Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
vib din wayata, bansan yaushe rabon da naji an kirani past 10 so da mamaki na bude idona
tareda mika hannu na cira wayar, take idanuna suka bude ganin number da take kira, Dr Kwaccido na
ayyana a raina at this time, kifar da wayar nayi inajin yadda ilahirin jikina ya mutu, ina ayyana me yasa
zai kirani, wata zuciyar tace just to check on you, kaina Na girgiza na ba tareda na yarda da uzurin da
zuciyata ta kawo ba. Amma se na samu kaina da kasa nutsuwa, na janyo wayar na kalla 1 missed call, na
danyi tsaki ina mitar har yaushe zaayiwa mutum call daya as if baa damu ba. Haka na gama yan mitocina
na bude wayata ina kallon pictures dinsu Amalin Adda Habiba sunyi birthday itada Aarif last week.
Washegari bayan nayi sallar asuba dake friday ce hakan yasa ban bar kan praying mat din ba har seda na
karanta kahfi savoda nasan idan na bar gurin ba lallae nayi ba, ill be much occupied. Ina kammlawa na
mike anan wayata ta katse min hanzari, ganin number seda zuciyata tayi fluttering, it kept jumping har
hakan ya bani tsoro, but ya zanyi dole nayi picking call din saboda banda uzuri. Dauka nayi murya can
kasa nace
“Good morning sir”
Manly muryar nan tashi me saka naji waves electrons cikin jikina ya amsa da fadin
“Morning Asmau”
I can swear akan ban taba jin wani ya fada Asmau so correctly kamar shi ba, kowanne harafi seda aka
bashi hakkinshi, har seda naji ina bukatar nayi ta jin shi yana kiran sunan.
“Ya jikin naki?”
Dan murmushi nayi nace
“Yayi sauki, Alhmdllh”
“Alhamdulillah, zuwa karfe biyu zan wuce kano, ki zama ready zamu tafi tare”
Baki bude na tsaya ina tunanin abinda yace min, seda ya kara maimaitawa kafin nace
“Sir zan fara call gobe, so bazan samu damar zuwa ba and thank you”
“Na rigada nayi arranging yadda zaayi, ya kamata ki huta saboda ciwonki stress ne”
Se na kasa musa mishi haka mukai sallama bayan yace zai aiko min breakfast sannan nayi bacci kafin
time din. Nidai na rasa tantance me hakan ke nufi na kuma kasa fahimtar inda zuciyata tasa gaba da
kuma wanne tarba tayiwa alamarin. 8am na bugawa aka kawo min abincin, cikin basket aka jero shi,
messenger daya kawo na bashi 500 yana ta godiya ya tafi. Chips ne cikin bowl se farfesun kayan ciki
shima a bowl, tea me kauri cikin wani karamin flask. Gefe leda ce a aje na bude tareda ciro abinda ke
ciki, rose flower ce hade da greeting card, mamaki sosae ya kamani na bude greeting card din naga na
get well soon ne, a kasa yayi rubutu cikin rubutun da ban taba kawowa ya iya ba kasancewar kowa yasan
handwritings din Doctors bashida kyau amma yadda yayi rubutun kamar calligraphy lettering style yayi
amfani dashi.
Come on, get back on your feet and continue that gorgeous smile of yours. Quick Shifaaa Cara Mia!
Shine abinda ya rubuta, zuciyata nasan dama is froze, dan tunda Salis ya betraying feelings dina shikenna
na daskarar da ita, ga mamakina wannan kalaman nashi take suka raga raga da wannan kankarar, wani
bugu da zuciyata ta shiga yi har seda nayi tsoron kada a samu over extension. Jikina yayi sanyi na kalla
rose 🌹 din na shafa na shinshina a karshe na rungume ta a kirjina ina adduar Allah yasa daga shi ne.
Greeting card na dauka na kara nanata rubutun ina bin kowacce kalma daki daki, komai na fahimta
banda wannan cara mia din kuma babu me amsa min. Abinci kadan naci sega kyaftun tayi ta ihu tana
murna tana fadin
“Yarinya kin saka yan maza a gaba fa, kinyi kamun full package”
Se na samu kaina da fara yarda da zancenta, kodai so na yake, ko dai......haka nayi ta tunanin kafin can
bacci ya daukeni se wajen 12pm na tashi nayi wanka na hada kayan dazan bukata sannnan na yi sallah
na karasa abincin da na rage na wanke na kife kafin na fara neman kaya. Ni dama ba maabociyar
kwalliyya bace dan powder ma se kayi da gaske nake siya hakan yasa na zizara khol tareda shafa charpet
kan tattausan lebena da ya fara bushewa har fata na neman dagowa. Dana kalla madubi se naga nayi
kyau daidai yadda ya kamata. Wani lace na dakko me laushin gaske irin vapers dinnan ne. Background
din Coffee ne se designs din suka tashi milk da zaren gold a jiki. Skirt da riga ne nasa na daura dankwali
tareda dakko matching veil da takalmi, har na manta last dana nutsu nayi shigar arxiki. 1:50 daidai wayar
shi ta shigo akan yana jirana, kara gyara zaman veil dina nayi sannan na dauki abinda zan dauka na fita.
Yana tsaye gefen motar yayi shigar da ban taba gani ba, yana cikin farar shadda ta zarce ayi masa coffee
aiki, kanshi sanye da zannan bukar yayi kyau very charming. Dake quarters din namu babu mutane
yawancin an tattafi weekend masu aiki nayi yasa yake tsaye shi daya. Back seat nasa kayan sannan na
shiga gefenshi danshi tunda na kusa karasowa ya koma ciki ya tashi motar. Tunda Na gaisheshi ya amsa
ban kara ko tari ba haka shima se gudunshi da yakeyi, seda mukaje wudil ne ya tsaya karbar document ni
kuma na samu saken kiran kyaftun na mata sallama. Yana dawowa ya kalleni tareda fadin
“You look disturbed, akwai abinda zan taimaka miki dashi?”
Cikin sauri na karkada kai alamar aa tareda lumshe idanuna ina shakar kamshin turarena nashi da kuma
car freshner da ya saka, ga sanyin AC. Yanayin was so romantic. A hankali naji waka ta fara fita cikin
speakers din, hannunsa yasa yayi increasing volume din tareda fadin
“Shirin yayi yawa, enjoy please”
🎶I’ve been looking for you everywhere, I’ve been asking god when I’ll found you dear? I know some
times last days where you least expect. But I’ll be patient i go wait, wait for you my dear. wherever you
are, you have my heart, my darling take me yes I’m. I’ll be loving you from now till i found you my love. I
hope say you like me d way i be, i go dey wait for you day and night dear future wife. 🎵
🎤When I need you will you be there my dear? I’ll make silly mistakes please forgive me dear, we have a
long a way to waka, hold my hands my dear. Wherever you are you have my heart my darling, I’ll wait
for you day and night dear future wife.🎷
Tamkar kada wakar ta kare haka naji, idanuna na bude tareda kallon sadhin shi, murmushi ne kwance a
fuskarshi wanda tsabar yadda ya kayatar dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi:
“Nayi kyau ne?”
Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani.
Ayshatuuuu
[6/13, 9:52 AM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻
_THIRTY SIX_
✍🏻 *SHATUUU❤*
_Jakadiyar kainuwa_
💖Shatuuu095@ wattpad
**بسم الله الرحمن الرحيم
*____________________________________*
*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
Har kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu
kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau
se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace
“Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan”
Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace
“Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?”
Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda
fadin
“Monday very early zanzo mu tafi”
Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude
kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni.
Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga
inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da
yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu
kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada
‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.
Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma
duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen
Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace
“Ummaah barka da gida”
Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace
“Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS”
Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace
“Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta”
Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko
kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka.
“Ya A’isha da halima da me gidan?”
Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani
muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta
daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da
Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan
iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up
the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar
rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani
tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta
tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata
tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana
ringing and it was him calling, haka nan na karasa jiki a sanyaye na dauki wayar tareda karawa a kunnena
nace
“Barka da dare Sir”
“Barka dai Asmau. Ya saukin jikin?”
Se dana kalla kaina kafin na amsa masa da sauki se kuma mukai shiru dan nidai bansan me zance msa ba
kuma baya son godiya. Hakan yasa nayi shiru. Se can yace
“Kiyi bacci and ki tabbatar kinci abinci”
Kamar wata doluwa haka na shiga gyada kaina in agreement amma sede bama gani na yake ba balle,
seda yace
“Huh! Asmau?”
Sannan nace
“Inshaaa Allah Sir”
Daga haka mukai hanging, wani irin raruma nayiwa wayar taredq rungume ta a kirjina inajin wani farin
ciki marar misaltuwa. Murmushi kuwan from ear to ear kamar bakina zai yage. Can kuma na kashe wutar
tareda yin addua na kara lula duniyar tunani a haka daddan bacci ya daukeni, it was peaceful dan ko
mafarkan da nayi where of love. Dan haka da asuba dana tashi komai lafiya lau jikina ba wannan rashin
kuzarin se ma wani karfi da nake ji. Hakan ya bani mamaki amma a kasan zuciyata nasan menene nasan
dalili. Ina idar da sallah na janyo babban quran dina na fara tilawa a kalla nayi izu daya kafin nayi azkhar
lokacin tuni gari ya waye hakan yasa na gyara dakina na shiga wanka. Ina fitowa na zura wata morning
gown ta wani silk purple yadi. Kaina na zura hula sannan na tafi kitchen.
Na jima tsaye a jikin working surface ina karewa kitchen din kallo wanda a zahiri kenan amma a badini
ina tuannin bidirin da aka sha a kitchen din, tun daga Yaya mukhtar down to Yaya Suleiman.
Kowannensu it started at this very place. Ajiyar zuciya me nauyi na sauke ina kara kallon guraren tareda
saka hannuna ina tattabawa wasu nayi murmushi a haka na kashe time din da bansan iya adadinshi ba.
Se can dana fara jin motsin yan gidan sun tashi sannan na dukufa fara aiki. Na kusa gamawa Mama da
Asiya suka zo muka karasa na wuce na gaida Inna sannan Abba da Ummaah. Muna kammalla breakfast
na koma daki na dudduba wasu soft copy pages da aka turon akan Breast cancer da Cervical cancer. Ban
wani dauki time ba na gama na janyo system dita na fara aikin da na saba wato kallon korean movies,
wani Love In The Moonlight.
Gaba daya na sakankance ina kallona naji an turo kofar dakin, normally mun saba indai zaka shiga dakin
koma waye seka yi knocking da sallama kafin ka shiga. Hakan yasa na dago da sauri tareda pausing film
din, mamaki sosae ya kamani ganin Nadia, its been long da naga kafafunta a cikin gidanmu kuma
dakina. Mikewa nayi ina sakin murmushi nace
“Nads manyan mata, sannu da zuwa”
“Yawwa!”
Kawai tace min se ban wani damu ba tazo ta zauna nace
“Bari a kawo ruwa, yau akwai hirar yaushe gamo kenan”
Na fada ina kokarin tashi daga gefenta, hannunta tasa ta rike nawa, hakan yasa nayi saurin kallonta kafin
nayi magana tayi beating dina to it tace
“Bashi ya kawo ni ba. Kina kallon yanayi na kinsan ba ruwa nazo sha ba. Gargadi nazo nayi miki, mijina
Suleiman nawa ne ni daya kinganshi yafi karfin wadda tayi kwantai ta gama aiki cikin kartin maza irinki.
Saboda kin kasa auruwa you decided kizo kimin snatching miji? Kul dinki!”
I was dazed, confused and amazed! Tunda ta fara magana nake kallonta da tsananin mamaki wanda ya
kasa boyuwa ya fit baro baro akan fuskata. Tana gama fada ta hankadar da hannuna ta mike da niyyar
fita, nasa hannuna na riketa ina kallon idanunta wanda na rasa meye a cikinsu amma nawa firgici ne a
cikinsu
“Ta yaya zaki fita baki fahimtar dani abunda maganar ki take nufi ba, Nadia ni ce fa”
Hannunta ta kwace kamar wata damisa, cikin daga murya tace
“Se me dan kece? Ai nasan ke dince shiyasa na sassauta miki, tunda bakiji kunyar kawancenmu kin kai
idanunki kan mijina ba bazanji kunyar na miki gargadi ba. Me mijina zaiyi dake tsofe tsofe dake.....”
Ban barta ta karasa ba na wanka mata mari ina wani irin huci, i was boiling in,
“Kada ki kuskura Nadia.....”
Se na dunkule hannuna na kasa karasawa, zuciyata na fada min Nadia ce fa, wannan dinnan, kin manta
ta? She doesn’t deserve this. Bana tunanin akwai circumstance da zai zo na manta matsayin rayhana da
Nadia a rayuwata, sudai zasu iya mantua amma ni nasan alheri bana mantawa dashi. Ai tana ganin nayi
shiru ta fara zage zage wanda ya janyo hankalin Inna da Ummaah dasu Mama, su basu san ta shigo bama
dan kowanne na dakinsu. Ummaah tazo tana fadin
“Nadia me ya faru? Me ya hadaku?”
Wani mugun kallo tayiwa Ummaah tace
“Ki fada mata ta fita harkar mijina, mijina yafi karfin ta shi ba tsaranta bane, idan ba haka ba......”
Gaba daya har Inna muka tsaya muna kallonta da tsananin mamaki, kuma shirun da mukai mata baisa
tayi shiru ba sema kara daga mirya da takeyi a haka Abba ya fito ya samemu a tsatsaye, Nadia tana ta
wulakanci ita me miji. Kallonta yayi yace
“Kiyi hakuri ki koma dakinki, ni na miki alkawarin Asmau bazata taba auren mijinki ba, itama nata yana
nan tafe da izinin Allah”
Kawai tana bude bakinta se cewa tayi
“Better!”
Ta juya ta fice, tana fita naji wani irin yanayi me wiyar na fada ya lullubeni, kaina kamar zai tsage gida
biyu, idanuna da suke neman lumshewa na bude da karfin gaske nace
“Abba me ya faru”
Ashe yaya Suleiman ya samu Ummaah akan yana sona zai aureni tace masa aa kar ya manta abinda ke
tsakanina da matar shi, bai jiba ya samu Inna ita kuwa kowa yasan yana daya daga cikin favorite jikokinta
hakan yasa tayi naam da maganar. Kallon Inna nayi kamar zan daketa idanuna se hawaye ke zubowa,
gaba daya na manta Inna bata jin turanci nace
“For goodness sake, Inna why will you do this? Danme? Kinsa yarinya yar cikinku tazo tayi muku fitsara.
Saboda banyi aure ba, kun taba ganin macen da takai age dina bata damu tayi aure ba, in bai zo ba zan
fita titi nayi shelar wa yake sona? Waye zai aureni...!”
Wani abu naji ya tokaren makoshi hakan yasa na juya dan tafiya daki amma wani mugun jiri ya kwashe ni
se gani a kasa, dukkansu suka yo kaina dan tashina amma na mike seda Abba ya rikeni aka kaini har daki
daidai shigowar yaya Suleiman a birkice, Abba yace baya son yaji komai kawai yazo ya dubani. Yana
dubani ya daura min drip se na lumshe idona kamar me bacci hakan yasa suka fita dan na samu na dan
huta amma maimakon na mutsu se kawai na tashi na hada kaina da gwiwa na dinga kuka, a raina ina
ayyana yadda rayuwa ta juya, ni Nadia tazo har guda ta ciwa mutunci akan mijinta? Su Ummaah basu
tsira ba. Asiya ce ta shigo ta sameni a hakan ta zauna tana ta lallashina har nayi shiru sannan ta dauki
wayata dan nace duk wanda ya kira tace banda lafiya.
Misalin karfe bakwai na dare nayi sallar maghrib, na dan nutsu ba kamar da safen ba shima Abba da
Ummaah suka zo sukai ta lallashina tareda nuna min haka rayuwar take, we must expect worst from life,
it’s a trial which are never meant to be easy. Wannan ya karfafa min gwiwa har nasha tea sannan nayi
wanka amma idanuna kadai zaka kalla kasan kodai ina cikin damuwa ko banda lafiya.
“Yar fara tashi maza maza ki canja kaya kizo parlor kinyi baki”
“Baki?”
Na maimaita ina kallon Ummaah data bude wardrobe dina da alamun kaya take nemo min kaya, mikewa
nayi jin bata bani amsa ba nace
“Ummaah su waye?”
Juyowa tayi tana kallona kafin tace
“MD dinku ne”
Idanu na zaro cikeda mamakin abinda ya kawoshi, taba ni Ummaah tayi tace
“Tun dazun sukazo so kiyi sauri kisa wani abin kizo”
Idanuna Na lumshe ina jin wani mintsini da ale min a cikin zuciyata na farin ciki, kallon kayana nayi ba
tareda daukar ko daya ba na rufe na nufi inda Abayas dina suke na samo wata simple royal blue abaya
wadda egde dinta aka mata ado da wani silk blue material yayi kyau. Mayafin na yafa bayan na wanke
fuskata na fito parlor Amma maimakon na ganshi se wata yar karamar yarinya wadda shekarunta bazasu
wuce shekara biyar ba, sanye take da jeans se top an saka mata hula kalar top din. Wasa take da throw
pillow din kan cushion din da take kai, gefenta wata middle aged mata ce tana zaune da waya a
hannunta amma kamar da suke da wannan yarinyar ta baci. Hakan yasa naji hankalina ya kwanta daga
tantamar da zuciyata take. A hankali na karasa inda matar