Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
shiga and there i saw him sitting looking at me. Da sauri
naje na rungumeshi nace
"Abbana"
Hararar wasa yayi min yace
"Nazo biko ne, tunda laifin wasu ya shafeni"
Dariya nayi tareda rufe fuskata , i cant remember ni ina dariya genuinely har haka ba. Ranar se dare ya
tafi ko seminar bankje ba, tare mukai lunch a cafeteria se naji ina missing gida sosae. Lallashi na yayi
yana nuna min komai zaizo karshe. Haka sati na kamawa naje kano se naga babu wanda ya takira min
like always do.
Ayshatuuuu
[5/31, 11:01 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_THIRTY_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Hannuna na zura cikin aljuhun lab coat dita na ciro wayata saboda jin alamar shigowar message a
wayata. Message dinne kuwa daga chief obstetrician dake last month na koma gynae team na bar
surgical team na fara residency dina. Kallon metron din nayi nace mata
“Mummy, zanje meeting idan akwai matsala a kirani”
Kanta ta gyada tareda min fatan alkhairi, inason matar she’s mother figure, a dan zaman da nayi a ward
dinta tana yawan bani shawarwari masu amfani tamkar tasan matsalata akan aure take kullum ni da
sauran nurses dinta akwai topic din da zaayi discussing akai. Kuma baka isa kace ka zauna bakayi gaining
wani abu ba. Office din Dr halima na wuce dake ita ce chief din tamu, na tsaya ni da Dr hafiz se gata ta
fito in her usual outfit wato lace gown an daura lab coat akai, irin classy mutanen ne yar gayun gayu
sosae. Da sauri na karasa inda take nace
“Maam naga message dinki gani”
“Yaawa nima yanzun nake shirin kiranki muje meeting zaayi na tarbar sabon MD”
Kaina na gyada tareda bin bayanta munata dan hira jefijefi, a office din Dr Mahmud anan muka zazzauna
akai briefing kowa akan washegari sabon MD da akai posting zai fara aiki , seda Dr Rashida ta ja mana
kunne akan kowa yayi watching takunshi saboda baya wasa mutumin idan zaayi aiki ayi dan shi baya
daukar kailula. Ta tsoratar damu sosae Amma banji komai ba dana nasan bana barin aiki Na unfinished.
Haka muka gama se kuma muka koma office din Dr halima danyin meeting da sauran yan team dinmu.
Kafin wani lokaci dukkan asibitin kowa ya shiga hankalinsa ko ward ka shiga se gyare gyare akeyi da fito
da sabbabin linens a haka dai ranar ta kare na tafi gidan kyaftun.
Washegari da safe da wurwuri na gama shirina nayi breakfast dan nasan it will be a busy day i know.
Hakanan na fito na shirya cikin coffee wando da riga na soft cotton yadi lab coat na daura ban mayi
buttoning ba na rataya stethoscope dina a wuya sannan nayi rolling da karamin coffee veil. Kallon kaina
nayi a jikin mirror babu laifi idanuna sun fara dawowa hayyacinsu, wannan zurmawar da yayi ciki duk
yadan fito dan hankalina ya fara kwanciya na daina tsangwamawa kaina tunda nasan wannan bashi zai
bani miji ba.
Gynae emergency na fara zuwa muka gaisa da staffs din gurin sannan aka bani patient din da zanyi
reviewing. Ina cikin aikin Dr halima ta karaso mukai rounds sannan muka shiga labor room nanma stable
babu wani damuwa sosae a ciki nan muka gama sannan nida ita muka fita. Ko ina cikin asibitin tas yake
kowa ya shiga taitayimsa haka kowa yana post dinsa se naji zuciyata tana kwadayin ganin waye wannan
sabon MD, naji dadi a raina saboda kowa zai dawo hayyacinsa kowa ya fahimci abinda ya taramu a
asibitin.
Karfe goma dukkanmu muna tsaye a reception Doctors mu shida daga kowacce cader mutum uku muna
tsaye dan tarbarshi, wayata tayi ringing na dauka Dr Ema ne wani house officer ne su na bari a labor
room akan duk yadda ake ciki su kirani, seda muka gama magana dadhi sannan na fadawa Dr halima ta
fadamin yadda zamuyi kawai se na juya na tafi, ina zuwa na tarar matar tana wani irin massive bleeding
babu anyi anyi ya tsaya yaki hakan yasa nabi shawarar da sister ta bayar akan mu cire mahaifar kawai,
dole muka tafi OT and that’s how i missed ganin sabon MD.
A wannan satin kowa ka kalla cikin asibitin kasan ya dawo hayyacinsa, aiki kowa yake ka’in da na’in nidai
bamu taba haduwa dashi ba har yayi wata a asibitin. Kowa complain yake akan ya takurawa mutane, to
dama hakane idan mutum yazo yana kwatanta gaskiya tabbas kowa zai tsane shi.
Ranar wata litinin nayi aiki na gaji daga nan na tafi Amenity unit wajen kyaftun, mun jima da ita muna
hira sannan na tashi n koma lounge. Muna da yawa cikin lounge din masu cin abinci nayi haka wasu na
research inda na saba zama naje na zauna bayan mun gaggaisa da Doctors din. Wata Dr hajja watching
buddy dita ce ta kawo min wani romantic doctor korean film.
“Shahada watch this film yayi kyau sosae fa”
Bakina na tabe nace
“Rabani da wannan romantic films din nasu, ana nuna soyayyar da bata existing gaba daya”
Dariya tayi tace
“Hooo Anty Asmau i cant wait naga wanda zaki aura, bama romantic din bane ba, surgeries ne kalakala a
ciki zaki karu”
Da haka tasa na karba film din cikin flash dina, komawa na gyara zamana kan cushion din nayi na fixing
wayata a charge tareda dan runtse idona a hanaklai bacci ya fara kokarin fizgata, dama gefena wasu
house officers ne mata suna zaune Ina jin dayar tace
“Ke kinga sabon MD kuwa”
Bude idona nayi a hankali na kallesu amma duk saboda yadda suka zama engrossed ko effect din
idanuna basuji ba, dayar tace
“Kin ganshi ne ke?”
“Sosae ma, though daga nesa ne, ban taba ganin mutumin da fada yake mishi kyau ba se shi, baya
murmushi fa amma he’s so cute mashaaa Allah”
Ta fada tana rungume fuskarta da palms dinta, se grinning take, se suka bani dariya. Na dauka ni kadai
nayi shashancin admiring maza da kuma one side love ashe inada yan uwa.
“Awnnnn I’m crushing him already”
Wayata ta katse min hanzari da ringing, kaina na kaudar da sauri, tareda sakin siririn tsaki sannan na
janyo wayar wata sabuwar number ce, picking nayi tareda karawa a kunnena
“Dr Shahada, Dr halima ce”
Da sauri na gaisheta se tace min
“Kina jina ko? Akwai wata middle age woman a labor room kamar ta samu ruptured uterus, kije yanzun
kiyi reviewing dinta in the next 20 minutes zakui mata aiki a OT keda MD”
Ambatar MD seda gabana ya fadi me yasa nida MD. Mikewa nayi na tattara kayana na fita cikin sauri,
muryar Dr halima nayi min echo a kunnena
“Nasan zaki iya, i trust your skills amma ki kula sosae sannan kiyi komai da sauri amma with care, kada ki
bari ya kamaki da wani matsala. All the best”
Ina shiga labor ward na karanta write up din matar naje nayi assessing dinta sannan na zauna aka
shiryata daga nan na wuce OT nayi changing, ranar chief anesthetist din shi zai bamu anesthesia da
kanshi sabida wannan shi ne first time da zaiyi aiki a OT tunda yazo. Cikin five minutes suka kammalla
komai hakan yasa na kira Dr halima na sanar mata mun kammalla.
“Bara na turo miki digits dinsa ki fada masa kun shirya”
Idanuna a warwaje nace
“Kai dan Allah ki fada masa”
Dariya ta danyi tace
“Shima mutum ne kamar ni”
Daga haka tayi hanging, se na rike wayar sororo ina kallo, aikuwa sega pop din message nata ya shigo, Dr
Kwaciddo nayi ta nanatawa kafin da kyar nayi summoning courage na kira shi, muryata a dan rikice nace
“Sir I’m Dr Shahada, muna jiranka a OT koami is set.”
Cikin stern voice yace
“Alright! I’ll be there inshaaa Allah”
Sauke wayar nayi tareda sakin ajiyar zuciya, se naji ya burgeni da yace inshaaa Allah. Ina nan tsaye baifi
10 minutes ba se naji shigowar shi. Dogo ne sosae dan idan na karu jikinshi Allah yasa zan kai aljihun
gaban rigarshi, nima a mata bana cikin sahun gajeru amma this is to show how tall he’s. Ba siriri bane da
ace bashida tsayi kibarshi se tafi fitowa amma dake yana da tsayi se ta shanye kibar. Shi ba fari bane yafi
ga a kirashi baki sede not that dark, ga jin dadi se yasa fatarshi take glowing, smoothly tamkar mace
kana kallon fuskarsa kaga ta bafullatanni ko ba usul ba amma an samu trait din cikin jini. Wannan shine
MD or i can call him Dr Kwaccido.
Hannunsa ya tafa yana fadin
“Set?”
Kaina na gyada nace
“Set sir!”
Ciki muka shiga bayan mun jira yayi changing, yadda yake aiki will tell you shidin ba na yau bane yasan
scalpel scapel tasan da zamanshi. I was extra careful akan aikin har muka gama muka stitching gurin
sannan ya kalleni yace
“It’s nice working with you”
Ayshatuu
[6/3, 7:49 AM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_THRTY ONE_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
“Thank you sir!”
Kawai nace mishi ba tareda na bari kalamamsa sun shiga kaina ba, nasan I’m skilled person duk wanda
yayi aiki dani komin yadda ya kware to tabbas se yasan nima na maida hankali. Cikin lounge yaje ya
zauna aka kai masa folder yayi documenting sannan ya yiwa kowa bangajiya kafin ya tafi, wata
nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan na fita baki daya daga OT. Ward na koma na karasa ayyukan da
suka kamata nayi sannan na tashi gaba daya.
Washegari ranar friday, muna kammalla ward tounds dinmu na shirya dan tafiya kano a raina ina
tunanin ya kamata yau ba se gobe ba na fadawa Abba kudirina. Misalin karfe uku na isa gida saboda na
biya gidan Adda Maryam da nayi niyyar se yamma na koma gida amma ta bata min rai shiyasa na taho.
Ina gidan kanin mijinta wani Nasir yazo, that wasn’t the first time dana hadu dashi a gidan sede baifi sau
daya muka taba magana ta minti uku dashi ba kullum daga gaisuwa bamu karawa saboda naga dan raijin
wayo me, ni kuwa bana cikin wannan class din. Tunda ya shigo muka gaisa naja mutuncin kaina na
cigaba da kallona sunata hira shida Adda, can sega mijinta ya dawo, Yaya Mansur muka gaisa ya zauna
yana ta jana da hira dake he’s very jovial to tamu ta zo daya dashi.
“Kina wuta fa matar nan, nazo kofar gidana naga wata benz, so inata tunanin wa muka samu? Seda na
hango wannan ear piece din naku kafin na gane ashe kece”
Dariya nayi dan Na fahimci stethoscope yake nufi, nace
“Babu wani wuta fa Yaya, amfani ake da dama”
Murmushi yayi ya gyada kai yace
“Yeah! Allah ya kawo miji na gari”
Amin na bashi amsa ina murmushi, kallona Adda tayi tace
“Kamar gaske”
Ko kulata banyi ba tashi tayi ta wuce ciki itada yayan, bata jima ba ta dawo hakan yasana wuce kitchen
akan na duba abinci dan a daura wani, idan naje gidan sisters dina se nayi musu dinner nake tafiya.
Kamar daga sama naji Adda Maryam na cewa Nasir
“Kaima kaki kayi aure kamar Asmau, ko baka da budurwa ne?”
Shiru nayi inason jin amsarshi se yayi dariya yace
“Kai time baiyiba, se an tara tukunna”
Gyara zamamta tayi tace
“Kaga Asmau shes 27 years yanzun, gata medical doctor, babu wani serious magana akanta, bana
tunanin tana da saurayi gaba daya so idan tayi maka why won’t you tag along kuyi aure”
Idanuna na lumshe jikina har bari yake na rufe warmer da sauri zan fito kawai naji yadda gayen yake
babbaka dariya hakan yasa na tsaya, naji yace
“Kina da abubuwan dariya Antinmu, ni wannan kanwar taki ai ta girmeni ma......in a mocking way ya
fada, se naji kafafuna sunyi wani sanyi.....27 kikace? Tabdi! Beside ni fa bazan iya auran health workers
ba ke wallahi ko a kafa aka daura min su se na kunce”
Tamkar walkiya haka na ganni a parlon, wani irin mugun kallo na masa nace
“Ai ko maza sun kare nafi karfin na aureka, Adda na gode”
Daga haka na dauki jakata dama veil dina tuntuni yake a jikina nayi waje na barsu baki a sake, mota ta na
bude na shiga se kuma nayi shiru ina ganin menene abin fushi har haka? Me yasa raina ya baci dan anyi
talla ta, tunda auren yaki zuwa may be kilan ta hakanne zan samu miji. Zuciyata se ta kasu biyu wata na
blaming dina wata na tafarfasa tana ganin an raina min hankali ajina ya wuce ayi kamar ana nanawa
namiji yana kin karba.
Ina gama parking sega Yaya suleiman, tsayawa yayi yana kallona ni at first ban ma wani lura dashi ba
kokari nake na bawa Baba me gadi key din ya shigo da kayan da nazo dasu. Ji nayi yace
“Ajhumma!”
Nasan shi daya ke kirana da wannan sunan hakan yasa na dago fuskata a sake na dubeshi nace
“Oppa”
Se naji na tuna da, kamar yadda oppa yake nufin Yaya a korea, yawanci suna fadawa saurayi hakan, tone
din da suke using kadai kasan cewar bawai brother yake nufi ba aa sede something else. A wancan
lokacin I’m feeling the same, lokacin dana fada se naji wani sanyi a raina but see me today, saying oppa
plainly and emotionless rayuwa kenan. Yaya suleiman da naso na kaunace and so much badly wanted na
zama mallakinsa amma ya dubi idanuna yace kawata yake son nayi hooking dinsu tare, i felt shattered.
That’s then!
“Ya aikin? Kinyi kudi kin manta damu, kullum Nadia tana cigiyarki ko ziyara baki kawo mana”
“Aiki sede godiyar Allah. A gaida Nadia da yara”
Na fada saboda zancen babu ziyara ba mutum daya le zumunci ba both parties keyi, bantaba tunanin zan
rabu da raihana da Nadia ba Amma yanzun ni ko numbers dinsu bani dashi. Duk yadda Yaya suleiman
yaso na tsaya na nuna masa a gajiye nake dole hakanan yayi hakuri na shige gida. Ummaah Na parlor a
zaune itada Asiya na shigo, Asiya ta rungumeni sannan ta bamu guri. Gaisawa nayi da Ummaah tace
“Ina kika tsaya? An shigo da kaya amma ke shiru”
“Nida Yaya suleiman na tsaya”
Bata kara cewa komai ba haka nima se na mike na wuce na tafi dakin Inna, tana zaune kamar kullum ana
goga goro. Karba nayi kamar yadda na saba ina gurza mata muna dan taba hira abin mamaki. Hirar arxiki
kuma wadda na jima bamui nida ita ba. Tana ta bani labarin ‘yan matancinsu ita da fara yar shehu
“Naso Asmau fara yar shehu ta rayu zuwa wannan lokacin ta ganki. Kawata ce wadda banda kamarta
kuma ko bayan data mutu babu wanda ya maye min gurbinta, da yake ita mahaifiyar ta yar Mambila ce
to dukkan mu tafi mu kyau, kyakyawa ce ta gaske hakan yasa tun muna shekaru tara aka sakata a lalle,
naso kin biyo farin jininta da tuni kina dakinki, da kuma ace shahada da Saude sun barki hannuna da tuni
baki shiga wannan kuncin ba.”
Dan murmushi nayi nace
“Inna lokaci ne”
Kanta ta gyada tace
“Da farko nayi tunanin laifinki ne shiyasa na matsa miki, amma a shekarunki na san kowacec so take ta
ganta dakin miji. Ina fatan baki rikeni a ranki ba”
Rungumeta nayi da sauri ina dariya nace
“Waye yake fada da kawar shi? Sede idan kawancen bai kai zuci ba”
A wannan na samu sauki, ranar aka tuna da tare muka kwana, Abba nata tsokanar mu wai yau mun hada
kai. Da safe nayi dukkan abinda ya dace wanda ya kamata sannan na koma bacci. Wajen sha daya nayi
wanka nasan Saturday ce Abba bazai je gona ba, dan baya fita Friday da Saturday he always say they’re
meant for rest. Kuma haka yake. Yana zaune shida Ummaah suna kallon Aljazeera, yau mun samu
bakuntar yaran Yaya halifa dana Adda ummiey so suma suna parlon se kinji suke. Ina zama muka gaisa
yaran suka gaisa se Ummaah ta fita naji dadin hakan sosae a raina dama bana son tana nan bazata bari
nayi magana cikin nutsuwa ba.
“Nasan wannan zaman akwai magana, ina jinki”
Abba ya fada yana rage volume din, zamana na gyara nace
“Abba kayi hakuri dukda baka taba magana ba amma nasan kullum yana ranka, nima ba haka naso ba
Abba na kai har lolacinnan banyi aure ba”
Murmushi yayi min yace
“Asmau! Ai bake kika hana kanki ba, shima Allah ba hanaki yayi ba he’s testing our faith kin gane?”
Kaina na gyada yace
“So, ki dage da addua Allah baya bacci. Ban taba miki zancen aure ba, bawai bana so kiyi ba ko kuma irin
ban damu dinnan ba, ko daya I’m worried, sede ya zanyi idan na takura miki me zai canza?..”
Kanshi ya girgiza yace
“...Nothing my dear, ‘ya’yana takwas kowanne is educated islamically and western, bakwai sunyi aure
kowanne peacefully, ke daya kika rage idan na kasa hakuri me nace da Allah? Ban gode bisa abinda
yayiwa ‘ya’yana bakwai ba. Kinsan musulinci is wonderful, komai is open sede idan baka sani ba. Aure
abu ne me girma, sunnah ce me karfin gaske sede mu bamu dauka sunna bace kawai aure wajibi ne idan
bakai ba gani ake kaika jawo amma i know kinsan tarihin Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S
batayi aure ba amma sura kacokan sunanta ne, so bawai se kayi aure zaka samu yardar Allah ba kede ki
tuna tarbiyar da nayi miki kawai, ki kare mutucinki da martabarki. I tried as much as i can na zama
mutumin arxiki saboda ku, nasan ko bani da rai zaace wannan yaran CP Shahada ce, amma idan na zama
mutumin banza akwai matsala abinda zai zama rightfully yours zaa iya denying muku.”
Se naji sanyi cikin raina saboda maganar shi tayi min dadi naji sanyi da farin ciki a raina. Gyara zamana
nayi nace
“Abba na samu wata school a America, idan ka yadda ina son zuwa”
Shiru yayi yana ta kallona har seda yasa na fara jin uneasiness, se yayi murmushi yace
“Zan iya yin tunani da shawara?”
Kaina na gyada nace
“Sure Abba”
“I’ll get back to you”
_I left you guys waiting and I’m so sorry for that. Nayi typing wannan breakfast din for you all, ina fatan
I’ll get some mind blowing and awesome comments from you guys as always. Yeah! Ina ganin comments
dinku na karanta but replying duka will be hectic y’’all know that Nagode sosae Allah ya bar zumunci.
Daga yau zanje hutu saboda my friend is getting married, pray please. Is an important biki da bazan iya
typing ba har se naga na rakata dakin miji kafin na dawo nutsuwata. I hope zaku min uzuri as usual_
Yours Truly
Ayshatuuuu😍
[6/7, 5:05 PM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_THIRTY TWO_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da