Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
masan ta shigo ba seda naji hannunta a wuyana, hakan yasa na dubeta da sauri, tace
"Zazzabi kike ai Asma'u, tashi kije daki, kamar dole? "
Dukda azabar da gabban jikina sukeyi, kuma nasan zazzabi ne tun ina daki, but to me rashin lafiya is the
worst enemy, na tsani na ganni ina jinya.
"Ummaah ki bari zan iya, kinga idan na kwanta dada rufeni zaiyi"
Kanta ta gyada, kamar ta amince se ta dawo tace
"Kin tabbatar? Nifa hankalina bai kwanta ba "
Faint smile nayi mata nace
"Ummaah ni ce fa"
Kaina ta shafa sannan ta fita, a hankali na Fara aiki amma mainmakon ya ragu se karuwa da yake, hakan
yasa na bar abincin halfway, nasa Amal din Adda ta fadawa Ummaah Bazan iya karasawa ba.
Ina zuwa na kudunduna cikin bargo, hakorana Har karkarwa suke saboda sanyin da nake ji. Ummaah
data zo seda ta tsorata, can se gata ta dawo da Yaya Suleiman Wanda da alamun zuwanshi kenan, naji
dai last week ana cewa zai fara Internship a Nassarawa kuma anan gida zai zauna. Ban wani ji dadi ba.
Ummaah fita tayi ta barmu, se Aleeya yarinyar Adda Sa'ada, bude bargon yayi yace
"I'll feel the temperature? "
Kamar tambaya amma kafin na bashi amsa se hannunsa me taushi naji a dokin wuyana, banida karfi
amma dukda haka seda nayi kokarin ture hannunshi. Ficewa Yayi a raina Ina mitar wannan abu. Har
bacci ya Fara daukata naji sallamar Adda Sa'ada data Yaya Suleiman. Se naji dadin zuwanta. Bude Kaina
nayi Ina mata Sannu da zuwa, hannuna ta kama tana ta yimin Sannu, se lokacin naga syringe hannunshi
yana hada allura gaba daya se naji raina Ya baci, kada dai ace allura zaimin? Ban gama tunanin hakan ba
naji yace
"Sa'adatu gyara ta nayi mata allura"
"Sule bazaka daina cemin Sa'adatu ba right? "
Dariya yayi yace
"Tit for Tat! Gyarata Dan Allah "
Mutsu mutsu na Fara amma hakan bai hana Adda Sa'ada yaye min doguwar rigar dake jikina ba, Allah
yasa akwai under skirt a ciki da naji kunya, da kanshi ya saukar da skirt din da pant dina ya caka. A take
naji wata muguwar kunya ta lullubeni, ga haushinshi, ai yana cire Allurar na Fara kuka. A'a Se ya Fara
lallashina Har da cewa
"Sa'ada duk kun bata yarinyar nan, Har kukan allura take. "
Ayshatuuu
[4/2, 10:40 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_ELEVEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ WATTPAD
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Anty Asma'u Madugu...... Thank you so much for always having my back, for been there for me....
Thank you. This page Issa token of appreciation from me.*
Naji haushin furucinshi sosae, se na bata fuska ina share hawayen fuskata. Dariya yayi sannan yace
"Kawo asaka canula"
Wanne musu zanyi, Dan hannu ai bazai hada fada ba, haka na mika yasa canular, Yayi allurai sannan yasa
min infusion. Wani dadi naji a jikina, Tun Ina jin hirarsu Ko ince musunshi shida Adda Sa'ada Har
nannauyen bacci yayi gaba dani. Bansan iyakar time din dana dauka Ina bacci ba. Amma nasan se da aka
idar da Maghrib sannan na tashi. God so kind ba sallah zanyi ba. Koda na tashi, babu inda yake min ciwo
se jikina da babu karfi. Amma haka na daure na sakko daga gadon, Amal na zaune da wayata a hannu
Tana game. Kallonta nayi nace
"Amaly!"
Dagowa tayi, tana ganin yanayina ta saki Murmushi, se kuma ta aje wayar tayi waje. Kaina na girgiza na
wuce bandaki Dan nayi wanka. Koda na fito yan dubiya sun cika dakin, kowanne na fadin Anty Sannu, ya
jiki? Lafiya nayi ta fada sannan nace suje waje na saka kaya, dukkansu suka fice a hakan na samu na
shirya Sannnan ya fito. Dakin Ummaah naje suna tareda Adda Sa'ada, dukkansu Sunyi farin cikin ganin
na warware. Zama nayi ina cin Abinci munata hira.
Ban jima ba, Ikhram Tazo akan naje Yaya Suleiman yana kirana. Bansan na zunbura Baki ba seda naji
dariyar Adda Sa'ada tace
"Meye hakan ke kuwa? Ki wuce kije mana"
Mikewa nayi ina gunguni, Inaji tana bawa Ummaah labarin allura Yayi min shiyasa. Banji abinda Ummaah
tace ba nayi gaba abina. A parlor na tadda shi Yara sun baibayeshi. Zama nayi fuskata a murtuke nace
"Gani Yaya Suleiman"
"To ku daga ni, Se da safe Zamui wasan"
Basu Musa ba suka daga shi, daya bayan daya suka wuce dining Dan tun fiwota naji ana fama dasu akan
Anyi serving dinner, amma da yake wasa ne a ransu basu lura ba. Bana takura musu saboda duk ranar da
suka tafi se naji na zama so empty tamkar Anyi min mutuwa. They're company gaskiya.
"Na zata idan patient ya tashi, Doctor dinsa yake fada nema? See you "
Dauke kaina nayi bance komai ba, saboda bansan abinda zan ce dinba. Kafadarshi yayi shrugging yace
"Ya kikeji Yanzun? "
"Alhamdulillah "
Kanshi Ya gyada sannan ya mukamin Leda yace magunguna ne, godiya nayi mishi na koma dakina.
Bayan sati biyu ko barbushin zazzabi babu kuma na warke tas, babu wani abu dake damuna. Shima kuma
baifi sau daya muke Haduwa a rana ba, kullum he's busy a asibiti. Da sassafe ina kitchen Ina daka
barkono zan zuba cikin Naman kai, inason Adan saka kadan saboda yadda yake fito da flavor din. Banji
sallamar shi ba se ji nayi yace
"Haba early morning kinzo kina daka, bakuda grinder ne? "
Dagowa nayi na kalleshi from head to toe, babu karya jinin Inna Ade ne, zancen bazaiyi kyau ba wannan
wasa ne.
"Bamuda ita amma tunda Kaima gidanku ne, idan ka siyo Bakayi shishigi ba"
Na zata zaiji haushi, Se naji yayi dariya sannan yace
"I'll try, zansha coffee "
Yadda ya fadi coffee dinma daban ne, tamkar mace Haka yake da kakale kakale, kallonshi nayi sannan na
juya Naman nace
"Bamu shan coffee, amma Munada Tea."
Ban jira abinda zaice ba, na shige store saboda turarenshi gaba daya Ya dameni, bansan zama kusa
dashi. Ina fitowa na samu ya zubar min da gyadar Dana Dama baki daya ta malale a Kasan kitchen, kawai
tsayawa nayi ina kallonshi raina a jagule.
"Biyani Sweetheart, naxo janyo cup ya bare"
Bance komai ba na kashe Gas sannan na dakko cup cikin wani rack dake a rufe, ba lalle ka gani ba in ba
kasan gurin ajiyarsu kenan ba. Mika mishi nayi sannan na bashi Tea bag nace
"Komai yana kan dining, don't stress yourself"
Hannunsa Ya hade guri daya yace
"Kumaya"
Se nayi Murmushi hakan ya tabbatar masa na fahimci abinda yace. Da yamma na samu bakuncin Nadia,
friend dita ce da mukai New Horizon tare, muna jimawa bamu hadu ba, dukda unguwarmu daya amma
dake ita Tana Karatu a wannan Private University dake Yola yasa haduwarmu Se lokaci zuwa lokaci.
Lokacinda ta shigo Ina daki, Yaya Suleiman kuma yana parlour shida Yara, so seda suka gaisa sannan ya
nuna mata dakina Wanda ta rigada ta sanshi tuntuni. Ina ninke kaya naji sallamar ta, rigarda ke hannuna
na wullar Inata Murmushi na nufi inda take tsaye Tana kare min kallo.
"Oh Nadia, Oyoyo..... Is this a surprise? "
Hararata tayi tace
"Kinfi kowa dadin baki idan aka zo gurinki, amma Kira a waya ya gagara, and you always brag of I been
your friend ko? "
Rufe bakina nayi ina Dan dariya kasakasa, idan da Sabo na saba da korafin Nadia, tanada zumunci Ina
tunanin ba dan ita ba inaga da tuni we're separated tuntuni amma ta rike abin.
Janyota ciki nayi na ture himilin kayan dake gefen gado nace
"Zauna mana, se magana kike"
Kanta ta gyada tace
"Bari na gaida Ummaah se na dawo"
Hannunta na kama nace
"Ummaah sunje Abuja zasuyi visa zuwa Hungary"
Kanta ta gyada tace
"Dan Allah su sani a jaka"
Dariya nayi sannan na fice na dakko mata juice da cake da fish pie. Na kawo mata, tanaci munata hira,
Dan banida kamar ta, ko islamiyya ma class dinmu daya. A mutanen dana zauna dasu Wanda bamu hada
komai dasu ba, tafi kowa tolerating halayena.
"Ya ake ciki, kuma karkice min babu wani motsi "
Langwabar da kaina nayi irin abin tausayi dinnan nace
"Nads karya kike so nayi miki? wallahi har Yanzun Ina nan as single as me zance miki? "
Dariya tayi sosae sannan tace
"Kiga yadda kike kwabe fuska Kamar wata marainiya"
Daidaita fuskata nayi nace
"To Ya zanyi, I'm lonely I need a partner"
Numfashi taja me karfi tace
"Dama loneliness dole ne, tunda shekaru sun kai, amma Kinsan me? Lokaci ne fa, kuma har kyayi
karatunki a nutse babu takura. "
Kaina na gyada nace
"An Kai kudin Rayhana da Abdul "
Wani ihu Nadia ta buga tace
"Shegu ce Rayhana, Kice an kusa? "
Dariya nayi nace
"Ke Kina ganin idan Baa saka ranar nan bazasu samu matsala ba. Ya jira da yawa ai, tun muna Js2 fa"
Daga nan muka wuce kitchen Dan ta tayani mu hada dinner, a parlor har lokacin Yaya Suleiman na
zaune, kallo yake cikin system dinshi, yana jin fitowar mu ya dago muka hada ido, dauke kaina nayi inajin
Nadia suna Kara gaisawa, ni kuwa ko ta kanshi banbi ba na wuce kitchen, seda ta shigo sannan tace
"Ke wannan handsome din fa? "
Tabe Baki nayi nace
"Handsome kam, Dan Anty Shamsiyya ne kanwar Abba. Internship yake a Nasarawa. "
Kanta ta gyada tace
"Yayi miki laifi ne? Naga Kamar kuna fada "
Kaina na girgiza Ina kokarin kuna gas nace
"Ko daya wallahi, in fact he's nice. Kawai dai bana son mu saba dashi yazo Ya mutu"
"Mutu kuma? Haba ke kuwa, kowa ai se lokacin shi Yayi, Mukhtar da ya rasu lokacin shi ne. To ya zaayi?
"
Na amince da abinda tace amma haka kurum nake jin bana son sabawa dashi, a rayuwata na tsani
rabuwa da mutane, I'm selfish nafi son idan na samu Abu to ya zama nawa, kada abinnan ya tafi, to a
wannan rayuwar ta Yaya, ai bazai yiwu ba.
Nadia bata bar gidanmu ba se wajen Karfe Tara na dare akaxo aka dauke ta tafi, Se naji inama ta zauna
dan naji dadin yinin ranar. Ban bar parlon ba se wajen twelve, muna ta kallo nida Yaya Halifa, can kuma
Yaya Suleiman yayi joining dinmu, anan na sake dashi for the first time Tun zuwanshi gidanmu.
Ayshatuuu[4/2, 10:40 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_TWELVE_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Hutuna Ya Kare na koma school, big lady na zama yar level 200, tunda naje registering courses dina Naga
babu su basics dinnan da nayi a level 1 na Fara jin wani shaukin dadi. Community based medical
education, physiology, Anatomy, pharmacology and many da zaisa naji yeah I'm a medical student. Koda
muka koma, first week ne kadai nayi day amma second week na tattara kayana na koma hostel, Dan na
lura the higher we go, the hotter it becomes.
Ranar Friday na fito daga lecture din Biochemistry, wayata a hannu na, sauri nake Zanje hostel na dakko
jakata saboda na wuce gida kafin a shiga sallah. wayata ringing tayi, na dakko na duba, Yaya Suleiman
ne,
"Ajhumma! "
Ya fada Ina picking, dariya nayi nace
"Ajhussi! "
Se muka kara kwashewa dariya, sannan yace
"Nazo wucewa ta school dinku nace bari na dakko Sweetheart"
Cikin jin dadi nace
"Kai Yaya Suleiman, naji dadi, ka jirani kofar hostel dinmu, jakata kawai Zan dakko"
"At your service Ma'am "
Ko bana kusa nasan saluting dina Yayi, nayi Murmushi na katse wayar. Na tuna ranar da ya Fara cemin
Ajhumma, naji haushi sosae, saboda ni nasan I'm not Ajhumma. Ina school ranar ya kirani da daddare
lokacin mundan Fara sakewa da juna, yace min Ajhumma, I was like Kasan me kake fada kuwa, se yayi ta
dariya, so ni kuma se nace mishi Ajhussi. Shikenan mukai naming kanmu, dake gaba dayanmu die hard
fans din Korean dramas ne. Munada abubuwa sosae that are related ni dashi. I can even say, hakan ya
karawa relationship dinmu karfi.
Wani sanyi naji cikin raina, I'm sure kowacce mace ta samu Yaya Suleiman tabbas ta gama morewa,
halayenshi sunada kyau, kuma kowa zaiji dadin zama dashi. Books dina na dauka sannan na fito kafadata
sabe da handbag dita na wuce dakin su Rayhana. Tana kwance da waya a kunnenta, na tabbatar
Maganar daya ce, Abdul ne.
"Ke Baki jiya da waya ne, kullum ace kuna Abu daya. Haba Dan Allah! "
Na fada bayan na tsaya a kanta, Allah su Rayhana are irritating, kauda wayar tayi daga kunnenta tace
min
"Duk ranar da kika Fara soyayya, soyayya da right man dinki, se kin fini sannan zaki gane abinda nake ji.
So ya ake ciki? "
Harara na wurga mata tareda sakin Tsaki nace
"Zan tafi, kin fasa zuwan? "
Maida wayar tayi kunnenta, tayi mishi sallama, sannan tace
"Oh Asma'u, Karatu zanyi kije kawai. "
Kaina na gyada na wuce, har naje kofar fita a dakinsu naji ta kwalla min kira, Juyawa nayi nace
"Sauri nake fa"
"Haushi kika ji ne?"
Kaina na girgiza nace
"Ke Wanne haushi, nasan bawai Karatu zakiyi ba, Abdul ne kawai zaizo. Allah yasa nanda 2 weeks kina
gidanshi ma huta muma. Amma...."
Tsaki nayi na fice, na rasa wannan jarababbiyar soyayyar tsakanin Abdul da Rayhana, kamar mayu
kullum suna waya, abin haushi yake bani, kuma bansan me yasa nake jin hakan ba. Yaya Suleiman na
zaune a drivers seat, ya kurawa kofar hostel ido, da dukkan alamu jirana yake yi. Straight inda yake na
nufa, fuskata se Murmushi ne akanta, kamar bakina zai yage, is this what I've been missing, dama Haka
akeji a soyayyar?
"Yaya kayi ta jirana Ko? Sorry "
Murmushi yayi yace
"Anything for Princess, nasan an tsaya yin girls stuff ne ko? "
Murmushi na kuma saki nace
"Kamar ka sani, muje Ko?"
Kanshi Ya gyada tareda yiwa motar key muka dauki hanya, seda muka fita wajen mun hau titi yake
tambayata Baiga Rayhana ba, nace Rayhana ta zauna yin ayyuka. Kanshi Ya gyada dan naga shi da ita ba
wani good time suke ba, unlike itada Yaya Mukhtar marigayi. A gida muna shiga nasan Yau Inada Babbar
Bakuwa, Inna Ade, tamkar yadda na saba haka na shiga a guje Tana parlor tayi daidai, gabanta an cikashi
da abubuwa, Abinci ne nama ne and stuffs. Rungumeta nayi nace
"Kawata! Sannu da zuwa"
Itama bakinta ta bude Wanda hakora suka Fara Ficewa sannan ga yadda goro ya rinar dasu. Tace
"Kawata, Karatu ya boye min ke"
Dariya nayi Ina gyara zamana nace
"Ya zanyi kawaliyya? Nasan Kema zakiji dadi ace kawarki Likita ce ko? "
Kanta ta gyada Tana kare min kallo tace
"Wannan haka yake amma se naga kin yi rama, Ina fata babu matsala"
Kaina na girgiza Ina tauna Apple din dana dauka akan table din gabanta nace
"Ko daya, kawai Karatu ne. "
Kanta ta gyada tace
"Allah Ya bada saa, kije kiyi wanka. "
Tura bakina nayi nace
"Kai Inna, wari nakeyi? "
Harara ta tayi tace Hali Zanen dutse. Nayi dariya sannan na tafi na Kai kaina wajen Ummaah, tunda na
ganta, naji jikina Yayi sanyi, saboda yanayunta kawai ya nuna min babu lafiya. Zama nayi nace
"Ummaah, Menene? "
Murmushi tayi Wanda ko makoshi bai kai ba, balle ace daga zuciya yake. Tace
"Babu komai, kin dawo? Ya Naga baku taho da Rayhanar ba? "
Kaina na girgiza nace
"Zatayi aiki shiyasa"
Daga Haka na mike na tafi dakina. Inna kwananta biyu amma ni bansan dalilin zuwanta ba Dan babu
Wanda ya fada min, sede ni din ba yarinya bace, nasan definitely akwai abinda ke faruwa, amma tunda
kowa boyewa yake, Meye nawa na bincike. Se naji Dama ban dawo ba, saboda yanayinsu duka ba cikin
jin dadi suke ba.
Ranar Monday mukai sallama da Inna Ade, Dan zata wuce Kwalam, Haka nima zan wuce school. Na tafi
abuna. Wajen Karfe biyar na yamma Adda Sa'ada ta kirani akan gata ta shigo cikin school dinmu, Nazo
wani eatery mu hadu. Haka na Mike da duk Gajiyata na tafi, ita tayi mana order chilled Fanta, Danni
inason Fanta babu ruwana da kakale kakale. Yadda ta tsira min idanu yasa gaba daya na kasa sakewa
balle na sha lemun.
"Asma'u kisha mana"
Langwabar da kaina nayi nace
"Adda nasan dole wani abu ya kawoku, Ki fada min Bazan iya sha ba. "
Hannuna ta kama tace
"Ki saurareni da kyau kinji"
Ban bata amsa ba na gyada Kaina, se ta cigaba da fadin
"Kinada saurayi? "
OK, to me tambayar Tazo min a bazata, Abu ne daban yi expecting ba, amma ya zanyi dole na bada
amsa. Kaina na girgiza nace
"A'a Adda, wani abu ne? "
Kanta ta gyada tace
"Suleiman fa? "
Shiru nayi bansan yadda zan Fara mata bayani ba, nida Suleiman babu Wanda yace yana son wani amma
kuma dukkanmu muna son junanmu, balle ni ai kada wani yaji labari, ina sonshi sosae, son abinda ban
taba yiwa wani abu ba. Kuma duk yadda muka zauna da mutum Ko awa ne se ya fahimci shakuwar mu
nida shi.
"Kinyi Shiru Asma'u "
Kaina na girgiza nace
"Adda, baice yana sona ba amma.... "
"Amma me? Mistake din da kikayi akan Mukhtar shi kike son kara maimaitawa. Me yake damunki ne
Wai? "
Tura bakina nayi nace
"Kai Adda, yana sona ne fa, kawai nasan zai fada idan time Yayi "
Idanunta ta kafeni dasu sannan tace
"Bakida hankali dama Har Yanzun? Wa yace miki ana haka. Ki daina kulashi kina jina ko"
Juyar da kaina nayi bansan yadda zanyi ba, ta Yaya Adda zatace na rabu da only source of happiness
dina, kaina na girgiza Se kuma tace
"Kinsan Inna tazo weekend dinnan. Baki San me ya kawota ba right?"
Kaina na girgiza, gabana yana faduwa nace
"Me ya kawota? "
"Zancen aurenki!"
Da mamaki sosae nace
"Ni? Aurena? Haba dai "
Dariya tayi tace
"Saboda Sajida, Nabila da Rayhana dukka sa'anninki ne kuma zasuyi aure, shi ne tazo ta bawa Ummaah
da Abba notice. Idan Kinada wani saurayi Ki turashi yayi gaisuwa idan yaso ayi Maganar daga baya. "
Raina a mugun bace nace
"Lallai! Nifa banda saurayi banda Yaya Suleiman sede idan shi zan tura"
Duka ta kaimin Tana fadin
"Dallah rufe min bakinki a gurin, Suleiman ai yafi kowa sanin halin da ake ciki, idan da yana sonki kinsan
da tuni yayi magana. Abinda nakeso dake Kiyiwa Allah ki daina grumping fuskarki, ko a samu
mashinshini"
Nidai Bance komai ba, Raina Ya baci sosae amma ko daya hankalina bai tashi ba, saboda nasa a raina,
aure da mutuwa lokaci ne.
Ayshatuuu
[4/2, 10:41 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_THIRTEEN_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
A hankali na ja kafafuna cikin hostel, duk jikina Yayi sanyi Dan ko sallamar Arziki bamui nida Adda Sa'ada
ba. Meye kuma Inna Ade take nufi da rayuwata zatace Ayimin aure, idan na tuna agreement din da
mukai da Abba, har Yanzun akwai more than a year zuwa lokacin da ya yarda na kawo mishi mijin aure,
but see what this old woman is talking about.
Koda na koma daki, rasa inda zan