Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fara Yar Shehu Complete Hausa Novel by Shatuuu

Author :  SHATUUU Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 23

42K to 45K   out of 67.2K words

naji ya tabbatar min it's a no kenan. Hakan
yasa na dangana ba tare da na kara masa magana ba. Wani sati na dawo na tarar da Ummaah ta cika
fam kamar zata fashe dama wannan mood din kam ai na saba dashi. Tunda naga haka na kama kaina
tareda jan mutumcina. Washegari inadakin inna muna hira ta aiko Asiya akan ta kirani. Ina zuwa na
ganta a zaune gefen gado tana ta karkada kafa, zama nayi kan carpet nace

"Ummaah gani"

Key din motarta ta mika min tace

"Dakko hijab dinki zamu fita"

Babu musu na mike hannuna rikeda key din na tafi dakina, dama atamfa ce jikina dinkin skirt da riga so
kawai se na dauki hijab coffee dake atamfar da coffee jiki, shoe rack dina na duba na dauki wani flat milk
vine se purse sannan na fito , ganin tana jirana yasa ko Inna banyiwa sallama ba kawai na wuce gaba
tana bayana. Seda nayi warming motar sannan nayi addua kafin muka fita. Kallonta nayi tana ta danne
danne a wayarta nace
"Ummaah ina zamuje?"

Dago idonta tayi ta kalleni, then ni kuma na rigada na maida hankalina akan titi tace

"Gidan Hajiya Zakiyya zaki kaini"

Seda naji kaina ya sara min baa taba matar da bana so a kawayen Ummaah ba kamar wannan matar,
tana daya daga cikin masu zuga Ummaah akaina. Babu yadda na iya haka na dauki hanya amma bakina
banda neman agajin Allah babu abinda nakeyi nasan shi kadai yasan abinda nake going through kuma shi
zai kawo min dauki. A hanya na tsaya a filling station nayi mata full tank sannan muka karasa gidan. Ina
parking nayi wining glasses din sannan muka fito, tana gaba ina baya muka shiga gidan, sunada kudi
haka kishiyoyinta uku kuma ita ce ta biyu amma kana shiga zaka san ragamar gidan a hannunta take ita
take juya kowa har shi mijin so bana son wannan kawancen. A katon parlonta muka zauna sannan yan
aikinta suka cika mana gaba da abinci kafin taxo, tana shigowa tazo ta rungumeni tana fadin

"Daughter da bata zuwa gurin mamanta ko"

Dan murmushi nayi nace

"Aiki ke hanani wallahi amma ai bazan manta Mami ba"

Zama tayi suka gaisa da Ummaah ni kam na bude exotic na tsiyaya na sha bana son tace naki cin komai.
Ina nan zaune inaji suna magana kasa kasa se kuma can Mami tace min

"Asmau jeki daki ki jiramu"

Mikewa nayi na tafi dakin tareda crashing akan gadon na dauki wayata ina random searching da ban
masan me nake dubawa ba, baki daya hankalina yana parlon. Har nayi waya da kyaftun ta dan dauke
min kewa sannan ta kara reassuring dina sannan naji hankalina ya kwanta. Wata Nannyyy ta shigo tace
min nazo inji Ummaah. Mikewa nayi na gyara zaman hijab dina sannan na fito kwatkwata idona bai ma
lura da mutumin dake zaune ba seda na zauna sannan na ganshi a zaune, mutumin yafi kama da boka
gaba dayanshu a birkice yake gashi fal fuskarshi yana zaune se karkada kafa yake, ga wani wari dake
tashi kuma nasan tabbas daga jikinshi ne, dan lokacinda muka zo parlon banda kamshin lavender babu
abinda yake, i love the scent of lavender so duk inda naji shi se matar ta fado min saboda kamshin
gidanta na dindin kenan.

Abu daya da bana tolerating duk kawaici na shi ne wari bana iya jurewa, ko minti daya ban cika ba kawai
se naji cikina ya fara kadawa zuciyata tana tashi, i was completely nauseous. Kallon Ummaah nayi zanyi
magana kawai naga mutumin yayo kaina gadangadan, fusace na mike tare da ja da baya ina muzurai,
instead ya tsaya se naga ya nannada malum malum dinshi yana neman kai hannu jikina,

"Karka taba ni, Ummaah kina kallo?"

Kamar bai ji ba haka ya dinga bina har nakai bango, idanuna na runtse bakina yana ambatar sunan Allah
kawai se naji hannunshi yana shafa fuskata, wata muguwar kara na saki tareda zubewa a gurin
sumammiya. Bansan me ya faru ba i don't even know, na dai san daga baya wai ashe me maganin aljanu
ne aka dakko shi saboda ana tunanin aljanu ne suka kama ni shiaysa na ki nayi aure. A gado na sameni
lokacinda na farka ni kadai, koda na tashi se na fara jin kaurin tukake, tashi nayi na zauna anan naga
yadda hayaki ke tashi wai duk ni akewa turare, gaba daya zuciyata tayi min nauyi, kirjina banda zafi babu
abinda yakeyi. Tashi nayi zan fita naji an maida ni gadon, se lokacin na lura da Ummaah da Mami da
kuma bokan dan a gurina he's never near Allah wannan mutumin tsubbu yake. Inaji ina gani haka ya
kwara min wannan ya zuban wannan, idan nayi ihu se yace aljannun ne hakan yasa kawai nayi shiru.
Haka ya gama ya bada wasu layu da itatuwa da saiwoyi da wasu kulle kulle da zaa binne. ita kuma
Ummaah se godiya take mishi, kuka ne ya kwace min, kukan takaici, kukan bakin ciki, kukan tausayin
kaina, kukan rashin madaga, se naji duk na sare naji kamar ni rahama ta sauka daga kaina. Nafi awa ina
kuka tun Ummaah na cewa aljanun ne har naga hankalinta ya fara kaiwa kaina, ganin haka yasa Mami
tace nayi wanka, kaina na girgiza ina cigaba da razgar kuka abuna.

Se laasar bayan nayi sallah sannan muka tafi, fuskata tayi jawur kada ma idanuna suji labari. Koda muka
tashi tafiya kasa driving nayi saboda yadda jikina ke shaking. Dole haka mami ta bada driver ya kaimu
gida sannan ya juya. Dakina na shige na kulle tareda saka key na datse, banma hau gado ba anan jikin
kofar na silale a baki na dinga kuka kamar raina zai fita, ban taba tunanin haka ake bakin ciki ba, nayi ta
kuka har bansan iyakar lokacin dana dauka a wannan gurin kuma cikin wannan halin ba. Time to time
nakan ji ana min knocking amma ko a jikina banma ni da niyyar tashi.
Ban kara fitowa ba se washegari, dake na saba dama ba fitowa nake sosae ba tunda zaman gidan ya
zama tamkar a living hell hakan yasa na koma zamana kawai sede aiki ya fitar dani. Ummaah tun daren
take kirana a waya amma naki dagawa saboda bansan abinda zance mata ba. Seda nayi wanka sannan
na zura wata purple abaya da stones a jiki se walwali take. Comb na dakko na taje kaina na tufike da
karamin ribbon sannan na shafa balm a lips dina da yayi ja, kallon fuskata nayi har lokacin bata ware
sosae ba ta kumbura saboda rashin bacci da kuka. Ummaah na zaune a parlor hankalinta dukka ta
tattara shi akan kofar tawa, ina fitowa idanuna ya sauka a kanta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,
gaisheta nayi ta amsa jikinta a sanyaye ni kuma na wuce kitchen. Ina cikin dama kunu naji shigowar t,
kujera ta ja ta zauna sannan tace min

"Asmau kinada hankali kuwa? Kinsan yadda kika tsoratar dani ki shiga daki ki kulle ko a jikinki? Kinsan
banyi bacci ba?"

Bance mata komai ba na cigaba da abinda nake, jin nayi shiru yasa ta dawo gabana tareda daka min
duka tace

"Bakya ji ne ?"

Na kyafta ido se hawaye, raina a mugun bace nace

"Ummaah me zance miki? Ya kike so nayi? Nidai nasan this wasn't my mother, uwata ba haka take ba
wani ya canja min ke."

Sororo tayi tana kallona kafin tace

"Saboda na kaiki gurin malami shiyasa zaki fadi haka?"

Kaina na girgiza nace
"Ummaah saboda banyi aure ba shi ne kike kokarin saida imaninki, ke kanki Kinsan wannan mutumin is
never near malami, kawai dai kin bi son ranki ne...."

Wani bugu ta kaiwa bakina hakan yasa nayi saurin rufe bakin, fita tayi ni kuma na zauna na dasa sabon
kuka.

Ayshatuuuu[6/7, 5:05 PM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻

_THIRTY TWO_

✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_

💖Shatuuu095@ wattpad

*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬
*____________________________________*

*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da naji ya tabbatar min it's a no kenan. Hakan

Ayshatuuuu

[6/9, 11:53 AM] Shatuu Kwalam: 🧕🏻 *FARA 'YAR SHEHU* 🧕🏻

_THIRTY THREE_

✍🏻 *SHATUUU❤*

_Jakadiyar kainuwa_

💖Shatuuu095@ wattpad
*‫*بسم الله الرحمن الرحيم‬

*____________________________________*

*KAINUWA
✍🏼 WRITERS ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

A fragile heart was broken before, i don’t think it could endure another pain, a piece of voice from deep
inside that calling you to make you relaxed!
Wannan kwanaki biyun dana kara sun zame min kwanakin da bazan taba mantawa a rayuwata ba, tunda
nake addua i was never specific sede nace Allah ya zaba min mafi alkhairi, a ganina hakan shi ne daidai
amma tunda naga an fara haka yasa na dukufa adduar Allah yasa nayi aure cikin kankanin lokaci. Ana
gobe zan tafi da daddare na dawo daga gidan yaya Halifa saboda gidan babu dadi, daga ni se Asiya se
ummaah and I couldn’t, i was suffocating hakan yasa na tafi tun sassafe, Inna ade da Abba sunje umra ,
jikokin gidan kowa yana gidansu hakan yasa naji zaman ya isheni. Mun jima nida yaya Halifa ina kora
mishi bayanin halin da nake ciki. To me zaiyi shi dinma Ummaah ta haifeshi, highest thing shi ne ban
hakuri kuma shi din ya bani, ya nuna min Allah yana sane dani kuma komai kaga ya faru to da saninshi.
Those words kept me going.

Kwana na biyu da dawowa daga kano, na koma aiki na saboda damuwar ma batada amfani. Da yamma
ina kwance a daki ba call nake ba so bayan na gama abinda zanyi na fita kasuwa nayo cefane na dawo .
Ranar i was craving for dambun shinkafa. Haka na zauna na daura a cikin steamer na koma na fara soya
kazar da zanyi pepper chicken da ita. Ina nan zaune na saka wani chilled chapman a gabana ina sha se
naji message ping, mikewa nayi da sauri na isa ga wayar tareda tapping message din

A 40year old null para with a diagnosis of ectopic pregnancy and ? Typhoid perforation. booked for ex-
lap. Prepare for emergency ex-lap ASAP.

Na karanta yafi sau shida ina kara duba number data turon da mamaki, wannan ai aikin general surgeons
ne kuma ma idan ance saboda ectopic dinne I’m not on call. Mikewa nayi na kashe steamer sannan na
juye abincin cikin warmer se kadan nasa a plate na saka salad da naman na fara ci. Banma kara komawa
takan message din ba saboda a tunanina mistake akai. Seda na gama na gyara dakin sannan naga call din
Dr halima yana shigowa, hannuna na goge jikin towel na dauka, ko gaisuwata bata amsa ba tace

“Asmau bakiga message ya shigo wayarki ba?”

“Na gani, I thought mistake ne shiyasa na share”

Cikeda damuwa tace
“This is unlike you, kije yanzun patient din tana Female surgical ward kiyi reviewing dinta”

Kaina Na gyada nace

“Amma bani bace da call bafa”

“Just follow orders kinji, nima order aka bani”

Katse call din mukai inata bubbuga kafa da zumbura baki hakanan dai na samu na dakko kayana na
kullum yau pink nasa wando da riga na soft cotton yadi na saba back pack dita na fita. A ward na sameta
mugun restless, ciwo yana damunta hakan yasa nayi order a mata allura kafin na kira a kawo

15 / 23