Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
taba
amincewa da zancen soyayya da Yaya Suleiman ba.
"Ma'u duk kin rame, me yake damunki haka, kinganki kamar ba Asma'u ta ba"
Murmushi nayi nace
"Mhmm, Karatu ne yake cakar Dani, I'm about to start project. "
Been the Nadiya she always is, seta yadda da abinda nace nan muka fada hira sosae anan nace mata
"Nadiya Ya Farouq? "
Tabe Baki tayi tace
"Ba nace miki Munyi breaking ba, ai tun wannan fadan da mukai muka kasa fixing abin, se naji Ya fita
kawai akaina, I can't continue with someone like him. "
Kaina na gyada nace
"Ki dinga hakuri and whatever, Dama ke dashi since from the start you were not meant to be. Yaya
Suleiman yace yana sonki kum...... "
Kallona tayi da confusion tace
"Yaya Suleiman Wanne? Naki Wai?"
Hannunta na kama ina Murmushi nace
"Meye kike wani panting saboda nace yana sonki, Eh Yaya Suleiman na gidanmu. Yaushe kike free na
rakoki"
Tsira min idanu tayi tana kallona tamkar tana son karanto wani abun, kaina na dauke saboda idanuna
are weak zasu iya badani Susa naji Kunyar da Bazan manta ba.
"Behind wannan smile din naki, Ina hango damuwa a tattare dake, Ki fada min abinda yake damunki
mana, ni ce Nadiyanki fa"
Murmushi nayi nace
"Kinsan talks dinki yana sani kuka ko? Maganar Yaya Suleiman muke. Ya kike ganin. Can you? "
Kallona ta kuma yi, a take na fahimci me take nufi ba girgiza Kai nace
"Karkiyi tunannin dating muke da, A'a we were just favourite cousins kin gane? So ni ce babbar kawar
Amarya, babbar Aminiyar Ango. How do you see it? Abin Yayi ko? "
Rungumeni tayi tace
"Duk tunanina soyayya kuke shiyasa nake hesitating karbar zancen. Ke a matsayin sister dita wacce
shawara kika bani? "
Gyara Zamana nayi nace
"Ki amince, so far mun jima tare dashi kuma ko a family ana yabon shi. Beside Mamanshi batada
matsala. Sede nace all the best "
Bakina na bude tareda kawar da kaina saboda hawaye da naji yana neman bada ni, hura iska nayi tayi
har na hadiye hawayen sannan na samu muka cigaba da hirar mu.
Da daddare nayiwa Yaya Suleiman text din number ta, address dinta sannan nayi mishi fatan alkhairi, Ina
kallo Yayi ticking alamun delivered ai se kawai na Fara kuka, na sadaukar da abinda nake so, na tabbatar
kodan wannan Allah zai bani lada kuma ya duba lamurana.
Tun Ina tunanin Yaya Suleiman zai Kira har na fitar da rai, se Washegari da yamma ya kirani akan na
shirya muje tare, kawai se naji Ya raina min Wayo da yawa hakan yasa nace tutorial Zanje kawai ya tafi.
Kamar wasa Nadiya ta kirani tana tamin ihu, Dama Haka Yayana yake, haka ya hadu Haka ya iya soyayya,
karshe kasa karasa Maganar mukai nayi pretending network baida kyau na kashe wayar.
Ranar da na cika sati biyar banje gida ba, muna ward, Senior Doctor da nake bi yana call so muna tare
dashi Sega Amina Aminu tazo, seda ta gaida Dr Mike sannan suka gaisa da Nurses din kafin tace min
"Asma'u Kinyi Bakuwa! "
Kallonta nayi nace
"Wacece? "
"Zo muje Ki gani"
Allah yasa mun gama abinda zamuyi Hakanan na bita muka tafi lounge din da muke, Tundaga Nesa naji
gabana yana faduwa, amma ban kara tambayarta bakuwar ba. Ina shiga na tarar da Ummaah a zaune
gabanta an aje mata lemu da ruwa, se naji wani dadi ya mamayeni, naji sanyi a raina. Rungumeta nayi ta
baya nace
"Ummaah! "
Hannuna ta bubbuga tace min
"Ai fushi mukeyi dake. Saboda Allah Asma'u sati biyar kina Kano amma Bazan kizo gida ba. Me akai miki?
"
Murmushi nayi na zagayo na zauna, tareda kwantar da kaina kafadarta, Murmushi yaki barin fuskata
nace
"Ummaaah bansan me zance muku ba, amma banida saurayin da zan kawawa Abba shiyasa"
Cikeda tausayi na tace
"Shiyasa? "
Kaina na gyada nace
"Ummaah! "
Kanta ta shiga gyadawa tace
"Komai nufi ne na Allah kada Ki takura Kanki, Allah is the perfect timer, so abinda yake naki zaixo sede
idan lokaci baiyi ba "
Mun jima munata hira, Tana ta kwantar min da hankali har tace min wani sati zaaje tambayawa Yaya
Suleiman auren Nadiya, dukda Nadiya ta fadamin amma seda naji gabana ya fadi, zuciyata ta motsa, nayi
saurin kawar da hakan muka cigaba da hiraramu.
Ina samun sukuni na tafi gida, kullum ina zuwa daga can, the only time nake kwana cikin asibiti sede idan
Munada call ne. Batun Suleiman tamkar da gayya yake Wasu abubuwan duk abinda ya faru tsakaninshi
da Nadiya, ni ke Fara sani Tun Ina damuwa Har na hakura, a Haka Manya suka shiga aka saka rana. Ranar
nayi kuka Kamar zan fitarda idona, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na hakura, a wannan lokacin
muka fara exams na shiga final year.
Ayshatuuu
[4/10, 3:27 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_EIGHTEEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Tunda muka fara exams na maida hankalina kacokan, na share duk Wasu Abu da zasu kawo min tsaiko
akan exams din amma dake Allah shi ke handling komai, kuma bazakai cheating nature ba. A karshe dai I
break the record, seda na fadi wani course under paeds. Omomomo! Nasha kuka Kamar zanyi hauka,
saboda na tabbatar damuwar da nake ce ta sani a ciki. Abba was the only one that supported me
amman su Yaya Halifa Kamar ya dakeni, yace na zauna wasa abinda banyi a baya ba shi nake kokarin
nayi Yanzun, to nasani karatunnan shi kadai ne rufin asiri na. Dama a gidanmu idan kaga ana yaba maka,
to sailing Kake successful amma da zarar Ance you failed babu Wanda zai bi bayanka.
Naji haushi Dan Hatta Adda Sa'ada wannan karan bamuyi da dadi da ita ba, hakan yasa na dawo
hayyacina Naga Meye nakeyi? Kashe Kaina zanyi saboda wani namiji, Wanda ya manta abinda ya faru
gaba daya, shi Yanzun house job dinshi Ya gama gaba daya, ya fara residency bayan nan aurenshi Zaiyi,
to ni Meye na rike wannan abin cikin zuciyata? Nayi dwelling a rayuwar da ta riga ta wuce. A lokacin na
kara fahimtar wani abu da son zuciya ya hanani gani, shi ne Suleiman bai yaudareni ba, ni na yaudari
Kaina, ni nayi hurting Kaina, tunda shi baice yana sona ba, yasan ina sonshi to me zai min? Zaice Asma'u
daina sona? Bazai yiwu ba. At the spot nayi making mental note cikin kaina akan wannan abin, wannan
Maganar ta wuce Har abada sede a hira.
Nayi Karatu kamar babu gobe, Dama six weeks ne favor din kayi resit, kuma Alhamdulillah Inayi nai
making, na zama final year medical student. A lokacin shirin bikin Nadiya da Yaya Suleiman yayi nisa
sosae, amma saboda postings, Karatu ga kuma project yasa banyi wani active perticipation a shirin ba,
sede duk abinda akai to zata kirani ta fada min, Haka ta bangaren Yaya Suleiman din duk ankon da muka
fitar shi ya siya min.
Biki saura sati uku aka gama hada Lefe, Ummaah tace Nazo na gani kafin akai, koda zanyi recommending
a kara wani abun. Yaya Suleiman yazo Ya daukeni shima bayan Ya gama aikinsa. Tunda muka gaisa bamu
Kara magana ba, seda Nadiya ta kirashi tana tambayarshi Ko muna tare ta kirani ban dauka ba, to ya
bani, bani Yayi mukai magana sannan nai mata sallama. To wannan ya bashi space din yimin magana,
itama random talks ne kawai har mukaje gida.
Gidan da mutane sosae, familyn Baban Yaya Suleiman sunzo ganin kaya, dan haka dakina kawai na wuce
nayi wanka sannan sun tattafi naje gurin Ummaah,
"Ummaah Sannu da gida"
"Doctor ta karaso, Sannu ya Karatu? "
Ta fada tana min murmushin dake healing zuciyata, akwatin na janyo Ina dubawa muna hira da ita, seda
na gama tas sannan nace
"Ummaah, kayannan Sunyi kyau sosae, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi taro lafiya! "
Kaina ta shafa tace
"Amin Autar Ummaah, saura naki kuma ko? "
Murmushi nayi Ina maida kayan cikin trolley, amma karkashin raina Amin nake amsawa, gyara zamanta
tayi tace
"Kinga baifi watanni bakwai Ya rage miki Ki kammalla karatunki ba, kiyi kokari ki saurari masu nemanki,
nasan Inna Ade tayi Shiru da Maganar ne amma da zarar kin gama zata dawo da zancenĺ"
Kaina na gyada nace
"Inshaaa Allah Ummaah"
Dan abar Maganar auren kawai se na Fara mata labarin Project dina da nakeyi akan CKD (Chronic Kidney
Disease) gaba daya ta bani hankalinta, ina mata bayani tana kara min bayanin Wasu abubuwan. A
matsayinta na project coordinator a department dinta. A Haka Abba ya dawo daga gona, mukaje tare na
mishi Sannu da zuwa sannnan na barta acan ni kuma na tafi gurin Yaya Halifa.
Lokacin biki yazo, dukda ba wani armashi Yayi ba, kasancewar bikin maza ne amma dukda hakan saboda
yawan danginmu naji dadin bikin, kusan duk taron a gurin Nadiya nayi shi. Seda aka daura aure sannan
na dawo gida, Dan Ummaah tace min Dani zaa dakko Matar Yaya Halifa daga Dutse. A motar Adda
Sa'ada muka tafi, munata hira Har mukaje, mutanen suna da kirki, sun karrama mu, muka dakko Sister
in-law muka taho da ita kano. Unguwa daya Nadiya da Adda Zannira matar Yaya Halifa, gidan baifi
50miles away ba, haka suke.
Rayuwa tana tafiya da dadi da babu dadi, amma dole duk yadda Tazo Haka zakai embracing dinta. A
rayuwata na fuskanci kalubale da yawa daga gurin mutane da dama, Harda Wanda ban taba tunanin
hakan ba. A Yanzun idan Bakayi aure ba, mutane kawai gani sukeyi Kaine baka so ba, Kaine Baka maida
hankali ba. Ya Ilahil alamin! Ya Zakayi? Zakace dole se kayi aure lokacin bai zo ba, A'a aure da mutuwa
lokaci ne, idan lokacin baiyi ba, Baka isa kayi ba.
Na kammalla karatuna at a very tender age, gaba daya shekaruna ashirin da uku na karba licence dina
under Medical and Dental Council of Nigeria(MDCN, na zama cikakkiyar Medical doctor, ranar da nayi
taking Hippocratic oath dina, ranar atttestation nayi farin ciki, nayi murna Kamar zanyi me, na Kalli
ilahirin family na da suka zo, ai da kyar bakina ya budu nake karanto oath din. Muna gamawa na fito akai
photo session, Yan gidanmu anata rungumeni a Haka muka gama na cire graduation gown din na rataya,
cikin yan set dinmu naje mukai hotuna, Dan Wasu ba lallai ku Kara Haduwa dasu ba.
Muna komawa gida, na nufi dakin Inna, tana zaune gefen katuwar katifarta, ko sallama banyi ba na mika
mata hannu nace
"Mun kunce ni dake, har na gama makaranta, na zama cikakkiyar Likita amma baki zo tayani murna ba.
Na daina kawar dake. "
Tabe Baki tayi tana bina da wani kallo, Wanda bansan me yake nufi ba tace
"To se me Dan banje ba? Da dai aurenki ne da ni ce kan gaba "
Dariya nayi naje na zauna gefenta nace
"Kawata ta kaina, Karki damu ina dawowa daga service zanyi aure da izinin Allah"
Baki a bude tace
"Wani karatun ne kuma, ke Kinci ubanki, so kike se kin tsofe kafin kiyi aure. To babu inda zakije, miji zaki
kawo ayi miki aure. "
Dariya na karayi nace
"Inna ba Karatu bane, maida wukar, bautar kasa zanyi. Kuma banda abinki aure ai lokaci ne...."
"Maganarki kenan kullum, aure lokacin ne, ki kalla sa'annin ki dukkansu Sun yi aure, Rayhana 'Ya'yanta
biyu amma ke kinata gantali"
Ta katseni, "Gantali" na maimata, se kawai nayi Murmushi nace
"Kawa kenan, ni bana fada da Kawata bari naje, idan kina son wani abu se kiyi min magana"
Daga Haka na mike gaba daya raina a jagule, saboda abinda Inna tace, Rayhana sa'a ta ce quite sure,
amma lokacinda aka rubuta mana kaddara dole kowa road din da zai bi, daban take. Me yasa mutane
basu gane komai MUKKADARI NE ba. Da Ummaah na Fara haduwa dake ta Tara mutane se shiga take
tana fita, seda nace ta bari idan an kwana biu ayi walimar amma tace gwara tayi rana daya.
"Na zata kin shirya, mutane na jiranki fa"
Kaina kawai na gyada nace
"Yaznun zanyi"
Juyawa nayi zan tafi daki Ta kwalla min kira na dawo, kallona tayi tace
"Akwai wani abu ne? Naga fuskarki tayi ja "
Taba fuskar nayi sannan na kirkiro Murmushi nace
"A'a Ummaah gajiya nayi, Bari naje"
Saurin Juyawa nayi saboda jin idanuna sun cicciko da kwalla, Se naji tace min
"Today Issa happy day, don't let anyone destroy it. "
Kaina na gyada na tafi dakin, Adda Zannira ce a kwance da katon cikinta, ta saki fanka, zama nayi gefenta
nace
"Adda Zanni, duk gajiyar ce"
Dagowa tayi ta kalleni tace
"Bari dai Adda Asma'u, Babyn ki ya takura min, na kagu Ya fito na Baki abinki. "
Dariya nayi tareda mikewa nace
"Kaji Adda Kamar gaske, Se Kinji zafin labor Kice kin fasa"
Dariya tayi tayi har na shiga wanka, Ina fitowa na shirya cikin wata red Abaya da Adda Habiba ta
kawomin as gift, muka fita bayan nayi kwalliya akai ta hotuna. Se Washegari na samu damar bude gifts
din da aka kawo min, yawancin duk gifts din daga yan gidanmu ne, Delivery kits, BP app, forceps da
sauransu. Naji dadi sosae, kowa na bishi da text din godiya.
Ina kwance a daki sati daya da graduation dina, Inata tunanin Yanzun kuma Ina zaa fada, posting anyishi
kuma Anyi posting dina Yobe state. In the next 2 weeks zan tafi. Shigowar Ummaah tasa na mike, kafin
nayi magana tace
"Dakko Hijab dinki kizo"
Zan tambayeta lafiya naga ta juyar da kanta hakan yasa na mike na dauki Hijab din na saka muka fito,
tunda naga Munyi dakin Inna Ade naji gabana Yayi mugun faduwa, tunda nake da Inna bata taba zuwa
gidanmu tayi fin kwana uku ba, amma wannan karan kwananta goma sha biyu bata tafi ba, hakan ya
tabbatar min da she's up to something kuma tabbas akaina ne, Dan ta dauke min wuta, nima bana son
case hakan yasa na tattara ta na watsar da ita.
Tana zaune kan katifa, tana murza goro a magogi Tana afawa a baki, nida nafi kowa saninta nasan wata
tsiyar zatayi, sallamar da Ummaah tayi yasa ta juyo tana kallona, Nima kallonta nake se ji nayi tace
"To Zuwairiyya (Uwarta kenan!) da kikai tsaye dukana zakiyi? "
Da sauri Abba ya juyo yace min
"Asma'u come and sit here"
Jikina a matukar sanyaye na nufi gefenshi na zauna ina kara tantamar Anya Inna ce, ni tayi addressing da
Zuwariyya? Ban gama tunanin hakan ba naji tacr
"Ke Asma'u, dago ki dubeni, idan wayannan mutanen sa'anni Ki ne, ni ba Abokiyar wasarki bace, Dan kin
Raina mu zaki ce bazakiyi aure ba.... "
Da sauri na katse ta nace
"Inna yaushe nace bazanyi aure ba"
Abba ne yace
"Kar naji Bakinki! "
Shiru nayi amma a raina Ina ayyana ni Asma'u Fara Yar Shehu, Inna take dagawa murya Haka? Bazan iya
tuna last time da ta kirani da Asma'u ba, I can even say she never, kawai cemin take Fara 'Yar Shehu, Ta
gaban goshin ko kuma Kawata. Amma yau Inna Ade ke cemin ita ba tsarata bace, kawai se naji hawaye
sun Fara min zarya, kaina ya mugun Sarawa saboda bala'in da take. A karshe tace babu zancen zuwa
Yobe!
Awnnnnnnnnnnnm....... A page is here, to all my followers I say Kumaya!
One word for
Fara 'Yar Shehu
Inna Ade
Ayshatuuu
[4/11, 8:50 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_NINETEEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Hannuna nasa na goge fuskata Dan banga dalilin kuka ba, idan tun Yanzun Ina kuka to nan gaba kukan
jini zanyi kenan. Nida Ummaah ta sallama, hakan yasa na mike na fito, kitchen na wuce na fara dama
custard Dan inason na Fara sabawa da irin wannan abin, Ummaah ce ta biyoni taga ina kokarin Dama
custard amma ya tsinke saboda bana cikin nutsuwata. Hannunta tasa ta dafa kafadata tace
"SABR! Asma'u, komai kika ga yana faruwa da bawa da sanin Allah. Kiyi hakuri "
Dan Murmushi nayi nace
"Ummaah babu komai, bari naje daki"
Tare muka fito da ita, daidai fitowar Abba da Inna, bakinta har kumfa yake saboda balai, Jakarta ce a
hannun Abba hakan yasa na karasa na karbi Jakar sannan nace
"Inna tafiya zakiyi? "
Kallona tayi sannan tace
"Tafiya zanyi Kawa, yaushe zaki zo? "
Kaina na girgiza nace
"Babu rana,"
Daga Haka muka karasa Mota mukai mata sallama, ta shiga sannan driver ya tada motar se Kwalam.
Dukkanmu haka muka tsaya har aka maida gate aka rufe amma babu Wanda ya matsa a gurin,
kowannenmu tunanin zantukan Inna ke yawo cikin kanmu, Se can Abba ya juyo Ya kalleni yace
"Asma'u let's talk"
Wucewa yayi dakinshi, nima na bishi yayinda Ummaah ta tafi daki. Yana zaune a Kan carpet na sameshi,
yayi shiru not like my Police Father, duk Yayi Shiru fuskarshi looking pitiful, Se naji na kara takura, naji
gaba daya Sauran space din dana bari a zuciyata Wanda Banji haushin Inna ba, baki daya se ya zamana
duk ya turnuke ni, har ni kaina haushin Kaina nake ji, at least da nayi auren da ban jawo musu magana
ba.
Zama nayi gefenshi nace
"Abba Dan Allah kayi hakuri, Inshaaa Allah zan kawo maka miji na...... "
Se na kasa karasawa saboda wani irin kuka da ya kubce min, kaina na durkushe Inata kuka, inajin yadda
zuciyata ke wani irin zafi, na kasa ci gaba da Maganar seda Abba ya dafa kaina yace
"SABR! My Daughter. Ya isa hakan"
Sheshakar a hankali ta dauke min, hawayena na share na bude baki zanyi magana ya girgiza kanshi yace
"Saboda Bakiyi aure ba se ya zama laifinki? Ba laifinki bane, haka Allah Ya kaddara miki, babu Wanda ya
tsallake kaddararshi. Koda zaki kara shekara goma a gidannan Bakiyi aure ba, I'll say nothing. Bake kika
hallici Kanki ba, shi daya halliceki yasan tanadin da yayi miki. So Karki kara kuka akan hakan, zakiyi aure
amma se lokacin Yayi. And for Yobe, you have me, you're your fathers daughter Bazan iya hanaki ba.
Inna Ade zata sakko Kinji? "
Kaina na gyada ina Dan Murmushi saboda words dinsa are more of Opoid Analgesic (Pain reliever) a take
sukai relieving duk wani bakin ciki da zuciyata ke ciki, a take naji wani karfin gwiwa da nutsuwa ya
sameni. Bai barni na tafi muka zauna munata hira, gaba daya hirar yana sighting mini examples ne na
rayuwa. Most thing da yayi capturing zuciyata shi ne da yace min
"Kinga Asma'u aure ba farilla bane, amma Sunna ce me karfin gaske, a wani gurin saboda Allah yace idan
kayi aure tamkar ka cika rabin addininka ne, so kinga akwai falala sosae a aure. Kuma a society dinmu
sun daukaka aure sosae da sosae, suna ganin mace is not complete without aure. Eh wani lokacin Haka
ne amma kin tuna tarihin Nana Maryam Mahaifiyar Annabi Isah (AS). Batayi aure ba amma a kur'ani Sura
guda ce da ita, so kinga zuciya is everything that matters. Ki maida hankalinki akan yadda zaki gyara
lahirarki, aure zaizo sede idan lokaci baiyi ba "
Shikenan kuwa na samu lafiya, na wartsake na Fara shirin tafiya Camp.