Author : NAZEEFA NASHE Category : African Stories & Novels
kawai ya yi baya da seat ‘d’insa ya janyo ni da k’arfi na zube
jikinsa a hankali ya fara bani wani irin passionate Kiss. Mun d’au tsawon mintuna
biyar a haka kafin ya sake ni. Ya danna lock motar ta bu’de “Sweet dream Ayshata,
ki yi mafarki na pls…. I mean romantic mafarki…” Da sauri na fice daga motar. Don
kamar lamarin Ustaz yana neman girman kwanyata.
Sa’daf Sad’af na shige bedroom ‘dina. Don bana son na yi k’wak’wkwaran motsin da
Mami zata ji ni. Ina shiga d’akin kuwa kayan jikina na cire da duk suke k’amshin
turaren Ustazu, idan ba hanci na bane ya ji ba daidai ba, sai na ji kamar jikina ma
k’amshinsa yake. Da sauri na fa’da toilet don a jikina nake jin ya wajaba na yi
wanka.
Ina wankan na dinga jin ana buga k’ofar toilet d’in da k’arfi gabana na wani irin
fa’duwa na fito. Ina fitowa kuwa idanuna suka sark’e da na Mami da yake wurga min
wani irin kallo mai nuni da zallar jin haushi. Idanunta a burkice banda bata shaye
shaye sai na ce ma a buge take… cikin rawar murya na furta “Sannu…sannu Mami, ke
ce?” Ta sake wurga min kallon tana mik’ewa ta iso daf da ni. Kallon sama da k’asa
take min kafin ta saka hannunta cikin sumar gashi na ta furta “Wanka AYSHA? Wankan
me kika yi na ji gashinki a jik’e don’t tell me kin mik’awa wancan wawan kan ki?”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎
♥︎♥︎19.
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
𝒫𝒶ℊℯ 19.
19.
Wani iri na ji kaina ya yi, na kasa d’aga ko ido na kalli Mami jin yarda nake jin
wani irin d’aci a mak’ogwaro na, na tabbatar b’acin rai ne ya haddasa min haka.
Bata jira jin abinda zan ce naga ta mik’e ta shige bedroom d’inta hakan ya tabbatar
min bata buk’atar yarda ta ko rashin yarda, umarni ne kai tsaye ta bani da take
tunanin tilas ne na bi shi. Hawaye naji suna zubo min masu d’imin gaske wanda suke
narkar da duk wata damuwata da take k’asan zuciyata. Jikina a salub’e na shige
d’aki, Ina ji lokaci ya yi da ya kamata na nunawa Mami nima y’ar Zamani ce, zan iya
jurar komai banda rashin waya da Ustaz, ya Riga ya saba narkar da zuciyata da
kalamai masu narkar da zuciya. Furucinta kam tamkar d’igar dalma ne cikin zuciyata
gwara ta min komai banda hana ni jin muryar ustaz wallahi.
Bayan Isha, still Ustaz yazo gidan mu. Kamar yarda ya saba wannan karan ma da shi
aka ci abincin dare. Ya kalleni bayan ya mik’e bai ji kunyar Abba ba balle su Mami
ya furta “AYSHA, zo mota ki amshi sak’o.” Ta gefen ido nake kallon Mami da take
zuba masa banzan kallo. Na mik’e jikina a salub’e na bi bayansa. Har ya shiga cikin
mota. Hakan yasa na masa knocking glass. Bu’de motar ya yi ya furta “Shigo mu fara
tsara yarda shirin bikin zai kasance, bana son hira a saman Mami, I can’t feel
comfortable…” Na shiga Motar jikina a sanyaye. Ya janyo paper da biro ya mik’o min.
“Lissafo min abinda duk kike so a yi a bikin, da duk abinda za’a kashe.” Ya furta
yana kallona. Kafin ya d’an tab’e baki ya ce “Why are you so quiet yau ne? Ko har
kin fara tunanin aure ne?” Lumshe idona na yi ina girgiza kai. Na furta “Bakomai
fa, kawai stress d’in exams ne yake tambaya ta.” Ya girgiza kai yana jan hab’ata ya
furta “Oh I see, am so sorry dana sani ban zo yau ba. Jeki gida zan shigo gobe ko
jibi, ina hoping by that time kin wartsake stress mu samu mu shirya bikin sosai,
duk da bana son event da za’a ha’da maza da mata please ko hoto mace nake so.” Na
d’aga kai. Ya ja hannuna ya yi kissing kafin ya mik’a min ledar hannunsa. Mai kyan
gaske tun kafin na bu’de na san turare ne a ciki saboda wani k’amshi na fitar
hankali da naji yana fita a ciki. “Sweet dream…” Ya furta a hankali cikin
Wata husky voice mai dashewa. Na amsa ta hanyar d’aga kai. Na fita daga mota.
Sanda na shiga gida duk sun watse daga tsakargida, na hau saman Mami bayan na lek’a
na yiwa Umma sallama. Mamin bata parlor na shiga d’akina.
Kyaututtukan da na samu na dinga bu’dewa ina binsu da kallo. Sai daga k’arshe na
bu’de ledar Ustaz wani rantsatstsen turarena da charbi da sallaya da aka saka
sunana a jiki da haruffan larabci “Zaujaty Ayshatu…” Murmushi na yi ina rungume
d’an zoben gold d’in a k’irjina bayan na fesa turaren mai k’amshin na Ustaz sak sai
dai shi wannan na mata ne k’amshin bai kai na Ustaz k’arfi ba. Lumshe idona na yi.
Sai jin tafi na yi a kai na. Da sauri na ware idona ganin Mami a tsaye idonta a
kaina. Ta furta “Weldone Aysha, kin kuma burge ni.” A daburce na furta “Mami me na
yi?”
Ta tako zuwa inda nake, ta saka k’afarta d’aya ta tokare a saman gado tana kallona
ta furta “Me kuwa kika yi AYSHA? Ba abinda kika yi illa kina so ki nuna min ke ma
kin girma. Ahmad ya fara shayar da ke da’di da zumar da ke cikin aure, tunda ga shi
har kin san ki rungume kyautar sa a jikinsa, alamu ya nuna kin fara sanin soyayya
kin kuna san menene sha’awa, tabbas lokaci ya zo…” Ta fa’da tana lasar leb’enta
“Uban me kika tuno da yasa ki lumshe ido da murmushi? Kin hango yarda yake
rungumeki ko? Ke a tunaninki wai na amince da aurenki ne? Ko ka’dan har yanzu
zuciyata bata so ina kuma adawa da haka. Na k’i jinin tarayyarki da wannan mutumin
da yazo ya wargaza min duk wani tanadi na a kan ki….
Sak na yi ina jin furucin Mamin kamar d’igar dalma a cikin k’irjina. Ji nake kamar
ana soya zuciyata saboda tsananin hucin da nake ji a k’asan raina.
“Mik’o min turaren.” Ta yi furucin cikin b’acin rai. Na saka hannu na mik’a mata
turaren. Ta fice da shi tana furta “Kin bar amfani da duk wani abu da zai baki,
musamman turare waya sani ma ko asiri ya miki a cikinsa. Shegen mutum mai azababben
naci..” Ta gama zaginsa ta fice daga d’akin sai sannan naji wani kuka mai tafe da
takaici ya zo min, ba shiri na saka kukan kuwa sosai. Raina ya b’aci sosai don haka
bayan na yi wanka na shirya nan je ‘dakin nata ba kamar yarda ta min umarni na yi
zama na a ‘d’aki.
Wajen sha biyun dare ta shigo d’akin cikin shigar wasu silk kayan barci sai baza
k’amshin gabbasa take. Ina kwancen ta zauna a gefen gadon. Da sauri na lumshe idona
don ko ganin Mamin naji bana son yi. Sunkuyo da kanta ta yi saman fuskata ta bani
kyakykyawan kiss a gefen kumatu. A kunne ta ra’da min “Tashi Babyn Mameey, don’t
tell me fushi kike da ni, na san dai idonki biyu.” K’in motsa wa na yi. “Ba zaki
tashi ba?” Ta sake furucin a hankali sai ji na yi kawai ta burkito ni jikinta a
hankali ta saka hannunta a gefen cikina ta min cakulkuli da sauri na bu’de idon ina
d’an ja jikina ba furta “Kai Mammy, am not that young fa…” Sake janyo ni ta yi
jikinta tana ha’da fuskata da tata ta furta “You are still my little Aysha, har
yanzu kallon Babyn Mameey nake miki. Sau tari raina ne yake b’aci bana son
kusancinki da Ustaz wallahi ina jin haushin hakan sosai a raina. A yanzu ba zan
k’i ki auri wani ba ki bar Ustaz ba don komai ba sai don na san zai yi tsauri zai
kuma takura miki zamantowarsa Malami, ba zai bari ki mori rayuwarki ba, balle….”
Sai naga ta ciji leb’en bakinta na k’asa ta yi shiru bata k’arasa ba. Ta d’an
girgiza kai sai naga ta ja pillow kawai ta kwanta ta furta “A dole za’a raba mu
abinda bana so, ba yarda zan yi ne, shi yasa nake so mu dinga kwana tare ina jin ki
kusa da ni, don na san wata rana ba zan samu damar hakan ba….” Kafin na yi wani
yunk’uri naji Mami ta kwanta daf da ni sosai tana sakin ajiyar zuciya… ni dai a
‘darare na yi barci a ranar da mamakin wasu daga halayyar Mamin…
Bayan kwana biyu da faruwar hakan aka ce za’a kawo lefe don haka ranar da wuri na
shirya duk raina ba da’di musamman takura ni da Mami take yi na kwana a d’akina ko
nata ko itace da girki sau tari sai ta dawo don kawai ta hanani waya da Ustaz. Waya
kam sai a sace nake yi da shi.
K’asa na sauka cikin shigar doguwar Rigar abaya da na na’de kaina da mayafinta, na
saka nik’ab kuma. Mami da Umma na gani a kitchen sai masu aikin mu suna ta hidimar
ha’da abubuwan da za’a tarbi bak’i da su. Bayan gaishesu Umma naga ta zuba min ido
kafin ta juya wajen Mami ta ce “Fateemah, wani abu ke damun y’ar taki naga tayi
wata Uban rama? Ko dai duk tunanin auren ne?”
Mami ta d’an tab’e baki tana kallon Umma ta furta “Me kike tsammani daga yarinya
kamarta da za’a mata aure a k’ananun shekaru, ba dole ta yi tunani ba tunda ta san
abinda zata tarar gidan Mijin ba mai sauk’i ba ne…” Umma d’auke kanta ta yi tana
furta “Allah ya kyauta, aure ne fa ba rayuwar azaba ba, menene na sakawa kai
tunanin? Sanda aka yi aurena shekaru sha biyar gareni kuma ba abinda ya same ni, ku
san dai na yi gaskiya ko Sabaya ki fara d’irka mata gaskiya… don ramar ta yi yawa.”
Mami ta tab’e baki ta furta “Idan taje gidan Mijin, ta fara samun abinda kuke so ta
samu Ai zata ciko. Zo ki wuce AYSHA kafin mutane su zo su tarar da ke, ki gaida
Aseeyar sai kuma yamma zaki dawo. Driver na nan a waje ya sauke ki.” Na d’aga kaina
ina fita daga kitchen d’in. Bayan na sake kallon Umma da ta zubo min ido…
A waje na tarar da Asma don tare zamu tafi. Driver ya taso don ya kai mu, na
girgiza masa kaina “Bar shi ma Baba, Ustaz zai kai mu, amma don Allah kada ka
gayawa Mami na.” Murmushi ya yi ya d’aga kai jin abinda na ce. Da sauri na ja
hannun Asma muka fice don Ustaz ya isheni da kiran waya. Muna isa kuwa ya wurga min
harara gaisuwata ma bai amsa ba sai ta Asma. Ban wani damu ba don na san laifukan
da na yiwa Ustaz a lokutan nan ba zasu lissafu ba. A hanya Asma ta masa zancen zamu
je fitar da anko. Ji nayi yana furta “Waye zai je kasuwar? Ba dai AYSHA ba wallahi
gwara na rasa miliyoyin naira da na barta ta shiga kasuwa ku fa’di colorn da kuke
so da adadin ku zan saka a kawo muku.” Asma murmushi ta yi ta kuma furta “Mun gode
Allah ya k’ara arziki.”
Muka gama tsara bikinmu da y’ay’an Anty Aseeya k’anwar Mami, kafin Ustaz ya sake
dawowa d’aukar mu. Sanda muka isa gida Asma tana fita ya saka hannunsa ya rik’e
hannuna. Tsawon minti guda yana murza hannun kafin ya ware idonsa a kaina. “Me yasa
ba kya amsa wayata da daddare?” Muryata a hankali na furta “Barci Ustazuna barci ne
ke hana ni sak’at.” Ya cije leb’ensa yana narkar da idonsa cikin nawa ya furta “Ki
yi barci ki more AYSHA, gwara ki yi barcin yanzu don ina tabbatar miki ranar first
night d’inmu ba barci till down zamu yi mai zafin gaske….” Da sauri na lumshe ido
na. Ya saki hannun yana furta “Good night, abinda bai yi ba a lefe feel free ki
gaya min.” Na girgiza kai na ina furta “Na san Ustazu na ya iya zab’e zan kuma yi
farin ciki da dukkan abinda ya fito daga hannunka.” “Jikina fa?” Ya furta yana
d’aga gira da sakin murmushi… da sauri na fice ina furta “Har jikin…” Sai naga ya
waro ido ya buso min iska alamar kiss yana sakin murmushi ya furta “I love you till
my last breath…” na shige gida cikin wani irin zallar farin ciki.
Tun a gate Asma ta wani rungumeni tana furta AYSHA ke mai sa’a ce kin ga lefenki
kuwa?” Murmushi kawai na saki wata kunya na sake baibayeni wai ni Aysha yau ake
zancen aure na a gidanmu. A parlorn Abba na tarar da su da yake na san lefen suke
kalla hakan ya saka ni guduwa sama don har ga Allah ba zan iya zaman kallon lefen
ba…
Da daddare Mami ta shigo still yau ma cikin shigar wata shegiyar rigar barci sai
zabga k’amshin turare take. Gashinta a sake sai baza k’amshi yake da alama ta yi
gabbasar gashi. Glass cup ne a hannunta mai d’auke da madara ta zauna a gefen gadon
ta mik’a min cup d’in. “Tashi ki sha AYSHA.” Na karb’a na kafa kai na shanye. Mami
ta zuban ido tana saki wani malalacin murmushi ta furta “Yau zan sanar da ke abinda
baki sani ba Aysha Zan koya miki yarda zaki mallaki Ustaz in a romantic way…. “
Dishi dishi na dinga gani a idona na fara kallon Mami bibbiyu da duk abinda take
furtawa yana shiga kunne na kafin na ga ta saka hannu ta baje gashin kanta ta ‘dago
tana min wani kallo…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️😉
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA…….20.
Gaskiya ku min kara, ku yi dandazo ku nuna wa Littafin mu ja Bright pens na Aysha
Cool. K’arfe a wuta….. soyayya wacce zata girgiza media… a fito a siyi k’arfe a
wuta ko na yi yajin aikin rubutu na sati guda 😒 yauwa eeehe.
Don samun littafin kai tsaye ka tuntub’i AYSHA COOL MARUBUCIYAR K’ANWAR MAZA. Kowa
dai ya san yarda labarin ya kara’de Media.. tuna da sunan K’ARFE A WUTA.
I dedicated this page to my lovely sis Nimcyluv. “Saboda sonki da littafin Na ga
rayuwa na mallaka miki wannan page d’in. Really appreciated 🥰.
Masu bina private kan na mayar da shi na ku’di saboda na dinga musu posting 2 times
a day. Ku yi hak’uri Na ga rayuwa dai kyauta na bada shi don haka In sha Allah
zamu gama cikin nasara idan ku'din ne ya muku yawa ku siyi books 'dinmu na Bright
pens. 🤗
_____________
Cikin lumsassun idona nake kallon abubuwanda Mamin take min a sunan tana koya min
yarda zan mallaki zuciyar Ustaz. Har k’afata ta ja a hankali tana matsawa cikin
wani salo. “Hakan da nake miki Aysha shine romantic tausa kuma haka ake son ki yiwa
Mijinki, ba kunya tsakanin Miji da Mata ki zage ki nemi zuciyar Mijinki ko ta wani
hali….” Wasu abubuwan daga baya sam kasa fahintar su nayi, sabida wani irin barci
da ya dinga fisgata k’arshe dai ban san ya aka yi ba sai wayar gari nayi naga asuba
ta yi. Har gari ya fara haske. Na juya Babu Mami a d’akin idona na lumshe duk
abinda ya faru a daren ranar ya shiga dawo min daki-daki. Ajiyar zuciya na sauke
kafin na mik’ na shiga toilet don abin na Mami ya girmi kwanyata.
Da yake na san alhamis ce ban wani damu da neman abin kari ba. Still bayan naje ba
gaishesu barcin na ji ina sake ji don haka na koma d’aki kawai na sake kwanciya.
Daga ranar ya zama kullum Mami sai ta bani wannan madarar na sha da daddare ina sha
kuma barci mai nauyin gaske zai d’auke ni ba zan farka ba sai asubahi. A haka
kwanakin bikin suka dinga matsawa na dinga zuba wani kyau ga k’irjina ya cika k’ugu
na ma haka na yi k’iba ta ban mamaki. Don bana manta wata rana muna zaune a parlorn
Abba ana auna ni d’inkin da za’a min wata k’wararriyar tela da ta yi shuhura a
‘dinkin Amare cike da mamaki Umma yake kallo na ta ce “Fateema kin ga yarda AYSHA
ta cika ta yi k’iba kuwa kamar ma har ta tare a gidan Mijin? Ko dai har kun fara
shan sabayar?” Mami murmushi kawai ta yi ta ‘d’auke kanta tana kallona k’asa k’asa.
Da yamma kuwa ina dawowa daga Islamiyya na shiga parlorn Mamin sai naga ta yi bak’i
wasu manyan mata, da kana ganinsu kaga y’an duniya… Sak na yi ina kallonsu a zaune
sun ci matsatstsun kaya dole na yi mamaki don ban saba ganin irin su ba a gidanmu.
Gaba d’aya k’irjinsu a waje yake, sun baza gashi ga sark’a a k’afarsu. Mami na gani
na ta tsuke fuska, k’ok’arin Gaishesu na yi amma sai ta dakatar da ni. “AYSHA sauka
k’asa wajen Umma na gama da bak’i tukun.” Sak na yi na juya sai na ji d’aya a
cikinsu tana furta “Ma sha Allah, Fateema wannan yarinyar fa komai ya ji akwai kaya
gaskiya…” “Ita nake baku labari…” Shine kawai abinda naji. Na sauka k’asa jikina a
sanyaye saboda mamakin abinda Mami ta ce na yi. Bata tab’a ce min na sauka k’asa
don na yi bak’i ba, sai yau bak’in ma irin wa’dannan marasa kamun kai.
Parlorn Umma na shiga sai na sameta tana waya. Da ido ta bi ni da kallo har na
zauna a kujerar da take kusa da ita. Sai da ta gama wayar ta juyo tana kallona ta
furta “Ke AYSHA lafiya? Naga kin shigo sukuku da ke.” Girgiza mata kai na yi
“Bakomai, Mami ce ta ce nazo nan saboda ta yi bak’i.” “Ki zo nan?” Umman ta furta
cikin mamaki don itama abin da bata saba gani ba ne. Na d’aga kaina a hankali. Sai
naga taja ajiyar zuciya ta ce “Tashi ki je kitchen maza cikin fridge ki d’auko min
wasu jarkoki guda uku suna nan. Ki ha’do da cup.” Na mik’e na shiga kitchen d’in
Umman da yake cikin parlornta. D’auko biyu na yi saboda da d’an girmansu kafin na
koma na d’auko d’aya da cup. Umma ta bu’de ta farkon ta zuba Rabin cup ta mik’o min
“Karb’i ki sha, ba kuma wai don da’di ake shan irin wannan kayan ba don na san ki
da shegen kwa’dayi.” Na runtse idona na shanye. Ta sake zuba min na sauran gororin
tana furta “Kullum ki dinga zuwa cikin fridge kina bu’desu ki sha, Ko Mamin naki na
baki?” Na girgiza kai bata bani komai. Na so gaya mata sai madarar da take bani duk
dare da take saka ni barci sai dai na kasa. Ina kallo ta d’an cije leb’enta ta
furta “Ai shikkenan, da ni da ita duk d’aya ne, ki dage sosai wajen shan su, akwai
wasu ma da zan saka a kawo miki duk da dai na san ko da wannan kika tsaya kin fita
zarra Magungunan