Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
ga pressure Inna from
other side.
Duk haduwarmu dashi yawancin gidan Adda Sa'ada muke Haduwa dashi, se lokacin da yazo Ya gaida
Ummaah da Abba yayiwa Abba bayanin plan dinsa na se na gama Service kafin zai turo, Abba ya amince
dan shima abinda yake so kenan. Abba ya kirani ya tambayeni yadda nake jin Salis, na amince? nace na
amince, shikenan ya bashi damar soyayya Dani. Yayi seeking consent dina. Abba yasa akai bincike sosae
akanshi kuma Alhamdulillah he worth a bashi aure.
"Ke Wai se yaushe zakiyi aure ne, Walahi kiyi aure shi ne rufin asirin mace"
Shine abinda na tsana a duniya, wannan tambayar, ko ya muke da mutum Se naji raina Ya baci, Nadiya
ce na rasa abinda yake damunta, she always challenge me akan naki aure, naki tsayawa na bawa mutane
chance, na zauna bokon da Bashida amfani.
"Keda yaushe kikai auren har da zaki dinga zakalkalewar wani yayi auren? Yaushe muka gama
yanmatanci tare dake? "
Da mamaki sosae ta kalleni tace
"To Asma'u Meye abin fada? Is just an advice"
"Bana bukata Kinji? Ke karfinki ya Baki miji? It's a matter of time, da kikace rufin asiri shi ne aure, asirina
ai ba a bude kika ganshi ba "
Nima nasan babu dadi na gaya mata magana amma mutane Haka suke, yanmatan Yanzun da Sunyi aure
se su zama tamkar Wasu preachers ko kuma scholars, su ta damunka akan kayi aure, as if badasu kuka
gama zama ba. Haka dai muka rabu nida Nadiya babu dadi, Tama ta fushi Nikam nayi haka Dan gobe
kada ta kara hakan.
General hospital Potiskum anan akai posting dina zanyi service, Itakuma Kyaftun tana Damaturu anan
zatayi, by far mun rabu da juna but we're still in touch da ita. Asibitin suka bani accommodation da
abinda ya kamata, dama a shirye naje so ban koma yin wani abu ba. Kwana na biyu Salis Ya dameni akan
zaizo nace mishi ya bari naga yanayin Garin tukunna. Seda nayi sati biyu sannan yazo. Ranar Saturday ne
banida call, so ina dakina ina hutawa yazo. Shida Friend dinsa suka zo, Se naji hankalina ya kwanta na
kaisu dakin. Suka ci Abinci sukai sallah sannan muka fita Verrender muka zauna ni dashi
"Asma'u Anya kina sona kuwa? "
Dagowa nayi na kalleshi nace
"Me ka gani ne? "
"Baki kula dani fa, Ki kalla naje gurin Abba, Ummaah ta sanni, Inna ma haka amma still kinki sakin jikinki
da kyau. "
Dan Murmushi nayi nace
"Kai kake ganin hakan, amma ba haka bane"
Ya jima yana kallona Kamar yana son karantar wani abu, hakan yasa na takura nayi kasa idona, deep
down ina jinshi a raina, but Tsoro nakeji, kuma na rasa tsoron Menene.
*Ramadan is fast coming our way! Let's all have fate and even the slightest or glimpse of hope, that this
plaque (Pandemic Covid 19) will be curbed before Ramadan. Let's all raise hands and pray, don't let
anyone destroy your Imaan. It sure is a plaque, that's bound to take away souls that are destined to die!
You can't do anything but take precautionary measures, make your Imaan still. Inshaaa Allah everything
will be over! Aminnnn! When are we going for our Ramadan break? You all know we can't take the story
down before Ramadan.*
Ayshatuuu[4/18, 2:14 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_TWENTY TWO_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Four Months Later
A hankali na cika watanni biyar cif a Potiskum, duk karshen wata nake zuwa Kano nayi sati daya sannan
na dawo. Komai yana nan yadda yake sede yan canje canje da aka samu kalilan. Like Yanzun kowa yasan
da zaman Salis kuma yasan cewar aurena Zaiyi, Dan haka babu Wanda ya ke takura min, sede kowa jira
yake Kamar yadda Salis Ya bukata, na gama Service dina. Ummaaah shirye shirye take sosae, ta sayi
wannan ta sayi wancan, inaje gida haka zata ta nuna min, duk se naji tausayinsu, a raina na raya, what if
idan Salis yaudarata Zaiyi? What if idan Allah bai amince shi din mijina bane. Hakan se yasa naji duk
tsoro ya kamani. Inason Salis, nasan bai Kai Wanda na yiwa Yaya Suleiman ba amma nashi ma abin a
duba ne. Yasa min soyayyar shi me zafi cikin zuciyata, babu abinda na tsana Kamar a kusheshi, shiyasa
bansan Adda Meeyna ta kirani ta dinga aibata shi kenan. Ni ce yawanci me kiran, hardly on his own ya
kirani, tunda mukai na watan farko na dauki, shikenan ya janye jikinshi, idan nayi magana Se yace ai
aikina baya son ya kiranki nace Ina aiki, amma idan na kira yasan I'm free kenan.
Ina clinic Ranar Thursday, uban files din dake gabana na kalla, wai kuma duk ni zanyi clerking dinsu.
Kaina na dafe ina takaicin yadda na zama detained a general hospital, had it been a tertiary facility nake,
ai sede Ina bin senior officers ina Kara koyar aiki. Wayata dake gefen table ta Fara ringing, cirewa nayi
daga chagi naga Salis ne. Dan Murmushi nayi na dauka
"An tashi lafiya? "
"Lafiya lau Doc, Ya aiki"
Kallon files din na kumayi sannan nace
"Horrible! "
Dariya yayi wadda naji ta har cikin zuciyata, se nayi Murmushi nace
"Like Yanzun nayi half, kuma Inada almost 20 patients to go, gashi ni nake call yau! "
"So, kice yau Se abinda na gani kenan? "
Kaina na gyada nace
"Gaskiya kam, Yanzun ma hanging Zakayi, Anjima I'll find time na kiraka"
Dan siririn Tsaki ya saki yace
"Kai! Mutum shi kenan Bashida full liberty akanki, kullum kina aiki"
Complain din kenan kullum, indai zai Kira nace Ina aiki to se ya fada, Tun ina damuwa Har ya zama jiki.
Lallabashi nayi sannan na hanging up, a hankali patient din suka cigaba da shigowa. A takaice Se daya na
kammalla dasu, Mikewa nayi Dan one hour kawai ya rage call time ya shiga gwara nayi wani abin arzikin
kafin lokacin Yayi. Handbag dita na dauka na fito, nayiwa cleaners din da Sauran staff din sallama.
straight gida na wuce nayi wanka nayi sallah sannan na hada cornflakes nasha, at least na bawa yunwar
hakuri kafin na karasa girkin. Wayata na janyo na Fara kiran wayar Salis, amma har sau biyu bai dauka
ba. Aje wayar nayi, daga nan wani wahalallen bacci ya daukeni.
Nayi saa har akai laasar Baa kirani ba, da nayi sallah se nayi wanka na shirya cikin Coffee Skirt da milk
long sleeve top, me buttons a gabanta. Hula nasa na rufe kaina sannan na dauki lab coat na daura, na
janyo stethoscope na Sakala a wuyana na dauki wayata da abinda Baa rasa ba na kulle dakin na fito.
Dama kaidar call dina kenan, Karfe hudu Zanbi dukkan wards na duba sannan na dawo lounge na zauna.
God so kind dukkan ward din babu wani problem, A&E nema suka rikeni se Maghrib sannan na fita.
Wajen Karfe goma na dare, har lokacin ban koma daki ba Ina kwance a lounge. Zuwa wannan lokacin na
gaji da duba notification panel dina, Haka call log dina Wai ko Salis Yayi returning call din da nayi mishi
amma Shiru bai yi ba, Haka babu text. Dan Tsaki nayi, bansan me yake faruwa dashi ba. Wasu calls din
guda biyu nayi mishi amma same baayi picking ba, karshe kawai na hakura na kwanta.
Wasawasa seda mukai sati biyu bai kira ni ba, nima ban kara kirashi ba, ko a whatsappp baiyi min
magana ba, Haka nima amma Ina kallon updates dinshi. Hakan ya dameni sosae, saboda Ina son salis
kuma Ina ganin shi daya shi ne hope dina, irin mata Kamar ni, Munada wani mentality, muna ganin
Kamar idan muka bari saurayi yayi slipping daga gurinmu to tabbas wani bazai zo ba. Ni dinma I've that a
raina shiyasa duk Iskancin da Salis yake min nake tolerating. Dan wannan bashi bane karo na farko da
mukai irin Haka ba, abinda na lura dashi ya rigada ya fahimci weakness dina, sonshi nake sannan kuma
ya fahimci aure nake so nayi and lastly Ya fahimci pressure da nake ciki, shiyasa yake min yawo da
hankali.
Ajiyar zuciya na sauke na kara kallon wayar, zuciyata se ingiza ni take akan na kirashi amma Allah yasa
kwakwalwata ta ankare da abinda yake faruwa ta hanani. I believe in love sosae, idan kana son abu,
baka gani kalilan mutane suke ji da gani, I'm the type that's blind and deaf indai inason abu ne. Haka
zuciya idan tana son abu, Tana iya acting kafin kwalkwalwa ta ankare. So zan kira all the youngsters da
suke karanta labarina, whenever you following your heart, take your brain. Saboda zuciya will lead you
astray.
Ban samu na kirashi ba, saboda internal battle da akai, at last my brain wins, Se kawai na dakko wayata
Ina rereading messages dinmu, wani nayi murmushi, wani na tura bakina wani naji Kamar na rankwashi
kaina, babu moments me dadi Kamar watanmu na farko ni dashi, Munyi soyayya sosae, he tolerated
komai nawa amma Yanzun duk ya canja!
*🎤I'm faded! So lost! Where are you now? Where are you now? Atlantis? Under the sea? Where are you
now? Another dream, the monsters running wild inside of me! I'm faded! 🎶*
Mikewa nayi daga kan sallayar da nayi Sallar asuba, Wando da riga na Maroon cotton yadi na saka, na
dikansu different colors suke serving Kamar uniform, bnda fari da blue Wanda na Nurses ne. Tea kadai
nasha Se wani short cake sannan na dauki abinda zan bukata na fita. Lokacin bakwai tayi, ya kamata naje
Naga wards, yadda kowa ya kwana. A hanya Kamar yadda na saba na kira Abba da Ummaah muka gaisa.
Kowannensu adduar kullum akai min, daga Haka na wuce, ban wani samu wani case ba saboda sanyi
ake, Normally da sanyi rashin lafiya, haihuwa gaba daya suna yin kasa, da zafi ne se nace pepper kenan.
Karfe uku na koma dakina nayi wanka naci Abinci, nayi laasar sannan na danyi tilawa ko Na samu abinda
ke damuna Ya Dan ragu. Aikuwa Ya ragu sosae. Wayata na dauka na Kira Kyaftun,
"Twinie! "
"Twin, ya aiki? "
"Lafiya lau, Twin ya naku? "
Kallon dakin nayi Kamar amsar anan take nace
"Not bad, yaushe zakizo? "
"Karshen week dinnan Inshaaa Allah "
Cikeda jin dadi nace
"Kai amma I'm happy, dama Inata missing dinki"
Haka dai muka Dan taba hira, inason in fada mata abinda yake faruwa tsakanina da Salis amma been the
Fara Yar Shehu I've always been, Se na kasa. A Haka mukai sallama na aje wayar tareda zamewa na
kwanta a gurin, zuciyata gaba daya tayi Baki, a hankali naji idanuna suna cikowa da kwalla, duk yadda na
daure na kasa seda hawayen nan suka sakko min, Dama abinda nake jira kenan, nayi ta kuka Har seda
Dan Kaina na lallashi kaina sannan na mike na wanko fuskata, a lokacin Adda Sa'ada kuma ta kirani, Ina
dauka tace
"Kinyi kuka ne? "
Shiru nayi Ina kara goge hawayen da ya kara sakkowa, cikin damuwa tace
"Asma'u Ina jinki? Menene? Keda Salis ne? "
Cikin kuka nace
"Adda kina ganin zanyi aure? Zan cikawa Ummaah burinta? Kin gani Salis Ya canja gaba daya, Baya
kirana, kuma ko na kira Baya dauka sannan bazai Kira ba. Adda ya zanyi? "
A muryarta nasan ranta ya baci hakan yasa tace
"Ki rabu dashi, tunda shi ba autan maza bane. Ni na rasa irinki Asma'u, nasha fada miki time without
number ke mace ce, mace me daraja, me kika rasa? Kin taba kallon Kanki a mirror, ke manta da zancen
kyau wannan bonus ne, kina sallah, kina azumi kina bin dokar Allah! Da iliminki, aikinki a hannun. Baki
san ke hot cake bace da kowa ke mafarkin samu. Ni from the start Yaran bai min ba amma naga yadda
kike sonshi, Bazan iya rabaku. Yanzunnan ki kira Kice kin rabu dashi, wallahi zakiga tanadin da Allah Yayi
miki"
A take zuciyata ta karye, Anya zan iya? Zan iya furtawa Salis break up? Kaina na girgiza nace
"Adda Ina sonshi fa! Bazan iya ba"
Adda takaici ya kamata tace
"Ubanki Asma'u! Kinji Ubanki nace. Shashasha kawai. Idan kikace mishi ku rabu idan da gaske yake he'll
not let you. "
Kaina na kara girgizawa nace
"Idan na rabu dashi, wa zai so ni, Adda wa zai aureni? Kina kallo kowa jirana yake na gama Service
dinnan, idan na rabu dashi saboda abu kalilan, kenan Bazan iya enduring zaman aure ba. "
Lumshe idonta tayi, tasan Inada taurin Kai amma batasan I'm a fool ba,
"Asma'u bari kiji, idan namiji yana sonki wallahi bazai yi sati daya bai kiraki ba, ke kaddara Babban Abu
ya faru, dole zai San yadda Zaiyi ko text Yayi dropping miki, balle kin kirashi amma bai dauka ba, you
telling me he's serious. AI idan namiji ya nuna miki shi autan maza ne, Sister nuna mishi zakiyi karya
yake, ki mishi albishir cewar a anguwanku an haifi sabon Bom Boy! Kiyi tunani"
Daga Haka ta katse wayar, Shiru nayi Inata tauna Maganar ta, kenan Salis wasa yake da zuciyata, kaina
na dafe hawaye na kara zuba nace
"Allah! Allah!! Ka kawowa rayuwata dauki"
Hawayen na share na dauki wayar a Karon da Bazan iya irgawa ba na sake kiranshi, wannan karan
ringing daya ya dauka, yana picking yace
"Asma'u Fara Yar Shehu! I'm very sorry! Nasan ban kyauta ba, wayata ce ta lalace Dazunnan na karbo
sabuwar. Kina raina. Ya aiki! "
*🎵So many words for the broken heart, it's hard to see in a crimson love, so hard to believe, walk with
me and may be wild and free I could feel the sun, your every wish will be done, they tell me. Show me
the meaning of been lonely, is this the feeling I need to walk with, tell me why I can't be there where
you are? 🎶*
Let's all wait for Fara 'Yar Shehus' reply. Zata yadda da Salis ko zatayi abinda Adda Sa'ada tace tayi? Have
you ever had such jerks like Salis?
Ayshatuuu
[4/19, 2:14 PM] +234 703 530 7398: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_23 to 25_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Shiru nayi bayan na gama sauraren reason dinsa, gaba daya kaina se ya kulle na kasa tantance Wanne
zanbi, Maganar Adda Ko Maganar Salis? Take kwalkwalwata ta birkice tana tariyo min each and every
Maganar Adda Sa'ada da kuma reason din Oga Salis..... Halfway zuciyata ke karfafa min gwiwar yadda da
Maganar Salis.
"Dear are you with me? "
Ajiyar zuciya na sauke me nauyi, nace
"Ina jinka! Is that all you want to say? Kwana nawa baka kira ba, kwana nawa? I called you Baka dauka
ba, not minding to call back. Do you know how I feel?..... "
"Calm down Beauty, amma nace miki wayata ta baci ko? Bana ganin call. Kiyi hakuri mana. So ya aiki? "
Se naji Bazan iya cewa komai ba akan Maganar Adda Sa'ada, instantly zuciyata ta blocking wannan
thought din naji Bazan iya abinda tace min ba,
"I'm fine Alhmdllh, how have you been? "
"Great, se missing dinki da idanu suke tayi, Kunne has been whining dole se yaji wannan tattausar
muryar taki. Kinsan you part of my happiness! "
🎶You got that smile, that only heavens can make, I pray to God everyday that you keep that smile, you're
my dream there's no a thing I won't do, I'll give my life all for you bcx you're my dream🎤
Murmushi nayi Wanda da wani a cikinku na gurin Se ya mangare ni, a take duk Wasu vessels dake tura
jini jikina suka kara budewa suna Kara tura sonshi zuwa kowanne sashen jikina. A takaice banyi abinda
kowa yake so ba, a ranar muka shirya, Munyi hirar more than an hour abinda Bazan iya tuna yaushe
mukai ba. Da zamuyi sallama yacr
"Asma'u Se yaushe zaki ce kina sona, baki Taba fada ba"
Dariya nayi nace
"Amma Kasan Ina sonka ko? Don't you know I can move a mountain for you? "
Sassanyar dariya yayi yace
"Awwnnnn! Amma Yanzun naji I'm satisfied, na zata ni daya kawai nake abuna. "
"Abu daya nake so da kai shine, ga zuciyata na baka ka rike, I hope bazakai mata rikon wasa ba, I hope ba
zaka riketa har wani ya kwace daga hannun ka ba. I hope zaka adanata bazaka cutar da ita ba"
Shiru yayi na kusan mintina uku kafin yace
"Promise! I promise you Baby"
Murmushi nayi inajin tamkar I'm complete, wani yanayi me dadi ya baibayeni , bakina saboda
murmushin da nake ya kasa rufuwa inajin nafi kowa saa a duniya, tamkar I was diving in the sky!
🎤 Baby, everything that I've is yours, you will never go cold or hungry I'll be there when you're insecure,
let you know that you always lovely, cuz your d only thing I got right now 🎶
Wannan shi ne shirinmu, muka cigaba da soyayyar mu, dukda Wasu abubuwan basu canja ba amma up
to 80% abubuwa Sun gyaru har hakan yasa na kasa tantance, inda Salis Ya saka gabanshi, Lokuta da
dama se na samu Kaina da tuhumar kaina Anya Inada hankali kuwa.
Ranar Thursday ina clinic, na gama abinda zanyi naji wayata na ringing, dake already har na zura a Jaka
yasa nayi saurin cirowa, da mamaki ganin sunan Rayhana a jiki. Bazan iya tuna last time da mukai waya
da ita ba, nasan lokacinda Zanzo nan Potiskum na kirata bata dauka ba nayi mata text se tayi min reply
akan Allah Ya kiyaye. Naji haushi sosae ba Dan kadan ba, kowa yasan yadda nake da Rayhana, kaf cikin
cousins dina babu wadda nake so close to kamar ita ba. Dauka nayi tareda mata kirarin da na saba
"Manya mata, Uwargidan Abdul. Yau kin tuna Sister kenan?"
Dan Murmushi tayi tace
"Da na manta dake ne? Kece kika manta Dani, kin samu Wasu kin yadda ni "
Zama nayi sannan nace
"Haka dai kikace, ai naga kinfi karfina tunda Kinyi aure, ni kuma se Yan mata Irina, Kinsan Yanzun Kwarya
tabi Kwarya ne. Kinga laifina?"
"Kiyi hakuri dan Allah, nasan ban kyauta ba amma Asma'u bari na Baki shawara, Kinsan wani abu?"
Kaina na girgiza Kamar tana ganina, tace
"Take your time, don't rush! Aure worth not rushing. Wallahi birgeni kike, inajin inama ni ce ke. Saboda
Bakiyi aure ba shi ne kike da option Asma'u, idan kikayi aure babu wani option, the only thing shi ne
tunanin yadda zakiyi saving aurenki. Nasan zakiyi tunanin me ya faru? Ina soyayyar take? "
Se tayi dariya sannan ta cigaba da fadin
"Babu! Ta kare. Daga ranar da aka daura aure shikenan, kun gama Kinsan me ya rage MUTUNCI, idan
yana ganin mutuncinki shi kenan. Nikam ni dashi munsan babu mutunci tsakanin mu, na zubar dashi tun
a titi. Ban bashi Kaina ba amma Kinsan sex talk, sex chat shi mukai, to me ya rage, I always brag cewar
practical kadai ya rage bansan hauka nake ba, Abdul ya