Author : SHATUUU Category : African Stories & Novels
kalleni yace ban cancanta na zama Uwa ba,
Abdul ya mareni... "
Se tayi Shiru nasan ciwon abin takeji, Nikam dama already na daskare a inda nake zaune, kasa Ko
lallashinta nayi dukda nasan kuka take. Se can tace
"I'm sorry Asma'u, Abdul! Ban taba tunani ba, a gabana Zaiyi waya da budurwa kuma ban isa nayi
magana ba, duk Menene? Babu mutunci, had it been akwai wallahi bazaiyi haka ba. Shiyasa nace miki
Mutumcinki should be your number one priority, kada Ki zubar dashi ko Yaya nene. Nasan it feels a
burden baki labarin nan, amma ke kadai zaki fahimceni, you the only one zaki bani kafadarki nayi kuka
akai. Nagode sosae for always being there for me Asma'u "
Bata jira abinda zance ba kawai ta katse call din, kaina na kwantar akan table din, gaba daya jikina Yayi
sanyi, I'm dazed and confused, saboda indai abinda yake faruwa a auren then me yasa mutane ke
damuwa akan kayi. Se wata zuciyar tace min, Tun ranar gini Tun ranar Zane. Dama daga curtship komai
ke farawa, daga nan mutum ke Fara Gina rayuwar aurenshi, su basu bi hanyar daidai ba shiyasa, tunda
musulinci bai bar komai a rufe ba, everything is open and ignorance is not an excuse, shiyasa Hatta
yadda bawa zai tsugunna a bayi seda Manzon Allah SAW Ya koyar, so idan bamu yadda yace ba, ta Yaya
kua zamu ga daidai, kullum aure ake amma auren mutuwa yake saboda su kansu building blocks din
auren ba haka akace ayi ba.
With a heavy heart, Haka na fito zuwa daki ilahirin jikina a sanyaye yake Kamar an zuba min ruwan
Kankara a jikina. Ina shiga na cire lab coat na aje sannan na Kwanta Kan carpet din ina tunanin yadda
rayuwa take, iyaye sunce kayi aure, kawaye da Yan Uwa sunce better take your time. Allah Ya zaba mafi
alkhairin kawai!
Ban kara kiranta ba se Washegari, na kirata mun jima muna magana, na bata shawarar da nasan zai
taimaken ta, a Haka mukai sallama. Karfe hudu na yamma Hajiya Kyaftun ta karaso, nasan makotana se
sunce yau Likita ta zama mahaukaciya, kamar Yara Haka muka dinga ihu muna Rungume da juna. Seda
muka gama sannan tace
"Ke Twin sakeni bayan gida nakeji fa. "
Harararta nayi nace
"Kedai ko Fara haka ta ganki ta kyale! "
Wuceni tayi ta shige toilet se ni ce na kai mata kayan ciki, Tana fitowa muka hau kan Abinci munata hira.
Muna gamawa Habibinta Ya kira, hakan yasa na mike na wanke tray din sannan na dawo Ina duba Peds
Meds dina, akwai Wasu conditions da nake son updating Kaina dasu. Seda ta gama sannan ta miko min
wayar, mun Dan taba hira dake mun saba dashi kafin mukai sallama dashi. Kamar jira ake na aje wayar,
Salis Ya kirani, dauka nayi bakina dauke da wani sihirtaccen Murmushi, ni Kaina bansan Inayi ba,
unconsciously kawai.
Ina aje wayar Kyaftun tace
"Twin waye ya kiraki, hope dai ba wannan useless Salis din bane? "
Bata fuska nayi nace
"Kai Twin, Har wani ma Useless. Shi ne Menene? "
Wani mugun kallo Tayi min tace
"Seriously Twin? Adda Sa'ada ba tace ki rabu dashi ba? "
Idanuna na zaro nace
"Ya akai kika sani? Ita ta fada miki? "
"Of course! Ita ta kirani ta fada min, saboda tasan taurin Kanki ba yadda zakiyi ba, ta fada min abinda ya
faru, nayi mamaki, nayi Dana sanin zama hooker din. "
Tabe Baki nayi nace
"Kinga Twin, wayarshi ce ta lalace, ya rigada ya fada min reason, kinga ya zaayi na rabu dashi? "
"Gaskiya kam! Amma tsaya kiji saddest truth sooner or later tabbas Salis zai yaudareki......"
Kallonta nayi raina a bace nace
"Twin!"
Wata muguwar harara ta sake min tace
"Dallah rufe min Baki, na fada Se ya yaudareki, nasan kina sonshi amma idan kiga namiji yana irin Haka,
aje son kike, kice ku rabu at least you save your pride, ko ba komai you will not be shattered much. "
Kaina na girgiza nace
"Twin Ina sonshi Bazan iya ba"
Batace komai ba ta Mike ta cire kayanta ta shiga wanka, ta banni a zaune ina tunanin yadda zanyi, babu
Wanda zai fahimci yadda nake, yadda zuciyata take. Ni dinnan I've a fear of losing people, bana son
rabuwa da mutane, na fison su zauna a tare dani. Kuma yadda nake kallon rayuwa is different from
yadda mutane suke kallonta, my views are simple about life, a nawa ganin duk Wanda ya shigo
rayuwarka to akwai reason kuma idan lokacin tafiyar mutum Yayi, ko kana so ko baka so, dole mutum ya
fita. Deep down nasan abinda kowa ke fada min gaskiya ne, amma zuciyata fada min take tunda Ina
addua babu amfanin challenging life, I should embrace whatever comes my way a ganina Allah is doing
his miracle.
Tana fitowa tace naje nayi, Tun ina cikin toilet naji ana kirana, da sauri na fito Naga wayar da nake call da
ita ne, na manta gaba daya Ashe ni zanyiwa Dr Harris call dinshi. Cikin sauri na shirya muka tafi,
maternity dake can ne kiran, Ina zuwa na Tarar da uban aikin dake jirana, tareda su mukai aikin, mutum
biyu nayi booking for emergency CS, Ina gama documenting na dubi Nurse din nace mata
"Sister, zanyi communicating da yan OT, duk yadda ake ciki zaki jini. "
Kanta ta gyada tace
"Babu damuwa"
Tare muka fita da Kyaftun tace min
"Nikam a ina zaki internship dinki? "
"Da a AKTH zanyi amma Se naga Dama zanyi bonding a Jigawa, Shekoni kawai Zanje nayi"
Kanta ta gyada tace
"Kice zamuje muyi confusing mutane "
Dariya nayi dan itama nan tayi applying. A Haka se yamma na samu Kaina, shima a gajiye na koma, naci
Abinci na tafi A&E.
Tafiya ta tafi har Allah ya kawo ranar POP dinmu, nayi farin ciki marar misaltuwa, sede a Kasan raina
inajin tsoron komawa gida, Dan nasan lokacinda na dauka tabbas yazo, na gama Service, wannan karan
bansan yadda zata kasance ba, bansan zanyi winning ko kuwa A'a.
Haka Yaya Halifa yazo da Adda Zannira muka tafi Kano, gaba daya hankalina baya tareda ni. Nasan an
dafa min kafa, Yanzun shekaruna ashirin da biyar a duniya, Nima I need to settle. Ko da naje Naga kauna,
tarairaya da komai, tabbas no place is sweet as home. Kwana na biyu ina hutawa, a rana na uku na kira
Salis, bayan mun gama lovey-dovey talks dinmu nace
"Tohm, kaga yadda duniyar nan take gudu, I can remember yadda muka hadu, shekara daya kenan,
gashi na kammalla service din Kamar yadda mukai alkawari Ina kammalawa zaka turo. "
Dan Murmushi yayi yace
"Kina tunanin na manta ne? Haba Ina sane, naga yaushe kika dawo ya kamata ki huta ko Yaya ne, kafin
kuma muyi Maganar auren"
Kaina na girgiza nace
"Ai na huta, kasan bana son Abba yayi min magana, nafi son tunda Kai kayi aure ka cika da kanka"
Shiru yayi sannan yace
"Kada Ki damu, Anjima zan Je nayiwa Alhaji magana, da Sunyi fixing date zakijini"
Se naji hankalina ya kwanta sosae, daga nan muka cigaba da hirarmu. Da yamma a gidan Adda Sa'ada
tayimin, Dama mundan kwana biyu hakan nan bamuyi waya da ita ba, tana fushin tace na rabu da Salis
ban rabu dashi ba, Nidai hakuri na bata sannan nayi mata bayanin latest development, addua tayimin se
dare sannan na dawo gida. Ko kayana ban cire ba Abba ya turo akan Nazo. Seda gabana ya fadi saboda
tsoron abinda zaice, Haka na wuce Inata Nanata Innalillahi wa Inna ilahil rajiun a cikin zuciyata. Shi daya
ne a parlonshi, gabanshi an yayyanka fruit cikin transparent glass bowl, Se fork ya caka akai, gaisheshi
nayi sannan yace
"Samo wani fork din kizo musha. "
Murmushi nayi na mike na tafi wata cupboard inda utensils dinsa suke na dakko fork, zama nayi muna
sha yana ta bani labarin lokacinda bana gida, wani abin nayi dariya a Haka kawai se ganin empty bowl
nayi, kallona Yayi yace
"Daga tayi shi ne kika shanye Ko? "
Dariya nayi nace
"Abba ai cewa kayi zo kisha "
Kanshi Ya gyada yace
"Allah Yayi miki albarka, Allah Ya haskaka rayuwarki, Allah Ya jibanci lamuranki! "
Cikin sauri nace
"Amin Amin Abba "
Idanuna har sun kawo ruwa, kamar zanyi kuka. Se kuma mukai Shiru kafin yace
"Asma'u a lissafina Yau satinki biyu da dawowa daga Yobe, Dama Kinsan alkawarin mu akan idan kin
dawo Yaronnan zai turo ayi Maganar aure. To lokaci yayi ya kamata ayi wadda zata yiwu"
Ajiyar zuciya na sauke nace
"Abba Munyi magana dashi, yace iyayenshi yake jira suyi fixing rana "
Kanshi Ya Jinjina yace
"Allah Ya tabbatar da alkhairi, "
Envelope ya miko min yace
"Congratulations! My daughter "
Da sauri na bude envelope din, permanent and Pensionable offer ce tawa a hannuna, ga kuma posting
letter zuwa Shekoni. Nayi ta murna Abba yana min dariya. Banma damu dare bane Haka na kira wannan
seven siblings din nawa a karshe na kira Salis na tuna mishi Maganar, amsar daya ce Zaiyi magana dasu
Alhaji.
Ban kara sati biyu ba a kano na tafi Dutse, rana daya mukai reporting nida ita, a ranar aka bani
accommodation akai allocating dina a Medical Team. Haka muka fara aiki babu ji babu gani. Watana
daya a Dutse Abba yace min na tura mishi Salis, na kirashi se yace min Bari Ya fada min gaskiya, akwai
wata cousin dinsa da ake son ayi musu Hadin gida to amma saboda ni yake so shiyasa yaki amincewa, to
Yanzun yana son sorting abubuwan kafin ya tura. Gaba daya jikina Yayi sanyi kawai se nace
"Kaje kayiwa Abba bayani! "
Kashe wayata nayi kawai ban kara komawa ta kanshi ba. Da daddare muna zaune nida Kyaftun take
cemin
"Ya kukai da Salis kuwa? "
Ban boye mata komai ba na fada mata yadda mukai dashi. Batace komai ba ta Mike tacemin seda safe
zataje ta kwanta, nima Bance komai ba mukai sallama. Tana fita Abba ya kirani yace min
"Asma'u kina jina?"
Kaina na gyada nace
"Eh Abba"
"Yawwa, yaronnan Salis yazo dazun, Inna Ade Tazo itama Dan tana ganin ke kika hana yaron Ya turo,
God so kind a gabanta yaron yake ta kamekame. Abinda na lura shi ne yaronnan bai shirya ba, ki rabu
dashi kawai, kina zaune Allah zai kawo miki wani Kinji? "
Idanuna sun cicciko da kwalla nace
"To Abba Inshaaa Allah, Nagode sosae "
Hakuri yayi ta bani sannan muka kashe wayar, tamkar an caka min abu a cikin zuciyata Haka naji, wani
zafi a kirjina Wanda Har bayana seda ya amsa, idanuna tamkar an barbada musu barkono saboda
radadain da suke min, gaba daya na rasa me zanyi? Ina zan saka kaina Inji dadi. The 3rd heart break kilan
kuma zuciyata tabuwa zatayi. Da sauri na dauki hijab na saka na fito zuwa dakin Kyaftun, tana zaune a
kofar gidan, alamun ko shiga ma Batayi ba kenan, waya take ranta a bace, ban tsaya gurin ba na shige
ciki, da mukullin hannuna na bude dakin nata, katifar ta na fada ba tareda nasani abinyi ba, idanuna
sunki barin hawaye suyi cascading Ko na samu naji sanyi da salama a raina. Amma ni Uwar kuka hawaye
ya Juyawa baya, to tunda hawaye dake jikina zai iya disappointing dina Ina ganin ai its normal Dan wani
ya yaudareka.
Ina nan kwance se naji sallamar Kyaftun, a take kuma Se kuka ya kwace min, gefena ta zauna tareda
shafa min Kaina batace komai ba, may be she has already sense abinda ke faruwa. A tunanina nafi
mintina talatin ina kuka Wanda ni Kaina seda na tsorata da irin kukan da nake, I was asking myself me
yasa soyayya bata min adalaci, dukda wannan ne Karo na uku da aka min hakan, amma duk biyun ai ni
nake sonsu, wannan shi ne Wanda ya yaudareni, shi ne Wanda na bawa amanar zuciyata but he ended
up throwing it into a bin.
Kafin wani lokaci zazzabi me zafi Ya rufeni, Dama Haka nake, idan pressure tayimin yawa to response
dina zazzabi ne, Tun Kyaftun na shafa min jikina ta sigar lallashi har ta Fara cemin
"Haba Asma'u! Dan Salis Yayi haka shi ne karshen rayuwa, Yanzun rayuwa ta fara. Ki daina wannan
kukan Haka, so kike kuma kiyi rashin lafiya? "
Nidai jinta kawai nake amma gani nake babu Wanda zai fahimci halinda nake ciki idan ba ni ba, kowa
kawai tausayina zaiji. Kafin asuba zazzabin nan ya wulakanta ni, Dama a dakinta na kwana Dan Haka tun
sassafe ta kira wani Doctor Lamin, suna shiri ita dashi, yazo Ya ganni. Drugs ya rubuta min Wanda zaayi
amfani dasu sannan ya dauki sample Twin ta kai mana Lab. Ranar ban fita aiki ba aka karbo min excuse
duty na zauna.
Kamar wasa Ina tunanin I got to fight this amma na kasa, I was so weak and tired kwakwakran tunani na
kasa. Haka nan nake lallabawa Ina fita aiki amma kullum jiya i Yau, abin ya taba ni sosae da sosae.
Bayan wata daya
Anyi shuffling na koma Obstetric Team, da yamma Ina maternity dake Munada call, aka kawo wata
patient referral case ce. Tareda Nurses din mukai attending mata anan muka gane babyn ne breech,
Gata haihuwan farko so bazata iya delivering babyn, dole we need emergency CS. Nurse din tayiwa yan
uwanta bayanin akan zaayi signing consent kuma zasui donating blood. Ni Ina zaune ina Rubutu sannan
nayi notifying senior doctor na, shi kuma yayi notifying scrubs din. Ina kokarin fita naji sallama tamkar a
mafarki, cikin sauri na juyo ina kallon Wanda Yayi sallamar, shi dinne Salis ne, yana tsaye as always, Cas
dashi Dan gayu, Yau ma like usual yayi kyau, Se naga tamkar an kara Kawata shi ne. Kallon kallo muka
tsaya yi, seda nurse din tace
"Malam me ya faru?"
Kallona Yayi sannan yace
"Are you the Doctor in charge? "
Ban bashi amsa ba se kallonshi da nake kara yi, kada dai ace tunanina Ya zama gaskiya? Kada fa he's here
to sign the consent.
"Me kakeyi anan? "
Na tamabayeahi idanuna sun kasa boye tsanar da nayi mishi, kallona Yayi yace
"Asma'u! "
Hannuna na daga masa nace
"Me Ya kawo ka kawai? "
Gumin kan goshinshi ya share yace
"Matata aka kawo, Nazo nayi signing consent ne! "
Lumshe idona nayi ban kara kallon inda yake ba na dubi Sister nace
"Ina OT, Ina jiranta"
Daga Haka na juya na fita, cikin hanzari ya biyoni yana fadin
"Asma'u please listen..... "
Dan Murmushi nayi nace
"Kasan me ciki management dinta da wuya, saboda ba rayuwarta ce kadai ba, akwai abinda ke cikinta so
ka hanzarta kayi signing, ko kaga fruit of your hard work "
Daga Haka na wuce, kafata kawai nake cillawa, bawai na gama warkewa bane tun can, kawai dai naji
lokaci yayi daya kamata na dawo hankalina, se gashi ya dawo, Ashe aure yayi, a lissafina yaron cikinta is
term kenan, Tun ina Potiskum Yayi aure? Kaina na girgiza kawai na wuce OT, changing kawai nayi naji an
shigo da ita, scrubbing nayi sannan na shiga ciki. Tana kwance lifeless, Dan an rigada an makar da ita.
Itama Fara ce Kamar yadda nake Fara, tana da kyau ga gashi da ya fito ta karkashin cap din aka saka
mata. Na jima a tsaye ina Kare mata kallo, if not because of the oath I took "I'll treat everyone equally,
irrespective of gender, race, religion, ethnicity. I'll render my service to whosoever disregards to
personal affairs....... " Da Bazan mata CS dinnan ba, amma nasan it can't be. Anaesthetic din ne yace
"Dr. Shahada are you alright?"
Kaina na gyada nace
"Yeah! Scapel please"
Ana miko min na yanka ta, I was praying komai ya tafi daidai idan ba Haka ba Ina cikin matsala. God so
kind komai ya tafi yadda akeso na ciro katuwar baby girl Itakuma na dinketa aka maida ta ward. Koda
muka gama lounge na shiga na cikin theater ban ma damu da mutanen dake ciki ba, kawai na samu
cushion din gefe na zauna tareda lumshe idanuna, sosae nayi zurfi cikin tunani. Na jima a zaunen har Dr.
Lamin ya buga min hannun kujerar yace
"Dr. Shahada, kina lafiya kuwa? You have not been yourself these days "
Dan faint smile nayi tareda mikewa nace
"I'm good, kawai yau da gobe ce"
Kanshi Ya gyada yace
"A'isha Tana nemanki a ward dinsu. "
Kyaftun yake nufi, mikewa nayi nace
"Oh, ashe na kashe wayata. Lemme rush"
Handbag dita na dauka ba Wanda nayiwa magana na fice, a kofar theater na sameshi a zaune alamu
jirana yake, dauke kaina nayi saboda banga abinda ya rage tsakanina da Salis ba, komai ya kare. Bashida
bakin da Zaiyi min bayanin komai tunda lokacinda Abba yace na rabu dashi, na kirashi Ina kuka nace ya
min bayanin abinda yake faruwa se yace min na jirashi kada na damu, I didn't give up bayan sati na kara
kiranshi, Se yace min na dameshi, na rabu dashi indai bawai Anyi tying destiny dina dashi ba. nayi kuka
bana wasa ba, anan na fahimci abubuwan da Adda Sa'ada da Kyaftun suke gaya min, it took me more
than days kafin na hakura na daina kuka, na tuhumi rayuwa akan walagigi da take dani, haka na zargi
soyayya da rashin yimin adalci, sede Ina fatan zuciyata bazata kara kaini ta baroni ba.
Ganin da gaske nayi tafiyata yasa ya biyo bayana yana fadin
"Haba Asma'u, Ki saurareni mana, ko Badan ni ba"
Numfashi na da sauri yake fita saboda tsabar masifa, amma cikin raina hakuri nake bawa kaina akan
komai will be ok, kallonshi nayi nace
"Me zakace min? Godiya zakaimin? Ni da Kai bamuda Sauran magana, ga 'Yarka can na ciro maka, Bazan
mata fatan tsiya ba amma ka sani ka barmin tabon da a zuciyata bazai taba gogewa ba, kuma Inshaaa
Allah Se ka dandani bakin cikin da kasani a ciki."
Daga Haka nayi tafiyata female ward, inda nan Kyaftun take, Ina shiga taga yanayina kawai se ta dauki
excuse gurin Metron dinsu muka fita, muna fita tace min
"Ya akai? Me ya faru "
Hannunta na rike seda muka zauna sannan nace mata
"Kyaftun Kinsan Ashe Salis aure yayi? Kin sani?"
Knata ta girgiza da mamaki tace
"Inji wa ke kuma? "
Hawaye a hankali suka gangaro min nace
"Yanzun nayi mata CS... "
Tsaki tayi tace
"Kiji wata magana, hallucination kika Fara ne? "
Ganin bata yadda ba yasa na bata labarin yadda akai, ranar kakannin Salis ma seda naji tausayinsu, yasha
zagi, da tace se taje ta zagi uwarshi a gabanshi na hanata. Ilai se gashi an kirani akan Nazo babyn na
convulsing, cikin gaggawa muka tafi Harda ita, yana kofar post natal a tsaye ya zabga tagumi, ban bi ta
kanshi ba, na wuce ciki, Kyaftun ta zauna a gurinshi. Ina zuwa muka hau rescucitation, da kyar Allah yasa
akwai kwana a gaba sannan yarinya tayi responding, nayi documenting sannan na fito, har lokacin suna
zaune, fuskarsu a bace nasan zancena akeyi, hannu na mikawa Kyaftun nace
"Twin muje, Babyn tayi responding "
Zaiyi magana na dalla mishi harara, kyaftun tace
"Kai har kana da bakin magana ma "
Se yayi Shiru ni kuma na jata muka tafi. Tana ta dariya yadda ya dinga bata hakuri, ni haushi naji da ta
zauna har sukayi magana dashi, to me banda makiyi Wanda na tsana Kamar shi.
This is a Combi-three page, daga