Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NAGA Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel by Nazeefa NASHE

Author :  NAZEEFA NASHE Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 15

15K to 18K   out of 42.5K words

♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

𝒫𝒶ℊℯ 9



Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR


“Kamar ya?” Abba ya furta yana saka k’wayar idonsa cikin ta Mami. Amma sam yau
Mamin wannan kallon na Abba na da alama bai ratsa ta ba, don tab’e bakinta ta yi
murya a sama ta furta “Kamar komai ma Abban Aysha.. Ta yaya za’a aura mat Uztaz
hakan na nufin makarantar da na ci buri akanta ba zata yi ba kenan? Wani Ustaz ne
zai bar matarsa tana yawo a titi fisabilillah, da ma wani d’an boko ne da sauk’i.
Amma wannan ha’din sam bai ha’du ba, in dai za’a min adalci akan Aysha a tuna bani
da wata da nake gani a matsayin y’ata a bar Aysha ta yi karatu…” Ta fa’da idanunta
suna zubar da k’wallar da ta sanya duk jikina sanyi. Amma ban hango sanyin gwiwa a
wajen Abba ba, kamar yarda na hango shi a wajen Umma, don a raunane ta ce “Abban
Aysha ka yi hak’uri ka janye maganar auren nan….” wani kallo ha hurgawa Umman da ya
sata shiru da bakinta tana kallon Mamin a raunace. “Ba zan janye ba, har abada
kuwa, don ba zan ga samu naga rashi ba, wani irin solob’iyon Uba kuke so na zama?
Allah ya kawowa y’ata nagartaccen Mijin da kowane Uba yake fata sai na masa butulci
sabida wani karatun boko na banza da na wofi. Mutumin da ko y’ay’a d’ari yake so
za’a ba shi a rana guda, duka ta tsallake ya ce Aysha ce ta masa Aysha yake son
aure sai na zuba masa k’asa a ido, Saboda wata maganar banza da wofi. Ita ka’dai ce
fa y’ata mace da nake fatan ta yi dace da Mijin k’warai.. ko yanzu yake so na tsame
ta a boko na mata aure wallahil azeem na shiryawa haka, ba abinda kuma zai saka ni
fasawa. Karatu dai idan ya ce zata yi a gidanta falillahil hamdihi idan ya hanata
ma gaba d’aya wallahi ba zan tursasa shi ba. Saboda ku iyayen banza ne ku da zaku
saka ta ta yarda ku rarrasheta ku ke sakata ta bijire min? To ku je ku yi na da ku
a ga wanda zai ci riba…” Daga haka yaja bakinsa ya tsuke ya kuma wanke hannunsa ya
tsoma cikin tuwo ya cigaba da ci. Fuskarsa a ha’de sosai alamar duk abinda ya fa’da
har k’asan zuciyarsa hakan yake. Mami ta ture kwanon tuwon da muke ci ni da ita da
Umma ta mik’e fuska a ha’de ta fice daga parlorn.


Jikina a sanyaye na mik’e zan bi ta Abba ya saka baki ya kira ni muryarsa a dake.
“Dawo Ayshatu, zauna ki ci tuwonki, ba cutar da ke zan yi ba, har ga Allah alheri
nake hango miki game da aurenki da Ahmad..” Na d’aga kai na ina wasa da zoben
hannuna. “Ki kuma bu’de wayarki ki fara amfani da ita, na san ba zai cutar da ke
ba. Ban kuma amince da duk wani tarkacen social media ba…” Na d’aga kaina don shima
Ustaz garga’di da ya min kenan. Na san tunda suke ta jaddada min to social media
d’in ba abu ba ne mai kyau. Cin tuwon kawai nake ba tare da ina fahimtar
d’and’anonsa ba, don dai kada Abba ya yi magana ne na zage na ci tuwon kafin na
mik’e cikin mutuwa jiki na haye sama. So nake na je naga Mami da halin da take
ciki.


Jikina a sanyaye na murd’a k’ofar d’akinta don bata parlour kamar yarda ta saba
zama. A saman gado na sameta hannayenta dafe da k’unci da alama ta yi zurfi cikin
tunanin da take. Zama na yi daf da ita ina d’ora kaina a saman kafa’darta. Sai na
ji ta saki ajiyar zuciya. Ta rungumoni sosai a jikinta tana furta “Aysha, yanzu kin
amince d a auren da Abba zai miki?” K’asa na yi da kaina idona na zubar da k’walla.
“Mami kema ki yi hak’uri please…” Janye jikinta ta yi tana sakin wani malalacin
murmushi “Na yi hak’uri Aysha? Na yi hak’uri Ustaz ya cuceni ya raba ni da duk wani
farin cikina? Ya kuma ruguza min da duk wani shirina a kan ki da na shekara da
shekaru ina shiryawa?” Ta girgiza kai tana taune leb’enta ta furta “Wallahi bai isa
ba, mu zuba ko ni ko shi?” K’asa na yi da kaina saboda ba zan iya sake cigaba da
juriyar kallon idanun Mami ba, don wani abu nake gani a cikin idon… Zamewa ta yi
ta kwanta tana mayar da numfashi idanunta a lumshe. “Tashi ki tafi AYSHA, ta shi ki
wuce d’akinki…” Ta fa’da a zafafe da sauri kuwa na mik’e ba fice don ban saba ko na
ce ban tab’a ganinta a irin wannan yanayin ba… na lura daf take da fara Aljannu…




Da safe har na shirya na gama shirin makaranta Mami bata tashi ba. Hakan yasa na
nufi d’akinta ina nocking a hankali. A zafafe ta furta “Waye ne?” “Nice Mami…” ta
bu’de k’ofar tana kallona idanunta kuwa da k’yar take lumshe su. Ta ja hannuna tana
murzawa a hankali cikin wata irin murya ta furta “Ayshatu…” Na d’ago ina kallonta
ta d’an sunkuyar da kai sai kuma ta saki hannun nawa. Tana sakin Malalacin murmushi
ta furta “Har kin yi shirin makaranta?” Na d’aga mata kai “Ina kwana Mami?” Amsawa
ta yi tana d’an ja baya ta furta “Wuce ki tafi AYSHA, ni ba abinda zaki ce min
tunda kin zab’i farin cikin iyayenki a kaina. A jiya na yi takaicin rashin haihuwa
da ni na haifeki da kaina na san ba zaki bujire min ba….” Kuka ne yazo min sosai
ban san sanda na fa’da jikinta ba na saki wani irin kuka. Mami ta rungumeni sosai a
jikinta ina jin yarda take sakin ajiyar zuciya. A kunne ta ra’da min “Kada ki
bujire min Aysha, kada ki guje ni zan shiga wani hali AYSHA….” Da k’yar ta zame
jikinta daga jikina ta juya bayanta tana furta “Je ki ki rufe min k’ofa…” Jikina a
sanyaye na fice daga d’akin nata.


A kitchen na tarar da Umma na tana ta aikinta ita ka’dai. Sai na ji duk ban ji
da’di ba don koda yaushe tare suke aikinsu da Mami. Da wayona dai ba zan tab’a cewa
ga ranar da suka yi aiki ba tare ba. Kallo guda ta min ta d’auke kanta tana amsa
gaisuwata. Na juya zan fice ta furta “Ba zaki k’arya ba ne?” “Umma na k’oshi…” Umma
ta bi ni da kallo mai kama da harara tana furta “Ki yi ta k’oshin mana Aysha? Cikin
wa? Kin zata ni d’in uwarki ce da zan ta bin ki ina lallab’aki, kin bi kin k’i ki
kwantar da hankalinki balle na uwarki ya kwanta sai kace a kan ki aka fara auren
early marriage, sanda Ubanki ya auro ni 15yrs nake, ban ma kai ki ba me ya same ni?
Mahaifinki dai kaifi d’aya ne, ba mai saka shi ba mai hana shi don haka ki nutsu ki
san abinda ki ke. Ban tab’a jin kan Fateemah da Abbanku sai a yanzu da take son ta
bujire masa, me ye ribarki idan kin haddasa sab’ani a tsakaninsu? Na ce meye
ribarki AYSHA?” Shiru na mata ina bulbular da hawaye. Me yasa Umma zata ga laifina
ce mata na yi bana son Ustaz? Bata san nafi kowa son haka ba? Tashin hankalin Mami
ne kawai bana so nake b’oye hakan a raina.. “wuce ki bani wuri, ki shirya bujire
masa kece zaki wahala don kin san ko magagin mutuwa kike Ubanki sai ya sadaki da
gidan mutumin nan…” Na ja k’afata na fice daga kitchen d’in zuciyata a k’untace
ranar na isa makaranta.



Har na dawo daga makaranta ranar Mami bata mik’e daga saman gadonta ba. Ko kayan
barcin bata cire ba. Na shiga na sameta na sanar da ita na dawo. Ta bi ni da kallo
kafin ta saki ajiyar zuciya ta nuna min gefenta. “Zo AYSHA ki kwanta ki huta…” Ban
k’i tayinta ba don ina buk’atar hakan na san kwanciya kusa da itan ne kawai zai
saka na daina jin b’acin ran da nake ciki. Sau tari idan na saka jikina a jikinta
ina samun nutsuwa idan ina cikin tashin hankali ko b’acin rai. Ta jawo ni na shiga
jikin nata sosai. Hannu ta saka a bayana ta shafawa a hankali kamar yarda ta saba
min. Muryata a k’asa sosai ta furta “Aysha me yasa kike son bujire min? Kada ki
cuci kanki ki yi aure at your young age, zaki cuci kanki, zaki yi nadama nan gaba
rayuwa ta canja. Ke ka’dai nake da hope a kanki AYSHA don Allah kada ki bujire min,
ko me za’a miki kada ki amincewa auren Ustaz.. kin yarda.” Na d’aga kai sai naga ta
saki ajiyar zuciya ta bani peck a kumatu tana sakin murmushi ta furta “Thanks my
beautiful Baby, I love you..” Shiru na yi sai da ta d’an ja kumatu na ta furta “Ba
zaki mayar min ba? Ko fushi kike da ni?” “I love you too Mamy..” na fa’da kamar
yarda na saba fa’da koda yaushe idan ta furtar kalmar. Ta lumshe ido tana sake jana
jikinta ta furta “Oya sleep…” zan yi magana ta furta “Shsssh!” A kunne na hakan
yasa na lumshe idon dole. Take ni da Mamy barci ya d’auke mu. Barci da ba mu tashi
farka wa ba sai da aka yi kiran sallahr la’asar. Na bu’de ido da sauri don na san
tabbas yau na makara a makaranta. Mami bata san Ustaz yana koyarwa a makarantar mu
don haka bata saka ido a kaina da zuwa makarantar ba. Ta bu’de idonta da k’yar tana
kallona “Ya dai Aysha?” Na sauka daga gadon ina furta “An yi sallah Mamy, kuma zani
Islamiyya.” Kanta ta rik’e a hankali tana d’aga min kai. Na fice da sauri.

A gaggauce na watsa ruwa na yi shirin Islamiyya na fito da sauri. A d’aki na samu
Mami daga ita sai rigar wanka. Ta mudubi take kallona ta furta “Kin shirya Aysha?”
Na d’aga mata kai. “Zo ku shafa min mai a baya na.” Na isa wajenta da d’an sauri na
zuba nan a hannuna ta zame rigarta na fara shafa mata. Ban wani damu ba don na saba
shafa mata d’in. Kuma Mami ba ta damuwa da suturce kanta koda ina wajen abinda ya
danganci k’irjinta kam bata damu ta b’oyeshi ba. Tun ina jin kunya har na saba.
“Ada lafiya ta fa’da tana mik’o min chocolates masu d’an yawa. Tana furta “Ki
tabbata kin cika min alk’awarina Aysha, kada ki sake ki amince da auren Ustaz..”.
Na amsa na fice da sauri..




Ina shiga makarantar na tabbatar Ustaz na nan don ga motarsa nan, gaba na ya fa’di
don na san na makara ba ta wasa ba. Amma haka na d’aure na nufi ajin. Harabar
makarantar shiru duk an yi sallah an koma aji. Zuciyata na bugawa na isa k’ofar
ajin fuskata a ha’de don ya kamata na fara janyewa Ustaz don na cikawa Mami
alk’awarinta, ya zama dole na mata halacci musamman ganin ita bata haihuwa kada
zafin ya mata yawa…


Idanu y’an ajin suka zubo min, Har shi Ustaz d’in da ya tsayar da karatun da yake
yana kallona. Na sake ha’de raina na nufi wajen zama na. “Aysha Imam Khaleel kin
makara.” Ya fa’da cikin dakakkiyar muryarsa cak na tsaya ban k’arasa inda zan zauna
d’in ba. Fuskata a ha’de na d’ago ina kallonsa. Ina ji kallon ne ya bashi mamaki.
“Me yake damunki?” Juyawa na yi na fice kawai daga ajin. Ustaz na ji yana kiran
“Aysha!” Na k’i na juyawa na koma saman step d’in na zauna kawai kaina a saman
cinyata idanuna suna zubar da hawaye. “Tashi ki shiga aji.” Na ji muryarsa a kaina.
Ban d’ago ba, ban kuma shiga ajin ba. “Ba kya ji ne Aysha?” Na d’ago a zafafe ina
kallonsa na furta “Ni ba zan shiga ba, ka k’yale ni…” Cak ya tsaya yana kallona
cikin narkakkun idanunsa ya furta “Ma Asabaki?” Wanda akan lab’b’ansa kawai na ji
furucin. Ya lumshe idonsa ya furta “Tashi ki shiga..” Ba musu na mik’e jikina a
sanyaye kamar zan shiga ajin sai na yi hanyar fita daga gate d’in. Ina ji Ustaz
yana fa’din “Aysha tsaya…” Amma Ina na bawa banza ajiyar sa na fice har da d’an
sauri na… Ina fita gate na juya naga Ustaz ya d’an rik’e kansa yana kallo na yana
cije leb’ensa…..




𝔍
𝔯𝔥
𝔞
𝔦𝔨 𝔢𝔰
𝔞
𝔑
★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://www.arewabooks.com/chapter?
id=669e462086c5cb5aff79fe08
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

𝒫𝒶ℊℯ 11



Runtse idonsa naga ya yi da sauri, kafin ya girgiza min kai, “Kada mu yi haka da ke
Aysha, kada ki sakawa zuciyata ciwon da zai yi wahalar warkewa.” Sai naga ya
durk’ushe a gabana idanunsa sun tara wata k’walla da ya k’ara idanun nasa kyau. Duk
da akwai tazara a tsakani na da shi sosai ma, don na lura yana taka tsantsan
k’warai da gaske wajen ganin ya kiyaye dokar Allah. “Ki taimaka min don Allah ki
amince na aureki, ba yarda idan kin gama secondaryn sai Ai mana auren, duk da haka
ma sai na yi k’ok’arin gaske kafin na iya daurewa, ni ka’dai na san me nake ji a
kanki, ni na san irin yarda girman son ki yake a zuciyata, Please AYSHA will you
marry me?” Runtse idona na yi ina jin yarda zuciyata ke matuk’ar gudu da tarin
k’aunarsa a ciki, da gaske dauriya nima kawai nake da kuma son cika alk’awarin da
na yiwa Mameey Amma ina ji a raina rashin Ustaz a rayuwata daidai yake da rasa
rayuwar tawa. “Ki amsa min AYSHA, please za ki aure ni?” Wallahi ban san sanda na
d’aga kai ba, Saboda wani irin kallo mai azababben kyau da Ustaz ya dinga zuba min
da narkakkun idonsa. Gani ya yi ya dunk’ule hannunsa duka biyun yana sakin ajiyar
zuciya ya furta “Shukran ya Rabbi, Shukran ilaiki Ayshata…”

Ya mik’e yana sake kallon Table bayan ya ajiye wata leda a kusa da ni. Ya furta
“Yau ma AYSHA ko ruwa babu?” Sai kunya ta kama ni na yi k’asa da kai na, ina wasa
da zoben hannuna. Murmushi mai sauti ya saki. “Shikkenan tunda rowa kike min, na
gode..” ya yi furucin da karyayyiyar murya. Da sauri na girgiza kai ina furta “Ai
ban san zaka zo ba…” “Ta ya zaki san zan zo bayan kin k’i picking call d’ina, kina
hora ni saboda kina tunanin kin yi yarinya sa aure ko?” Ya furta yana d’an murmushi
ha’de da cije leb’ensa ka’dan. “Allah ya nuna mana lokacin, Jibi zan wuce Egypt,
zan samu one week a can. Idan na dawo kashegari zai kama litinin anan zan sha ruwa.
Ina jiran girki mai kyau daga wajen kyakykyawar budurwata, za ki yi min?” D’aga
kai na yi da sauri ya yi dariya “Kamar gaske Allah yasa kin iya girkin.” “Allah
kuwa na iya..” Ya mik’a min hannunsa “Zamu gani ai, Allah ya kai mu ranar kuma ban
amince kowa ya tayaki ba. Kina girkin muna vedio call, ba ni zoben hannunki.” Na
waro ido ina girgiza kai. “Ai ya yi maka ka’dan, ji fa hannunka.” Ya kai duba zuwa
hannunsa “In dai ba rowa zaki min ba, ai sai ki bani na gwada na gani, ko ya yi min
ka’dan ina so zai min rakiya Egypt..” Na zare zoben ya nuna min gefen kujera “Ajiye
a nan, Zan d’auka.” Na kuwa ajiye ina sake girmama halin Ustaz na kiyaye dokokin
musulunci. Ya ‘d’au zoben ya saka a k’aramin yatsansa sai ga shi kuwa ya ‘dan
shiga. Sumbatar zoben ya yi a hankali yana lumshe ido ya furta “Ina sonka zobe,
Saboda ka fito a hannun AYSHA ta..” Ban san sanda na saki murmushi ba ina jin kamar
ni Ustaz ya sumbata.. Daga haka ya fice daga sitroom d’in yana sakin murmushi…



Tunda na saka k’afata a benen Mami, na ji gabana yana fa’duwa, fatana Allah yasa ta
yi barci. Da san’da na tura k’ofar parlorn sai dai ba kamar yarda na yi tsammani
ba, Mami na nan idonta biyu. Tana zaune a kan kujera ko T.V bata Kunna ba. K’afarta
ta ‘dora ‘d’aya saman d’aya tana girgiza ta fuskarta a ha’de sosai. Jikina a
sanyaye na k’arasa kusa da ita na zube a gabanta… “Mami na, don Allah ki yi
hak’uri ki yafe min laifi na, wallahi ban yi don na b’ata miki rai ba, na yi ne don
bin umarnin Abba….” “Abba ba? Dole ki bi umarninsa tunda shi ya kawoki duniya, ni
mecece a wajenki da na wuce Uwar goyo, ba abinda zaki ce min kin zab’i iyayenki a
kai na sakamakona kenan a wajen ki Aysha? Duk da tarin k’aunar da na nuna miki?” Ta
fa’da wata k’walla na zubo mata. Nima kukan na saki, jijiyoyin kaina suka d’aure na
dinga kuka mai tafe da ajiyar zuciya. Ta matsar da ni daga jikinta tana mik’ewa ta
nuna min k’ofa “Sauka min daga bene AYSHA ki koma wajen iyayenki da kika fi
k’auna….” A tsorace na dinga kallonta jin furucinta kuma na hango tabbas da gaske
take har k’asan zuciyar ta . Hannunta na kama da sauri ina furta “Me yayi zafi haka
Mami na? Duk duniya ba ni da kamarki, Abba da Umma kawai haihuwata suka yi, amma ke
kika ci dukkan wahala da ni, kika bani tarbiyya kika kula da ni da jiki da
aljihunki me yasa zan bujire miki?” “Zaki bujire min ne AYSHA saboda d’a namiji,
d’a namijin da nan gaba idan ya kuntaka miki iya shege sai kin yi dana sanin
ha’duwa da shi, d’a namijin da idan nan gaba ta ciyoshi zai auro wayayyiya mai
ilimi ke kuma ya mayar da ke Bagidajiyar gida… Ilimi shine garkuwarki don haka ki
yiwa kan ki fa’da ki rabu da shi ki zab’i karatunki…” Runtse idona na yi na furta
“Ya ce zai bar ni na yi karatun har sai na ce ya isheni…” “K’arya yake AYSHA yana
samunki, zai manta da wannan alk’awarin, bana burin nan gaba ki zama
k’ask’antacciya nafi so ki zama tauraruwa a cikin duniyar mata masu ilimi, ta yarda
zaki shiga ko ina a goga da ke… Ki bijirewa auren nan AYSHA in dai ba so kike na
‘d’auka har a raina don kun san bana haihuwa ba ne bani da kuma y’ar da zata shafe
min hawaye…” Fa’dawa jikinta na yi ina furta “Zan share miki Mami, wallahi zan
share miki kuma na hak’ura da Ustaz ko da hakan na nufin rasa dukkan farin ciki a
rayuwata…” Murmushi ta saki tana sake rungume ni a jikinta. “Ba wani farin ciki da
zaki rasa Aysha, farin ciki yanzu ma kika fara in dai zaki rabu da wancan mutumin
ni kuma zan baki farin cikin da har sai kin dinga mamaki, zan maye miki gurbin Uba,
Uwa da shi kansa Mijin…” na d’aga

6 / 15