutum ya aureki yana tsananin son ki Sannan ya sake ki a daren da aka
d’aura muku aure? Dole akwai wani abu ki gaya min gaskiya kawai… kada ki bari
zargin da nake a zuciyata ya tabbata don ni zuciyata na gaya min tabbas ke da
uwarki sun san komai, Mami ba, tabbas akwai saka hannunta a cikin lamarin haka nake
ji a raina….


Ji muka yi an turo k’ofar da k’arfin gaske, an shigo, idanuna suka fa’da cikin na
Mami da suka ka’da suka yi jajur. “Umar! Ni kake zargi da mutuwar auren Aysha?” Ta
furta a tsawace idanunta suna zubar da hawaye… Umar ya cije bakinsa yana jijjiga
kai ya furta “Ai ba abin mamaki ba ne, tunda kowa ya san kina adawa da auren….”
“Faruk!” Umma ta fa’da a tsawace tana nuna shi da yatsa. Tashin hankalin da kake
son ka jawo mana kenan a gidan nan. Ta yaya kake tunanin Fateema zata cutar da
Aysha ta hanyar kashe mata aure? Kada na sake ji… bana so wani irin zancen banza ne
wannan..? Kana cikin hayyacinka kuwa…

Gani muka yi Mami ta juya zata fita daga ‘dakin, sai dai shigowar Abba ya hanata
don

14 / 15